BABBAN GIDA

12

by @nazeefanashe

*BABBAN GIDA….*

New…..

**NAZEEFAH SABO NASHE✍🏽*

BRIGHT PENS.


**I DEDICATED THIS BOOK TO NA’IMA SULAIMAN SARAUTA.**

0803374837.


GODIYA MARA IYAKA DA JIKAR NASHE REAL FANS GROUP… hope wannan karan ma za ku karb’i Babban gida kamar yarda kuka saba karb’ar kowane irin book nawa. Na gode sosai sakamakon Aljanna gareku In sha Allah.🥰



**YOTA004**


***


12.



Da sauri suka fice daga gidan, Zayyad yana d’aki duk hankalinsa a tashe. A kwance suka sameta saman gado jikinta idan banda rawa ba abinda yake. Mommy ta dake sosai ta danne tsanar da take ji Tana mata, ta saka hannu ta d’agota. Nanna da take Jin kamar zata mutu taimakon kawai take nema, don haka bata damu Wai da su Mommy bane, Wanda Mk ya ce ta yi takatsantsan da su. “Me ke damunki ne?” Kanta ta nuna mata Sai Mommyn ta saki murmushi kafin ta furta “Sannu Allah ya baki lafiya, gashi masu ciki baa son şu da Shan magani barkatai, don haka bari na baki wannan ruwan addu’a ce na yi miki ita, ki shanye za ki samu lafiya In sha Allah.” Nanna da sauk’in kawai take nema bata yi wani jinkiri wajen shanye ruwan da ya zama fari tas kamar ruwan famfo ba abinda ya canja taste d’insa. Mommy ta kalli Sakina suka saki murmushin samun nasara kafin ta mik’e tana furta “Bari a Kira Family Doctor, don naga jikin naki kamar yana needing Doctor kada mu yi abu da kai, zan turo miki Nafeesa yanzu ta kula da ke, Allah ya sauwak’e.” Suka şaka kai suka fice ko bakomai burinsa ya çıka, abu na gaba da zata yi ta saka Nafeesa ta shiga jikinta, ta haka ne zata samu duk wani aikinsu ya kama. Nafeesa ido ta zubawa Mommyn kafin ta furta “Ni kuma? Ni meye nawa na zuwa wajenta ni fa na tsaneta Wallahi ko ganinta bana son yi….” “Ai kuwa dole ki ganta Nafy, na ce miki dole ki ganta ki kuma shiga jikinta matuk’ar kına son burin da kike da shi na auren Mk ya çıka, idan kuwa ba haka ba wallahi sai na zare hannuna daga sabgarki, haba yarinya duk wata wahalata a kanki take k’arewa amma kina neman ki yi min iya shege, to wallahi wannan karan kika yi sanadin da aikin ya ruguje ba zan sake wahalar da kaina ba.” Nafeesat ta had’iye wasu hawaye Tana Jin wani zafi a ranta ba na komai ba sai na tilastata shiga sabgar Matar Mk. “Ki tashi ki je ki gyara mata gida, ki kuma dafa abinci kin gamawa ki zuba musu wannan cikin abincin sannan ki zuba wannan a cikin turaren wuta, tunda an ce Mk d’in ma yana hanya yau.” Nafeesa ta amshi k’ullin maganin Zayyad da yake zaune ya yi kamar baya Jin abinda suke cewa Sam Mommy Ma bata Ankara da Shi ba, don bata zaci Zayyad yana da wayo har haka ba. Ya cije leb’ensa kafin ya mik’e jikinsa a salub’e ya bar gidan. Tun safiyar ranar yake kiran Uncle d’in nasa wayar bata shiga. Nafeesa da taga yana binta ta jiyo ta zuba masa ido, kafin ta ce “Ya aka yi ne?” Sai ya d’an karyar da wuya kafin ya ware hannu ya kuma d’aga gira guda ya furta “Nothing, ba kya son na bi ki ne?” Tsaki kawai Nafeesan ta yi ta ja hannunsa a fusace suka shiga part d’in da ko da wasa bata son shigarsa. Sai da ta mayar da numfashi ta bi parlorn da kallo wannan ne shigarta na farko, ta yi k’wafa kawai kafin ta furta “A wani d’akin take Malam.” Zayyad ya nuna mata Sai kawai ta k’ara tab’e baki ta tura k’ofar d’akin a hassale ciki ciki ta yi sallama. Nanna da idar da sallahrta kenan ta d’ago ta kalleta ta amsa sallamar tana kawar da kai don haka kawai Yarinyar bata mata ba, don musamman wasu daga dangin Mijin suka gaya mata yarda aka sha artabu da Mahmud akan sai ya aureta. Nafeesa ta kawar da kai tana tauna chewingum a hankali kafin ta furta “Ya jikin?” Nanna ta furta “Alhamdulillah” murya a sanyaye aka samu bak’uncin shiru a tsakaninsu kafin Nafeesan ta gaji ta ce “Mommy ce dama ta aikoni ta ce ko akwai abinda za’a miki?” Zayyad da yake bayanta ya yi saurin girgiza mata kai bayan sun had’a ido da Nannan. Mamaki ya kama Nannan, sai dai kafin ta ce komai Zayyad ya fice daga d’akin kamar walk’iya. Nanna ta sauke ajiyar Zuciya mamaki fal zuciyarta a sanyaye ta ce “Na gode wallahi, ai jikin nawa da sauk’i ba abinda nake buk’ata.” Nafeesa ta tab’e baki dama kamar akan k’aya take ta yi saurin ficewa ta je ta sanar da Mommy. Cikin takaici Mommyn ta ce “Daga ta ce haka kuma don shashanci sai kika d’ebo k’afa zalau-zalau kika taho? Ina maganin da na baki? Shashashar yarinya kawai.” Hannunta ta kalla kafin ta ware ido ta furta “Na shiga uku, wallahi na barshi a saman kujerar parlorn gidan…” Mommy ta saka salati ta bud’e baki tana kallon Nafeesan kallon da ya hargitsa cikin Nafeesan bata sanda ta fita da sauri ba ta koma sashen Mk. Tana shiga taga Zayyad zaune a wajen yana kallon cartoon hannu ta saka ta d’auki ledar maganin, Zayyad ya bita da ido yana sakin murmushi don tuni ya canja maganin da wasu spices da ke kitchen da kuma garin kuka. Ta fice da sauri ta kaiwa Mommy maganin. Nanna da taga duk abinda ya faru don tana tsaye a walk way da zai Kai ka d’akunan harcın gidan. Ta fito jikinta a sanyaye Tana kallon Zayyad kafin ta furta “Mantuwa ta yi ne?” Zayyad ya d’aga Kai kawai Sai ta zauna tana furta “Kiddo me yasa ka ce kada na bari ta min aiki?” Ya d’an d’ago yana kallonta kafin ya girgiza kai ya furta “Mommy forced her to come…. Na san kuma zata miki abinda ba daidai ba that’s why na nuna miki da Kai kada ki yarda….” Ko duk jikin Nanna kunne ne ba zata yarda ba, sai dai kawai ta saki murmushi tana sakin ajiyar zuciya kuma sai yaron ya burgeta at his age har ya san ya b’oye aibun Uwarsa. Zayyad dai ya cigaba da danna IPad d’insa kafin ya mik’e ya shige bedroom don haka kawai yanayin kallon da Aunt din ke masa sai ya ji yana tsargar kansa kamar tana so ta gane k’arya yake. 


