AKWAI SILA

Chapter 13-14

by @amanarcool323

💦 AKWAI SILA 💦


BY AMANARCOOL 


YOTA ID/021


*SHIN RAMA CE MATSALARKI? BUSHEWAR JIKI KO KUMA MATSALAR SANYI? TO ALBISHIRINKI, NA ZO MUKU DA INGANTACCIYAR SABAYA DA AKA SARRAFATA DA NATURAL GRAINS, HERBS DA KUMA SPICES, WADDA ZA TA INGANTA LAFIYAR JIKINKU, TA CIKO DA JIKI, SAMAR DA RUWAN NONO GYARAN BREAST, TA KUMA YI MUKU MAGANIN SANYI DA MA SAURAN GYARAN JIKI NA MATA, DUK A KAN KUƊI ƘALILAN. SABAYARMU BA MA SANYA ƘWAYA A CIKINTA, DA TSIRRAI KAWAI MUKE SAMAR DA ITA. SANNAN AKWAI MAGANIN SANYI GA MASU FAMA DA MATSALAR INFECTION KOMAI DAƊEWARSA. AKWAI COMPLETE SET NA GYARAN BREAST, SPECIAL PACKAGE, KU NA IYA TUBTUƁA TA KAI TSAYE KU TUNTUƁE NI AYSHERCOOL TA LAMBOBIN WAYATA ****.


PAGE 13-14


"Dady kada ka tafi da ni don Allah, kada ku raba ni da shi!" Ta yi maganar cikin gunjin kuka kamar wadda ake ƙoƙarin raba ta da rayuwarta "Dady dubi hannunsa, duba ka gani bai ci abinci ba, Dady a siya masa abinci ya ci kafin mu tafi".

Dady ya sauke numfashi mai zafi, zuciyarsa na yi masa zafi kamar an yi masa duka a ƙirji. Ya rasa kalmomin da zai yi amfani da su, gani yake kamar zai fashe idan ya ƙara kallon yadda yarinyarsa ke riƙe shi take yi masa kuka mai tsanani saboda mahaukaci.

"Shalele ki tsaya, ki nutsu zan sa a kawo masa abinci yanzu, ki daina yin kukan nan kin san ba lafiya ce dake ba" ta girgiza kai kamar za ta karya wuyanta "Dady ka duba hannunsa, zai mutu, ni ce kaɗai nake zuwa wajensa, ba shi da kowa sai ni" kukan da take yi ya tsananta, ya cika gurin da sautin da ya yi kama da wani abu mai tarwatse zukata. Jama'a suka fara tsaya wa da mamaki, suna kallon ikon Allah, wani dattijo dake gefe ya yi murmushi yana jinjina kansa ya ce "Farawa ce, yanzu ma kuka fara ganin irin wannan abin, saura ɗayan".

Mahaukacin yana kallon su cike da tsoro. Ya ja baya yana ƙara riƙe hannunsa, idonsa jajir tamkar mai neman mafita ta ƙarshe. Yana kuka, irin kukan da mutum ke yi idan ya ga zai rasa wani abu na ƙarshe da ya rage masa a Duniya, security biyu suka ƙaraso da sauri suka kama Joriyya a hankali ganin halin da take ciki. "Shalele ki yi haƙuri don Allah ki kwantar da hankali…"

"Ku ƙyale ni ku ƙyale ni!" Ta fara ture su, sai dai ƙarfinsu ya rinjaye nata. Dady ya fizgeta daga hannun mahaukacin da ƙarfi. Wata irin ƙara ta yi "Dady don Allah kada ku bar shi haka, ku duba hannunsa, ka duba yadda yake kuka, ku bashi abinci ya ci!" Da hannu ya yi wa yaransa alama da su karɓo masa abinci, da azama ya tsallaka titi ya isa gurin matar nan mai siyar da abinci ya karɓo da ruwa ya kawo masa. Dady ya ce "Kin gani an kawo masa abincin? To zo mu je gida" ya faɗa yana janta zuwa mota, shiga suka yi aka ja motar da ƙarfi suka bar wajan. Joriyya ta jingina kanta da gilas ɗin motar tana kuka mai sosa rai. "Dady ya isa, ka tsaya, ka dawo Dady ba haka ake yi ba, ka dawo mu taimaka masa". Babu wanda ya kuma kulata a motar, Dady na jin zuciyarsa na yi masa zafi da ɗaci, har suka ƙarasa gida kuka take yi, Dady ya fito da ita ya riƙe hannunta zuwa ciki, Momy na zaune a falo hankalinta a tashe. Dady ya shigo riƙe da Joriyya a hannunsa, zaunar da ita ya yi kusa da Momy sai shashekar kuka take yi, "Hajiya ki kula da ita sosai, ka da ki bari ko harabar gida ta kuma fita, ni zan wuce gurin aiki".

