7
by @rufaidaumar
ALWASHI
32
Rufaida Umar
***
MAMAN MEENAT SUPPLEMENT/SKIN CARE
Yar uwa muna saida kowanne irin supplement na gyaran jiki wanda zaisaki fito fes kamar sabuwar Amarya, yar uwa shin kurajene suka dameki, ko matsalolin jikine kamarsu rama, ko kibace tayi miki yawa kikeso ki rage, bushewar fata ko karancin ni'ima ko budewa ne ko infection? Ko kuma so kikeyi fatarki tayi laushi ki dinga sheki kina haskawa wato kalar madara dai Haj to ki garzago
Yan uwa kusani duk wani supplement da zamu kawo muku sai munyi bincike mun tabbatar da ingancinshi, mun kuma tabbatar da cewa bashi da wata illa ga lfy
Akwai masu cewa sunsha supplement amma har yanzu basuga wani canji ba, to yar uwa kodai an baki fake ko kuma ba'a baki wanda ya dace dakeba, kokuma bakisha yadda ya dace ba, kisani yar uwa kafin ki fara shan supplement akwai ka'idoji daya kamata ace kin kiyaye kuma kin kula dasu matukar kinaso suyi miki aiki yadda ya kamata kuma cikin sauki ***
1. Akwai Supplements na gyaran jiki ciki da waje, munada set na uwargida dana Amare da masu jego
Sannan ga wadanda sokeso jikinsu yayi kyau sosai amma basa son susha supplement to albishirinku muna da kowanne irin mai na gyaran jiki da kuke bukata irinsu lotion, cream, soap, scrubs, face Cream,sun screen, serums concentrate, hair oil, hair cream face mask etc
Muna saida duk wasu nau'in supplement Lotion da kuke bukata, sannan Maman Meenat collection ba anan kadai ta tsaya ba muna saida turaruka kowanne irin na wuta dana jiki, da Airfreshners da air wick, sayen daya ko sari ke dai kawai neme ni a wannan number ***
***
Na'eem wanda tun soma wayar Laila yake tsaye daga gefe don ba ta ma ji shigowarsa ba, shi kuma bai ce uffan ba balle ya yi sallama wanda hakan shi ya hana Laila ankara da shigowar wani falon. Mamaki ne tsantsa da kuma ƙullewar kai suka kama shi lokaci guda, wani irin kallo kawai yake watsawa Laila amma uffan ya kasa cewa. Ita kuma sai ta yi azamar saita yanayin fuskarta ga kirjinta na bugu da sauri-sauri, kar fa Na'eem ya ɓata mata wasan. Kar a je ya ji komai din kamar yadda ta karanta ya ji ɗin wanda hakan bai ɓuya ba a saman fuskarsa. Ita kuwa me za ta yi idan burinta na tsawon lokacin nan ya rushe sanadin Na'eem? Don ta sani matuƙar Uncle Hashimu mahaifinsa zai ji ko kuma Baba Tsoho, to fa kamar Mama ta ji ne. Jin wadannan iyayen nata kuwa na nufin rushewar dukkan shirinta.
Ya ƙaraso cikin falon sosai, ita kuwa kamar an tura ta haka ta koma mazauninta ta zauna. Kauda kai ta yi gami da daure fuska ganin har a lokacin da yake zama nesa da ita kaɗan saman kujera bai bar jifanta da kallon tuhuma ba.
"Lafiya?" Ta yi tambayar cike da dakiya a ƙoƙarinta na nannaɗe tabarmar kunya.
"Na ji komai fa Sis, na ji duk abin da kuke shiryawa ke da matar da ku ka gama waya yanzu. Sai dai kaina ya ƙulle, tana ambatonki da Sameera, please ki fidda ni duhu don na kasa gasƙata abin da na ji mai kama da almara."
'Ta faru ta ƙare.' Cewar Laila a ƙasan ranta. Nan ma cikin dakiya ta yi shiru tana wasa da wayar hannunta.
"Sis ki..."
"Ka yi min alƙawarin komai zan faɗamaka zai kasance kawai tsakaninmu? Babu wani mahaluƙin da za ka sanarwa?"
Kansa tsaye ya gyaɗa mata kai.
"I promise you babu wanda zai ji."
Nan ta sauke ajiyar zuciya, ta ɗauko masa tarihi tun daga asalin abin da ya faru ga Sameera, rufe sun da suka yi na cewa mijin Sameerar mutuwa ya yi kafin ita da ma duka dai abinda take shiryawa a yanzun.
