48
by @surayyahms
ABUNDA KE ƁOYE💫
arewabooks@surayyahm.
⏯️4️⃣8️⃣
haka rayuwa ya cigaba har na tsawon sati guda kowanne bangare da kalar Abunda ke ɓoye acikinta, uncle moh da abokansa tuni suka hau shirin bikinsa a ɓoye kusan komin sa agidan alhaj ameer suke shiryawa na biki akwatuna da komi na amarya da uwargida ya rarumo anata cikawa da kayan gani na fada baiko damu da saka ido akan ayaana ba sabida yasan burinsa yanxu ya riga ya cikka bamai iya hana yuwar auren nan tunda hajiya mairo ta amince. babu wanda ya gane shirinsu,anty safeera ce kawai was left confuse at the middle of the chaos, dan babu wani alaman daya nuna mata cewa ayaanah is sumhw responsible da zumudin da uncle moh yake tafkawa agidan nasu kwana biyu, ayaanah is more inclined to ibaad company abokansa biyu suna gari suna yawan fita tare, daga nan kuma sai sauran exams inta dan baifi saura paper biyu ne ya rage mata sutarkata su gama makantar gaba daya ba.
soyayyarsu suke kurba da ayaanah kamar ba auren zee arifah ke jiransa anan da sati uku ba. saidai the more hjy mairo tana ganin shakuwar ibaad da ayaana kwana biyu the more ranta na dada baci,
tanata mamaki wai har rayyanu ne zai cuceta ya kuma cuce taawure data damka masa amanar yarinya yazo kuma yana kaita otel otel suna yawon dare. sosai ta riƙe abun nan aranta bana kadan ba, ta dawo tana ma ayaanah kallon lalatacciya badama ammi karama ta zauna sai ta fara kawo mata magangunan gyara tanacewa lallai lallai kawai aje afara gyara mata ayaanah duk a tunanin ta ai angama lalata.
ammi karama sam bata gane abun ba dake kusan dukansu take matsa masu akan batun gyaran wata rana sassafe ma zata harhada abubuwanta na hadi dakanta ta kawo musu dukansu harda safiya sai tace susha saidai na ammin da na ayanah sai kaga yafi yawa
abun har yazo ya fara damun ammi ranar data kawo kazar matsi ammi ta mayar mata tace wann abun yay ma ayana tsauri ajiki kar tay aure ya zamo sai anje asibiti daren farko,..hajya tace sam tasan metakeyi haka ta saka ayaana agaba da zagi da masifa saida tasata ta cinye duk dama dataje daki saida ta amayo da rabi waje
fannin zainab arifah kuwa duniya sosai tay mata dadi, kafin kace wani abu anyi sabbin zubin masu kulawa da ita kusan kullum ana mata gyaran jiki, abinci da sauransu, gashi ta sake ranta tana shan maganin sosai duk abunda iyayen suka sakata kuma tanayi batare da gardama ba
wann satin za'a mata small corectional surgery, the oda week kuma idan akaga she is fine zataje bridal fittings a paris babanta ya bata kudaden da zata sauya wardrobe dinta gabaki daya, in short kawai kayan da zata dawo sakawa intay aure. the house the everything da sai shafi gidan ana ta famar re arrnging they are going to live in the U.K tunda anan babu nisa da schl, work da kuma inda ibaad shima zaiyi karatu they are all within the states of United kingdom.