"In sha Allah zan kula Alhaji, Allah ya kiyaye a dawo lafiya" fita Dady ya yi, Momy ta mayar da hankalinta ga Joriyya ta ce "Auta, ina so ki nutsu, ki gane cewar bai kamata kina bibiyar wannan mutumin ba, ba girmanki ba ne, hakan da kike yi kina zubar mana da mutunc..." ba ta ƙarasa ba Joriyya ta tashi da sauri ta haye sama tana ƙunƙuni.

Zauna yake bayan tafiyarsu ya zuba wa hannunsa ido, da ƙyar yake jan numfashinsa, idonsa sun ƙara yin ja saboda azabar ciwo, karensa sai kuka yake yi yana zagaye shi, ya ɗaga kansa ya kai hannunsa zai shafa kan karen ya kasa, saboda ciwon da yake ji. Karen ya matso ya kwanta a gefensa, shiru ya yi kamar mai tunanin wani abu, yara sai tsokanarsa suke yi, babu wanda ya kula a cikinsu. Abincin da aka siyo masa yana ajiye bai taɓa shi, duƙar da kai ƙasa ya yi, yana jin yadda hannunsa ke ci gaba da yi masa zogi da azaba. A hankali ya yunƙura da ƙyar ya nufi cikin kangon da yake zama, kwanciya ya yi a ciki yana fitar da numfashin a wahale.


****

Houses no 18 GRA Kano.

Katafaren gidane mai tsanani kyau da tsari irin na zamani, harabarsa na da faɗi sosai a ƙalla zai iya daukar motoci sama da goma. Kallo ɗaya za ka yi wa gidan ka gane cewar mai gidan ba ƙaramin mutum ba ne. Alhaji Kabiru Umar mai nera, ɗaya daga cikin manyan attajiran da Kano ta sani kuma take alfahari da shi saboda taimakonsa ga al'umma. Mutum ne wanda kalmarsa ke da ƙima, duk inda sunansa ya shiga ana ja da baya saboda girmansa da kuɗinsa. Kasuwancinsa ya bazu daga cikin Najeriya zuwa ƙasashen waje, yana da masana'antu, gidajen haya, kamfanoni, da kadarori fiye da tunani jama'a.

Matarsa ɗaya Hajiya Maryam, mace ce mai kunya, nutsuwa, da tarbiyya, wadda ke da mutunci a idon jama'a da dama. A duk faɗin birnin Kano, idan ka ambaci familyn Alhaji Kabiru, to ka ambaci iyali ne da babu wanda ya san ƙarshen arzikin su. Sai dai duk da wannan yalwar arziki akwai wani abu da ba daidai ba a gidan, abin da tarin dukiyarsu bai isa ya warware musu shi ba. A falon gidan wanda yake ƙyalli, fitillun falon na fitar da wani kalan haske na ɗaukar hankali. Hajiya Maryam na zaune riƙe da wayarta ta tsora mata ido da alama abu ne mai muhimmanci take kallo a wayar, ta sauke numfashi a hankali "Ya Allah" ta faɗa cikin murya mai sanyi.

Alhaji Kabiru ya shigo cikin falon fuskarsa cike da damuwa, zuciyarsa cunkushe da wani irin tunani mai girma, idan ka duba shi ba za ka iya gane cewar akwai wani abu dake damunsa ba. A waje mutane na yi masa kallon mutum mai cikakkiyar natsuwa, sai dai a cikin zuciyarsa akwai rauni ɗaya da ya gagara warkewa.


"Hajiya lafiya dai?" Ya tambaye ta yana ƙoƙarin karɓar wayar hannunta, da sauri ta yi baya da wayar saboda ba ta son ya ga abin da take kallo a wayar, ta ce "Alhaji wai wannan karon wane gari za'a je yin taimakon kamar yadda aka saba?" 


Ya nisa sannan ya ce "Wannan karon ina son tura wasu daga cikin yarana su je asibitin mahaukata dake garin Abuja da ma sauran wasu asibitocin, idan akwai waƴanda zasu iya warkewa daga matsalar dake damun ƙwaƙwalwarsu, da marasa lafiyar da ke buƙatar taimako duk zan ɗauki nauyin kula da komai har Allah ya basu lafiya daga nan idan ta kama a fita dasu waje ne duk zan yi" Hajiya Maryam ta ce "Ma sha Allah, Allah ya taimaka ya yi jagora, na ji daɗin wannan abin, Allah ya ƙara tsare mini kai Alhajina". Ya amsa da Amin tare da rumgumota jikinsa yana shafa ta "Alhaji a falo muke fa, ka da Nihal ta tarar damu a haka, kasan wayo ne da ita" . Dariya yana laƙace mata hanci kafin ya miƙar da ita tsaye ya ja ta zuwa bedroom ɗinsa.


