15
*BABBAN GIDA….*
New…..
**NAZEEFAH SABO NASHE✍🏽*
BRIGHT PENS.
**I DEDICATED THIS BOOK TO NA’IMA SULAIMAN SARAUTA.**
0803374837.
GODIYA MARA IYAKA DA JIKAR NASHE REAL FANS GROUP… hope wannan karan ma za ku karb’i Babban gida kamar yarda kuka saba karb’ar kowane irin book nawa. Na gode sosai sakamakon Aljanna gareku In sha Allah.🥰
**YOTA004**
Follow this link to join my WhatsApp group: ***
15.
Wannan karan Mommy ta samu nasara sosai a kan aikinta, don kuwa ya tafi successfully as she wished. Wani irin murmushi ta dinga saki sanda ta fara cin karo da tabbacin yiyuwar aikinta. Sun dawo daga bikin wata Y’ar wan Jadda kenan, da yake da su Zakiyya suka je sai kuwa ta hango Zayyad da sauri ta fita daga motar ta isa wajensa a guje kamar yarda ta saba…. Tun kafin ta isa jikinsa Zayyad ya wani irin hanb’areta cikin matuk’ar masifa da wani irin zafin zuciya suka ga ya saka hannu ya tsinka mata mari… kafin ya murd’e kunnenta. “Are you mad za ki zo ki b’ata min kaya? Ko ni sa’anki ne?” Kaf jama’ar da suke wajen ba wanda bai shiga shock ganin abinda Zayyad ya yiwa Kiyya ba, Ammeey kuwa sai da ta ji zuciyarta ta daina bugu na lokaci gudu wani irin tsoro ya shigeta idanunta a waje take kallon Zayyad. Jadda da k’arfin gaske ta ce “Zayyad ka sha giya ne? Ko hauka ka ke Kiyyan taka ka yiwa wannan dukan?” Hannunsa ya karkad’e yana sake tsuke girarsa kafin ya furta “Ko yanzu ta sake tab’a ni, ni kuma I will slap her wallahi….” Jadda sai da ta tsorata da kalamansa ganin yarda yake magana cikin nuna Rashin kunya da fitsara. Kuma ya shige ya tafi. Mommy wani irin smilling take saki, farin ciki ya cika zuciyarta, muryarta a raunane kamar gaske ta ce “Amma dai Zayyad baka kyauta ba, koda yake ba’a shiga tsakaninku da Zakiyya anjima ma za’a ganku tare, ke sai ki yi hak’uri da Yayan naki ki daina shishshige masa ai.” Daga haka ta shige abinta tana tafiya cikin isa farin ciki ne fal a cikin ranta. Ammeey ta bita da kallo Jadda ce ta ja hannun Kiyya da duk ta gama tsorata fuskar nan ta yi jajir sai kuka da ajiyar zuciya take. “Sharifa d’auko min yarinyar nan mu je wajen Baba Alhaji ba zan yarda da wannan Çin zalin ba.” Jadda ta fad’a tana kallon Mami Sharifat. Da sauri kuwa ta sunkuci Kiyya duk da kasancewarta Chubby ce a lokacin yarintarta Nanna ce ta yi saurin rik’e hannun Jadda tana k’ok’arin d’auke k’wallar idonta ta ce “A’a Jadda, ki yi hak’uri maganar nan ba sai ta je wajen Baba Alhaji ba, a barta anan ba mamaki ransa ne a b’ace, kuma kin san a irin wannan shekarun na girma yara şuna jin kansu zan yi mata fad’a ta daina shishshige masa In sha Allah.” Ido Jadda ta zuba mata tana hango yarda take k’ok’arin shanye damuwarta. Murmushi Nanna kawai take don son kawar wa da Jadda damuwarta ta kuma amshi Zakiyya daga wajen Sharifat tana fad’in. “Itama fa Jadda d’an banzan rashin ji ne da ita, ga rawar kai shi kuma ba mai son hayaniya ba ne, ai gashi nan jiki magayi wuce mu je ki kwanta ki yi barci.” Jadda ta saki ajiyar zuciya tana bin bayansu da kallo, salihanci da kyakykyawar zuciya irin ta Nanna abin a yi koyi ne abin kuma a so ne. Amma kuwa Zayyad bai ci buluş ba zai zo ya sameta sai ta masa wankin babban bargo, banda tashen rashin kunya ma me zai saka har bai ji kunyar Uwarta ba ya doketa a gabanta, ai ko mutuwa tana tsoron idon Mahaifi. Ta yi k’wafa ta nufi part d’inta.
