INA MUKA DOSA?

Chapter 2

by @reza12

INA MUKA DOSA?

                      S-Reza✍️


                         Page 2️⃣
Bakin window tazo ta tsaya har sai da ta hango shigowar Abi. Tana tsaye a gurin har ya fito daga motar tasa ya shiga cikin gidan shima tayi masa kallon ƙarshe ba tare da ta sani ba. A hankali ta buɗe ƙofar dakin ta, ta sanɗa a hankali har ta bar palon, sannan ta zagayo ta bayan motoci guda ukun dake cikin gidan. Tana zuwa bakin get ɗin gidan ta tura ya buɗe sannan tasa kafarta a waje. A hankali ta juyo tana kallon gidan nasu da hasken wutan lantarki ya haskaka shi sosai. Duk taku ɗaya da take yi tana ƙara jin cewar wannan itace hanya guda ɗaya da zata iya bi wajan kaucewa jin kunyar da mahaifin nata ke son saka ta a ciki. Ta yaya zata ko iya kallon ƴan unguwar su da wannan abun kunyar, bare kuma yan makaranta, ko ƙawayenta, balle kuma a kai ga batun shiga kotu. Gara dai tayi nesa da kowa muddin har mutuncinta ba zai zube ba har abada. Wata zuciyar kuma tana sanar mata da cewar hakan da zata yi kuskure ne, kuma ba mafita bace, sannan kuma ina zai Kaita, idan sunje gurin auranta zai yi ko yaya, to waye zai ɗaura musu auran, ana yin aure babu dangi ne?!  Lokacin da ta hangosa tsaye a gurin sai ta fara jin wani abu mai kama da zare na harɗe mata ƙafafuwan da suka kawo ta har gurin da yake, kamar zata harɗe ta faɗi amma ta daure tazo har gurin da yake. Hannunta ya kama yana sakar mata murmushin da take jinsa kamar shine ƙwarin guiwar da take ƙoƙarin rasawa. Bai ce mata komai ba sai mota da ya saka ta ya zagaya ya shima ya shiga mai tuƙawa ya ƙama hanya suka bar gurin.

Babu wanda yayi magana sai hannunta da yake murzawa a cikin nasa, sai hakan ya zama kamar yana ƙara kwantar mata da hankali ne, domin wata irin natsuwa ce ke shigar ta. Sunyi tafiya mai tsayi cikin daren har suka iso wani ɗan ƙaramin gida wanda dreban ya shiga dasu har cikin gidan bayan ya sauka ya buɗe get ɗin da kansa. Shine ya fara sauƙa ya zagayo ya buɗe mata ta kama hannunsa ta sauko tana bin gidan da kallo. Tana tsaye ya fito musu da kayan su da yasa a but sannan ya sallami dreban ya juya da motar, shi kuma ya kama hannunta suka shiga cikin gidan. Zaunar da ita yayi a ɗaya daga cikin kujerun palon sannan ya ce "Misalin ƙarfe biyar na asuba jirgin mu zai tashi, dan haka bana so muyi barci mai tsayi. Ya faɗa yana zama kusa da ita. Kamar tace masa ina zasu je amma tana jin wani abu mai nauyi na mata karan tsaye. Jin tayi shiru ya sake faɗin "Ina sonki sosai Laila kuma nasan mahaifinki ba zai aura min keba, na yarda na bar komai nawa domin na rayu dake, dan haka please ki kwantar da hankalinki ina tare dake. Ya ƙarasa yana rage murya yana kamo hannunta. A hankali ta furtar kalmar da tasa Alpha kallonta yana bata amsa. Ta ce "Ina ne zamu je? Ta fiɗi kalmomin a rarrabe muryarta har rawa take yi Kamar mai koyan magana.

