Chapter 10
by @reza12
INA MUKA DOSA?
S-Reza
Page 10
A bakin ƙaton get ɗin gidan Alhaji Alpah Abdul ya tsayar da motar yana hon mai gadi taso da sauri ya buɗe musu yana ɗaga musu hannu. Har lokacin Alpah kuka yake yi Kairi kuma tana bin tsarin gidan da kallo kamar dai irin tsarin gidajen su na Saudiyya. Abdul na tsayar da motar bugun zuciyar Alpha ta ƙara gudu domin har lokacin bai daina hawaye da kuma tunanin abun da zai faru a gidan ba. Haka ya sauƙa ya zagayo ya buɗewa Katii sannan ya kama hannunta da take ta kalle-kalle fuskar nan a haɗe babu sauƙi. A haka suka shiga cikin palon gidan wanda babu kowa a ciki. Guri ya nunawa Katii ta zauna tana cigaba da kallon palon da yayi tsit kamar babu kowa, a ranta tana tunanin matar gidan ba, ko basu san da zuwan su bane ganin ko tarɓa basu samu a gurin kowa ba. Alpha ya taimakawa Abdul suka shigar da kayan nssu sashen da aka tanadar musu. Tun daga nesa Katii take ta kallon Abdul da Alpha da suke nufo gurin da suke. Suna zuwa kuwa kafin suyi magana Katii ta ce "Shi wannan da kake bari yana shigo maka har gida shi ɗin waye? Ina ce shi ɗin direba kawai amma shine kake bari yake shigo maka har cikin gida? Katii ta faɗa da harshen larabci tana kuma cigaba da hararan Abdul ɗin. Shima Alpah cikin harshen larabcin ya bata amsa da cewar "Kati ai wannan ya zama ɗan gida a cikin wannan gidan namu, domin mun daɗe dashi tun lokacin da na fara zuwa Nigeria dashi muka haɗu kuma bashi da matsala ya taimaka mana. Kati ta sake faɗin "Kuma shine harda shigowa cikin gida da shi, to daga yau na tsayar da shiga cikin gida idan zai zo ya tsaya daga waje bai dace ƙato dashi yana shigowa cikin gidan matan aure ba, to kai baka kishin matar taka ne ko meye, idan ma baka yi yanzu ga Kairi nan budurwa a gidan ai bai dace ya shigo ba. Alpha da yasan za'ayi haka yayi saurin kawar da zancen da faɗin "Abdul kaje zamu yi magana zuwa anjima. Yana faɗa kuwa Abdul da yasha jinin jikinsa da wannan matar yayi hanyar waje yana aiyana yadda zama zai yiwu tsakanin wannan matar da Hakim da Ziyach a guri ɗaya. Alpha na zama Katii ta ce "Wai ina ita matar gidan ne, ko bata nan ne gida shiru kamar gidan mutuwa, babu yara babu matar gida, ko ɗan irin tarɓar nan da akewa mutane mu babu wanda muka samu kaman wasu mabarata, ko dai baka sanar dasu zuwan namu bane?. Lokaci ɗaya cikin Alpha ya juya da sauri ya ce "Yaran basu dawo daga school ba ne, ita kuma Laila bata jin daɗi ne tana ɗaki a kwance tun jiya ko tashi bata iya yi, kuzo na nuna muku sashen naku Katii. Ya karasa yana nuna musu hanya. Yana gaba suna binsa har sashen nasu, ya nuna wa Katii ɗakinta da an saka komai na buƙata sannan ya nunawa Kairi itama nata. Sai da ya fito kuma ya fara tunanin ko ruwa fa ba'a basu ba bare kuma ayi batun abinci. Da sauri ya ɗauki waya ya kira uncle Abdul ya sanar da shi irin abincin da zai kawo musu ya ce ya sayo da yawa harda yaran domin dai yasan Laila batayi girki ba. Yana sauke wayar ya fara tunanin dole nefa sai an samo masu aiki a gidan nan.