ana shiga sati na biyu ibaad yafara shirin yin tafiya harkokin dake gabansu ranar da zai tafi ayaanah ce ta rakashi har aiport yariga yagaya mata in ya tafi zaiy abubuwa da yawa ba lallaine tana samun kiransa ko wayarsa ba har sai ya dawo nan da sati biyu nd dats just one week to his weding. tunda ya gama lallabata da kalamai masu sanyaya zuciya sai bata wani damu ba,bayan sun rabu ita ta tuko motarsan ta dawo masa da shi gidan bappa zaidu
samun cewa ammi babba bata nan sai tabararraje a dakin sultana sukasha zaman hirarsu tare ranar daga suci abinci suyi kallo sai su kira kulthum suyita tsokanan tumbinta that is almost 3 months old ynxu
sai can yamma snn bappa zaidu yasaka aka kawo ayaanah gida hajy mairo batama tsaya tantance waya kawo ayaanahn ba ta kirata ta saka mata tsauraran dokoki akan yawan fita, rantsuwar duniya ayaanah tamata akan cewa agidan ammi babba ta wuni amma matar nan tay burus tace mata kartadai sake ficewa agidan inba da kwakkwaran dalili da aka sanar da manya ba.
itade batasan meye matsalar hajy mairo da ita ba,she just tot is old ppls mentality sumtimes in agaka yarinya ta zare kominta ya fito da wuri sai afara matsa mata da tsaro, ko ajikinta dan sama ibaad ne dai in yazo dole take fita toh gashinan ma baya gari kuma bazai dawo nan kusa ba saiyaci sati biyu.
ana tsaka da satin bayan anyi wa zainab surgery ta samu dama dama itada babanta suka tafi kasar waje, mamanta ne kawai agidan yanxu.
ranan da su ayana suka je scnd to the last exams dinsu kwasam hajiya mairo ta kira ammi karama ta bata waya wai su gaisa da kawunnan ayaanah
da murna ammi karama ta karbi waya aka gaggaisa taji mutane sunata mata godiya duk tadauka kodan rike ayaana da sukayi ne tsawon shakarun nan ashe su godiyan bada aure suke yi wai. bayan sun gama wayar ne hajiya mairo ta hau fayyace mata batare da ta fito fili tagaya mata dalili ba sabida bataso wann karon ma ta zage tarbiyan rayyanu a idon fatima ace taci mata fuska.
saka maganan tay a tsatstsaye cikin bada doka baneman shawara ba, tace ita tariga ta yanke hukunci zata aurar da ayaanah kawai wa danta muhammadu sabida ya cigaba da kulawa da ita suma ta taso agaban idonsu tunda ibaad aurensa zaiyi bataga amfanin aje ayaana tana galantoyi a titi da mutanen banza ba.
ammi tay tsammanin akn ruth ake magana dan maganan ruth ya fara zagawa gari ba zallan akan lesbianism ba har da wann sex addiction da gang din cult datake rolling dasu
ammi ko kadan bataso wann maganan auren ba dan ta san bazai taɓa zamowa adalci ace ayaana ta taso agabansu snn azo a hadata zaman kishi da safeera ba musmn ma a age inta
yau kusan cire kunya ammi karama tay ta rinka gaya ma hjiya gaskiya dakuma fayyace mata irin fitintinun da hakan zai jawo...amma hajya tace sam ai ba wann ne kadai dalilinta baz kuma bataso ta furta ne ace tay musu cin fuska dan haka kawai kowa yay hakuri ai muhmmdu baima safeera alkwarin cewa bazai kara aure ba barema wann auren na rufin asirinsu ne duka baki daya kowa yayi hakuri
tace ma ammi karda ta sake ta gaya ma ayaana komi sabida bata bukatar permision inta tunda ma ta gama magana da wakilan uwarta da ubanta kuma sunce zasu sanar da taawure zasu ma yarta aure. tace already sun wakilta wani dattojo dan uwan su juma dagata fannin kishiyar uwarsa
sunansa Alhaji hanza ranar auren zaizo da sauran kannensa su zasu bada auren ayaana a masallaci duka duka ayi komi danasu zainab arana daya.