Na'eem idanunsa suka kaɗa jajir, tsananin tausayin Sameera ya ji ya mamaye sa. Bai taɓa hasaso hakan ba koda wasa duk da cewa yana son sanin waye mahaifin Haidar din tun ba yanzu ba, sai dai kuma fyaɗe? Bai taɓa hasashe ba. Wane irin baƙin ciki Alh Sada da ahalinsa suka ɗanɗanawa bayin Allahn nan haka? Allah kadai ya san yanayin da suka tsinci kansu a lokacin da babu wani dangi na kusa tattare da su sai su ukun kawai.
"Innalillahi wa inna ilaihir raaji'un!"
Ya furta a fili cike da wani ɗaci a saman harshensa. Laila kuwa ɗan murmushi ta yi mai ciwo don zuwa lokacin abin ma ya rage sanya ta kuka.
"Ka ji komai ake ciki Na'eem, wannan shi ne mission dina. Auren Areef, rusa rayuwarsa da ta mahaifansa. Waɗannan abubuwan ne kaɗai idan na yi zan samu relief, zan kuma iya facing tawa rayuwar. A yanzu koda na ce zan watsar da komai na manta, wallahi Na'eem i can't. Na sani ba zai taɓa yiwuwa ba. Ba zan iya tunanin kaina ba face na aiwatar da aikin da na sa a gaba. Ina fatan za ka kasance tare da ni a wannan shirin nawa tunda yanzun dole ta saka you are part of it. Na faɗamaka ban da su mutanen nan da kuma Zakiyya babu wanda ya sani. So please."
Ta ƙarashe tana kallonsa cike da wani irin rauni, ɗan murmushi ya saki duk da tarin damuwar da ke bayyane a saman fuskarsa.
"Don't worry my Sis, I'm with you, and I won't say a word. Let's make them pay tunda su din kansu kaɗai suka sani."
Tare suka ƙara sakarwa juna murmushi, ta sauke ajiyar zuciyar samun nutsuwa. Wayarta ta buɗe, saƙonnin da Hajja ta ce za ta aikomata wanda ta tura wa Areef da kuma amsar da shi kansa Areef din ya turo duka su ta ci karo da su sun faɗo. Ta karanta tiryan-tiryan sannan ta mikawa Na'eem shi ma ya karanta.
"Good, matar ta iya takunta. Ta tsara komai ya tafi daidai, to amma wane sharaɗi ne za ki gindaya kafin auren? A ture duka wannan, ta ya ya za ki ɓullowa iyayenmu batun aurenki? Mama might be the toughest one to convince." (Mama ce za'a fi wahala a shawo kanta)
Laila ta jinjina kai.
"Shiyasa ba zan bayyana musu ko waye shi ba yanzu."
"Kina nufin za ki yi auri ne ba tare da saninsu ba?"
"Ba tare dai da sanin ainahin fuskar wanda zan aura din ba. Sai dai wani daban."
"But why? Na yi zaton ko Mama ba ta san shi ba. Ko saboda sunan mahaifinsa da yake sananne a can?"
Cikin yanayin damuwa Laila ta girgiza kai kafin ta karɓi wayarta a hannunta ta hau dannawa, lokaci guda ta ƙara miƙa masa gami da fadin.
"Ga kuma wani dalilin nan."
Na'eem ya dube ta sannan ya kai duba ga fuskar Areef da ya bayyana cikin hoton.
"Ya Allah, fuskar Haidar nake gani."
Ba tare da ta kalli hoton ba ta yamutsa fuska tana jin zuciyarta na mata wani iri babu dadi ta ce.
"Areef kenan. Haidar's Father. Ina fatan ka fahimce ni yanzu?"
"Sosai na fahimceki. Faɗa min yadda shirin naki zai kasance idan da shawara sai na ba ki."
Nan ta kwashe duk yadda suka yanke ita da Zakiyya a waya ta sanar masa, ya yi na'am da hakan. Ya kuma ƙara mata da wasu shawarwarin da ta ji dadinsu kwarai. Sun jima a nan dai har ba su san lokaci ya ja haka ba sai da suka ji an soma kiraye-kirayen sallar la'asar. Nan ne kuma suka miƙe, ta yi ɗaki yayin da ya fice.