*SARA*
Kallonta Mommy kawai take yi tun ɗazu da ta shigo ganin sai farin ciki take yi tana ta sakin murmushi ita ɗaya. Bata ce mata komai ba har lokacin da suka gama cin abincin dare wanda Mommy ɗin ta girka kudu domin kawai ta faranta wa ƴar tata. Suna zaune suna kallo Mommy ta tsayar da kallon ta dawo kusa da ita ta ce "Sara kina son zama dani ko kuma na komar dake gurin ubanki?" Sara da gabanta ya doka da sauri jin abun da Mommy take faɗa. Ita da take murna ta samu sauyin rayuwa sai kuma azo mata da batun zuwa gurin Daddy da tasan baya sonta, ita yanzu ai ta gama samun gata wanda bata jin zata iya yarda ta bar nan. Da sauri ta shiga girgiza kai har ta fara ƙoƙarin sakin kuka. Mommy ta ce "Ok ya isa tsaya kiji ni da kyau. Nasan ke yarinya ce ba Laila ki gane abun da nake nufi ba, amma muddin kina son zama tare dani to kimin alƙawarin komai na saka ki zakiyi? Mommy ta faɗa tana hango irin maƙudan kuɗaɗen da zata samu tare da ƴar tata. Ta ce "Yes Mommy ai promis Zanyi komai idan kika saka ni. Ta faɗa tana jin cewar zata iya yin komai ɗin da zata saka ta, zatayi muddin zata cigaba da ganin irin wannan soyayyar da take gani daga gurin uwar tata da ta rasa tun tuni. Mommy ta jawota jikinta tana bubbuga bayanta. Sun dan daɗe a haka kafin Mommy ta rakata har cikin ɗakin ta ta kwantar da ita ta rufo mata ƙofar. Tana fita Sara ta sauke ajiyar zuciya ta lumshe ido tana ta tunanin ko mai Mommy ɗin take son sata zatayi idan har ba gurin Daddy zata turata ba, kuma idan har ba korar ta zatayi ba. A haka barci yayi gaba da ita.
Washegari kuwa sai ga Mommy da kayan sakawa na kanti masu kyau da yawa irin dai na yaran masu kuɗi, sosai mommy ta saka ta sai da ta gwada dukkanninsu taga yadda sukai mata a jiki. Wasu riga da wando wasu kuma riga da sket da dogoyen rigunan. Sara dai baki yaƙi rufuwa ana ta murna. Mommy ta nuna mata wasu riga da wando tace idan tayi wanka ta saka zasu je wani guri. Da sauri Sara ta faɗa jikin Mommy fadin thank you so much mommy. Misalin ƙarfe huɗu na yamma Mommy ta gama shiryawa cikin shigar riga da sket ɗan ƙarami wanda bai gama kaiwa guiwa ba, gashin dokin nan har gadon baya, ta ci uban wani taƙalmi mai tsini. Lokacin da ta iso ɗakin Sara har itama ta gama shiryawa cikin kayan da suka matseta sosai, ga ƴan albarkacin ƙirjin nan sun fito waje abun su, wanda kallo ɗaya za kai mata ka gane yanzu ta fara fitar dasu. Koda Mommy tayi ido biyu da ƴar tata su ta fara hangowa sannan ga gashin Sara ɗin da shima kawai abun kallo ne. Bata san lokacin da ta saki murmushin nasara ba, tana jin komai ya zo mata karshe. Sai da ta ƙara gyra ta sosai ta shafa mata blue ɗin janbaki wanda yayi daidai da rigar jikinta. Sosai Sara ta fito wata kyuti da ita kamar ka sace ta ka gudu. Keke napep suka shiga bayan ta sanar dashi gurin da zai kai su. Suna tafiya tana aiyana daga yau ta daina hawa abun hawa na haya. Suna sauƙa ta basa kuɗinsa sannan ta riƙe hannun Sara suka fara tafiya. Waya ta ɗako tayi kira sanan ta mayar da ita cikin jaka suka ci-gaba da tafiya. A jikin wani ƙaramin gida suka tsaya minti ɗaya aka buɗe musu get suka shiga.
