KAMAR DA WASA

Kamar da wasa pg 23

by @mrsomar

KAMAR DA WASA💘






                 Fatima Isa 
        (Mrs Umar)




                    Page 23



Ƙarar announcement ɗin
   “We are now descending into Mallam Aminu Kano International Airport, please fasten your seatbelts”
 Ta cika cikin jirgi.
Khalid ya juyo yana murmushi.
“Sir, looks like we’re almost there.”

Shattima ya ɗaga kai kawai, idanunsa na kallon hasken gari da ke bayyana daga taga ƙasar Kano tana da wani irin salo mai ɗaukar hankali.
Ade kuwa ya ɗan zaro wayarsa yana ɗaukar hoton ƙasa ta cikin gilashin jirgin.
Jirgin ya sauka lafiya. Bayan mintuna goma sha biyar, Shattima, Khalid da Ade suka fito daga cikin arrival gate, suna tafiya cikin nutsuwa.
Iskar safiyar Kano ta daki fuskar Shattima mai haɗi da zafin ranar arewa.
A dai-dai lokacin wayarsa ta ɗauki kira Naana ce.
Ya ɗaga cikin nutsuwa.

“Assalamu alaikum, Sir.”
Muryarta na rawa kaɗan, kamar wacce ke ƙoƙarin boye kewarsa.
“Wa’alaikumus salam, Naana. Kin tashi lafiya?”

“Alhamdulillah. Dama ina so in tabbatar ka sauka lafiya?”
Tayi shiru, sai daga baya ta ƙara da cewa:
“Yaran suna missing ɗinka tun safe.”

Ya ɗan murmusa.
“I know… ki kwantar musu da hankali. Zan kira su in mun isa Katsina.”

“To Sir, Allah ya tsare hanya.”
“Amin.”

Bayan ya kashe wayar, Khalid ya dubi agogo.
“Sir, flight ɗin Katsina sai ƙarfe 12:00 zai tashi. Muna da kusan awa biyu da rabi kafin su fara boarding.”

Shattima ya ɗan gyara tsayuwa, yana kallon mutanen dake ta shiga da fita kafin ya lumshe idanunshi can ƙasan makoshi ya ce.
“Good. We’ll rest a bit. Find somewhere quiet.”

Suka nufi wani VIP lounge da ke gefen filin jirgin. Cikin ɗakin akwai sanyi da kamshin turaren.
Ade ya zauna gefe yana duba waya, Khalid kuma ya fara duba takardun briefing.

Shattima kuwa ya zauna shiru, hannunsa na riƙe da kofin coffee da yasa aka kawo mashi, idanunsa na tafiya cikin tunani mai nisa.
Zuciyarsa ta cika da abubuwa aiki, iyali, da kuma wani abu da bai iya fassara shi ba.

Yana kallon gilashin window, yana hango jiragen da ke sauka da tashin sama, sai ya furta cikin zuciya

“Katsina... another battlefield, another chapter. Allah ya dafa mana”
  "Amin Sir"
Daga Ade har Khalid suka furta. Sai a lokacin ya gane ashe a waje ya yi magana kai ya kwantar jikin sofa da yake zaune tare da lumshe idanunshi ya yi shiru yana sauraron firar da suke Khalid na cewa Ade cikin harshen turanci.
  "Kasan su Anas har sun isa Katsina yanzu nake ganin sakonsu yanzu haka suna cikin barrack ɗin Katsina sun sauka a soldiers club kafin mu ƙarasa"
 "Gayen nan fa shege ne idan ya ɗau hanya wannan har tsoro yake bani yau motar oga ta ci gidan su dama gata sabuwa"
  "Wallahi"
Daga haka aka kawo masu abincin da sukayi  order.