***
Washegari da asubar fari Na'eem ya yi musu sallama ya fice. Bacci ya hana su yi masa rakiya Airport. Haka dai ya tafi, Laila na ƙara kwanaki uku a gidan ta tattara ta koma gidansu. Zuwa lokacin tuni layin da Hajja ta yi alƙawarin aikomata ya iso gareta. Ta kuwa ɗora shi a ƙaramar wayarta wanda ta fi amfani da ita wajen amsa kiran customers dinta. Ta ga saƙonnin Areef har kusan guda goma sha wanda ciki duk magiya ne da neman alfarmar ta sanar da shi inda take. Ba ta ko ji ɗarr ba don ta san tuban na muzuru ne da kuma na tsoron razanin da yake ciki na tozarta a idon duniya.
Ranar Juma'a da safe misalin sha ɗaya da rabi ta aikamasa gajeran saƙonta.
*_"Na ji duk soki burutsun da ka ke yi, sai dai idan har dagasken kake ka shirya karɓar kowane irin hukuncin da zan yanke. Ina jiranka gobe a garin Kano. Idan ka shigo ka kira ni._*
***
KATSINA
"Koma ka zauna, akwai maganar da zamu yi." Faɗin Abba kenan yana mai duban ɗan nasa wanda ke ƙoƙarin miƙewa bayan ya gaida shi a safiyar ranar ta Juma'a. Mami da ta ke kokarin maida ɗan bowl din fruitsalad a firij ta kai duba gare su, fuskarta ta ɗan sauya domin tana da masaniya a kan tambayar da Abban zai yi masa.
Shi ko Areef din zama ya gyara yana sauraron me zai fito daga bakin Abban, daidai sadda wayarsa ta yi ƙarar shigowar saƙo. Ba halinsa ne duba waya a ire-iren lokutan nan ba da wani a cikin iyayen nasa ya nemi su tattauna wani zancen. Amma a yau saboda ƙaguwa da son ganin daga inda saƙon yake. Burinsa ya kasance ita din ce, aikuwa yana dubawa ya ga sunanta na yawo saman screen din. Daidai sadda shi kuma Abba ya watso masa tambayar.
"Areef, ka faɗa min gaskiya. Mene ne ra'ayinka dangane da aurenka da yarinyar nan Kausar? Kana sonta ko kuwa dai..."
"Haba Abban ya.." Mami ta katse shi. Shi ma ya tari numfashinta a fusace ya ce,
"Tashi ki bar ni da ɗana Salma, magana zamu yi."
Areef wanda ya kai aya a karanta saƙon da Sameera ta aikomasa, sai a sannan ya sauke ajiyar zuciya. Shi dai ya ji kamar Abban tambaya ya yi masa amma kuma bai fahimci kan zancen ba sai dai ya ɗago ya ji Abban na ba Mami umarnin barin falon. Aikuwa ta miƙe bayan ta watsawa Areef ɗin kallo mai kama da gargaɗi. Ya sauke kansa ƙasa, ban da abin Mami, ai ko ba ya son Kausar zai karɓe ta hannu bibbiyu don yin biyayya ga umarninta. Kuma ma tarbiyyar Kausar din ta bambanta da na Nihla, da dai a ba shi Nihla matsayin matar aure ai zai gwammace Kausar ɗin don ta fi nutsuwa kuma za ta tanƙwaru.
"Game da batun yarinyar da uwarka ta zaɓarmaka ne, ina so na samu tabbaci daga bakinka kana sonta ne ko a'a? Sanin kanka ne mata ma bana yi musu dole balle kuma kai da kake namiji da ka san mene ne rayuwar duniyar ma. Da ace zan tilasta ka da yin auren, da tuni an wuce wurin na aurar da kai ga ɗiyar Alh Affan kai ma ka san da hakan. What's your decision?"
Areef da kansa ke ƙasa cike da zullumi da tunanin Sameera da ma abin da za ta zo mishi da shi na sharaɗin karɓar tubansa, sai a lokacin ya ɗan numfasa.
"Abba ba ni da matsala da auren Kausar. Allah ya sa hakan ya zame min alheri. Amma kuma Abba idan har na zo da buƙatar auren wata a can gaba, za a ba ni damar haka?"
"Ƙwarai ma kuwa Areef, ai na gama faɗamaka, ni ba na tauyewa yarana ƴancinsu na yin abin da suke so. Na yi maka alƙawarin ko yau ka kawo wata kuma ka ga za ka iya haɗa auren mata biyu ko uku lokaci guda ni Sada zan tsayamaka. Ni kaina nan gaba kaɗan sai na cike sun zama huɗu cif."