Tun daga nesa mutumin ya kafe Sara da kallo har sai da ya miƙe tsaye ba tare da ya san yayi hakan ba. Mommy tayi murmushi tana kwllonsa. Sara tayi saurin faɗin "Good evening uncle" ta faɗa tana bin bayan uwarta ganin har tayi kanta gurin zama. Mutumin da bai ma ji mai tace ba sai kallonta da yake tayi, domin sai yake ganin ta zarce yadda ma ya ganta a hoto, gata masha Allah irin yaran da yake so kanana. Mommy ta ce "Hi are you okay?" Da sauri ya dawo daga kallon tv da ya tafi ya amsa a rikice. "Amm umm yes yes yes I'm okay welcome. Ya faɗa yana kwallon Mommy da ta kashe masa ido ɗaya ganin dai ciniki ya faɗa. Ya sauke ajiyar zuciya ya ce "Dother ya kike ya school? Sara ta Mommy tace mata duk abinda da yace kawai ta ce eh, kuma karta sake ta ɓata masa, hakan yasa ta amsa da lafiya. Mommy ta ce "To yaya small or macho? Da sauri ya amsa da nomarl. Mommy ta mika masa hannu sai ya tashi ya shige ciki itama ta bi bayansa. Sun ɗauki a ƙalla awa ɗaya kafin suka fito tare. Mutun mai suna Fita ya kalli Sara ya ce "My Dother tashi mu tafi ko? Sara ta miƙe tsaye suka kama hanya su ukun hannunta na cikin nasa da yake ta murzawa, Mommy sai murmushi take yi jin tayi kasuwa. Sai da ya fara biya dasu shopping suka siya abun da suke so, yasa Sara ta siya kayan ciye-ciye da na shaye-shsye da dai abubuwan wasa da yawa, harda siyawa Ziyach nasa domin komai take yi yana ranta. Haka suna tafiya yana mata wasa duk dan ta samu sakewa da shi, ai kuwa lokaci ɗaya ta sake dashi tana ta faman dariya domin ita duk wanda ya nuna mata so ai ya zama masoyi. Daga nan gurin sayar da motoci ya kaisu ya cika mata alƙawarin da yayi mata, ta tsaɓi mota wacce take so ya saya mata sannan ya raka su har unguwar su. Sosai mommy da Sara suke ta murna da irin wannan abun arziki bayan sun huta ne Mommy ta ce "Sara kin ga uncle Fita yana da kirki ko? Sara tayi dariya ta ce "Sosai kuwa Mommy yana da kirki kuma yana sona ba kamar Daddy ba. Mommy tayi dariya tana faɗin "Ai shi ne yasa nima na daina miki faɗa ya ce min na jawoki jiki na daina dukanki, dafa har gidan sa yace zai komar dake amma nace ai ba zaki yarda ba, ya ce to shi dai idan har na cigaba da dukanki zai zo har nan gida ya tafi dake. Sara da taji wani irin daɗi ta ce "Allasarki uncle ashe yana sona har hakw. Mommy ta ce "Sosai ma, mutumin da yanzu haka da muka je gidan sa yana ta damuna akan na bar masa ke a gidansa, amma dai nace ba yanzu ba tukuna. Sara tayi dariya kawai. Mommy ta sake faɗin "Amma ke idan yace ki koma gidan sa da zama zaki koma kuwa? Sara da sauri ta ce "Eh Mommy zanje ai shima yana sona zanje wallhi.