Mommy kuwa da Takaicin abin ta kwana a ranta, Nafeesa ta gama b’ata mata plan ga wancan ma bata Jin ya yi aiki, don ta ji shiru ba wani sab’ani da aka ce Nanna da Mk sun samu. To me yasa kuwa aşırı zai ci su? Bayan kullum safe da yamma sai sun yi Azkar ai sun katange kansu da babban bango ga duk wani mai nemansu da sharri.


Tun safe şaşsan Mk yake cike da jama’ar gidan, don jikin Nannan ya k’i da’di tun dare take ta haraswa Hakan yasa duk suka shiga dubata ganin Jadda a gidan. A lokacin ne Family Doctornsu ta zo. Ta shiga bedroom d’in da sauri almost 1 hour ta fito Fuskarta d’auke da murmushi ta kalli Jadda Tana furta “Ciwon na Mrs Mk ai abin so ne, Tana d’auke da ciki har 3 months….” Zuciyar Mommy ta yi wani irin bugawa ta gefen ido ta dinga hararar likitan. Jadda kuwa sai Hamdala take Tana furta “Allah shine abin godiya, Allah Ubangiji ya sauketa lafiya….”



Bikin Jabeer ne ya taso gadan gadan, don haka kowa a gidan shirin bikin yake, Banda Nanna da bikin yazo mata a wani irin yanayi na laulayin ciki, bata da wani walwala. Ranar yinin ma da zazzab’i sosai ta tashi, kawai sai suka dinga jama’a şuna gaya musu Wai don Nanna ta ga za’a auro wacce Babanta ya fi nata ku’di shine duk hankalinta ya tashi. Wannan maganar da Nanna ta ji shi ya k’ata mata damuwa ta sake rafkewa a cikin d’aki.


Bayan dawowa daga d’aurin aure, Mk ne hannunsa rik’e cikin na Zayyad şuna tafiya şuna hira k’asa k’asa. Zayyad ya furta “Uncle, next week Ten year’s birthday d’ina fa.” Mk ya d’aga Kai yana furta “I know My Boy, amma ka daina surutu kaga Ammi fa bata da lafiya.”  Zayyad ya rik’e leb’ensa yana waro ido ya ce “Daddy, it is true wai Baby zata kawo mana?” Mk ya d’aga Kai yana murmushi ya ja hancinsa ya furta “Who told you.” Zayyad ya yamutse fuska murya ciki ciki ya ce “That Old Woman….” Mk ya waro ido ya ce “Zayyad ba zaka daina cewa Jadda Old Woman ba, She is my mother fa.” Zayyad ya yi shiru don shi haka kawai basa shiri da Jadda don Tana da fad’a sosai shi yasa baya wani sakewa a wajenta Sosai. 