.Sai da ya kalleta sosai kafin ya iya bata amsa da cewar "Ina kike so muje a cikin kasashen duniya? Ta ce "Ban san ko ina ba bayan Saudiyya, babu inda na taɓa zuwa, please dan Allah kar ka kaini inda zan sha wahala. Ta karasa tana sakin kuka a hankali wanda ya sa Alpah sakin murmushi mara sauti. Da sauri ya rungume ta ya ce "Nima ban san ko ina ba bayan Saudiyya, hakan yasa na rasa ina ya dace muje, amma kin san mahaifina ɗan Nigeria ne, duk da ban san a wani gari yake a Nigeria ɗin ba amma cen muka dosa in sha Allah ba zamu sha wahala ba. Ta sake cewa "Nigeria wacce ƙasa ce haka? Ya ce "Idan munje zaki gani, nima ban taɓa zuwa ba". Ta sake cewa "Baka taɓa zuwa ba amma zamu tafi cen?. Ya ce "Karki damu babu abun da zai faru. Ɗaki daya suka kwanta ya jawota jikinsa har sukayi barci a haka. Misalin ƙarfe huɗu da rabi alam ɗin da ya saita ya tashi su. Babu bata lokaci suka shirya suka kama hanyar filin jirgin da dama kusa da shi suke. Babu bata lokaci jirgin su ya tashi izuwa Abuja Nigeria kaman yadda yake a jikin biza ɗin nasu. Suna cikin jirgin tana ta tunanin abubuwa da dama, sosai take tausayin halin da ta baro iyayenta, har tana kwatanta yadda zasu ji take yi idan suka wayi gari ba'a san inda ta tafi ba. Tana cikin tunanin aka kawo musu abin kari wanda sai da Alpha ya taɓa ta kafin ta ankara. Sauke ajiyar zuciya tayi tana kallon abincin da har Alpha ya fara cin nasa. Dankali ne da ƙwai a soye, sai bredi yanka uku da kuma shayi a wani ƙaramin cufi. Kallon sa tayi ganin yana cin nasa hankali kwance kamar wanda zai je Saudiyya gurin iyayen sa, sai kawai itama ta fara ci tana aiyana yanayin da zata ga Nigeria da suka dosa. Kaɗan taci taji cikinta ya cika hakan yasa ta sha shayin da yayi mata daɗi sosai har sai da ta shanye. Misalin ƙarfe huɗu na rana suka sauka a ƙasar Nigeria babban birnin taraiya Abuja. Hannunta ya kama suka sauƙo daga cikin jirgin da sune na karshe wajen sauƙa kasancewar suna karshen jirgin. Sosai Laila da shi kansa Alpha ɗin suka fara bin filin gurin da kallo. A karon farko da yaji gaban sa ya faɗi tun lokacin da ya fara shirin barin gida. Ita kuwa Laila gaba ɗaya ma rikicewa ma ta fara yi ganin yadda al'umma suka cika a gurin ji take kamar za'a gane tana ɗauke da ciki, ga kuma wasu irin halittu da ta dinga gani masu launin baƙi babu sirki, hakan yasa ta fara ɓoyewa a bayan sa domin kuwa ta tsorata sosai. Haka suka fito har wajen filin jirgin da kusan duk wanda suka haɗu dashi sai ya ƙara kallonsu domin kuwa kallo ɗaya zakai musu ka gane sudin baƙi ne a ƙasar. Gasu fararen larabawa wanda basa da bukatar yin tambaya ko kallon rashin sanin inda suka fito. Haka dai suka ci gaba da tsayiwa a gurin kusan minti ashirin sun kasa yiwa kowa magana sannan suma mutanen gurin sun kasa yi musu magana. Shi Alpha a lokacin tunani yake meye