Chapter 5
by @reza12
INA MUKA DOSA?
S-Reza✍️
Chapter 5️⃣
Shi idan yaji tana magana akan faɗan iyayenta jinta kawai yake yi, domin shi a ganin sa faɗa tsakanin mata da miji abu ne mai kyau muddin kowa a kan gaskiyar sa yake, domin kuwa haka a keyi a gidan su, hakan yasa bai taɓa mai da hankali akan hakan da take yawan faɗa masa ba. Shi dai kawai yafi mai da hankali akan rashin kulawa da basa bata da har take shiga matsala haka, ace wai iyaye su haifi ƴa amma su kasa ciyar da ita dan uwarsu. Yana jin yarinyar a ransa kamar ƙanwar sa Nadiya duk da kuwa babu abun da suka haɗa shi da ita, hasali ma shi musulmi ne ita kuma Kirista. Ya haɗu da ita ne wata ɗaya baya watarana ya fito zai tafi filin ƙwallo ya ganta sunkuye tana kuka, duk da cewar shi ɗin yaro ne mara jin magana kuma wanda baya shiga sabgar kowa amma ganinta ƙaramar yarinya yasa ya ƙarasa gurin yana daka mata tsawar da tasa yarinyar ɗagowa zata gudu. Taku ɗaya ya rike ta yana zare mata ido wanda yasa ta sake fashewa da kuka tana ƙoƙarin guduwa. Da yaren Hausar sa da bata fita sosai amma dai kana iya gane abun da yake faɗa ya ce "Me kike yi anan ke ɗaya da ba zaki je gida ba dan ƙaniyar ki? Kasancewar da karfi yayi maganar yasa ta sake fashe da wani kuka tana son ƙwace hannunta ta gudu. Ta shiga girgiza masa kai duk tana a tsorace. Sosai ya bi jikinta da kallo ganin ko takalmi babu gashi rigar jikin tata itama ta yage ta hamta har kana iya hango farar fatar hammatarta, ga datti da doguwar rigar tayi kamar wata almajira. Ya ce "Ke ƙazama ce ko dan ubanki ba kya wanka ko? Ina gidan ku yake dan uwarki? Sosai take ta kuka hakan yasa ya fara sassauta muryar tasa har ya samu tayi masa magana akan cewar bata jin Hausa, kuma yunwa take ji. Ya kalleta da kyau ya ce "Ina ne gidan ku da bazaki je kici abinci ba kina ce mini yunwa kike ji? Ta ce "Yana bayan layin nan. Ya ce"Muje gidan naku na gani uban me ya hana iyayen naki su dinga baki abinci. Ya faɗa yana duba agogon hannunsa domin kar ya makara a filin wasan nasu. Haka suka ƙarasa yaga gidan a rufe. Ya ce "Ina mamanki da baban ki ɗin suke? Ta ce "Basu dawo daga aiki ba sai da yamma. Da harshen larabci Ziyach ya saki wani katon zagi yana kallonta tsabar mamaki jin wai sun tafi aiki. Sai kuma ya ce mata "Su iyayen naki basu da hankali ne da zasu rufe gida su barki a waje, to gidan uwarsu suke so kije ko yaya wawaye kawai? Kasancewar da harshen Ingilishi yayi wannan furricin yasa sarai taji mai yace amma kasancewar ita kanta kallon da takewa iyayen nata kenan yasa ko kaɗan bata ji zafin abin da yace ɗin ba, saima daɗi da taji ganin ransa ya ɓaci akan abun da ya shafe ta. Abun da bata sani ba kuwa haka halin Ziyach yake koda waye kuwa muddin aka ɓata masa rai zagi baya masa wahala, ko yanzu ya chakume mutum da faɗa, ko kaji cikin harshen larabci yana cewa Allah ya la'anci ka. Haka yake da zuciya sosai kaman ɗan kuturwa.
