Page-19
*FASAHA WRITER'S ASSOCIATION*
(*F.W.A)*©✍️
⭐⭐⭐
Ƙungiya masu aiki cikin salon hikima da fasaha gurin juya tunanin al-umma, kaifin alƙalumansu ya zarta takobi ©✍
___________________________________________________
بسم الله الرحمن الرحيم.
اللهم صلي وسلم على نبينا محمد.
❁ 𝐒𝐀𝐍𝐀𝐃𝐈𝐍 Ƙ𝐀𝐃𝐃𝐀𝐑𝐀𝐓𝐀 ❁
Free book📓
By
*Aisha G Umar*
_*🌹𝑍𝑎ℎ𝑟𝑎-𝑡𝑢𝑙-𝑄𝑎𝑙𝑎𝑚🖋️*_
Page1️⃣9️⃣
Bayan na karɓi wayar na kuma tsayawa kallonsa 'tsoro na ke ji? Me yasa na ke jin tsoron yin waya da wanda ban sani ba?' Na jerawa kaina tambayar a zuciya, sannan na saita wayar akunnena ina jin yadda zuciyata ta ke bugawa a hankali.
Abba kuwa ko da ya ji Asma'u ta ce za ta haɗa shi da Nuriyyah, sai ya yi shiru yana jiran jin saukar muryarta, don su gaisa kamar yadda Asma'un ta ce, sai dai jin shiru da ya yi ne yasa shi ya buɗe baki a hankali ya furta, "hello". Wani irin sauti na ji ƙirjina ya bada, da jin wannan muryar Abban, baki na ɗan rawa me makon ingaishesa sai nima na maimaita kalmar da ya ce, "hello". Sai da Abba ya lumshe ido haɗi da yin shiru, jin sautin da aka yi masa hello da shi, saboda ba ƙaramin buggan zuciyarsa sautin mai daɗi ya yi ba.
Sai ya ƙara maida hankalinsa ga wayar don jiran jin sauti na biyu. Ni kam ko da jin shiru ba a sake cewa , sai na juya na kalli Asma'u, tai min murmushi da ɗaga min kai kaɗan alamar yi magana mana, sai da na haɗiye nyawu cikin wani yanayi da ban san me shi ba, sannan na buɗe ba ki zan yi magana, amma kafin na kai ga yi aka fisge wayar a hannuna.
Ɗaga ido mu ka yi da sauri ni da Asma'u, sai mu ka ga ashe Sadiya ce, "tun ɗazu fa na ke jiran wayar nan, amma kun ƙi kawo min, kuma fa magana zan yi da Faruq" ta faɗi tana yi mana hararar wasa, dariya muka yi ni da Asma'u na ce, "kai Anty Sadiya, ki ce dai kawai kina son yin wani magana ke da yaya Faruq kawai".
Bugan kafaɗata ta yi tana dariya ta wuce, ni da Asma'u muka kalli juna muna murmushi. Abba kuwa ko da ya ƙara yin magana ya ji wayar ta tsinke, ba tare da wani tunani ba ya kuma lafewa a jikin kujerarsa....
Momy tashi ta yi daga kan kujerar sannan ta nufi inda Hajiya Kaka ta yi wato ɗakinta, sai da ta yi sallama aka ba ta izinin sannan ta shiga, "Hajiya Kaka zuwa na yi akan maganar yarinyar nan Nuriyyah, don Allah kada ki yi min mummunan fahimta, don Allah ki amince da zaman Nuriyyah tare da mu" "me ya kawo wannan don Allah Rahama? Ina ce kun riga kun yanke hukunci tsawon wannan lokacin? To ni ai ba kowa ba ce a cikin lamarin, saboda haka ba ki da matsala akaina, ku cigaba da yin gaban kanku mu dai ido kawai namu". Cewar Hajiya Kaka tare da zama gefen gado fiskarta a haɗe.
Momy ma sai da ta zauna a gefenta da kulawa ta ce, "don Allah Hajiya Kaka ka da ki yi fushi, dana san ranki zai ɓaci wallahi da na faɗa miki, amma kimin afuwa" sai da Hajiya Kaka ta miƙe sannan ta ce, "kamar yadda na ce da farko, ni ban da ta cewa, don haka wannan damuwarku ne, ku cigaba da zama tare da ita, ku ku ka ga zaku iya daman" "Amma Hajiya Kaka don..." kafin Momy ta kai ƙarshe Hajiya Kaka ta ce "ya isa! Ba ni da buƙatar sake jin wannan maganar".
