INA MUKA DOSA?

Chapter 8

by @reza12

INA MUKA DOSA?

                       S-Reza✍️

  
                    Chapter8️⃣

Cikin dare taji ƙirjinta na yana ƙaiƙayi sosai, tun tana sosawa a hankali tana jin daɗi har dai abun yafi ƙarfin hankalinta ya girmi tunaninta, domin wani irin zafi ne ke ratsa ta idan ta sosa gurin. Ihu ta sake haɗi da kuka lokaci guda tana kiran Mommy harda tsalle a cikin ɗakin. Ko kafin Mommy ta ƙaraso ta cire rigar jikinta tana kuka game da soshe-soshe ko wani ɓangare daga jikin nata. Mommy na zuwa ta shiga tambayar ta lafiya mai ke damun ta. Cikin kuka ta faɗa jikinta tana faɗin ƙaiƙayi ne ke damuna gaba ɗaya jikina. Mommy ta kunna fitilar wayanta tana haska jikin Sara ɗin, ita babban burinta taga abubuwan sun fara tashi kar tayi a saran kuɗaɗen ta a banza. Ganin dai Sara ta kasa natsuwa ne yasa ta daka mata wata gigitacciyar tsawa haɗi zagin duk a lokaci guda, amma ina azabar da take ciki yasa bata ko bi ta kan ta ba, bata ma san mai take faɗa ba. Ganin dai babu abun da ya fara ne yasa Mommy jan tsaki tana kallon Sara da har lokacin kuka take tana sosa ko ina. Mommy ta ce "Dalla rufewa mutane baki shegiya mai rakin tsiya, akan ɗan wannan abun duk kin cika mana gida da kuka cikin dare, kuma hakan ma ba ke za'a taimaka wa ba, idan ba'a miki hakan ba ta yaya za'a samu abun da ake so a tare dake. Ita dai Sara kuka take bata ma jin me take faɗa, domin jin jikinta take kamar ana saka reza ana tsagawa. Komawa ɗaki Mommy tayi ta barta ita ɗaya ta cigaba da kukanta har wajajen asuba kafin abun ya lafa mata. Ai kuwa da sauri ta faɗa Toilet tayi wanka ta kwanta a haka tana jin har yanzu ƙaiƙayin na ɗan damunta amma kaɗan -kaɗan. Sai kuma kan ƙirjinta da take jin kamar tashi suke yi, domin wani irin zullo take jin abun na mata, idan kuma ta kalli gurin ba zata ga komai ba, tana cikin wannan halin barcin dole yayi gaba da ita. Misalin ƙarfe tara Mommy ta farka ta nufo dakin Sara domin har mafarki tayi wai zuwa safiya ƙirjin Sara ya fara tashi ya girma ya zama tula-tula. Ai kuwa da sauri ta shigo dakin tana kallon yadda take yin  barcin wahala, domin ko daga yadda ta kwanta ɗin zaka gane bata jin daɗin barci. Kasancewar babu riga a cikinta, kuma tana kallon sama ne yasa Mommy ƙare mata kallo tana sakin murmushin nasara. Harda ɗan saurinta ta ƙaraso gurin tana kallon yadda abubuwan suka fara tashi a dare daya kawai. Har gurin ta ƙaraso ta sa hannu ta ɗan shafa tana ƙara jin daɗi a ranta. Ganin Sara tayi juyi ne yasa ta tashi da sauri ta fita domin karta tashi ta, gara ta barta tayi barcin huce gajiya. Haka ta haɗa mata abun kari ta kawo mata har ɗakin ta ajiye mata. Ganin har lokacin bata tashi bane yasa ta bar gidan ba tare da Sara ɗin ta sani ba.

Misalin ƙarfe shida na yamma aka sallamosu daga asibitin bayan an wanke masa gurin an kwantar da shi an saka masa jini leda ɗaya. Har suka dawo gidan Ummu bata ko leƙa asbintin ba, domin ita tace abun bai shafe ta ba. Shi kuwa wanda yayi abun tun bayan da ya dawo hankalinsa ya tafi asibitin ya tare acen, sai uncle Abdul da Anty Bintu da Abbu, sai kuma Sadiq da shima yaje asibitin duba abokin nasa. Tunda Hakim yaje gurin bai masa magana ba, amma dai yana zaune yana danna waya, kuma shima Abbu bai ce masa komai ba, kaman yadda shima Ziyach ɗin bai ce komai ba. Amma yasa a ransa wallhi sai ya rama wannan abun da yayi masa, kuma sai ya ramawa Sara dukan da yayi mata. Sosai abu yake ta basa mamaki wai Hakim ne ya chaka masa wuƙa! Wuƙa fa! Kenan kashe shi yaso yayi da ya samu dama. Idan ya saci kallonsa sai kawai ya aiyana irin abun da zai masa da zarar ya warke.  