*******

Bayan sati ɗaya da dawowar Papa.
Friday yau rana ce da duk idan ta kama da kuma talata matan barrack ke tururuwar zuwa cin kasuwar kutungu wasu matan ma tsabar bala'i basu da ko sisi haka zasu kwashi kafarsu suje yawan cin kasuwa ko su gano gari su dawo.
Ummie ta samu kuɗi ta yi sa'a wani yayanta dake aiki Abuja kawu Musa ya aiko mata dasu duk da ba tambayar shi tayi ba tasan ya samu labarin halin da take ciki. Ta ce naje na tsinto mana wasu abubuwan kayan abinci kafin muga abinda Allah za yi.
Tashi na yi naje na yi wanka na saka abaya baka mai ratsin ja na ɗan nada veil ɗina akai fuskata sam babu kwalliya ko kaɗan sai ɗan lip gloss dana saka sai ko maiko bakin yake.
  "Jannat kije da Ahmad ya kamata ace kina bashi mashin ɗin nan yana ja saboda kinga tafiya zaki yi ko da wane lokaci kinga idan babu ke shine zai dinga zuwa min aika"
 Baki na turo saboda dama banaso naje ni ɗaya sai in biyawa Yusuf muje tare nace.
 "Ummie wannan wawan yaron naki kullum ana koya mashi abu amma sam kwanyarshi bata ɗauka wallahi haushi yake bani"
  Murmushi ta yi a hankali ta ce.
 "Allah ya shirye ki naji dai duk da haka kuje tare"
Babu yanda na iya haka muka fita tamkar wadda ba'a taɓa gani ba matan layin mu suka min chaaa da ido kamar mayu.

**

Ƙarar announcement ta sake tashi a cikin filin jirgin.
  “Attention please, passengers traveling to Katsina on Flight NAF-204, boarding will commence in ten minutes.”

Khalid ya miƙe yana duban Shattima.
“Sir, sun fara kiran mu.”

Shattima ya ɗaga kai daga takardun da yake dubawa, ya ce cikin nutsuwa,
“Alright, let’s move.”

A haka suka nufi ƙofar departure gate, Ade yana tafe a bayansu cikin farar riga da jaka a hannu. Bayan mintuna kaɗan suka shiga cikin shuttle bus ɗin da zata kai su bakin jirgin.
Iskar Kano ta busa a hankali, tana ɗauke da ƙurar da ta haɗu da zafin rana.
A cikin jirgin, komai shiru ne. Khalid ya ɗauki kujera kusa da taga, Ade a gaba, yayin da Shattima ya zauna a waje me ɗan nisa kadan.
Yana sauke numfashi a hankali yayin da injin jirgin ya fara yin ƙara

   “This is your captain speaking. We are now cleared for take-off to Katsina. Estimated flight time: forty-five minutes.”

Jirgin ya fara motsi a hankali, ya tashi cikin iska.
Shattima ya rufe idanunsa, yana jin yadda zuciyarsa ke ɗan bugawa cikin yanayi na shiru da tunani.
Bayan mintuna arba’in da uku, jirgin ya fara sauka a filin jirgin sama na marigayi Umaru Musa 'yar'aduwa Katsina.
Yanayin ƙasar ya bambanta da na Lagos iska mai zafi, cike da ƙamshin ƙasa.

Lokacin da suka fito daga cikin jirgi, Anas ya karɓe su da gaisuwa.
“Good afternoon, Sir! Welcome to Katsina base.”

Shattima ya ɗan gyara tsayuwa, ya ce,

“Thank you, drivern zamani da fatan ba aci uban motata ba dan wannan karon in kayi min ɓarna a cikin albashinka na shekara goma zan cire”
  "Dariya suka yi. Anas ya sosa kai cike da girmamawa ya ce.
  "Sir ni na isa motar da ko wata bata yi ba zan fara bata matsala lafiya qlau muka iso"
 "Alhamdulillah"
Agogon hannun shi ya duba yaga 1:30 saboda sun dan ɓata lokaci kafin suka sauko a hankali ya ce wa  Anas.
  "Drivern zamani ƙarfe nawa suke Sallah a barrack dan nasan ka zama ɗan gari"
 "Sir ƙarfe 2 naji ance Imam ɗin ke tayarwa"
  "Ok zamu iya zuwa can mu yi sallah idan yaso sai mu huta, kai kuma Ade idan muka je sai ka wuce officers mess ka huta kada ka jira mu"
  "Ok Sir" 