ko na minti daya abun baima ammi karama dadi ba, auren dole ne ma ayaana, kuma da mijin anty safeerah sosai taga rashin mutunci da rashin adalci da tsokano fitina aciki, she wanted to tell bappa zaidu hajiya tace wallah wallah inta fada ma zaidu zasuyo kaca kaca sabida babu ruwansa acikin wann maganan aikinsa kawai miƙa auren ibaad ne dana muhammadu ita bata son munafurci
tun ranar ammi karama tabi ta sauya ma hajiya mairo tazamo babu wani walawala a fuskarta kwata kwata, dan sai yanxu ta gane cewa ashe duk gyaran nan da ake ma ayaana na auren dole ne, duk sanda tay yunkuron gaya ma bappa zaidu sai kuma ta tuna irin masifar da hakan zai iya jawowa sai taja bakinta tay shiru dan karshe ciwon ayaana ne zai tashi, shikuma tace zata tsine masa in yace aa, ga safira itama ba shiru zatay ba.
duk tausayin ayaanah takeji sosai har bata iya nitsiwa taci abinci
hardai ammin tay fushi taja baya da zuwan shashen hajy mairo kwata kwata tacire hannunta tadena ma basu maganin mata, but still hajiya mairo haka zato biyosu har sashen har da itama tasakasu agaban tace sai sunsha.
ana cikin wannan yanayi hajy hajara ta dawo daga kauyensu na jukunawa ranar ma wuni sukayi a daki suba kuskus da hajiya mairo har tagama ta fita
washe gari sassafe tun asubah bai gama yi ba ammi karama tana bacci taji hayaki ya cika mata daki, tana bude ido taga hajy mairo ta hade rai tace maza maza ta sauko kasa tay hayakin nan..
ammi duk ta rude ta rasa meye wannan, hajiya tay burus ta rufeta da zani ta mata hayakin nan tasss for the first time da aka ma ammi karama wann hayaki wuni tay tana ciwon kai
hajiya bata daddara ana daf za'a kira magrib ta sake dawowa ta mata. harsaida sukayi haka na tsawon kwana uku snn ta kyale ammi karama, ta dawo kuma yamma zata dama mata nonon rakumi da wani gari aciki ammi ta tsane abun nan ammi haka zata tsaya aknta tace mata wallah sai tasha. bata wasa da ita.
wani bin har taji kmr zatay amai amma haka zata sha tun tuna guje ma abun harta hakura ta sake ranta hajy mairo tace mata daga tay aman jini maza maza tazo ta gaya mata tace toh amma haryau dai batay aman ba tukuna
ana kkrin shiga sati na kusa da karshe kafin aure ayaana suka gama exams aka musu mini walima agidan as usual sai yau uncle moh ya shagala ya fara nuna zumudinsa a fili
irin reaction din kallon tsana da haushi da anty safeerah tay ma ayaana yasa ana gama hidimar da yamma suna zaune da anty safeeran a falo ta shigo da duk wani kyautarsa daya bata yau din ta dauko ta dawo masa dashi agaban matarsa tace masa ta gode amma bazata iya karba ba
tambayar duniyan nan yay mata agaban matarsa ammi taki ta amsashi firrr haka ta kama hanyarta ta fita
anty safeera tana jinshi ya dinga bambami yana daurawa ibaad laifi kan kace wani abu suka fara musu da matarsa
tace masa karya wani lakama ibaad, kowa yasan ibaad has travel ba a ma samunshi awaya kawai de yarinya ta gajine da haukar da yakeyi kawai inzai bari ya bari, tace masa ga dansa mujaheed yana son ayaana kuma next week zai dawo auren zainab gida what if mujaheed yazo yace yana son aurenta haka kenan zai cigaba da wann creepy bvhrs din bayan yarinyan ma bataso amma sai yana cusa mata kai yake?
yadda tay maganan da zafi da kuma gatse yasa ransa ya balain baci sai baice mata komi ba kuma yana gani ta kwashe gift din su abun wuyane da atampopi da su takalma kaiwa dakinta tay tay kasonsu da sunan yan uwanta,yay zuciya bai kwana a dakinta ba ita kiwa sasafe ta kyauyar ma yan uwanta komi dake ciki.
