BABBAN GIDA

10

by @nazeefanashe

*BABBAN GIDA….*

New…..

**NAZEEFAH SABO NASHE✍🏽*

BRIGHT PENS.


**I DEDICATED THIS BOOK TO NA’IMA SULAIMAN SARAUTA.**

0803374837.


GODIYA MARA IYAKA DA JIKAR NASHE REAL FANS GROUP… hope wannan karan ma za ku karb’i Babban gida kamar yarda kuka saba karb’ar kowane irin book nawa. Na gode sosai sakamakon Aljanna gareku In sha Allah.🥰






**YOTA004**



***


10….



Gaba d’aya jama’ar gidan suka yo sashen Mommy, kowa hankalinsa tashe dafatan ba wani abu bane mai muni ya faru. Turus suka yi ganin yarda Nafisan take kwance kamar mara rai a jikinta. Mahmud ya shigo hannunsa rik’e da na Zayyad kallo guda ya yiwa Nafisa ya girgiza kansa murya a hankali ya furta “She is Alive, bata mutu ba fa.” Ba wanda bai saki ajiyar zuciya a wajen ba. Musamman sanda Mahmud ‘din ya yi hikimar zuba mata ruwa a fuska sai gashi ta kawo wani gauron numfashi ta ajiye. A hankali kuma ta ware idonta ta zube su cikin na Mahmoud da yake jin kamar tausayinta na son rinjayar zuciyarsa, sai dai idan ya tuna wacece Hajarat da munanan halayenta na b’oye sai ya ji zuciyarsa ta sare ya ji ba zai iya auren Nafeesa ba, don ba zasu bar Nanna ta zauna lafiya ba, ga Nannasa macece mai matuk’ar sanyin hali. A hankali ya janye nasa idon ya mayar da kallonsa kan wayar hannunsa, sai yaga msg ne da abokinsa ya yi describing wasu magunguna ya mik’awa Wata mai aikin gidan tare da instructing dinta ta kaiwa Driver ya nemo su. Daga haka ya saka kai zai fita daga cikin parlorn. Cikin zafin rai Mommy ta ce “Yanzu Mahmud ba zaka tausayawa halin da Nafeesa take ciki ba? Saboda kai fa ta shiga wannan halin?” Tsit wajen ya yi Hakan yasa Mahmud danne leb’ensa ya lura gaba d’aya so take ta jingina masa laifin. Don haka ya juyo yana kallonta karan farko ya fara mata irin kallon da ke bayyana mata tsananin tsanarta a idonsa, kamar yarda shima yake hango tasa tsanar a idonta…. “D’azu me kika ce? Da kanki kika furta ke kike son ha’da auren, to me yasa Nafeesa zata damu kanta a kan rashin amincewata?” Shiru ta yi tana kautar da idonta a ranta take jin wata irin tsanar duk wacce Mahmud zai kawo gidan, kuma ta yi alk’awarin za ta yi duk me yiwuwa ta hanata zaman lafiya, wannan shine kudirinta na farko. Mahmud ya saka kai ya fice Jadda ta bi bayansa. Yana shirin shiga mota ta kira shi. Jin muryar Jadda ce ya saka shi fasa shiga motar ya juyo yana k’ok’arin kawar da damuwar da take fuskarsa, ba don komai ba sai don baya son ko ka’dan ya sakata cikin damuwa. “Mu je ‘daki Auta, ina son ganinka…” murfin motar ya saki sannan ya bi bayanta cikin mutuwar jiki, a ransa yake rik’o dafatan Allah yasa ba umarni za ta bashi ya auri Nafeesa ba. 


“Me yasa ba zaka amince ka aure su su biyu ba Auta?” Jadda ta fa’da idanunta cikin na Mahmud ‘din. K’asa ya yi da kansa sosai yana jin yarda zuciyarsa take fa’da da ruhinsa da yake son tilasta masa tausayin Nafeesa. Wani b’arin zuciyarsa na hasko masa Hajarat da dükkan munanan halayenta tun baa je ko ina ba har sun fara son mallakarsa ta hanyar Asiri, ina ga nan gaba…. “Jadda, wallahi ba zan iya adalci a tsakaninsu ba, ina tsoron kuma Ubangiji ya kama ni da laifin aikata hakan shi yasa, amma idan hakan bai yi miki ba, zan yi k’ok’arin ganin ba aure…….” “A bar maganar kawai Mahmud na fahimce ka, Allah ya kawo mata nata rabon na alheri.” Mahmud ya ji wani relief a ransa ya yiwa Jadda godiya ya mik’e don fita. Jadda ta bi bayansa da dukkan addu’ointa na alheri. Sam ba zata yiwa Mahmud dole ba, koda ita ta haifeshi balle amana ne shi ‘din a wajenta. 




