BADAƘALA

Part 3

by @chefmuaysh

BADAKALA

✍️✍️✍️AISHA HAMZA ( MUAYSH)

Bata farka da wuri ba sai wajen tara na safe ta mike ganin yanda gari yayi haske yasa tafara innalillahi wa'inna'ilaihirajiun nabani haka gari ya waye ban tafi Makaranta ba

Da sauri ta sauko kafarta ƙasa tana neman mikewa tsaye saidai kafarta taki bata haɗin kai ko kaɗan

Ba ƙaramin ciwo take mata ba don taki takuwa ma hada yan hawayenta tana faɗin nabani Allah yasa ba karyewa nayi ba jiya

Gwaggo ce ta shigo hannunta riƙe da bokiti da kwandon da suke saka sabulu da alamu wanka ta fito

Ayrah kin tashi kenan ta faɗa tana ajiye bokitin daga gefen dakin da kwandon sabulun

Ƙarasa shigowa tayi ta zauna akan katifar da take malale a tsakar dakin yar ƙarama irin ta yan boarding amma zata dan kwana biyu ba tsohuwa bace kamar ta saman gadon

Robar man shafawa tajawo tace Ayrah ya jikin naki ina fatan kinji sauqi sosai cikin marairaicewa tace gwaggo naji sauqi amma kafata ciwo take man nakasa takawa

Subhanallah gwaggon ta faɗa tana kallon kafar don har kumburi tadanyi daga gefen agarar ta

Sannu wai garin yaya abinnan yafaru ne jiya ni najiki shuru anata zuwa ana ceman Ayrah tana nan nace ko lafiya shine nafita da naje can gidan naku sai naga wani saurayi a kofar gidan nan

Shine ma ya hanani fita naganshi tsaye don da farko ma tsoro ni yabani Saida naga yawuce ina tsaye a soro can kuma sai naganshi ya saɓo ki nace to duk takare dai ba lafiya don inata masa godiya ma amma baice man komai ba ko kin sanshi ne

Tunda gwaggo tafara magana ta nutsu tana sauraren ta don ita kanta batasan wanene ba kuma tanason sani ashe gwaggon ma batasan shi ba

Gwaggo ce ta katse mata tunanin ta tana faɗin ba dake nake ba iñata zuba

Ah ah gwaggo bansan shi ba nima kawai dai na rike wasu maza don ina tunanin ma su Alolo ne suka sameni a hanya shine ya ceceni daga hannunsu

Nan ta kwashe duk abinda yafaru take faɗawa gwaggon hada kukanta akan dukan da Malam yayi mata

Ba ƙaramin takaici gwaggon tajiba ƙarshe ma tace Ayrah tadaina zuwan musu tallan tunda abin yazama tsiya

Suna cikin firar kuwa gwaggo tagama shiryawa tasa kayanta ta zauna saiga sallamar malam ɗin ya shigo

Ayrah ce ta amsa masa tana zaune inda take don takasa motsawa tunda ta tashi gaishe shi tayi ya amsa mata kafin yasamu waje daga gefen ta ya zauna

Saida ya gaishe da gwaggo yana yan sunne sunne don yasan indai Ayrah ta faɗa mata dukan da yayi mata jiya bazasu wanye lafiya ba

Ai kuwa bata amsa mashi ba sai tayi kamar ma batasan yana wajen ba kallon tuhuma yake bin Ayrah dashi wanda ya haɗa dana ta tashi tabasu wuri

Sai tace Baba banida lafiya ne hakan yasa gwaggo ta dago tana ƙare masa kallo tace amma wallahi Salah kabani mamaki yanzu kai ko tsoron Allah bakaji

Yarinyar nan amanarta aka bani nikuma na baka saboda tunanin koda ta Allah ta kasance amma salah duk ƙoƙarin yarinyar nan baka gani tajewa matarka tallah da safe tallah da rana tallah da daddare duk ban hanaku ba saboda banison yawan tsegumi amma shine abinda zaku saka min kenan tun ina raye koh

Ayrah ce ta fashe da kukan da batasan dalili ba tana cusa hannu cikin baki gudun kada kukan nata ya fito fili duk da hakan bai hana suji ta ba