akan wann abun saida yay kwana biyu baya mata magana abun sosai yay mata zafi...
bayan komi ya lafa su ayaanna angama secondry tunda ibaad ya tafi saudaya ta samesa awaya sukayi hira me tsawo har yau bata sake jinshi, bappa zaidu ma sao yazo yay tafiyan shima haryau dai basu dawo ba gashi anata shirin bikim nan saura kwana goma sha biyu ya rage musu kacal
bayan komi ya lafa ranar wednesday tsakiyar sati amarya zainab arifah ta dawo gida ita da babanta da babban aminiyarta nala sabida su shirya ma biki atare., her weding dress wanda zata saka shi a ranar daurin aure nd everything komi is on the processs week din auren zaa kawo mata komi.
already kayan da suka siya kuma acan kasar wajen suka bari masu aiki zasu jera mata su a new closet na agidan mijinta a UK
nan shirin aure kawai sukeyi, she still on her drugs amma tuni ta katse shan kwaya mai bugarwa dan iyayenta su tabbata lafyarta kalau, kowani dabian banza duk ta rage, dan kar ace bata hankli har yanzu wani abu ya kawo cikas ma aurenta she is still deeply scared maganam rukky
tana Allah Allah ayi auren ya wuce kar maganan rukky na cewa bazata aure ibaad ba ya zamo gaskiya..
bayan dawowartan ne garin kuskus hajiya hamida tajiyo wayar da prof yakeyi a falo da mamansa, yasata a handfree yanamai jadadda mata cewa ya gayyaci manyan mutane dan Allah kar azo a kunyatashi kuma wallh inhar ibaad ya saɓa dokokinsa ya kara cutar masa yarsa zai musu haukan da basu taba gani ba, mita ya dinga mata yana gaya mata uban kudin daya kashe wajen jinyar zainab yace ai likita yace yanxu abu kadan ne zao iya dawowa mata sa ciwo dan haka dole ne ibaad din yay hakuro su zauna har sai hanklinta ya dawo jikinta kafin duk wani abunda zai biyo baya yabiyo baya...
she have no choice face ta gaya masa toh de auren nan bana yarsa shikadai bane kaninsa karamin ma zai kara mata duk kuma a llco daya zaayi auren gabaki daya. yace shi bai damu ba kawai de lafyar yarsace damuwrta kar sake ayi wani drama da zai maida jinyar zainab baya musmn ma da likitoci suka yi gargadin bata gama warwarwa ba. shikansa baisan zainab din bane ta biya aka harhada masa wnn report din dan ya matsa ayi komi cikin sauki..
hajiya hamida najin hirar tazo ta samesa sukay maganganun banzansu akan auren uncle mohd dinsuka gama,
prof yace ai duk zuciyar kuruciya yan uwan nasa suke dashi hakama babban yayun su marigayi mustapa yaje ya auro yar kwaila, shide haryau wnn maganan auren ammi karaman da baban ibaad din yatsaya masa a wuyarsa sosai
bayan kwana daya da wann maganan ranar friday ana gab za'a shiga week na hidiman aure anty safeera ta kira hajiya hamida akan batun waliman gida da za'ayi na kawayen hajiya hamidan a mansion din su zainab bayan daurin aure
tana yatsina tace ita
wallah bazata iya gayyatar matan gidan su waliman zainab agidanta ba ita din kawai tazo ya isa.
anty safeera tafara rokonta tace gaskiya bazai kyautu ace ita daya kawai zatazo waliman auren zainab ba....