***Bayan Sati biyu***

Aka tura da dukiyar aure garin Bauchi, ba wani b’ata lokaci Maimartaba ya amince aka bashi auren Nanna, bayan biyan sadakinsa Saura biki na al’ada. Abinka da al’ada irin ta garin Bauchi basa saka biki Ranar biki da yawa, don haka sati hu’du kaçal aka saka bikin Nanna da Mk daidai saba’ar watan da zai kama. Nan kuwa mahaifinsa ya dinga masa tsiyar yarda ya dage sai ya riga yayansa Jabeer aure. Murmushi kawai yake saki idan Baba Alhajin ya fa’di hakan. Ya ce “Ai shi Yaya jAbeer yana nan yana jiran y’ar larabawa ta gama karatu kafin a sha nasa bikin.” 



Gab da bikin Mk ya dinga samun alhairai, ga kwangiloli da ya dinga samu daga ko Ina a fa’din k’asar nan, manyan kwangiloli na ban mamaki wanda suka sake mayar da shi matashin mai arziki. Hakanan Allah ya yi shi da zafin nema, Şam bai dogara da arzikin mahaifinsa ba, samun ku’din da yake yi akai akai, ya sake fisgar hankalin Nafeesat da Hajarat. Dangi kuwa aka dinga zuzuta cewa tabbas matar da Mahmud zai aura mai k’ashin arzikin alheri ce, kamar yarda dai canfin Malam bahaushe yake. Wannan kalma ita tafi tunzira zuciyar Hajara, bata gane komai idonta ya rufe ruf, ga Nafisa da take kwance magashiyyan, don ma tana yawan ja mata kunne akan cewa kada ta bari a gane halin da take ciki, idan ba so take idon jama’a ya dawo kansu ba, ya zama duk abinda za su aikata kowa yana hankalce da şu. Don tabbas aurenta da Mahmud babu fashi.



An gyara shiyyar amarya fes, gini na zamani mai matuk’ar da ya zarce na kowa a cikin Babban gidan. Hakan ya sake tunzira zuciyar faccalolin. Kowa ya shigo sai ya fa’di kyau da tsaruwar gidan, Mahmud fa Masters Wayewdegree yake da shi a b’angaren Zane-zane da fasalce fasalce ba dole ya zage k’wanji wajen ganin cewa taşa basirar ta zaunu a nasa gidan ba?



Wayewar garin yau, Hajarat ta tashi zuciyarta na mata wani irin zugi, musamman ganin yarda har a lokacin burinta ya gaza cika, gashi dai aikata asirin suke ka’in da Na’in, amma baya cinsa, don Zayyad da suke bawa abincin ya kai masa shi yake zuwa ya gaya masa kada ya ci an zuba abu a ciki, sai ya zama şuna aikata abu Zayyad yana warware musu ba tare da hankalinsu ya kai kan hakan ba. 


Da zafin rai ta zura Hijabinta ta nufi b’angaren matar Sani wacce ta zama itace aminiyatta ta k’ut da k’ut, musamman da bikin nan ya tashi, duk hankulansu a tashe yake ganin yarda Mk yake ta samun ku’di kusan duk ya fi mazajensu ku’di a gidan, gashi kuma zai auro Nanna yar gata kuma Yar sarauta şuna da labarin irin gatan da ake mata a gidansu. 