Haka ya kama hannun Sara ya Kaita har ƙofar gidan su ya shiga cikin gidan ya samo mata abinci ya bata yace taci ta tafi da sauran gida. To tun daga lokacin ya zama kullum sai tazo gurin ta zauna har tsawon sati ɗaya. Hakan yasa ya ce mata ta daina zuwa kofar gidan su, ta dinga zuwa wani guri da ya nuna mata wanda zasu dinga haɗuwa, kasancewar ya ce mata shi baiga laifin iyayenta da suke yin faɗa ba, kowa ya ƙwaci ƴancin sa kawai. Tayi tayi dashi akan yazo gidan su amma yace shi ba zai je ba, hakan yasa sukayi sabo sosai shi da ita. Duk ranar da yazo gurin bai sameta ba haka zai zauna har sai tazo ya bata a bincin taci a gaban sa. Zuwa yanzu har kaya yana siya ya bata ko taƙalmi da dai duk abun da yarinya ƴar shekara sha biyu zata bukata kamar dai ita. Tana jinsa kamar yayan ta, domin idan yana tare da ita babu abun da bata faɗa masa wanda ya shafe ta, harma da faɗan da ake yi a gidan su. Shi kuwa ya ce mata idan wannan ne tazo gidan su taga yadda ake faɗa ba irin nasu ba. Ita kuwa babu abun da ta sani a kansa face tasan shi ɗan masu kuɗi ne kuma yana buga Ball. Domin wani lokaci tare suke zuwa da ita amma ya tsayar da ita a gefe guda domin baya so ɗan uwansa yasan yana tare da ita. A takaice dai Sara da Ziyach sun zama kamar yaya da kanwa ne a cikin wata ɗaya, domin idan iyayenta sun fita aiki sun rufe gida haka zata zo gurin sa su zauna suna ta hira, domin yanzu a tsakiyar hutun karatun boko ne. A duk lokacin da ya fahimci tana cikin damuwa yakan so ya kwantar mata da hankali koda kuwa daga gida ranta ya ɓaci. Abun da ya faru yau kenan, ya zo mata da abinci amma bai sameta hakan yasa ya tafi duk jikinsa babu daɗi yana tunanin Allah yasa dai taci abinci, haka yaje filin wasan nasu yana ta tunanin me ya hana ta zuwa yau, gashi bai bata waya ba, kuma shi baya son zuwa gidan su, domin kuwa ya ce muddin yaje yayi ido biyu da iyayenta zai iya zage su babu ruwansa. Idan ya faɗa mata haka sai dai tayi dariya kawai domin tasan zai iya hakan, amma shima zaiji a jikinsa dan mahaifinta da ko ita ma da take ƴarsa bai raga mata ba bare kuma shi. Hakan yasa koda za'a fara wasan jikinsa babu ƙwari har kuma yaga tazo har filin wasan ta kira sa.