Har cikin ɗakinsa suka rakashi uncle Abdul ya kwantar da shi ya jera masa magungunan da aka basu yana nuna masa yadda zai dinga sha. Shi dai Hakim na tsaye yana kallon su, yayin da Nadiya ke kusa da Ziyach. Abdul ya gama ya ce "Nadiya ke tabbatar da cewar ko wani lokaci yana shan maganin kinji? Kuma yanzu ma ya sha idan yaci abinci. Nadiya ta amsa tana kallon Ziyach ɗin da yayi kamar baya jin su. Uncle Abdul ya fita ya rage su uku a ɗakin. Hakim ya kalli Nadiya ya ce "Je ki haɗo masa shayi mai zafi yanzu, idan yasha sai a basa maganin. Ya faɗa babu wasa a muryarsa. Amma Nadiya tayi kamar bata ji sa ba, domin wallhi wani irin haushin sa take ji kamar ta rufe shi da duka. Jin tayi shiru ne yasa ya kalleta sai suka haɗa ido. Har ya buɗe baki zai yi magana Ummu ta turo ƙofar ɗakin ta shigo tana binsu da wani irin kallo gaba dayansu kallo. Kallon Hakim tayi wanda yake tsaye kamar kurtun soja ta ce "Au wai dama baka kashe shi ɗin bane? Ai nayi tunanin ba zai dawo gidan nan ba sai dai a wuce dashi cen. Ai ni ba zaku taɓa burgeni ba idan har ɗaya bai kashe ɗaya ba a cikin ku. Shine yanzu tsabar munafunci da gulma harda wani binsa asibiti bayan kuma kaine ka yi yunkurin kashe shi. Wawa babban banza kawai, kuma kaman yadda na faɗa muku idan har baku kashe junanku ba ko wani ya kashe wani ba ba zaku taɓa burgeni ba Wallhi. Ummu ta faɗa tana tana nuna Hakim da ya haɗe rai kamar tsohon kuturun da yayi bara bai samu komai ba. Shi har ga Allah baya son matar kwata-kwata, tunda ta nuna bata sonsu yasa shima yake jin babu ruwansa da ita . Hakim ya ce "Karki ƙara ce min wawan banza domin ni ba wawa bane, kuma da kike maganar mutuwa sai dai ke ki mutu amma ba dai mu ba wallhi. Ya ci gaba da faɗin "Idan har baki son mu mai yasa kika haifo mu, haka kawai duk kinbi kin tsane mu bamu san me mukayi miki ba, idan Abbu ne yayi miki laifi to mu ina ruwan mu, wallhi duk wanda yace baya sona nima bana sonsa koma uban waye shi!. Yana faɗa yana yin hanyar waje yana cigaba da magana. Ummu ta tsaya tana kallonsa ta ce "Shege babban banza, wawa mara hankali, kuma ka sani har a bada wallhi ba zan taɓa sonku dinba, domin babu albarka a tare daku, la'anallahu alaika. Ta karasa da karfi kasancewar ya bar cikin ɗakin. Ta dawo da kallonta ga Ziyach da yake ta sauraronsu yana jin ransa na ƙara ɓaci. Yasan cewar shima ba barinsa zatayi ba, tunda ko asibiti bata zo duba shin ba. Hakan yasa kafin tayi magana yayi saurin yunƙurawa ya zaune ya ɗaga mata hannu a lamar baya son jin maganar ta, domin ba zai iya yin magana da tsayi ba gurin na masa zafi. Amma kamar wanda ya kunnata. Cikin ɗaga murya kaman zatayi kuka ta fara faɗin "Ai naso ace kasheka yayi da sai kowa ya huta, wannan wacce irin masifa ne, ace ka haifi yara da kanka amma gaba daya babu mai hankali da tausayin ka, yara basu da abokin faɗa sai junansu da iyayen su, to dan Allah kar ku daina, kuci gaba daga inda kuka tsaya, ba dai halin ubanku kuka ɗauka ba, to in sha Allahu kullum kuna cikin wahala. Ganin dai taƙi dainawa yasa ya tashi ya shiga Toilet ba tare da yace mata komai ba. Haka Ummu ta dinga faɗa har Abbu ya shigo shima ya hauta da faɗa karshe dai fadan ya dawo tsakanin su. 