Ta faɗi tare da fita daga ɗakin tana ƙwalawa wata mai aikinta kira, Momy na biye da ita cikin rashijin daɗi, saboda ko kaɗan ba ta ji daɗin yadda Hajiya Kakar ta yi mata magana ba, hakan ya nuna mata Hajiya Kaka ba ta amince da Nuriyyah ba, tun yanzu kenan. "Haɗa min baƙin tea, ina son samun natsuwa" cewar Hajiya Kaka wa mai aikinta, jin haka yasa da sauri Momy ta ce, "a ah Hajiya ai tea ko ni zan haɗa miki" Momy ta faɗi tana wucewa don zuwa sashinta ta haɗawa Hajiya Kaka tea.
Ita kam Hajiya Kaka da kallo ta bi Momy haɗi da sauke numfashi, ta dubi mai aikinta da ke tsaye ta ce, "ke kuma me ki ka tsaya jira? Dama tea na ce ki haɗa min, kuma ita ta ce zata yi, ko jira ki ke sai na ce ki tafi?" da sauri mai aikin ta bar wurin domin ta lura ran Hajiya Kaka a ɓace ya ke. Juyawa Hajiya Kaka ta yi zuwa ɗakinta, tare da zama tana tunanin maganar da su ka yi da Momy, a fili ta ce, "Rahama ba ta da hankali, a ah ba zan yarda da wannan iskancin ba, dole na yi magana da shi Aminun" tana faɗi ta kuma sauke ajiyar zuciya...
"Nuriyyah karɓi ki kai sashin Hajiya Kaka sa sauri" cewar Momy tana miƙo min tea ɗin da ke cikin cofi mai plate, sai tururi ya ke da alama yanzu Momyn ta kammala shi, amsa na yi ba tare da wani tunani ba na fice a falon, ita kuwa Momy dama 'yar uwarta ce ta kirata, hakan yasata bani ni in kaiwa Hajiya Kaka tea ɗin. Ko da na isa sashin Haajiy Hajjiya Kaka da sallama na shiga falo, kan kujera na isketa don haka na nufi inda ta ke, domin amsa sallamar ma ciki-ciki ta yi sa, zuwa na yi gabanta ina faɗin, "ina, ina wuni Hajiya Kaka?" Buɗe idonta dake rufe ta yi tana kallona da mamaki sosai.
"Kee!!" Ta faɗi da wani irin murya da ya razanar da ni, ba wai da wani ƙarfi ta yi kiran ba, sai dai zan iya cewa sautinsa ya fito ne daga cikin tsananin tsanar da mai muryar ke yi min. "Me ki ka zo yi à nan? Akan me zaki zo sashin nan? Wa ya gayyace ki sashina?!" Na sake tsinkayar muryarta mai cike da dakewa, jikina ne ya fara rawa saboda tsabar tsoro, tsohuwar nan yadda ta ke magana da 'ya'yanta ba za ka taɓa cewa tana da irin muryar nan ba, amma sai ga shi ta yi min.
"Mo...Momy ce ta bani tea, ta ce in kawo" na faɗi cikin rawar murya, kallon hannuna ta yi da ke rawa har ina zubar da ruwan shayin cikin plate ɗin, sannan ta buɗi baki ta ce, "ijje ki ɓace min da gani!" Da sauri na ijje akan table, da yawa ya zube kan plate ɗin, a hanzarce na fara fita daga falon idona ya ciko ƙwallah. A hanyar fita falon na haɗu da Momy na shigowa, saboda sai bayan ta ba ni inkaiwa Hajiya Kaka tea ɗin ne ta tuna ta yi kuskure, saboda Hajiya Kaka ba za ta ji daɗi ba idan ta ga Nuriyyah ce ta kai mata, tun da tun yanzu ga abun da ta ce.