Ya ƙarashe da dariya, Areef ya murmusa yana sadda kai. Ya sani sarai Abban zai iya yin abin da ya ce ɗin. Nan suka ɗan taɓa hira kafin ya tashi ya bar falon.
Kai tsaye motarsa ya shiga da nufin fita daga gidan, ba don zuwa wajen aiki ba sai domin samarwa kai nutsuwar ƙara nazarin saƙon Sameera. Yana fita kuwa ɗan nesa da gidan sosai ya yi parking gami da duba saƙon karo na biyu. Ba tare da wani jinkiri ba ya tura mata da reply.
_"Na shiryawa duk wani hukuncinki Sameera muddin zai wanke laifina a zuciyarki. A wace rana kike son gani na? Na maki alƙawarin zan shigo garin Kano duk sadda kika buƙaci hakan da yardar Allah."_
Yana tura wa kafin ya bar wurin da mintuna goma ya ji shigowar saƙo. Da sauri ya buɗe.
_"Let's meet tomorrow at 5pm. I will send you the location. Ruwanka ne ka riƙe sirrin haɗuwarmu, tonuwar asirinka ne kuma ka sanar da wasu."_
Ya sauke ajiyar zuciya gami da ɗan murmusawa.
***
KANO
Da wuri Laila ta tashi a safiyar ranar Asabar, kasancewar Baban su Faruk na gidan ba aiki. Ita ta shirya komai na kayan kari. Kunun tsamiya ta yi da ƙosai. Haseenah ba ta gidan tun dawowarta ma daga gidan Baba Tsoho. Biki za'a yi na ɗiyar yayar Momi Fannah da suke a garin Kano. Tun ana gobe za'a soma bikin ita ta je gidan ta yi wa Amarya lalle da mutane da yawa ma. Gobe lahadi ne ɗaurin aure. Yau kuwa kamu zasu yi a wani hall da suka kama. Wannan ce hanyar da ita kuma za ta samu ta sulale ta je ga Areef su yi maganar da za su yi. Don haka ba ta da fargabar ta yadda za ta fice ba tare da an nemi jin ina ta nufa ba. Tunanin Mama ne ya yi mata dirar mikiya sa'ilin da ta ke jere kwanukan Gwaggo Samha a saman tire za ta miƙa mata ɗaki. Ko ya ya Mama za ta ji idan ta gano ƙudurinta? Ta san dai ba za ta taɓa mara mata baya ba. Ita kuwa ba ta jin za ta iya janye alwashinta. Nata farin cikin ma na rayuwa ba zai taɓa samuwa ba muddin ba ta cika burinta ba.
Koda ta dawo falon, suka ci karo da Momi Fannah sai ko su Faruk wadanda su ka yi asubancin tashi suna kallon cartoon.
"Sannu da kokari Laila. Yau wani bacci ne ya yi awon gaba da ni. Ki ce har an kin kammala ma."
Murmushi Laila ta yi, ta san gajiya ce zallah don Momi Fannah ba ta wuni a gidan tun soma shirin bikin nan, za ta iya cewa ma yayarta Yakura ita ta damƙawa komai a hannu. Don haka duk wata siyayya ta kasuwa tare Momi da Amarya Khadija suka je yi. Daidai da gyaran jikinta Momi Fannah ce ke kai ta wajen wata ƴar garinsu. Shi ɗin ma don ayyukan ne da suka yi mata yawa amma kam da ita ce za ta yi.
"Ai nasan a gajiye kike Momi. Kunun tsamiya ne da ƙosai. Ko za'a ƙara da wani abin?"
Girgiza kai Momi ta yi cike da jin dadi ta ce.
"Ke dai Allah ya miki albarka kawai. Amma hakan ya yi sosai. Bari na miƙa na Yallaɓai."
Daga haka ta ƙarasa tebur din ta ware na mijin nata da already Laila ta haɗa.
Ita kuwa Laila ɗakin Gwaggo Samha ta shige ta ajiyemata ba tare da sun gaisa ba ganin tana sallar walha. Fitowa ta yi ta sallami yaran da nasu bayan ta tabbatar sun wanke bakunansu. Daga haka ta fice zuwa ɗakinsu. Sai da ta fara da yin wanka ta ɗora alwala kafin ta fito ta zura doguwar rigar sallah itama ta yi nata nafilar. Ta ɗan jima tana addu'a dangane da lamarin da take tunkara, fatan nasara da ma zaɓi take yiwa kanta. Tare da fatan ko mene zai biyo bayan auren tsakaninta da iyayenta da yan uwa, ya zo mata da sauƙi.