A ranar duk yadda yaso ya fita yaje ya duba Sara Abbu yaki basa dama haka dole ya haƙura ba dan yaso ba. Shi kuwa Hakim gurin abokinsa ya tafi mai suna Hasan, shima ɗan biyu ne kuma shine babban abokin Hakim ne tun na yarinta, tasu tazo ɗaya sosai domin duk makarantarsu daya, kuma duk wannan shekarar zasu yi kandy. Sannan duk wasu halaye na iskanci da Hakim ɗin ya kaye tare da Hasan ɗin ne, domin tun suna haka sun iya samun yarinya su lallaɓata suyi abun da zasu yi, idan ma suka ga wacce ta musu kuma ta ƙi bada kai har fyaɗe zasu yi mata. Amma bayan wannan barsu da neman magana da rashin Kunya. Labarin abun da ya faru ya bashi kasancewar abun ya dame shi. Duk yanda suke faɗa da ɗan uwan nasa baya son wani abu ya same shi, yanzu haka gaba ɗaya yaji ya tsani kansa hakan yasa dole sai da yaje asibitin. Hassan yayi dariya ya ce "A she dai yau an raba raini kenan ko? Ka san fa shi babba ko a gidan giya Wallhi babba ne, ai gara da ka nuna masa cewar ka riga shi shan iskar duniya, to ma idan ba raini ba kawai dan ka samo wata yarinya shikenan sai shi yazo ya mareka, sai kace wata ƙanwarsa, ni Wallhi da na san yarinyar ma sai mun aikata mata wallhi dan uwarta. Hakim ya ce "Ni ba wannan ba, ina tausayin Ziyach Wallhi ban so nayi masa haka ba, amma in sha Allah ba zan ƙara ba. Hasan ya ce "Yanzu ai shima zai kiyaye maka Allah kuwa, daga yanzu zai ƙara baka girman ka da Allah ya baka, ai kai kawai kasa a ranka cewar gyra kayi abokina. Hakim ya kawar da maganar da cewa "Yaufa suwaye suke da wasa ne, domin ina neman gurin zuwa? Hasan ya ce "Wai ita yarinyar da nake maka magana ƴar ina ce, ai ita ya kamata mu hukunta ba shi ba. Hakim ya ce "Kai nifa ban san yarinyar ba, domin ban taɓa ganinta ba, kuma ma fa yarinya ce ƙarama sosai batayi wani girma ba. Hassan ya sake cewa "To ai ta kwana gidan sauƙi tunda dai yarinya ce, kuma idan ka ganta ai zaka gane ta ko? Hakim ya ce "Sosai ma zan gane ta. "To ai shikenan ciniki ya faɗa kawai. Hakim yayi shiru na minti ɗaya kafin ya ce "To anya kuwa Ziyach bai san wannan yarinyar ba, domin lokacin da ts rungume ni, kaman ta kira sunan Ziyach, to ko dai tana tunanin shine!. Hasan yayi dariya ya ce "Tabbas haka ne shi yasa da ya fito ya ga kana dukan ta ya rama mata. Hakim ya ce "La shakka fihi, tabbas Ziyach ya santa, to a ina kuma yaushe? Hasan ya ce "To ko dai shima yana latsawa ne? Hakim ya ce "No Ziyach baya da wannan zuciyar, kuma da yana yi da na sani. Haka dai ya kamo hanyar gida yana ta tunanin abun dake tsakanin Ziyach da yarinyar. 