*GIDAN ALPAH*
Yauma tun daga school ta haɗo su, babu yadda dreban nasu bayi dasu akan suyi haƙuri ba amma kowa na ƙara kuzarin mayar da martani, hakan yasa yaja baki yayi gum. Ita kanta Nadiya har ta gaji. Suna sauƙq Ziyach ya ce "Ai ba zaka taɓa bani mamaki ba har sai ka nemo gurin da take ka daketa shine zan san ka cika ɗan taurin kai, Wallhi da sai na nuna maka kai ƙaramin mara kunya ne. Hakim dake binsa a baya ya ce "Ai unguwar da take zaka nuna min kaga aiki da cikawa, wallhi sai na kakkaryata a gaban ubanta ma ba kai ba, ina ma baka haƙuri kana faɗin idan na sake nata magana sai naga abun da zaka yi, to mai zakayi ita ɗin ƙarwar uwarka ce, ko wani abun kuka haɗa da ita. Ziyach ya juyo a zuciye ya ce "To kai ɗin ƙanwar uwarka ce ko ta ubanka. A haka suka shiga cikin palon kowa yayi hanyar ɗakin sa ana cigaba da zage-zage. Nadiya ce ta fara Sakkwato bayan ta cire kayan school tasa na gida kuma tayi wanka, ta nufo gurin cin abinci wanda tun daga nesa ta hango Katii da Kairi. Hakan yasa kallo ɗaya tayi musu ta koma sama dakin Mommy da gudu domin jin ƙarin bayani. Hakim ne ya nufo gurin shima yana danna waya sanye da gajeren wando da senglet yana baza ƙamshi. Sai da yazo kusa dasu sannan ya kula da mutane a gurin. Da sauri ya ƙaraso gurin yana zuwa ya ce "Ke suwaye ku? Daga ina kuke da zaku shigo har cikin gidan mutane ku zauna? Baku da hankali ne? Ya jera musu tambayoyin yana kuma binsu da wani irin kallon wulaƙanci da raini da rashin Kunya. Shi har ga Allah ya ma manta da batun zuwan su Katii hakan yasa ganin sun yi shiru suna kwllonsa ya ce "Ba magana nake muku bane dan uwarku?. Sai a lokacin Kairi ta ce "Kai ɗan uban waye, baka da tarbiyya ne, ko mu ɗin sa'an yenka ne da har kake zagin mu? Kafin ta gama rufe baki Hakim da ya gano ko suwa ya ce "Oo ok kune Su Katii ɗin da Daddy yace zaku zo kenan, ashe dai kunzo ko? To Wallhi bari kuji baku isa ku zauna a wannan gidan ba, domin Bama bukatar ku, dan haka tun wuri ku haɗa kayanku ku bar mana gida kafin na fitar daku ta dole. Ya faɗa yana zama a gurin abun sa, kuma yana jin cewar ko me zai faru sai sun bar wannan gidan domin shi dama haka yake baya son mutane sam. Kairi ta kalli Katii da take ta kallon Hakim ta ma kasa magana, domin mamaki take yi, wai wannan ɗin ɗan gidan Alpah ne. Hakim da yaji basu ce komai ba ya sake mikewa tsaye ya kalli Katii da take ta tsaye har lokacin ya ce "Nasan kece Katii domin naga kinfi tsufa sosai, dan haka ki kama hannun wannan yarinyar taki ku bar wannan gidan ko kuma na fitar dak..." Ai Kafin ya rufe baki Katii ta ɗauke fuskarsa da mari, sannan ta ƙara masa ta sake ƙara masa afusace har wani irin zaro ido waje take yi, wanda hakan yayi daidai da sakkowar Ummu da Nadiya a tare suna kallon abun da ke faruwa. Katii ta ɗora da faɗin "Kai yaro ka shiga hankalinka, ni ba abokiyar wasan ka ba ce, ka tambayi shi uban naka lokacin da shima yayi tashen rashin jin sa taka masa birki nake yi bare kai majina a gurin, duka nawa kake dan uwarka da har ina matsayin mahaifiyar ubanka kake faɗa min irin wannan maganar, ko haka aka baka tarbiyya a gidan, to idan ma baka da tarbiyya ne zan saita maka zama yanzu, domin ni bana wasa da yara, ubanka na haifa kuma da shi da wanda ya haifa duk a ƙasa na suke. Tun daga nesa Ummu da take jin wani abu na rashin jin daɗi a karon farko a akan an taɓa ɗaya daga cikin yaran nata ta ce "Sai me dan kina matsayin uwar ubansa, dama kina da matsayi a gurinsa da har ya iya tafiya ya barki, ya zaɓi mace ya bar uwar tasa ne?...📝
Love all
One house
Comments
And shering
Love my fans
Ina muka dosa
By S-Reza write 📝