abu yi ina zaije wa zai ce yazo nema, shifa gaba ɗaya lokacin da zai shirya tafiyar bai kawo irin wannan abun ba dama ita Nigeria ba kamar Saudiyya take da kana zuwa zaka faɗi sunan gurin da zaka je bane a kaika. Sai kuma ya tambayi kansa da cewar to kai ɗin yanzu kayi tambayar ne ba'a kaika ba. Laila ce ta dawo dashi daga tunanin da yake yi ta ce "Nan shine Nigeria?" Alpha ya ce "Eh Nigeria kenan?" Ta sake faɗin "Yanzu ina zamu je ko dai anan zamu zauna?. Kafin ya bata amsa wani kyakkyawan saurayi ya ƙaraso gurin yana yi musu sallama. Alpha ya amsa yana miƙa masa hannu. Yaron cikin turancinsa mai kyau yake tambayar su ina zasu je. Kasancewar duk suna jin turanci yasa Alpha faɗin "Yauwa mu baƙi ne muna son Hotel mai kyau wanda zamu kwana. Yaron ya ce "Ok tom ku biyo ni. Haka suka bi bayan wannan yaron har gurin wata jar mota ya buɗe musu suka shiga sannan ya rufe ya shiga gidan gaba ya ɗauki hanya. Suna tafiya Laila da Alpha suna bin cikin garin Abuja da kallo yayin da wannan yaron yake satar kallon Laila ta cikin madubin gabanbmotar. Sosai kyawun yarinyar ya tafi da imaninsa har yake mata kallon tsoro. Yana cikin haka suka haɗa ido da ita wacce itama ta kai idonta gurin. Da sauri ya kawar da kai yana ɗan rikicewa, itama ta kawar da kanta tana ɓoyewa a bayan Alpha. Wani ƙaton hotel ya kawo su har lokacin yana satar kallon Laila domin shi dai zai iya rantsewa bai taba ganin mace mai kyau irin wannan ba. Bayan sun sauƙa Alpha ya tambaye sa nawa ne kudinsa. Yaron ya ce dubu biyar ne. Alpha da Laila suka kali juna. Da harshen larabci ta ce "Nawa ne dubu biyar? Alpha ya ce "Nima ban sani ba, amma bari nayi masa magana "Abun da za'ayi yanzu rufe motar taka ka biyo mu. Yaron ya rufe motar ya bisu a baya har cikin hotel ɗin, shine yayi musu komai na kama ɗakin sannan ya biya kuɗin kwana biyu kaman yadda Alpha yace. Har cikin dakin ya raka su kafin ya ce "Gobe karfe nawa zan zo? Alpha ya ce "Karfe goma na safe zaka iya zuwa". Har yaron zai fita Alpha ya ce "Am Sorry menene sunanka? Yaron ya ce "Abdul". Alpha ya ce "Ok ni sunana Alpha" Abdul yayi murmushi yana sosai kai ya ce "Eh ai naji lokacin da kake faɗa a reserfshon. Alpha yayi murmushi shima ya ce "Tom Abdul good night sai ka dawo goben ko. Bayan fitar Abdul Alpha ya juyo da nufin yin magana amma yaga bata bayan sa.  A hankali ya maida kallonsa izuwa cikin dakin da yake babba, babu komai a ciki sai gado da kujera guda ɗaya sai tv da wani ƙaramin drowa da ake zuba kaya. Sai ƙofar Toilet da yaji ruwa na zuba a lamar dai tana ciki. Ɗan Kayan su ya jera a cikin drowar yana yi yana kallon Film ɗin da ake nunawa a tv da ya kunna. Har ya gama bata fito ba, hakan yasa ya tashi da nufin zuwa ya duba sai yaji ana buga musu ƙofa. Sai da ya tsaya ya kalli ƙofar sosai kafin ya iya tambayar waye da turanci. 

