Namiji Ƙanin Ajali (Book 01)

Chapter -- 01

by @amdeeytejjdunique587

Da sunan Allah mai rahama mai jin kai"

**Namiji Kanin Ajali **

=Page 01

Farko

"Ni na fita sai na dawo, ki duba gefen katifa akwai kudin cefane,ni na wuce"

Ko kafin na ɗago kai har yaja mashin ɗin sa yayi gaba, na girgiza kai nayi murshin takaici, dan nasan acikin biyu za'ayi ɗaya ko bai ajiye ba ko ba abin arziƙi ,cigaba da aiki na nayi na watsar da tunanin dake kunno kai cikin ƙwaƙwalwata, na kammala wanke-wanken da nake yi nayi shara na goge ledan ƙasa ya ɗau ƙyalli na kunna turaren tsinke dana siya jiya tsinke uku dan bana son ƙazanta ko kaɗan,dan wasu sai kaga dan suna cikin talauci ko wani hali na rayuwar aure ko makamancinsa sai su zama ƙazamai na rashin tushe,har lokacin Husna bata farka daga baccin data koma bayan nayi mata wanka hakan yasa na fito na nufi ƙofan Inna Lami hanya muke gaisawa da sauran matan gidan kasancewarsa babban gida ne mai ɗauke da mutane kala-kala da haka ƙarasa muka gaisa da ita na tambayeta malam tace yaje kasuwa, inna Lami ƴar uwata ce ta wajen mahaifina dan muna ƴaƴan maza ne da ita sai dai ta haifeni mahaifinta ne yayan mahaifina,bayan mun gama gaisawa na aiki mustafa yaronta ya karbo min shinkafa a gidan ƴar kanawa , ƴa kanawa maƙocyiarmu ce ina mata busan shinkafa ta biyani , ko daya ke ba aikin da banayi a biyani nice surfe,niƙa, wankau dama dai sauransu , bayan na koma ɗaki na duba kuɗin da ya ajiye aiko kamar yadda na zata ɗari biyu ce kuma a haka a ciki cafane ,awu ,gawayi da komai da komai ma , girgiza kai kawai nayi na fito jin mustafa ya dawo na karba shinkafar na sauke shi sannan bashi kuɗi yaje yayi min cefane ,ba tareda bata lokaci ba na ɗauko matankaɗi na soma aikin shinkafar ,ina cikin aikin mustafa ya dawo na karɓi aikan daidai ya kawo, na tashi na hura wuta ina gama hura wuta husna ta tashi na wanke mata fuska na bata guntun ɗumamen tuwon safe na kwaɗa mata da ƙuli ƙuli dan bata cin tuwo da miya saida ƙuli-ƙuli ko mai da maggi,wutan na kamawa na ɗora ruwan tuwo, ya tasusa nasa a flask na ɗiba na wankan Husna sauran nayi ruɗe tuwon masara, ina gama busan shinkafar kasancewar ba yawa sosai yazo daidai tuwon masaran ya yi na tuƙa na sauke na mai da sanwar miya, sannan na kwashe,nasa mai nashi a kula na rufe sannan na kwashe sauran a wani babban,kula ina cikin ɓare magin miyar sai Imrana ya shigo.

"Yaya Halima aiki ake yi haka? "

Ya tamabaya

"Eh Imrana ina kafito haka da yamman nan?"

Na bashi amsa haɗi da tambaya dan lokacin la'asar batayi ba amma ba zaifi saura minti goma ba

"Gidan malan wada, na fito karbawa umma magani dan bataji daɗi jiya ba"

Da sauri nace " umman me ya sameta? "

Na tambaya a rikice dan bana son abin da zai taɓa min lafiyar ta, umma itace mahaifiyar mu imrana ƙanina ne uwa ɗaya uba ɗaya muke dukkanmu ba ɗan uba ko ɗan uwa a cikinmu kafin shi yayan shi Abdul shine mai bina.

"Amma ya jikin? " na sake tambaya dan duk hankalina ya tashi duk nasan dama bata da lafiya tun rasuwar babanmu wata goma kenan bata sake lafiya ba sai godiyar Allah kawai .

"Ki kwantar da hankalinki da sauƙi shiyasa tace kada a faɗa miki ni bazan iya shirun bane ba saboda nasan yadda kika damu da ita sosai,amma ki nutsu idan ki kammala aikin ki sai kije,dan da sauƙi sosai dan da kanta ma ta yanka kifin siyarwanta Abdul kuma yana kan soyawa"

Ya faɗa a tausashe danna na kwantar da hankalina , dan shima baya son yaganni cikin damuwa kaf cikin ƴan uwana munfi shiri dashi da babbar yayanmu mai sunan Husna ta rasu itama,kamar yadda yasobna ɗan samu nutsuwa kaɗan dan nasan idan ba na ganta ba hankali ba zai kwanta ba, da haka muka yi sallama akan bari na ƙarasa aiki in tafi.