A Daren ranar aka kawo Shareefat matar Jabeer. Addu’a Nanna ta dinga yi Tana fatan Allah yasa kada Itama ta k’i ta kamar yarda sauran faccalolin suka k’i ta. Sai dai sab’anin tunaninta Shareefat bata nuna mata tsana ba, jininsu sosai ya had’u musamman kusan sa’anni su ke, ga shi yawancin halayensu şuna kamanceceniya da juna, Sharifat ma macece mara son hayaniya, gata da ibada da nutsuwa kamar dai Nanna Hakan yasa suka had’a kansu waje guda, wannan ya sake tunzira zuciyar Mommy ganin har yanzu burinta bai çıka ba na auren Mk da Nafeesat. Shak’uwarsu ta zama irin ta kusa kusan nan suka zama kamar y’anuwan juna, Hakan Sai ya kwantar da hankalin Nanna don kuwa ta samu mai d’ebe mata kewa.


Watan haihuwar Nanna ya tsaya, tuni Mahmud ya gama mata duk wani tanadin haihuwa, hakanan Jadda, gidansu Nannan Ma baa barsu a baya ba su ma sun yi duk wani tanadinsu. Sun so ma su tafi da ita can wajensu, Baba Alhaji ya rok’i alfarmar a barta anan suka duba dattakon mutanen suka hak’ura suka barta a d’akinta.


Cikin ikon Allah Nanna ta haifi sankaceciyar y’arta fara kyakykyawar gaske kamar y’ar larabawa, ta fi Uwa da Ubanta kyau nesa ba kusa ba, don kuwa Sai ta zama mai kamanni biyu, ta kwashe duk wasu kyawawan halittu da suke jikin iyayen nata don haka ta fi su kyau nesa ba kusa ba.

Daidai lokacin Sharifat itama Tana da nata cikin wata shidda, Sunan Jadda y’ar Nanna ta ci, wato Hajiya Binta,’don haka aka b’oye ake ce mata Zakiyyat, Nanna ta so Mk ya saka sunan mahaifiyarsa, ya ve Şam shi ba zai zama bütulu ba nata sunan zai fara sakawa. Zayyad kuwa Barbie yake ce mata, saboda tsananin son Yarinyar da yake yi, in dai yana nan baya bari kowa ya d’auketa sai shi, barci ne kawai yake raba su, Hakan kuwa sosai yake b’ata ran Mommy. Sai dai Zayyad baya Jin bari in dai Akan Barbie ne, ta Lura kuma fad’a da duka ba zai raba su ba, don haka ta tattara ta zuba masa ido Tana jiran lokacin da zata rabasu koda ta k’arfin tuwo ne, don ba k’aramin tsanar Yarinyar ta yi ba, don ko d’aukanta bata tab’a yi ba.



Bayan wata uku. Shareefat ma ta haihu, itama y’a mace kyakykywa da ita, aka saka mata sunan Mamansu Mahmud, sai ake kiranta Yasmeen. Haka suke rainon yaransu cikin kulawa da kuma managarciyar tarbiyya Wanda dole idan ka kallesu su baka sha’awa. Ba kamar Barbie yarinya mai shiga rai sosai, don tana da wayo da surutu sosai shi yasa ta zama y’ar fadar Baba Alhaji da Jadda, inda jama’ar gidan suke gulmar Jadda na sonta ne don taga Ubanta yana tashen kud’i. Da ita kad’ai Zayyad yake hira, don kuwa sakata yake a  gaba su yi ta hira yana tuntsira dariya, abinda kowa ke mamaki don ba Wanda yake ganin dariyar Zayyad Sai idan yana tare da Kiyya. Goyo da wanka duk shi yake mata kuma a d’akinsa ma da gadonta don lokacin yana Js 1. Mommy ta rasa yarda zata yi ta raba su duk da abin yana mata zafi matuk’a ainun a Zuciya. Hakan yasa ta fara zama tana shirya masa zance tana masa wayo da dabara wajen ganin ta cusa tsanar Yarinyar a zuciyarsa lokacin su Kiyya şuna shirin barin nursery su shiga Grade 1. Amma duk da haka Zayyad bai amince ba, Hakan yasa ta gaji ta yi abinda bata son aikatawa na kai Zayyad da Zakiyya wajen Malami don a yi musu farrak’u, bata san Farrak’un zai zame mata abin dana sani ba, zai kuma girgiza Ahalin Zawiyya Family…..




JIKAR NASHE✍🏽