Gwaggo ta cigaba da cewa tasamu yarinyar nan tana son makaranta ni nasamu na sanya ta da taimakon Sameer duk da haka tallahr safen makarantar kuke bata takai amma ku ba'a iya muku ba Koh

Zufa ta ko'ina ke ketowa Malam don shi kansa yasan bai kyauta ba saidai ba yanda ya iya indai yanaso ya zauna da Inno lafiya sai yayi abinda tace

Daƙyar yasamu yabawa gwaggo hakuri karshe tace taji gashinan ai sun ɓalla kafar da za'a jewa yar lelen matar tasa tallah yanzu sai su hakura dole

Shi kanshi ba ƙaramin tashin hankali ya shiga ba da yaji gwaggo tace wai an ɓalla kafar Ayrah

Fita yayi sai gashi da idi wanzan sun dawo domin a duba kafar tata aikuwa saida baban ya riƙe ta tasha ihu hada majina targade tayi a kafar

Saida ya fita ya kuma dawowa hannun sa rike da ledar kosai da kunu ya siyo musu ya kawo kafin yatafi

Da taimakon barira matar Iroro take komai tunda taji abinda ya samu Ayrah koda yaushe tana gidan dama bata taɓa haihuwa ba shekarar su shida itada Iroro shi kuma Lagos yake zuwa neman kudi ba zaune yake ba

Yanzu dinma abincin rana ta shigo kawo musu Ayrah tace ta taimaka mata tayi alwala

Tana sallah saiga Khairiyya ta shigo da sallamar ta uniform ne a jikinta na Secondary Saida ta gaishe da gwaggo tasamu waje ta zauna daga gefen katifa domin gwaggo tana saman gadon dakin nasu

Barira kuma tunda tadawo da'ita daki takoma gidanta domin tayi yan gyare-gyaren ta saboda bata zama bini bini aiki yi wannan yi wancan

Ganin da tayiwa Ayrah na sallah daga zaune gashi ta mike ƙafa ya tabbatar mata da batada Lafiya kuma an daure kafar

Saida ta idar da Sallah tayi addu'o'in ta suka shiga gaisawa Khairiyya tace Uncle Sameer ne ya aikoni

Murmushi Ayrah tasaki don dama tasan indai bai ganta ba zai aiko nemanta ne tace me yace

Yace nazo na duba naji meyasa bakizo makaranta ba yau kuma kinsan anfara shirye shiryen zana jarabawa don yace namiki albishir ma Indai mukaci jarabawa zai kaimu birni boarding muyi karatu

Murmushi tasaki har Saida fararen haƙoranta suka bayyana tace don Allah fa Khairiyya da gaske kike yar harara Khairiyya ta watsa mata tace dama ina miki wasa da karatu ne

Gaba ɗaya suka tun tsire da dariya can kuma sai Ayrah ta haɗe rai kamar xatayi kuka tace Allah sarki uncle Sameer yadamu damu Khairiyya gashi ni yanzu ba lafiya bansan ma ya za'ayi ba wajen yin jarabawar

Nan Khairiyya take tambayar ta abinda ya faru saidai tace mata faduwa tayi dutse ne ya kada ita don ita bamai fadar sirrinta bace ga kawaye dukda cewa ma Khairiyya tazamar mata kamar yar uwa

Saida suka gama Khairiyya ta tafi gida bayan tayi mata sannu gwaggo tace ke yanzu Ayrah ko makarantar aka samo miki a birni tafiya zakiyi kenan kibar gwaggon ki

Ayrah ta zaro ido tana faɗin kai ni na isa gwaggo in tafi in barki ai tare zance yasama mana makarantar da zamu iya zuwa tare suka saki dariya

Sau biyu Inno na aikowa Ayrah tazo sai gwaggo ta kora yar aiken tata don tace zatazo ta sameta ne

Aikuwa haka akayi washe gari tunda safe saiga Inno tazo da kanta don jiya ba ƙaramar asara tayi ba data bawa bawale babban danta tallar ba uwar ba ribar kuma ba yanda ta iya dashi

Sallama tayi har cikin dakin ta shiga lokacin Ayrah na

bacci saman katifa gwaggo kuma na zaune a saman gado tana duba wani littafin addu'o'in ta

Muje zuwa dan kuji yanda zata kare tsakanin inno da gwaggo 😮‍💨 ya rayuwar Ayrah zata cigaba da kasancewa