Bata ko ci rabin abincin ba tace ta koshi, ta ɗauki ruwan ta sha. Sannan ta miƙa masa sauran, sai ya girgiza mata kai alamar ba zai sha ba amma ta ɓata rai kamar zata yi kuka, sai ya buɗe baki. Hakan yasa ta kai masa bakinsa, sai ya sake kawar da kai. Ta ce "please kasha kaji" ya karɓa ya ajiye a gefe ya kamo hannunta suka zo gurin mai abincin ya ce "Nawa ne kuɗin abincin? Mai abincin ta ce "Dubu biyu da ɗari biyu harda lemon. Ya ce "To zan je gida na dawo zan kawo miki kuɗin ki yanzu ban fito da kudi ba kuma wayata ma na barota a gida. Ya ƙarasa yana mata misali da hannu. Matar ta ce "Wani gida kuma yaro, ni ai ban sanka ba, kawai bani kuɗi na ka tafi. Matar ta faɗa tana ƙarasowa kusa da shi har tana riƙe shi jin wani sabon zance wai sai ya dawo. Ziyach ya ce "Akan dubu biyu da ɗari biyun ne har kike riƙe ni? Ziyach ya faɗa a zuciye ganin yadda ta riƙe masa riga kamar ta kama ɓarawo. Matar ta ce "To bani kuɗi na sai na sake ka. Kuji min yaro ba dole na rike ka ba tunda baka biya ni ƙuɗina ba, kuma kake cewa akan dubu biyu, yo ko nera ɗari ne ai sai ka biya. Ziyach da zuciyar tasa ta gama zuwa wuya ya ce "Sakar min riga wawiyar mata kawai ƙazama. Ya faɗa kai ka rantse da Allah kuɗin zai ciro ya bata ganin yadda yake maganar cikin fushi. Matar kuwa ta sakar masa riga tana faɗin "Duk rashin kunyar ka ka fara bani kuɗi na tukan kafin sai kayi duk uwar da zaka yi, amma wallhi muddin baka bani kuɗi naba babu mai ƙwatarka a gurin nan har sai ka fito min da kuɗi na. Ziyach ya shiga karkaɗe rigarsa da ta sake cikin larabci a hankali ya ce "Allah ya wadaran matsiyata. Sara dai tana tsaye tana kallon sa. Ganin har mutane sun fara taruwa a gurin ne yasa ya ce "Yanzu daga filin ƙwallo nake zan je na kawo miki kudin ki domin yanzu bani da su. Ya sake faɗa kamar mai bada umurni. Matar ta ce "Kai amma ka cika ɗan rainin wayo, yanzu ka gama zagina amma ashe baka da kuɗi, to na fika iya rashin Kunya wallhi, idan kuma kaga kabar nan gurin to sai dai kabar wannan ƙanwar taka a nan kaje ka dawo amma idan ba haka ba babu inda zaka je. Tana rufe baki yayi mata wani irin kallo. Kasancewar duk da turanci ake maganar yasa Sara matsawa kusa da shi tana riƙe hannunsa jin batun za'a barta anan, tana bin matar da wani irin kallo itama. Cikin rashin iya magana da na gaba Ziyach ya ce "To dan uwarki sai kizo ki riƙe ta ɗin akan dubu biyu tunda baki da hankali banza majnun kawai. Bai rufe baki ba kuwa matar ta ɗauke shi da mari wanda yasa bakin nasa fitar ta jini lokaci guda. Shi aka mara amma Sara ce ta ƙwalla ihu da wani irin kara kai ka rantse ita marin ya shiga. Jin ƙarar da tayi sasa matar faɗin. "Duk sai na haɗa ku na ci uwarku anan, kunji min ƴan iskan yara kusan baku da kuɗi zaku ci min abinci, kuma harda zagi na. Lokaci ɗaya Ziyach ya fara suburbuɗo zagi da larabci da turanci yana yi kamar zai naushi matar, sosai matar ta tsorata ganin yadda ake riƙe shi amma yana ƙwacewa yana cewa sai ya mata duka, ko Allah ya la'anci uwarta ko abincin nata. Hakan yasa wani mutum yazo yake tambayar abun da ya faru. Nan matar ta kora masa bayani ya ce zai biya. Amma Ziyach ya ce shi babu wanda zai biya masa domin yana da kuɗi, duk wanda yazo sai Fahimtar da shi sai Ziyach ya zage shi yace baya bukatar taimakon sa domin yana da kuɗin. Ganin rashin kunyar yaron tayi yawa yasa kowa ya goyi bayan matar, gashi ance ya bata kudinta yace sai yaje