hajiya hamida tace ke safeerah bari kawai na fito na gaya miki akwai wata tsinanniyar bazaura agidan nan naku mijina babu sanda za'ayi maganan gidanku bai ambace sunan ta ba kinga kuwa maganin bari karma afara
wani irin tuntsirewa da dariya anty safeera tay tace haba haba anty hamida meyayi zafii? to wallh ki ma kwantar da hanklinki bappa zaidu yariga yay marking territorynsa kuma ma soyayya sukey auren ne kawai baiyu ba da anjima da yi bakiga shiyasa basa jituwa da ammi babba ba
hajya hamida tace what ever..kawai dai bazata kara zuwa min gida na bane..kinsan ai dama zayyan da zaid yan biyune mai yuwa suna da abun maitarsu na son abu daya, gara na datse tun yanxu shi mijina yana gane cewa yana son abu toh wallah sai ya samu koda kuwa kashe dan uwansa zaiyin
anty safeera ta kyabe baki tace toh ba damuwa anty hamida i understand nima ai bazanso amiki kishiya ba
hajyy hamida tace hmm shine ke kika bari za'a miki kwanan nan? wallh safeera kin ban mamaki da kyanki da iliminki zaki zauna namiji har ya miki kishiya kuma it seems like ure even happy abt it..ni banga alaman kinma damu ba ,ke ko irin kishin matan nan baki dashi
kirjin anty safeera ma bugawa tara tara tace tsaya anty hamida bangane za'a min kishiya ba..ni din?? anya kinji da kyau kuwa..ni wallh mijina bai taba mafarkin zaimin kishiya ba i use to go tru his phone sumtimes baida wata budurwa ma
hajy hamida tace hmm safeera kenan, it seem like ure abt to be shocked!! nide ba abaki na zakiji gulma ba amma wallh uwar mijinki ne jiya ta gaya ma alhaj cewa aure biyu za'a daura dana zainab dana kaninsa muhammadu
wani kalar dariyar mahaukata mai karfi anty safeera tay kafin nan ta fashe da kuka abazata batace komi ba ta katse wayar cikin sauri
hajiya hamida tay kwafa tace hmm yanxu sai ace na hada waje kenan ko???hehehe toh Allah ya raba lafiya
****
wani irin haukataccen kuka anty safeera tay for a moment in shock, dan tasan dai hajya hamida bazata taɓa mata wasa ko karya ba...saida tay kukan sosai dan shock din ya fice ajikinta snn ta share hawayenta ta fita tana jan zuciya luckly enuf tana sharoro kwana kuwa taji muryansa a daki yana kan maganan auren da wani abokinsa ta labe a bakin kofa taji yana kyakyatwa da dariya harma maganan ma anko sukeyi na abokai..
lokcin wani hajijiya ne ya fara juyi da ita dan batamasan awani duniya take yawo ba dan tay kamar bata sama bata kasa bata tsakiyar kamr a iska kawai take yawo kirjinta yay nauyi kamar an daure dutsi a haukace ta shigo dakin tana huci suna hade ido yay maza ya katse wayar ya mike tsaye yace "lafya kuwa Safeera what is dis zaki shigomin babu sallama u cud run into my private conversations
ɓari gabaki daya jikinta ya farayi maqudaan hawayen datake kkrin dannewa suka watso mata a lokaci daya akan fuskarta suka sauko baja baja tana kallonsa kamar zata kasheshi the call has already confirmed everything to her
muryanta har yana amo tace "i cud run into ur private stupid cnvrsation ko kuma wani munafurcin kake kullawa abayan ido na bansani ba
adan rude yace meye hakane kam safeerah pls what is wrong with you ne
wani dan uban mari ta daka tsalle ta watsa masa da ihuu tace "you are what is wrong with me muhammad...how dare u..how dare u ...how dare u plan ur weding behind my back, dama sau yaushe ne zaka gaya min? bai gama farfadowa daga marin ba tay wuff ta cakumo wuyarsa a borance tace sai ranar auren ne zaka tozarni a bainar jama'a sann ka gayamim cewa zaka min kishiyya. what wrong ive i ever done to you da zaka saka min da irin wann walakancin
dakyar ya fincike hannunta da karfi ya riketa muryansa na rawa rawa guilt ya gama rufeshi dan yama rasa me zaice yafara bare bare yana cewa "safeera is not what u think...i was going to tell u bansan ya zan gaya miki bane
..you knw i love u..i care about how you will feel shiyasa ban gayamiki
kara fashewa da kula tay a mugun haukace tafara cewa "so, now you care abt how i will feel..amma da banji awani waje ba wallah da bazaki gaya min ba...kai durun uwarka, inka sake cewa you care about wallah saina kasheka, banza
..munafiki kawai,, wallh i dont deseve this frm you.., ranta a mugun bace ta fara kai masa duka tana cewa wallah baka isa kayi auren nan tunda ata hanyar munafrci zaka yi..u want to embrass me...inkaga kayi auren nan it will only mean i am dead. wallah wallh ka gwada kagani..