Momi ba ta jira tasowar yara daga makaranta ba ta shirya ta bi Abban Faruk ya miƙa ta can gidan bikin.
Laila kuwa sai da yaran suka dawo ta shirya su tsaf, itama ta yi nata shirin cikin wata jar atamfarta mai sheƙi wanda ya ƙarawa atamfar kyau, itama ya zauna ɗabas a jikinta sai ko mayafinta da jaka da takalmi suma jajaye. Ba ta yi gigin saka ankon kamunsu ba duk da cewa Momi ta ɗinka mata, gudun kar Haseenah ta disga ta yasa amma ko Amarya Khadija suna mutunci sosai domin hatta da ƙunshin bikin ita ce ta yi mata. Bayan ita da yan gidan babu wacce ta yarda ta yiwa don cewa ta yi ba ta jin dadi, dalili kenan da yasa Momi dakatar da ƙunshin ta ce su nemi wata a bar mata diyarta ta huta.
Ƙarfe sha biyu da mintoci ta ji wayarta ta yi ƙarar shigowar saƙo. Daidai lokacin shigarta gidan Yakura kenan za ta ajiye su Faruk can kamar yanda suka yi da Momin don tace ba za su je wurin kamu ba. Bayan sun gaisa da mutanen falon ciki har da Haj Yakura mahaifiyar Amarya Khadija, ta fito barandar wurin ta buɗe saƙon.
"Assalamu alaikum, I've just arrived in Kano. Can you send me the address where I can meet you?"
Haka nan sai da ta ji faɗuwar gaba, yau za ta haɗu da mutumin da ta tsana fiye da komai a duniya, wanda ya ruguza dukkanin farin cikin rayuwarta. Makashin Sameerarta. Domin a wurinta, shi ya kashe mata yar uwa.
Ta sauke wani irin nannauyan ajiyar zuciya kamar na wacce ta ci kuka. Ganin idanunta na neman fallasa sirrin zuciyarta a bainar jama'a ne yasa ta saurin fiddo baƙin gilashinta ta saka. Hakan sai ya ƙara mata kyau na musamman duk kuwa da cewa ba kwalliya ta yi ba face man leɓe da ɗan layin da ta zizarawa leɓɓanta. Sai ko kwalli.
Madadin ta ba shi amsa sai kawai ta mayar da wayar jakarta ta koma cikin gidan ta cigaba da sabgoginta har zuwa lokacin da aka fara miƙewa domin soma shirin tafiya wurin Kamu. Cikin Haseenah da Momi babu wacce ta gani, ta bada tazarar awa biyu daga saƙon da Areef ya aikomata da ma kiran da ya yi har sau uku ba ta ɗaga ba, kafin ta miƙe ta fice daga gidan gaba ɗaya. Sai da ta ɗan yi nisa da gidan ta fito bakin titi sannan ta aikamasa da gajeran saƙo wanda kawai adireshi ne a cikinsa. Ta maida wayar cikin ƴar jakarta ta saƙale a tsintsinyar hannu. Drop ta ɗauka na abin hawa da zai kai ta har inda ta nufa, zuciyarta cike fal da addu'o'in samun juriya da ma rinjaye akan maƙiyi. Can ta tuna ba su yi magana da Hajja ba, hakan ya sa ta fiddo wayarta karo na uku ta danna mata kira. Bayan sun gaisa ne ta ce,
"Ya iso Kano, ina hanya zan je mu haɗu da shi."
Hakan kawai da ta faɗa ya ankarar da Hajja ko wane ne, muryarta dauke da wani irin sauti na farin ciki da kuma mamaki ta ce.
"Ikon Allah, Areef din? To shikenan, Sameera nasan ba sai na ce maki komai ba. Koda dai, mai rawa ya fi mai kallo sanin inda ƙafarsa ke masa ciwo. Fatan alhairi."
Laila ta yi ɗan murmushi mai ciwo gami da gyaɗa kai tamkar Hajja na gabanta, ciki ciki ta ce "Thank You."
Daga haka suka ajiye wayar.
***
*AREEF*