Part 2
by @chefmuaysh
✍️ A'isha Hamza (MUAYSH)
BADAƘALA
Gashi ya riƙe mata hijabi gam ba damar guduwa saida ya tabbatar da iccen ya karairaye a jikinta kafin ya kyaleta ya shige dakin inno
Bata barta haka ba saida ta taka mata ruwan ciki inda take kwance tana kuka don takasa tashi takara bi ta kafarta tawuce
Duk abinda sukeyi Halima na jinsu itada yaranta mai dan wayan harta fara kuka Hindu tana faɗin Umma Baba yana dukan Yaya Ayrah
Saida ta tabbatar sun shiga daki kafin ta fito tayi kan Ayrah ta ɗaga ta, daƙyar ta mike kan ƙafafuwan ta tanajan numfashi daƙyar
Saida tabata hakuri kafin ta rakata har wajen kofar gidan nasu tace ta wuce gidan gwaggo tayi hakuri
Tana tafiya tana tangadi saboda yanda takejin kafarta kamar ba a jikinta ba batasan ma yanda akayi ba saidai jinta tayi ƙasa jigib aikuwa ba karamar buguwa tayi ba har takasa tashi
Duk yanda taso ta tashi takasa sai wasu zafafan hawaye da suke ta sintiri saman fuskarta na radadi da ɗaci
Saida ta kwashi wajen mintuna goma kafin taji muryar wasu samari su uku akanta lalalala mutumin ai Ayrah ce da alama bata da lafiya
Wanda aka kira da mutumin yace kai to ai kayana ne ma ku kwaso man ita mutafi jeji suka babbake da dariya ɗayan yace haba dai kai ka isa yau saidai a more ta mu duka wallahi
Nanfa suka fara neman yin faɗa tsakanin su duk tanajinsu hankalin ta ba ƙaramin tashi yayi ba amma tanaji tana gani takasa tashi
Da alama dambe suka haure dashi ɗaya yana faɗin haba wai akan me zaku tsaya kuna faɗa akan mace ɗaya shima nan suka dawo kansa da alamu dai kamar duk suna cikin maye ne
Hasken fitilar daya haske sune yasa suka tsaya da damben suna faɗin waye yake haska mune
Bai basu amsa ba har yazo inda suke ganin bata su yake ba ya nufi Ayrah gadan gadan yasa suka tasam mashi gaba ɗayan su ai kuwa sunci na jaki don ba ƙaramin kakkarfa bane ba giant ne duhun dare ne yasa bazan iya misalta muku kamannin sa ba amma muje gaba zamuji yanda yake
Duk abinda ake yi akan kunnenta tanaji sanda mutumin ya sabeta kamar yar baby tafiyar minti biyu zuwa uku suka shiga gidan jin maganar gwaggo ne ya tabbatar mata da inda aka kawo ta
Gwaggo ta taresu tana faɗin sannu ɗan albarka kaji Nagode sosai daki ta nuna masa suka shiga ciki ya kwantar da Ayrah akan gadon nan na ƙarfen ɗakin
Gwaggo tana ta yi masa godiya amma baice ko uffan ba Ayrah kuwa duk da zafin ciwo amma ta kasa kunne don taji koda muryar sace don tagane shi koda sun ƙara haduwa saboda kauyen nasu bawani Babba bane ba zaka iya sanin mutanen ciki saidai idan suna dayan ɓangaren ne saboda sunada bangarori daban-daban a kauyen har shida kowane bangare dai basuda yawa amma
Bata ƙara sanin inda kanta yake ba sai wajejen karfe biyu na dare ta farka da wani irin matsanancin ciwon kai ga yunwa da take neman illata ta
Gwaggo tagani zaune saman sallaya da alamu batayi bacci ba ƙasa ƙasa taji ta ambaci sunanta hakan yasa tagane ta fahimci ta farka
Zaune ta tashi tana dafe kanta tace na'am gwaggo bakiyi bacci ba ashe
Gwaggo tace na kwanta farkawa dai nayi don inyi sallar dare naga bakida lfy shiyasa ban tasheki ba
Saukowa tayi tadawo ta zauna kusa da gwaggo tadan kwantar da kanta saman kafadar ta tana faɗin gwaggo na yunwa nakeji sosai
Gwaggo tazagayo da hannunta tana shafa fuskarta tace Ayrah ai jikin naki har yanxu da zazzaɓi ma wani kwano ta nuna mata tace gashinan dauko kici sai kisha magani yana cikin kwanon kasan gadon can ta faɗa tana nuna inda kwanon yake
Har sauri take wajen jawo Robar abincin tafara ci dan wake ne duk da sanyin da yayi hakan bai dameta ba gashi ko man arziki babu a ciki haka ta dage ta cigaba da cusashi
Tass ta cinye shi kafin kuma tafara jin tashin zuciya tace gwaggo zuciyata tashi take kaman zanyi amai
Lemun tsami ta bata tace tasha idan ya lafa saita sha maganin zazzaɓin
Haka kuwa tayi sai da tagama tamike tanufi toilet tayi alwala tadawo daki ta jera da gwaggo ta tayarda sallah
Gwaggo tace Ayrah da ƙoƙari ai yau da kin huta tunda baki da lafiya shiyasa ma ban tasheki ba tun farko
Sai wajen karfe uku da rabi suka idar da sallolin nasu nan suka fara addu'o'i Gwaggo takasa kunne tanajin addu'ar da kullum Ayrah sai tayi ta a cikin dare idan tayi sallah
Ya Allah na rokeka ka rayani Allah kabani miji nagari ya Allah kasa kafin in mutu in cika burina Allah ga gwaggo na ita kaɗai take kaunata a duniya Allah ka ƙara mata lafiya da nisan kwana Allah yabawa Uncle Sameer abinda yake so duniya da lahira haka take ta jero addu'o'in ta hada yar kwallarta
Ita kanta gwaggon Saida ta tausaya ma yarinyar Ayrah yarinyace ƙarama bawata babba ba amma akwai hankali tanada nutsuwa saidai akwai tsiwa don batasan raini ko kaɗan
BADAƘALA ✍️ labari ne mai sarkakiya mai cike da abubuwan mamaki da al'ajabi ga ban tausayi kudai ku biyoni don jin ya zata kasance a gaba
Kuna tare da A'isha Hamza (chef muaysh 😊)
Wacece Ayrah ❓
ya rayuwar ta take ❓
Su waye iyayenta ❓
Wanene uncle Sameer ❓
Su waye take rayuwa a wajen su ❓
Amsar tana anan 👉 👉 👉
Ku biyoni muje zuwa
Akwai littafin mu kayatacce
mai suna EASHERT shima yana hanya in kuna bibiyar mu da sannu zaku same shi