Sai da na kammala komai zuwa ƙarfe huɗu har wanka nayi na shirya na goya husna na fito, ba kowa a tsakar gidan kuma nasan baza su wuce gidin bishiyar darbejiya dake babban filin waje ba, gurin da za a zauna ayi gulma wannan ayi wancan kina tashi akafa naki ,ranaku ɗaɗɗaya ne ake tashi lafiya agun hirar ba ayi faɗa ba, ko akan yara ko akan waccan tayi munafurcin wannan, da ma dai sauransu, nidai tunda nake, iya zama na a unguwan wallahi daidai rana ɗaya ban taba jin sha'awar zama agunba ina wannan tunanin har na ƙarasa ƙofan inna lami amma bata nan kuma itama nasan bazata wuce can ba, haka na fito kamar yadda nayi hasashe kuwa suna nan haɗu har da maƙota anyi convoy anata chapta, nidai ban ƙarasa ba daga inda nake nayi musu gaisuwar jam'i nayi gaba abina ina jin hassana tana tambayata ina zanje ko kallo bata isheni ba tunda bata aike ni ba kuma ba zamanta nakeyi ba,dan nasan munafurci yasa ta tambaya.

Ina isa gida nasamu umma ta fito daga banɗaki hanunta riƙe da buta , na ƙarasa na karbi butar na ajiye ina faɗin "sannu umma ya jiki" na faɗa cike da tausayinta

"Yauwa wato saida imarana ya faɗa miki ko? bazai barki ki huta ba" ta faɗi bayan bayan ta zauna akan tabarmar dake shinfiɗe a barandar bakin ƙofarta.

"A a umma ay gwamma daya faɗa da bai faɗa ba ai laifinsa zan gani" na bata amsa

"To shikenan ai allah dai yayi Albarka ya baku masu tausayinku kuma "

"Amin" nace daga nan kwance husna ta soma wasanta " ina farisa?" na tambayi abdul dake fitowa daga kitchen duk yayi zufa hannunsa riƙe da farantin kifin da ya soya

"sunje siyan madara ita da layla" ya amsa a daƙile , bandamu dan nasan hali , muna cikin haka farisa suka shigo da layla ,layla tana gani na tazo da gudu tana oyoyo ummi ɗan tureta nayi saboda idon umma kasancewarta ƴar fari duk ba ita na fara haifa ba amma itace babbar a yanzu kasacewar itace ta tsaya,umma ta kau da kai,ni kuma nace

"Farisa zo ki sayo min dankalin turawa"

ta ce "to" na ciro ɗan kuɗin da nake ƙullewa idan nayi aikatau nake tarawa dan hidimar mahaifiyata da kuɗin alajihu na ba wai dan tarasa yadda zatayi ba,dan iyayena suna rufin asiri daidai gwargwadon hali tunda ba ɗawainiyarmu daidai ƙwaya ɗaya wanda mahaifinmu ya taɓa barin mahaifiyamu dashi ko na rana ɗaya bamu kaɗai ƴaƴan da aka goya a gidan,saidai tayi itama dan sauke nata hakkin ko kyautatawa, ba abinda muka taɓa nema muka rasa daidai ƙarfinsa yanayi, abinci kuwa sau uku rana akeyi ba'a taba tsallake ba tun mahaifinmu na da rai har kuwa yanzu da ya kwanta dama, bakai na gida ba baƙon da zai shigo da ba'a san da Zuwan shi zaici ya ƙoshi, ina yine kawai saboda samun ladar da Allah ya tanadarwa waɗanda suka kyatatawa iyayensu, duk da ina cikin wani ni hali kuma amma bai hanani yin bakin ƙoƙarina ba, dan wasu ga damar amma kuma ba iyayen nasu,dan haka kada kace wai sai kayi kuɗi kafin kace zaka kyautatawa wa iyayenka dan baka da tabbacin zasu kai lokacin a raye ko kuma kana tabbacin zaka kana da rabon tara dukiya a duniya,kaga baka tara arzikin duniya ba baka tara na lahira ba kenan,wasu kuma allah bai ba arziƙin yin hakan ba dan duk da suna da halin da zasu kyutatawa iyayen nasu amma Allah bai basu wanna arzikin ba,dan kyautatawa iyaye babban arziƙi da bakowa allah ke azirtawa da hakan ba,Allah ka bamu ikon kyautatawa wa iyayenmu tun muna da dama Amin.

To masu karatu ga tafiyar mu na Namiji Ƙanin Ajali dafatan zaku biyoni a cikin labarin dan jin me ya ƙunsa ina labarin zai kaimu ku cigaba da kasancewa dani Nagode 🙏🙏🙏.....