*****

Dady tunda ya je ofis zaune ya kasa aikin komai, tunani da damuwar halin da Joriyya ke ciki sun hana shi suku ni a zuciyarsa, noking ɗin ƙofa ya ji, sai da ya ɗauki lokaci kafin ya ba da izinin a shigo, ɗaya daga cikin ma'aikatan sa ne, "Sir saƙo ne aka ce in ba ka" ya faɗa tare da miƙa masa wata ƙaramar takarda, har ya juya zai fita Dady ya ce "Waya baka saƙon ka kawo mini?" "Sir ban san shi ba" da hannu Dady ya yi masa alama da ya tafi. A jiye takardar ya yi ba tare da ya duba ta ba, ya ciro wayarsa yana dubawa bayan ya gama duba wayar ne, ya ɗakko takardar ya buɗa, idonsa ya sauka a kan rubutun dake ciki, wata irin zabura ya yi da ƙarfi ya miƙe tsaye, jikinsa ya soma rawa, ya ƙwalalo idanu waje yana sake kallon rubutun. Duk da sanyin Ac dake cikin ofishin bai hana zufa ya fara fira fita daga cikinsa ba, komawa ya yi ya zauna daɓas, yana sauke numfashi, tare da lumshe idanunsa. A hankali ya furta "Ya Allah, waye wannan ɗin? Me yake nufi da wannan takardar?" . Ji ya yi ba zai iya zama a ofis ɗin ba ya miƙe da sauri bai tsaya duba komai a ofis ɗin ba ya ɗauki wayarsa ya fita, ma'aikata sai gaishe shi suke yi, bai kula su ba, tun daga nesa security suka ganshi ya fito kamar baya cikin nutsuwarsa, kafin ya ƙaraso suka buɗe masa mota ya shiga, cikin ba da umarni ya ce "Ku yi sauri ina son in ganni a gida yanzu". Ta motar suka yi kamar walƙiya suka bar kamfanin.


Kwance yake a takure cikin kangon, da ƙyar yake fitar da numfashi saboda raɗaɗi da azabar da yake ji, sai juyi yake yana yunƙurin tashi ya kasa saboda ciwo da hannun ke yi masa. Hawaye masu zafi na bin gefen fuskarsa, ya ƙara ɗaga hannun kaɗan ya ɗan juya sai ya ga karensa baya gurin. Joyawar da zai yi sai ya ga mutum tsaye a gurin. Ƙuri ya yi da ido yana kallon Jiniyo da idanunsa suka yi ja, fuskar nan tasa babu alamar imani balle tausayi, kallo ɗaya za ka yi masa kasan tsantasar mugunta da rashin imani ne kwance a kan fuskarsa "Ka ga abin da ka jawo mini ko? A kan ake ƙoƙarin nisanta ni da Joriyya, yadda ka hana mini jin daɗi kai ma ba za ka ji daɗin ba, sannan kai da Joriyya har abada". Ya ƙarasa maganar cike da ihu da hargagi, cikin rashin imani ya sa ƙafarsa ya take masa yatsun ƙafa, wata ƙarar azaba ya saki yana so ya tashi zaune ya kasa, "Ai wallahi baka ga komai ba, ba kai mahaukaci ba ne yanzu zan koya maka hankali. Ka ga yadda hannunka ya fara yi ki? Zan tabbatar baka mance wannan ciwon ba har abada"

Mahaukacin ƙoƙarin tashi yake yi ya kasa, cike da raunin murya ya ce
"Ka bar ni"

Jiniyo ya yi dariya mai cike da mugunta.
"Kai ba ni da niyyar barinka, ai tunda ka bari Joriyya ta fifita ka a kaina ba zan taɓa barinka ba". Tsayawa ya yi yana kallon hannunsa da ya kumbura sosai, cikin rashin tausayi ya sa ƙafarsa ya taka hannun iya ƙarfinsa. Mahaukacin ya sake wata irin ƙara, ƙarar da ta karaɗe gurin, daga nan kuma ya yi shiru saboda numfashinsa da ya ɗauke, Jiniyo ya kuma kai masa harbi ga ciki sannan ya bar gurin cike da rashin imani, yana isa bakin ƙofar fita ya yi turus yana ƙwalalo idanu waje, jikunsa ne ya ɗauki rawa, lokaci ɗaya tsoro da firgici suka bayyana, ja da baya ya fara yi yana girgiza kansa cike da kaɗuwa. 


Amanarcool
***