A zafafe ta dinga Nocking ganin k’ofar a rufe ruf. Da sauri matar gidan ta bu’de k’ofar da mamakin wanda yake mata irin wannan bugun, duk da zuciyarta ta bata Hajarah ce. Tana bu’dewa ta saki murmushi ka’dan Tana furta “Lah! Mommy ce, wallahi kin ga barci ne ya fara ‘dibata.” Hajarah ta zuba mata wani banzan kallo kafin ta furta “Rabi’a, ai ke ki ka ga barci, naga alama dükkan abin nan ni yake damu, ku ba abinda ya dameku….” Rabi’a ta ‘dan saki murmushi kafin ta furta “Me ya faru Mommyn yara?” “Me ye ma bai faru ba Rabi? Ba kya ganin wani rawar k’afa da iyayi da Jadda da Ahalinta ke yi a gidan nan, saboda zaa auro yar sarauta, koda yake naga rashin kishin kanki da ke damunki ba zai Bari ki ga aibubbukan da ni nake hangowa ba wallahi.” D’an tab’e baki Rabi’a ta yi kafin ta ce “İkon Allah, ni fa wallahi yanzu abin ya fara….” Tsaki Hajara ta yi kafin ta ce “Idan ma ya daina damunki nan gaba ka’dan zai fara damunki, saboda babu Babban tashin hankali irin Faccalarka ta zama y’ar mai mülki ko yar sarauta sarautar ma y’ar Sarki, Mhmn! Na rantse miki nan gaba ba abinda ba za’a mayar da mu a gidan nan ba, y’ay’anta su ne zasu zama jikoki abin so ga su Jadda, musamman ganin yarda Mk yanzu duniya take damawa da shi. Bayan wannan baki ga yarda ake ta zuzuta kyanta ba, ni kaina da naga hotonta sai da zuciyata ta sare yarinya kamar ita ta k’era kanta, ga wani kirari da dangin Miji ke mata wai mai k’ashin alheri, me hakan yake nufi? Mu masu k’ashin tsiya kenan ko? Muna nan da ke sai tazo  ta fi kowa matsayi a gidan nan, ni nan da kike gani na ‘daura ‘damarar zaman cutar da ita wallahi yanzu na d’ana belt, sai dai a mayar da ni baiwa a garin Bauchi, amma ba zan tab’a yarda ina gaba da ke, Mijina gaba yake da Mijinki sannan ki zo ki fi ni iko da mulki a gida na ba, duk a cikinku wanda yaga zai iya zama ya zama bawanta sai na ce Allah ya bada sa’a. Tunda na lura kamar abin ni ka’dai ya fi dama, don haka ni kin ga tafiyata….” Da sauri Rab’ia ta rik’o hannun ta tana murmushi dama haka take ita fuska biyu gareta da wuya ka gane halinta, a zahiri mace mai sanyin hali amma a ba’dini munafuka ce da son ha’da husuma ta gaske. “Mommy kenan! Ni yanzu ce miki aka yi zama zan yi ina kallo ta shigo ta fi mu nuna isa da mulki, ke dai kawai je ki sai gobe akwai wani shiri da nake shiryawa.” Nan fa suka tafa hannu suka tintsire da dariya, Hajara ta fita da farin ciki da murnar samun kan Rabi’a. Haka ta bi ta zige sauran matan gidan., ta hanyar siyasa.


Kana shiga gidan zai sake baka sha’awa ganin yarda aka sake k’awata shi da kayan Baffi furniture gida sai walwali yake, duk inda Mk ya saka k’afa Zayyad  yana biye da shi. Tunda aka fara bikin kuwa kaya iri d’aya suke sawa da Niece d’in nasa hatta d’inki da hula iri guda ake musu. Haka aka sha Biki aka kawo amarya daga Bauchi bayan ta huta aka isa da ita sashen Jadda, ita da Baba Alhaji suka mata tarba ta musamman kafin su yi umarnin a zagaye da ita sashen y’an uwanta faccalolinta.


Da sauri y’ar rahoton Hajarah ta je ta gaya mata ga masu kawo amarya nan za su shigo sashenta. Wani murmushi Hajara ta saki kafin ta kalli k’awarta ta furta “Make sure kin turare kan amaryar nan da sinadarin nan, ki tabbata ta shak’i k’amshin sosai….” Sakina ta jijjiga kai alamar ta gane, suka gyara zamansu jin gu’dar y’an kai amarya a zuciyar Mommy Hajara ta furta “Barka da shigowa gidan da zai zame miki gidan dana sani da bak’in ciki, ke dai jin da’di kun yi hannun Riga Nanna…..


Zayyad da duk ya ji abinda suka tauna kafin ahigowar Amaryar ya yi saurin shiga bedroom ‘d’insa ya zaro Ipad d’in da Mk ya bashi saboda irin haka ba tare da kowa ya san akwai layi a ciki ba. Mk da sauri ya matsa daga cikin jama’a gayyar abokansa da suke ta masa tsiya ya kara wayar a kunnensa yana furta “Ya aka yi Kiddo?”  Zayyad ya saki ajiyar zuciya kafin ya furta “They planned something bad….. Ina ji ana cewa a yiwa Aunt Amarya turare idan an shiga da ita part ‘din mu….” Mahmud ya ji kansa ya sara a ransa ya fara tunanin “Yanzu me zan yi na kare Nanna daga sharrin Matar nan? Innalillahi wa inna ilaihirrajiuna if something bad happens to her me zan ce ma iyayenta… “Uncle say something, ni Yanzu ba zan iya canja abin ba, ban san menene za su saka mata ba….”  Mk runtse idonsa kawai ya yi shi kansa a lokacin bai san menene mafita ba…..




'Yan uwa 
Barkanku da zuwa FAMAS SCENTS OF LEGENDS,
duniyar turarukan wuta masu kamshi na musamman mai samar da nutsuwa da kwanciyar hankali.
Mun tanadar muku da turarukan wuta masu dadin kamshi kamar su
Sandal flakes
Hawee
Gabgab
Halut
Dorot 
Coconut chips
Dufr(farce)
Black khumra
Brown khumra
White khumra 
Oil perfumes da 
Body sprays
Dan turara gidajenku,tufafinku da jikinku.
Ga duk mai buqata zai iya tuntuban mu ta lamba kamar haka
Call/WhatsApp 
***
Location:Gonan Ganye,zaria
Kaduna state 
Nationwide Delivery.


JIKAR NASHE✍🏽