Tsayawa na yi ina kallon Momy da ke bina da kallon tambaya ganin alamar sauyi a tattare da ni, "me ya faru Nur?" Faɗin Momy ba tare da ta daina kallona ba, ƙoƙarin haɗiye ƙwallah da ke idona na yi sannan na mata murmushi ina faɗin, "ba komai Momy" na faɗi tare da wucewa, bayana Momy ta bi da kallo sannan ta ce a zuciyarta, "me ya faru? Ko Hajiya Kaka ta faɗa mata wani abun?" Sai kuma ta shige falon rai babu daɗi.
Ni kam ina tafiya jikina ya gaza natsuwa, kawai ba tare da na lura ba na bangaji mutum, bayan na yi gefe da sauri na juyi sabida inga wanda na buge, ina cewa, "yi haƙuri don Alla..." kafin na ƙare ban haƙurina idona ya sauka kan idon Mama, wacche ta ke bina da wani irin kallo wanda zance ya take na Hajiya Kaka ya shanye gurin fitar da tsana a bayyane, zuciyata ce ta fara harbawan wani tsoron a diririrce na shiga ba ta haƙuri, sai dai ban yi nisa ba na ji saukar lafiyayyen mari akan kuncina, ban san lokacin da na ɗaura hannuna duka biyu a fiskata ba, ƙwallah da ke maƙale ya taru ya zubo.
"Ni sa'ar ki ce?! Ba kya ganin inda ki ke sa ƙafarki ne? Yanzu da na faɗi fa me zaki ce? Hankali ne ya yi miki kaɗan ko me?" Faɗin Mama cikin masifa tana sake jefa min wani irin kallo. Kai na a sunkuye ban ɗaga ba na shiga sake ba ta haƙuri, "don Allah ki yi haƙ..." sake sauke min marin da ta yi ne ya sani gimtse baki ina sake dafe wurin zuciyata na min ɗaci sosai.
"So ki ke ki ce min ba ki lura ba ne ko? To ki saurareni ki ji, idan ki ka ƙara yunƙurin maimata abun da ki ka yi min yau, sai na koya miki hankali na musamman, saboda ni ba Rahama ba ce, 'yar banza kawai tsintacciya mtseww". Ta ƙare maganar da jan tsaki mai tsawo.
Momy kam kafin ta ƙarasa shiga falon ta canza ra'ayi, gudun kada ta je wani abun kuma ya faru, hakan yasa ta juyo zata koma sashinta, jin maganar da Mama ta ke yi ne, yasa da sauri ta ƙarasa tana tambayar ba'asi. Idona da ke rintse tun lokacin da Mama ta kirani da tsintacciya, na buɗe jin muryar Momy, Mama ta ce da Momy, "wannan 'yar riƙon na ki ce ta hankaɗa ni, wallahi ta ji sa'a, don da ace wani abu ya sameni zata gwammace da ba ta biyoku tazo gidan nan baa!".
Sake rintse ido na yi kamar ɗazu saboda zafin maganganu da ta ce min, sabida a yanzu ni ba yarinya ba ce, zan fi jin zafi idan aka min abu saɓanin da "ki yi haƙuri Hajja Mama, na san ba da niyya ta yi ba" cewar Momy, da mamaki Mama ta ce, "dama taya zata yi da niyya? Ke dai ba kin yarda da ita ba?" Ta ƙarashe tare da wucewa.
Ganin Mama ta wuce yasa na juyo na dubi Momy na ce, "Momy wallahi ba da gangan na yi ba" na faɗi cike da damuwa, hannuna Momy ta riƙe sannan ta ce, "na yarda da ke 'yata Nur, kar ki damu muje" murmushi na yi haɗi da share hawaye, sannan muka wuce sashinmu.
DARE.
Hajiya Kaka ta sa ankira mata Dady cewa tana son magana da shi, dubansa ta yi bayan sun gama gaisuwa da kuma hira sannan ta ce, "Aminu ina son yi maka magana akan wannan yarinyar da kuka ɗauka wato Nuriyyah!"
Last page
___________________________________________________
Hmmm, me kuke ganin zai faru gaba?
Mu kasance a next page don jin me zai faru?
_*🌹𝑍𝑎ℎ𝑟𝑎-𝑡𝑢𝑙-𝑄𝑎𝑙𝑎𝑚🖋️*_