tana gama furta haka a zuciye ta juya zata fita wanda yasan bazai wuce gidansu zata tafi yay sauri ya biyota yaga ta kama hanyar waje kusan a guje yana kkrin jawota kukan ta saida ya ratse koina kowa ya fito a rikice ana lafya lafya...
atake jikin ammi karama yabata abunda yake faruwa tay sauri ta rikotata snn a sann ta zube ajikin ammin kusanma ba acikin hayyacinta ba sai kuka kawai take kamr zata cire ranta.
duk su ayaana suka fito saboda kuka ne me kara anty safeera takey bana kadan ba
hajy mairo tace ke kuma safeera meye haka mutuwa akayi miki ne, muhammdu waye ya mutu..badai jikana mujaheed bako? dan jiya munyi waya dashi yace zaixo bikin nan sati na gaba
da sauri kuma a rude uncle moh yace yawwa hajiya dama akan batun aurena ne taji shine take fushi batama tsaya munyi magana ba
da muryan tausayi tace ayyoh Allah sarki yo ke safira kiyi hakuri mana karki cutar da kanki da irin wann kukan
...karka kanki yazo yana miki ciwo auren nan ai na rufin asirin mu ne baki daya nida nace ma bazaki ce komi ba saidai kisaka albarka...yarinya ne kin riga kinsanta tun tana karama kusan ma agabanki ta girmaa yanzu fisabillah da aka kawo miki wata shegiya awaje ba gara da za'a hadaki da ayanahn ba kinga saiki riketa kmr yar cikinki...
wani irin kukan kura anty safeera tay tace ""waaaa?? ayaanahhh fa kikace hajiya..
in shock ta kalle unlce moh jikinta na kar kar tana vibrting da tsawa da ihu tace 'dama ayaanah zaka aura??...
yace safira calm down i was abt to...wani irin mari ta kai masa saida ya kusa kifewa,
kafin ammi karama ta rikota tay kan hajiya mairo da naushi tana ihu tana cewa" munafukar tsohuwa, azzaluma wallah sai namiki dan bura uban duka dan ni ba kalar wacce zaku walaknta bane...
adaskare ayaanah ta tsaya cak tana kallonsu ana tirka tirka sd anty safeera ta riga ta kai mata naushi tsohuwa saida ta fado akasa tana ihu uncle moh yaje da gudu yana kkrin dagata
jikin ayaana yafara rawa rawa ita da safiya suka kalle juna in shock
anty safeera tana ihu tana zage zage tana kawo naushi dakyar ammi karama ka janta sai cewa take wallah wallah inhar ayaana zaka aura saina kashe ka..baka isaka ka dawo dakin nan ba har lahira zan kai ka yau, dacan gidan ubana zanje amma tunda abun naku walakanci ne da cin fuska wallah ina nan daram sai na kashe ka, mugu kawai, munafuki daga kai har tsohuwar taka saina numa muku cewa haukata yafi taku.
ana tsaka da wannn rikicin bazata sukaji ayaanah tafadi kasa sumammiya..
da sauri ammi ta sake anty safeera tazo kan ayaanah tana girgizata ayaana ayaanah sai shiru aka fara salati
anty safeera taja wata arniyar tsaki ta haura sama ammi ta dauki ayanaa ahannu tace safiya yi sauri ko kawomin key muje asibiti .