gida. Ita dai Sara ta rike masa hannu tana kuka tana kallon bakinsa da har lokacin jinin na ɗan fita kaɗan. Ganin haka yasa wani da ya lura da yaron kamar ɗan manya ne, kuma kallo ɗaya zaka yi masa ka gane shi ɗin Balarabe ne yasa ya ƙaraso gurin ya ce "Ɗan wasa yanzu ni bari na ara maka sai ka biya ta idan ka dawo sai ka bani ko? Sai a lokacin aka samu Ziyach ya yarda aka bashi aron dubu biyu da ɗari biyar ya bata. Zata bashi chanji ya ce "Matsiyaciya ki riƙe gaba ɗaya kuma wallhi daga yau abinciki ya daina dafuwa dan uwarki har sai kin zo kin bani haƙuri akan abun da kika min. Zaki san ni kika mara. Matar da bata ɗauki maganar serious ba ta ce "Tunda dai ka biyani kuɗi na kaje cen da rashin kunyarka, ɗan marasa mutunci. Haka ya kama hannun Sara suka dinga tafiya ran nan nasa a mugun ɓace gafatar bakinsa da ya ɗan taso, ji yake kamar ya koma ya rama abun da matar nan tayi masa ko zaiji sanyi a ransa. Bayan sun bar gurin kowa ya fara mamakin irin wannan ƙarfin hali na wannan yaron, matar dai taci gaba da siyar da abincinta ana mayar da maganar. Daidai lokacin an fara kiraye-kirayen sallar magriba hakan yasa ya Kaita har kusa da gida ya ce ta tafi. Sai kuma ta tsaya ta ƙi tafiya ta ce "Please Ziyach ka wanke jinin bakin ka kaji, I'm sorry for everything. Ta faɗa kamar ta zata sake dawo da kukan nata baya. Ya ce "Tafi gida na ce!. Ya faɗa duk fuskar nan babu annuri. Sai kawai ta fashe masa da kuka tana dawowa gaban sa. Ita tasan halinsa idan ransa ya ɓaci harda ita baya ragawa yanzu zai sarfa mata zagi ko a jikinsa. Ai kuwa da karfi ya yakiceta daga jikin sa, cikin tsawa ya ce "Na ce ki tafi gida ko!!. Ya faɗa yana ɗan tura ta domin har yanzu abun da matar nan tayi masa bai bar dawo masa a rai ba. Ai kuwa tayi hanyar gida da sauri tana kuka tana juyowa ta kalleshi. Sai kuma yaji wani irin tausayin ganin yadda take yi ɗin. Hakan yasa ya sake kiran ta da hannu, amma taƙi juyowa kamar yadda yace ɗin, hakan yasa ya bita da guda ya rike ta ya kwantar da ita a jikinsa yana rarrashin ta yana huci ita kuma tana sauke ajiyar zuciya. Har tayi shiru ta nuna masa masallacin kusa da su akan ya wanke bakin sa. Gurin ya ƙarasa ya wanke bakin nasa ya dawo gurin ta sa hannu a kan leɓen nasa da ya fashe ta ce "Da zafi ko?" Ya kalleta ya girgiza kai. Ta sake cewa "Sorry kaji duk nice naja maka?. Ya ce "Nace miki babu zafi fa kuma ba komai. Ta ce "No ai duk wani ciwo yana da zafi, nima ranar da Daddy ya Jimin jiwo a nan, ta faɗa tana nuna masa bayan guiwar hannunta da tun kafin su haɗu da shi taji ciwon. Ya ce "To ai ke mace ne, zaki ji zafi, ni kuma Namiji ne ba zanji zafi ba. Ta ce "Maza basa jin zafi kenan? Ya ce "Suna ji amma daurawa suke yi. Ta sake cewa "To me yasa mu mata bama daurawa?" Ya ce "Saboda ku baku da juriya abu kaɗan ke saka ku yin kuka, ji fa yanzu ni aka mara amma kin fashe da kuka. Ta ɗan ɓata rai tana turo baki sai kuma ta ce "Harda mommy na itama bata da dauriya? Ya ce "Kowacce Mace ma bata da juriya. Ta ce "Mommy fa idan suna faɗa da Daddy bata kuka. Ta faɗa tana ƙara jin sakewa da shi fiye da kowa a duniyar ta, harda iyayenta kuwa. Domin idan ba da shi ɗin ba ba zaka taɓa yarda cewa ta iya magana har haka ba. Ko a gidan su kamar baƙuwa take kasancewar iyayen nata basu shirya samuwar tata a lokacin da suka sameta ba, hakan yasa kowa ke ɗaura laifin samuwar tata ga ɗan uwansa harma kowa na gudun zama da ita.