Lokacin da ta tashi daga barcin sai taji kamar ba ita ba, domin wani iri taji jikinta yayi mata nauyi, sannan ga ƙirjinta da taji yana mata wani irin fizga. Da sauri ta kai kallonta izuwa gurin domin sauyin yayi yawa. Da sauri ta zaro ido tana kallon ƙirjinta da tasan da babu komai yanzu kuwa gashi ya ɗan yi a lamar tashi, yayi tsini sosai kamar an kwaɓa fulawa an ja, kan gurin kuma yayi jaa kamar zai fashe. Ai kuwa tana taɓawa ta saki ƙara domin wani irin zafi taji har sai da ƙwalla suka fito mata. Lokaci ɗaya kuma ta fara tsoro tana jin ko dai ciwo ne taji a gurin. Lokaci ɗaya kuma ta fara murna ganin itama ta fara fitar da abun da take gani a gurin yara kaman ta, tana son tabawa amma tana tsoro. Haka dai ta wanke baki ta sake yin wanka taci abincin da  ta gani a gurin tana ta kallon breast ɗin nata tana dariya ita ɗaya. Misalin ƙarfe biyu tana zaune tana ta tunanin zuwa gidan su Ziyach kuma tana tsoro haka dai ta hakura da zuwa har Mommy ta dawo. Har lokacin kuma bata saka riga ba, domin tana yin ƙoƙarin sakawa ta cire sabo da wani gigiceccen zafi da ya ratsa ta. Sosai mommy ɗin tayi murnar ganin abun Masha Allah tabarakalla.  Haka dai har tsawon sati guda Sara bata ƙara fita ko waje ba, kullum tana gida, yanzu idan ma Mommy zata fita kulle ta ta ke yi ta waje domin yanzu tace ƴarta ta zama ƴan mata babu wasa kuma. Izuwa lokacin ƙirjin ya dai na mata ciwo sosai har sai idan an taɓa ta karfi, wanda kusan kullum sai Mommy ta mata wasa da su, kuma babu laifi abun sun fito dai ƴan kanana dasu wanda ko riga ta saka kana iya hango shatin su ba kamar sati ɗaya da ya wuce da idan ta saka riga kamar ƙirjin maza ba. Sosai itama take murna da wannan sauyin nata, yanzu babban damuwarta sanin halin da Ziyach yake ciki, tayi iya yinta amma ta kasa samun damar da zata je gidan su, shi kuma gashi yaki zuwa. 

*GIDAN ALPAH*
Alhamdu lillahi jikin Ziyach yayi sauƙi sosai domin cikin sati dayan nan har masifa yana samun damar yi idan an taɓo shi. Kuma kaman yadda Abbu ya ce Katii da Ummul Kairi zasu dawo nan da zama haka ne, dama rashin lafiyar Ziyach ɗin ce ta hana zuwan nasu a satin da ya wuce. Hakan yasa yace wannan satin da zamu shiga a shi zasu zo. Sann kuma a cikin satin ne za'a koma makaranta daga hutun da aka je. Har lokacin kuma Ummu na nan akan bakanta na tona asiri idan har su Katii suka zo cikin gidan. Shima dai Hakim bai yarda da zuwan nasu ba yayin da mai gidan yace sai dai suyi duk abun da zasu yi. Yasan cewar katti tana da faɗa sosai gashi bata da wasa, hakan yasa yake ganin idan har tazo nan ɗin zata saita masa gidan nasa da ya gama lalacewa, a tunaninsa Hakim da Ziyach da ita kanta Ummu ɗin zasu dinga jin tsoron Katii wajan yin wasu abubuwan, bai san cewar ita kanta Katii ɗin problem ce mai girma ba, domin kuwa tsufa ya ƙara mayar da ita masiffafiya sosai gata bata ɗaukan wargi. Ita kuwa Ummul Kairi mace ce mai iya yi ga rashin Kunya, domin abun da ya raba ta da mijin nata kenan, bakinta baya shiru, ga rawar gafa kuma ita bata aihuwa kaman yadda likitoci suka tabbatar hakan yasa shekarunta kusan bakwai da Aure har dai yanzu da auren ya mutu.