uncle moh yay sauri yakai hajya dakin tana ta rabza kuka kmr dukantan akayi
yana fitowa yazo ya samu dede safiya ta kawo key kenan yafara kkrin kwacewa yana cewa bani keys din ni zan kaisu...
ammi karama batasan sanda ta mike jikinta na rawa ta daka masa wani irin hatsalallen tsawa ba...
ranta a mugun bace tace muhammad are u out of ur mind? wai baka ganin abunda ka jawo ne..kaje ka kashe wutar dake gabanka mana and for ur informatiom dont u ever come near this girl ya isheka haka.
hawayenta ya fara zuba tace "Dama ai abunda kuke so kenan, inbanda son zuciya ina ayanaa da zamowa matarka kaje kawai ka juya ma hajiya tunani..wallah Allah ya isa ma yarinyar nan, inba dai so kake ka cusa ma rayuwarta baqin ciki ba meye naka da auren yar cikinka kuma wanda ta taso agaban matarka wann ai baqin jini da tsana ka siya mata nide wallh karka sake kace zakazo kusa da ayaanah enuf is enuf
...tana ga firta mai hakan ta dauki ayaanah cak ta fice da ita tana kuka ta sata mota bata kira kowa ba saida ta isa asibiti
ayaanah went into nervous breakdown aka lankaya mata engine taya numfashi bata ko motsi..
ta kira layin ibaad baya shiga, ta kira bappa zaidu duk shiru har saida ta kira maheer ya dauka sann taji sanyi ahaka ma tanakan gaya masa tana kuka, hanklin sa sosai ya tashi dajin wann maganan, ya rasa yadda zaiyi yay, haka yaki gaya ma kulthum yay shiru atake atake yace mata zaizo gida akwai wani abu urgent da zaiyi.
he left malaysia by 10am bai iso kano na sai tara na dare, yazo ya samu ammi karama ce kawai anan asibiti sai safiya har ayaanahn tafarfado ta sake komawa she is still on sedatives nd oxygen
babu alamar shigar numbar bappa zaidu bare na ibaad kuma sam sam taki ta gaya ma hajiya asibitin datake bare suzo, anan tawuni batasan me ya gudana agidan ba.
saida maheer yazo kafin taji safiya tana bada labari cewa data koma yi musu abinci taga anty safeera ta dauko wuka tabiyo uncle moh har waje kan titi tatara masa makwabata, waihar ma yace zai saketa hajia ne tace masa a'a zafin kishi ne zata sauko.
case a gidan bai kare bahar washe gari ayaanah tana farfadowa in btwn amma daga zarar taga ba mafarki takeyi ba she will faint back...
gurmi yasaka ammi babba ta dawo gidan wai tazo danna kirji ma anty safeera amma inbanda kata hura mata wutan abun babu abunda takeyi dan agidan ma takwana komi anayi a idonta
a idon hajy mairo saita nuna hakuri kawai take bayarwa amma tana komawa sashen anty safeera sai ta cigaba da xugata sosai..ranar da abun ya faru uncle moh bai iya kwana a gidansa ba sabida tsoron ransa, kusan a hotel ya kwana shima acan alhaj ameer yazo ya karasa cire masa sauran tausayi da kunya yace masa ya share safeerah borin hauka kawai takeyi zatama yi ta gaji ta bari karda ya sake ya fasa auren nan sabida haukar kishi da matarsa safeera takeyi
BOOK 1 ZAI KARE NE A PAGE 50. PLS WANDA BASA IYA KARANTA BOOK DAGA FARKO KU daure KUNEMI PAGE ONE KU AJESHI KURKUSA DAN IN AZO CIGABAN LAST PAGE KUGANE INDA ZAMU DOSA COS I WILL HATE TO BE ANSWERING SILLY SILLY QUESTIONS IN THE FUTURE..💋❤️❤️👍 MORE LOVE!!