A hankali ya buɗe yana kallon ma'aikaciyar hotel ɗin ɗauke da abincin da shi dai yasan baiyi odar ba. Tana ajiye wa ta juya ba tare da yayi mata magana ba. Sake rufe ƙofar yayi ya nufi Toilet ɗin yana kiran sunanta. Kafin ya shiga sai gata ta fito daga Toilet ɗin ya bita da kallo bai ce komai ba. Shima wankan ya shiga, kafin ya fito ta saka doguwar riga ta kwanta tana jira ya fito ya bata wayarta ta kunna. Koda ya fito ya sauya kaya yana kallonta da ta kwanta a kan gadon tana kallon tv da yasan hankalinta baya gurin. Bayan ya gama ya ƙarasa kusa da ita ya taba ta. Ai kuwa da sauri ta zabura zaune. Ya ce "Me kike tunani haka Laila?" Ta sauke ajiyar zuciya ta ce "Ina tunanin Abi ne tsiro nake ji, dan Allah bani waya na sai na kira sa?" Tayi maganar duk da larabci kuma cikin kuka. Alpha ya ce "Kinga ina so ki natsu ki saurareni. Wannan tafiyar munyi tane ba tare da sanin kowa namu ba, saboda haka bamu buƙatar waya ko labtop, ina so ki kwantar da hankalinki idan har mukayi Aure kika aihu zamu koma gida Lokacin kinga Abi ba zai raba muba, kuma zamuce yaran da aure muka same su, ko kina so mu koma gida yanzu kowa ya ganki da ciki ne? Da sauri ta gyaɗa masa kai tana girgiza wa. Ya ce "To ina so daga yanzu Karki ƙara yin maganar su Abi ko kuma kiyi kuka, yanzu yadda zamu zauna a Nigeria har ki aihu mukoma gida zamu dinga tattaunawa. Ya faɗa yana shafa bayan ta har sai da ya tabbatar da cewar ta natsu sosai. A hankali ta ce "To yanzu yaushe zamuyi auran? Kuma idan munje gurin yin auren baza'a ce ina da ciki ba ko? Ta faɗa da wata murya mai kama da shagwaɓa. Ya ɗagota yana murmushi ya ce "A'a ai babu wanda zai sani. Ta ce "To yanzu anan zamu zauna ne?. Ya ce "A'a nan hotel ne, zuwa gobe Abdul zai zo ya kaimu inda zamu sauya kuɗi sannan mu kama gida. Ta ce "Kazo da kuɗi da yawa ne?" Ya ce "Eh duk abun da zamu bukata har ki aihu na tanada, kuma idan sun kare ma a kwai wanda zan nema. Ta ce "Wa zaka nema? Kuma da wacce wayar?" Ya ce "Bada waya bane, kuma baki san sa ba. Ta ce "Nima na zo da kuɗi da yawa". Ya ce "Tom ki ajiye su watarana zakiyi amfani da su. Ta ce "A'a ni babu abin da zanyi da su. Ya ce "To ki ajiye zan amsa zuwa gobe. Abincin ya ɗauko suka fara ci, suna ci suna hira har sai da suka ƙoshi. Bakinsu suka wanke kafin suka kwanta. Wannan karan ma duk yadda yaso da ta basa hadin kai taƙi tace har sai an ɗaura auran. Haka ya hakura sukayi barci mai daɗi a ƙasar Nigeria.