Ya ce "To Daddy ɗin ne rago kenan ko?" Ya faɗa yana mamakin yadda take dariya kamar ba yanzu ta gama kuka ba. Ta ce "Yaya wasan naku kunci kuwa? Ta faɗa tana kawar da waccer maganar. Sai a lokacin ya tuno da ƙurar da ya baro a baya. Ya ce "Ya salam! Sara tafi gida gobe idan su Daddy sun tafi aiki kizo da wuri kinji zan jira ki, kuma zamu je wani guri. Yana faɗa ya kama hanyar tafiya amma ta ce "Gobe fa Daddy zai tafi to idan ya tafi dani fa? Tsayawa yayi yana kallonta daga nesa, kusan minti ɗaya ya ce "Bayee Allah ya kiyaye hanya. Ya faɗa yana jin kamar ba zai so ta tafi ɗin ba, amma haka ya cigaba da tafiya bai ƙara juyowa ba. Yana gudu yana aiyana abun da zai faru da shi da team ɗin su idan aka ce ancisu a wasan da yasan shine ya jawo idan ma hakan ta tabbata.
Babu ko sallama ya tura ƙofar palon gidan nasa yana aikawa matar sa wani irin kira wanda kana ji kasan ransa a ɓace yake. "Laila! Laila!! Laila!!!. Haka ya dinga ƙwaɗa mata kira har ya haura sama ya dawo ganin bai sameta ba. Amma da mamaki yana sauƙowa ƙasa yaci karo da ita a zaune a ɗaya daga cikin kujerun alfarmar da suka ƙawata makeken palon nasu, ta ɗora ɗaya kan ɗaya ta ba banza a jiyar sa. Tsayawa yayi ya kasa ƙarasowa yana binta da wani irin kallo. Sosai tayi kamar bata ma san da tsayuwar sa a gurin ba dukda kuwa tun shigowarsa na farko da baiyi sallam ba sai kira da yake mata ta gansa. Sanye take cikin wata ɓakar abaya ta sha kwalliya kamar budurwa ƴar shekara ashirin da wani abu. A kallo ɗaya ba zaka gane ita ɗin babbar mace bace saboda gyara da kuma hutu da ya nuna a farar fatar tata, a zahiri kuwa kadan ya rage bata kai arba'in ba, amma kasancewar ta balarabiyar da ta samu hutu yasa shekarun nata suka ɓoye ɓat a jikinta. Da wani irin ɓacin rai ya karaso gurin da take ya ce "Ke dai wallhi Laila kin yi a sara a rayuwarki ta gidan duniya da lahira, wato ke baki da abun rainawa a nan duniya sai mijin ki ko, mijin da Allah yace aljannar ki tana karkarshin ƙafarsa shi kike mayarwa ba kowa ba ko, to wallhi kiji da kyau muddin sai na ɗaga wannan ƙafar zaki shiga aljanna, to Wallhi ba zan taɓa ɗagawa ba muddin wake zan ɗagawa, haka zan barta a ƙasa har karshen rayuwa kizo a banza ki koma a hofi. Ya faɗa yana ɗaga kafar yana bugawa da karfi a ƙasan dakin. Jin bata tanka masa bane ya ce "Kin je asibitin ne ko dai baki je ba sha-shar mata kawai wacce ta girma amma bata san ta girma ba. Alpha da kallo ɗaya zakayi masa ka hango wani fushi da yake ambaliya a kan fuskarsa. Ya sake faɗa yana ƙarasowa kusa da ita. A zuciye ta mike tsaye ta ce "Wai kai Alpah wani irin mara zuciya ne, asbinti ne na ce ba zan je ba ko ana dole ne, kai wai kullum baka son a zauna lafiya ne, kana girma kana ƙara komawa baya, dan Allah ni ka barni da abun dake damuna please. Da karfi cikin harshen