Nadiya ce sanye cikin shigar wando da riga kai babu ko ɗankwali riƙe da wata ƙatuwar waya da ƙaramar jaka a hannunta ta sauƙo tana danna wayar alamar dai sauri take yi. Ɗaga kai yayi ya kalleta ya ce "Ina zaki je? Ta ce "Gidan uncle Abdul zamu je sayayyan kayan school da su Nana da Maryam. Wato yaran Abdul kenan. Ziyach ya ce "Jira ni sai mu tafi. Yana faɗa ya tashi ya haura sama yana jin yadda take masa ƙorafin idan ya daɗe zata tafi ne abunta. Yau yake so ya je har cikin gidan su Sara da yaje har sau uku amma yana samun gidan a rufe, da yayi tunanin ko sun tashi ne amma zuwansa na jiya wani yaro ya tabbatar masa da cewar suna nan basu tafi ba. Hakan yasa yau yaci alwashin ko haurawa ne sai yayi, idan ma ya tarar da iyayen nata a gidan duk yaci uwarsu in ma sune suka hana ta fitowa 
Dukda kuwa bai gama warkewa ba amma yana jin zai iya karawa da iyayen Sara muddin ya samu suna cutar da ita. Tana tsaye tana ta ɓata rai Ummu ta sauƙo ta na tambayar ta me ta tsaya yi. Ta sanar mata da cewar Ya Ziyach take jira. Ummu ta ce "Kin kama hanya kin tafi ko sai na zo na bige ki a gurin, bashi da lafiya ɗin ne zai fita da shegen iya yi irin naki. Tana cikin faɗan Ziyach ya sauƙo cikin shigar sa ta korayen kaya ƙanana, kallo ɗaya yayiwa Ummu ya kawar da kai kamar bai ganta ba. Ya ce "Zo mutafi" Nadiya ta kalli Ummu sai kuma tabi bayan sa. Ummu ta bisa da kallo har suka bar palon. Dukkanin su sun iya tuƙa Mota amma babu wanda aka bari ya fara hawa har sai sun gama secondary school kaman yadda Abbu yayi musu alƙawari, hakan yasa duk inda zasu je direba ne yake kaisu wani lokaci kuma idan ƴan rashin jin suna nan sai wani ya saci hanya ya fita da wata motar, ko kuma suje su ɗaki motar uncle Abdul a gida. A kwai ranar da Ziyach ya saci motar Abba ya je yaci karo da motar ƴan sanda, aka kama shi. Amma ko awa ɗaya baiyi ba Alhaji Alpah yazo ya fitar da shi. Tun daga lokacin ya daina wasa da makullayen motarsa. Ya daina ajiye wa a gurin da suka sani. Kuma ya hana uncle Abdul basu Mota.

Yana fitowa yaga mai gadi suna ta rigima da wata mata a bakin get, tana son shigowa amma ya hana ta. Hakan yasa ya ƙara gurin yana kallonta, yana son tuno gurin da ya santa. Ya kalli mai gadin ya ce "Lafiya dai ko? Mai gadin ya ce "Yau kwana na uku kenan tana zuwa wai tana neman mai gidan, nace ta faɗa min sunanta amma wai ita dole sai ta shiga. Kafin Ziyach yayi magana sai ga Hakim ya shigo gidan a kan Keke. Tsayawa yayi yana kallonsu ganin yadda suka yi cirko-cirko. Ziyach ya kalli matar ya ce "lafiya dai ko? Matar da take ta kallonsa kamar tayi kuka ta ce "Dan Allah nice mai abincin da ka siyawa wannan yarinyar har muka ɗan samu damuwa, to shine har yau abincina baya dafuwa, shine aka ce min wai kai ɗan biyu ne nazo na baka hakuri. Tana rufe baki kuna ta kalli Hakim. Ganin a kwai bandeji a wuyan Ziyach ne yasa ta dawo gurin Hakim ta ce "Yauwa kaman wannan ne ko, domin ranar babu wannan abun wuyan na wannan, dan Allah kayi hakuri na tuba. Ta karasa tana rusinawa a gaban keken Hakim. Hakim ya kalli Ziyach ya ce "Kaine? Ziyach ya ce "Ba kince min ke ma shegiya bace, to sai kawai mu zuba mu gani ko. Matar ta dawo gurin Ziyach ta ce "Kenan dai kaine ko? To dan Allah kayi hakuri na tuba ɗan uwa ka rufa min asiri domin wannan sana'ar itace rufin asiri na. Ziyach ya tuna lokacin da ta sarara masa mari, sannan ya tuna washegarin ranar da ya koma gurin domin bawa wannan mutumin kuɗin sa sai da ta ƙarasa masa wulaƙancin. Ziyach ya ce idan har kina so na hakura sai na rama marin da kika min, kuma ni guda biyu zan miki. Yayi maganar yana nuna kumatun matar. Shi kansa mai gadi sai da ya buɗe baki. Hakim kuwa kallon Ziyach yayi yana mamakin rashin mutuncinsa, Nadiya ma da mamaki take kallonsa, matar da suka zo da mai abincin ma dai tayi mamakin jin haka domin kuwa koda bata haife shi ba to kaɗan ne. Ita kuwa matar da take jin ba iya Mari ba, ko zane ta ne zaiyi muddin zata cigaba da kasuwancin ta zata yarda. Da sauri ta ce "Na yarda. Ta faɗa tana turo masa kumatun harda share masa...📝

Love all 
One house 
Comments 
And shering 
Love my fans 
By S-Reza ✍️