Da safe ma haka aka kawo musu abinci irin nasu na larabawa kaman yadda Abdul ya ce. Bayan sun zauna sunci, sai suka fara hira Alpha yana bata labarin Katii mahaifiyarsa yadda take da faɗa da rikici, ko yaya zatayi idan ta wayi gari taga baya nan. Suna cikin haka Abdul ya iso. Buɗe masa ƙofa Alpha yayi suka gaisa ya sakar masa fuska sosai kamar sun daɗe da sabawa. Dama tun daren jiya Alpah ya shirya kuɗaɗen sa a cikin jaka, dan haka babu ɓata lokaci yayi sallama da Laila da tun da Abdul ya shigo ta kasa sakewa, daga ta ɗaga kai sai taga yana kallon ta, hakan yasa ta kasa cewa komai har sai da Abdul ɗin ya fita ta ce "Kuɗin da nace zan baka bari na kawo maka? Alpha ya ce "Bari sai na dawo. Haka suka fita tana jin kamar ta bisa. Ai kuwa ko minti biyar ba suyi ba ta fara jin tsoro, gashi tana tsoron fita, sai kawai ta fashe da kuka ita ɗaya a cikin ɗakin. 

Suna cikin mota suna hira Alpha yake sanar dashi cewar su baƙi ne sun zo yin wani aiki ne, amma suna buƙatar gida wanda zasu zauna. Farko Abdul yace to suzo gidan sa shima bai fi wata da yin sabon aure ba, kuma gidan zai ishesu. Amma Alpha ya ce "A'a nasu suke so domin zasu daɗe. Alpha yayi karatu sosai, domin yaji turance kuma ya iya karantawa, hakan yasa koda suka zo gurin chanjin kuɗin bai sha wahala ba, kuma ba'a cuceshi ba, saima ganin yadda kuɗin nera yake a banza wato babu albarka gaba ɗaya ma shi sai yake ganin kamar shi ya cuci masu yin chanjin. Domin Riyal ɗari biyu (Jaka ɗaya)ta Saudiyya a lokacin dubu dari biyu ne da ashirin da biyar (Wato ɗari biyun
ɗin Nigeria kenan) . Hakan yasa bai chanji kuɗin nasa gaba ɗaya ba. Gurin bada kuɗin ma aka ce ya bada account a tura masa ya ce a bashi su a tsabar su. Duk yadda Abdul yake sheda masa cewar nan ba Saudiyya bace nan Nigeria ce amma bai ji ba haka aka jera musu kuɗin a jaka bayan Abdul ya gama masa bayanin yadda kuɗin suke. Suna hanya Abdul ya ce "Ko zamu bi ta bank sai ka buɗe banki a zuba su a ciki kamar zai fi. Farko bai yarda ba, daga baya suka je bakin da Abdul ya kira wani abokinsa yayi masa bayanin su Alpha da abun da suke so. Abokin ya ce "Kasan ba'a buɗe banki saida katin ɗan ƙasa, Kuma dole sai da layin Nigeria, so dan haka duk sai kun kawo wannan tukunna. Ai kuwa a ranar Alpha suka koma suka ɗauko Laila. Suka fara zuwa gurin katin ɗan kasa, ganin kalar su, kuma ga alfarma da Abdul ya nema da kuma kuɗi yasa basu ɓata lokaci ba dukda kuwa su ɗin ba ƴan ƙasa bane, a take akayi musu komai. Daga nan gurin rijistar layi sukayi nan ma akayi musu layika bibbiyu MTN da aitel. Basu tsaya a nan ba suka shiga shagon siyar da wayoyi duk Abdul yake shige musu gaba. Duk wannan abun gaba ɗaya Laila ta gama rudewa, sosai take mamaki da ganin baƙaƙen fata cike da Nigeria, ita fa tayi tunanin suma fararen fata ne, domin bata taɓa kawo cewa haka zata gansu ba, tun abun na fara bata tsoro har ta koma bawa idonta abinci, kuma takan yi ƙoƙarin rike wani abun da ta gani domin idan suka dawo gida ta tambayi Alpha duk da taga shima ɗan kallo yake zama a wasu guraren. Sosai take godiya da yasa suna jin turanci da bata san yadda zata yi ba, tunda ita bata taɓa jin sun yi larabci ba, daga turanci sai wasu yaruka da bata san ma ta yaya ake iya yinsu ba, bare kuma har taji. 

Bayan sun dawo gida Alpha ya bawa Abdul kuɗi masu yawa yace sai gobe idan ya zo zasu koma gurin buɗe account ɗin. A daren kuwa sun sha hirar ƴan Nigeria, Laila harda dariya tana kwatanta yadda jikinsu yake da yanayin kaiwa da komowar su da irin karamcin su. Ta ce "Wai shima Abi ɗin ku haka yake kamar mutanen garin nan baƙaƙe?. Alpha yayi dariya sosai har sai da ta tsaya tana kallonsa. Ya ce "Shima haka yake kamar su, hakan yasa Katii bata son su, duk da cewar shima yace laifi suka yi masa yasa baya ma yi mana maganar su, kuma cikin ikon Allah Kinga duk babu wanda yayi kama dashi daga ni har Ummul Kairi. Ya ƙarasa yana kallon fatar jikinsa da yake fari tass irin na Katii. Laila ta ce "To yanzu ta ina zamu fara nemansu, kuma idan mun gansu ta yaya zamu gane su, kuma suma zasu yarda cewar kai ɗan uwansu ne?.  Alpha ya ce "Nifa ba wai nemansu ne ya kawo ni Nigeria ba, nazo ne domin mu samu lokacin mu ni dake, musha soyayya, abun da yasa na ce muzo Nigeria koda Allah zai sa na gansu ne, idan na samesu to shikenan, idan ma bamu haɗu ba shima shikenan, kuma idan naga wani dangin sa zan gane domin suna da fashin goshi a fuskokinsu kamar yadda yace mana. Yana cikin maganar  ta kunna waya tasa camera ta ɗauke sa hoto tana sakin murmushi. Hakan yasa yayi murmushi shima yana sake sakin fuskartasa. Haka suka ƙara biyan kuɗin hotel harna sati guda, kuma a cikin satin komai nasu ya kammala, ya mayar da kuɗin sa account. Kuma cikin ikon Allah duk abun da Abdul ya nuna masa baya ƙara nuna masa. Sosai suke yawo a cikin garin Abuja har Alpha yaji zai zauna anan bayan ya tambaye shi inane yafi ko ina kyau a Nigeria. Shi kuwa Abdul da yake so su zauna guri ɗaya da sauri yace masa ai nan ne Abuja. Nan yasa ya kaishi cikin babbar unguwa suka siya gida, wanda shima Abdul ɗin Alpha ya siya masa wani madaidaici kusa da nasu...