nasu Alhaji Alpha ce "Allah ya tsinewa ke da abun dake damun naki munafuka kawai, ya ina miki magana kina min maganar abun da ya dame ki, ina ruwana da abun da ya dame ki. Yana rufe baki itama ta ce "Kaima Allah ya tsine maka kai da kake damun nawa babban kwabo kawai, ai kaine damuwar tawa, kaga kenan kanka ka tsinewa. Taci gaba da faɗin "wallhi kaji kunyar rayuwarka Alpha wallhi kana daga cikin aikin da nayi da na sani a cikin rayuwarta na auran da nayi har na samu zuri'a da kai, kuma ka sani wallhi ko me zakayi sai dai kayi aihuwa ce ba zan ƙara yi da kai ba, wannan ma da muka samu tare babu abun da zan ce sai Allah ya isa tsakanina da kai, domin babu abun da na tsinta zamana da kai sai masifa da bala'i da ƙaruwar yaran da basu da amfani a gareni, kuma ko kaso ko kar kaso gida ne sai na koma. Alpha da ya gama jin zafin furcinta shima cikin kumfar baki ya ce "Tun farko nine nayi kuskure wajen yarda dake dama ance"Idan zakuyi aure ku nemawa ƴaƴanku uwaye nagari, amma ni na ɗauko musu ke wacce yanzu gashi dalilin haka har yaran ma kin lalata mana, dama duk matar da zata iya bawa Namiji kanta tun a waje ai ba matar Aure ba!. Cak Laila ta ƙame a gurin tana kallonsa, babu abun da yake fado mata sai lokacin da ta yarda da shi ta basa kanta sabo da soyayya, yanzu gashi gori yake mata. Hawaye ne suka cika masa ido amma ta kasa cewa komai sai kallonsa da take ta yi. Kafin Ummu tayi magana sai ga yaran nasu sun shigo gidan suma cikin faɗa kamar yadda aka saba. Ziyech ya ce "Kai idan ana maganar lusari ma har ka saka baki, idan ba yau ba ka taɓa gani na yi amfani da wani abu naka, ai wallhi Allah ya sawaƙe kai a wa yaushe ma ka kai na taɓa kayan ka.
Hakim ya ce "Eh naji dai aje a cire min taƙalmi tunda dai ba naka bane, kuma na gode Allah da yasa aka ciku a wasan da kuka buga, kaga daga yau kuri ya ƙare na cewa za'a ɗaga kofi. Ziyech da ransa ya gama ɓaci domin tun daga hanya mutane ke masa magana akan wai shine ya cisu, hakan yasa duk wanda ya faɗa haka sai ya tsaya ya zagi mutum har ya ƙaraso gida ya samu ɗan uwansa na jiransa da lilin ɗauke masa taƙalmin Ball da yayi. ya ce "To idan ba'a cire bafa wani abun zakayi?. Ziyach ya faɗa yana kallon abokin aihuwar tasa cikin ido. Sosai suke kama irin kamar da baka isa ka gane su daga kallo ɗaya ba. Hakim ya ce "Dole nema sai ka cire wallhi tunda ba naka bane. Ziyech ya sake cewa "Wannan Banzan takalmin ma nawa yake gaba ɗaya, kuma ma da nasan naka ne uban me zanyi da kayan ka aikin banza, takalmin ma da baya dukan ball da kyau. Ziyech yana faɗa ya shiga cire takalmin yana cigaba da maganganu na kushe taƙalmin da ya ɗauka bada izinin mai shi ba, kuma ko lokacin da ya ɗauka shima filin Ball ɗin zaije amma ya ɗauka ya gudu...📝
One love
One house
Comment's
And shering
Love my fans
By S-Reza ✍️