Khalid da Ade suka bi shi, suka shiga motar Hilux mai ɗauke da tambarin Nigerian Army.
Tafiyar zuwa barikin soja ba ta kai mintuna goma sha biyar ba.
Shattima yana kallo ta taga yadda garin yake komi cikin natsuwa sai garin ya burge shi saboda babu yawan cunkoso kamar sauran garuruwa.
Sai ya sauke numfashi yana furtawa a cikin zuciyarsa
 “Katsina..."
Tun a bakin gate yaga tabbas wannan barrack ta bambanta da sauran barracks ɗin daya sani. 
Ganin motar da tambarin soja a jiki kawai aka basu hanya suka wuce..
 
**

Tunda muka taho nake wa Ahmad bala'i saboda irin yadda yake tuka mashin ɗin sam hannunshi bai nuna ba.
Bala'i da nake mashi ne haɗi da tsawa ya sake ruɗashi sai da muka zo daidai kwanar da zata sadaka da officers quarters muna dab da zuwa bakin get wata farar mota katuwa sai ɗaukar ido take ta taho a guje shi kuma Ahmad wajenta kawai yake nufa damu.
  "Baka da hankali ne dan ubank.."

Tsawar dana daka mashi ce ta tsorata shi ya nufi cikin ƙatuwa kwata damu ai basan lokacin dana buga tsalle ba na yi gefe shi kuma daga shi har mashin ɗin suka faɗa a cikin.
  "Birki Anas ya taka a lokaci ɗaya yana faɗin"
  "Ya Allah.."
 Sai a lokacin Shattima ya ɗago kanshi a kan wayar da yake dannawa. Idanunshi suka sauka a kan kyakkyawar fuskar Jannat sai faman zabgawa Ahmad harara take da yake ta ihun neman agaji.
Da sauri Anas da Khalid suka fito suna faɗin.
 "Ya Salam yaron fa kamar yaji ciwo ya kasa fitowa"
  A hankali shima Shattima ya buɗe marfin motar ya fito a tsaya daga jikin motar tare da harɗe ƙafafunshi hannuwanshi sake cikin aljihunshi fuskarshi sanye cikin bakin glass sam baka iya ganin kwayar idonshi.
  "Wallahi Ahmad ko kayi min shiru a wajen nan ko naci ubaka to wayace ka fadawa Ummie zaka ja mashin ɗin ba duk tsabar munafunci bane irin naka shege da katon kanshi a wajen"  
 Ido ya lumshe saboda yadda take zuba masifa baji ba gani"
Cikin ɓacin rai Anas ya ce.
  "Ke wace irin yarinya ce kina ganin yaro yaji ciwo kuma kina mashi masifa"
 Harara ta watsa mashi haɗi da ɗan murguda baki kaɗan ta ce.
  "Ai ɗan uwana ne ba naka ba ko? To ina ma ruwanku damu waya gayyace ku?"
Ya buɗe baki zai bata amsa muryar Shattima ta ratsa wajen....



Alhmdullih a nan na kawo karshen free page na wannan book mai son ci gaban sa zai iya biyan kuɗi kai tsaye ta wannan account 0169285831 Fatima umar GT bank. Ko kuma katin waya *** a kan kuɗi 500. Sannan kuma akwai vip wanda zaku dinga samu page 3 a rana a can 1k zaku iya tura min shaidar biya ta akwatin Whatsapp ɗina kamar haka *** 

#Makirci
#Soyayya
#Son zuciya 
#Yaudara
#Bemty