Nanna kallon Mamy Sharifat take kawai da take ta masifa tana shafawa Zakiyya robb a inda ya daketa. “Wallahi Nanna idan za ki farka daga barcın da kike ki farka, wannan ai iskanci ne kawai ya kama yarinya ya yi ta duka, to wallahi idan baki nutsu ba haka zai mayar da Yar nan jaka shi ya daka uwarsa ta daka, to Ina dalili, y’a guda d’aya tilo.” Nanna murmushi kawai take saki ita kad’ai ta san me take ji a cikin ranta, idan ta ce ma bata ji zafin abin nan ba ta yi k’arya wallahi. Sharifa kuwa sai masifa take tana k’arawa.
Mommy dai na d’aki farin ciki ne kawai ya sakata har da tsalle ta kwanta a saman gadonta, fuskarta fal murmushi, “Kad’an ma kenan Nanna, sai na saka ki kuka da idanunki wannan alk’awarine na d’aukar kai na….” Ta tuntsire da dariya tana sake kallon laya ta uku da zata je ta burne wanda itace cikon aikinta da zarar kuma ta aikata burinta na k’arshe ne zai cika ko kallon Kiyya Zayyad ba zai so ya sake yi ba.” Ta cije leb’enta tana furta “Shegiyar yarinya, mai kama da d’iyar Aljannu, sai kin bar duniyar ma duk da izayar da zan miki, a kanki zan huce duk wani laifi da iyayenki suka min kafin na koma kansu na Raba su ta k’arfi fa yaji.” Ta furta zuciyarta cike fal da hassadar sake bunk’asar arzikin Mahmud, ta manta alherinsa gareta na yarda yake son d’anta Wanda ko yar cikinsa ba ya yiwa wannan soyayyar.
A wata ranar Zayyad ya gama yankewa zuciyarsa abinda zai yi ya hargitsa kwanyar Kiyya. D’in haka ya tara duk yaran gidan ya sanar musu ya sallami mai lesson d’insu shine zai dinga yi musu lesson. Kiyya ta sunkuyar da kanta zuciyarta nata harbawa da k’arfi don yanzu wani irin tsoronsa take ji, duk sanda ta ji ko muryarsa ne sai ta ji kamar ta yi fitsari. “Ke d’ago kanki ki kalleni, Uban wa kike sunkuyarwa kai, am I your mate?” Cikin rawar jiki Kiyya ta girgiza kanta. Ya zuba mata harara kafin ya saki tsaki ya ce kuma lesson d’in zai zama one by one ne, mutum kada ya dinga yin abinda na umarcesa na rantse da Allah sai na kulle yarinya a dark room ba ruwana, ba wanda zai zo ya kawo min iya shege a cikin ku. Understand?” Da sauri suka d’aga kai “You better understand, ku fice ku bani waje.” Da sauri suka fice ta mik’e zata fita ya ce “Ke…” cak ta tsaya don ta san da ita yake saboda ya canja mata suna, daga Barbie zuwa Ke, shima a tsawace. “Wa ya ce ki fita?” Da sauri ta zube a gabansa don ta san last abinda zai ce mata kenan Kneel down… ta rufe idonta hannayenta a sama jikinta sai rawa yake shi kuwa ya cigaba da sannan system d’insa ba tare da ya sake bi ta kanta ba, har almost 2 hours sannan ya ce ta tashi ta tafi, hannunta da k’afarta duk sun kumbura ta nufi hanyar part d’insu idanunta sai zubar da hawaye suke… sai dai ko kafin ta shiga parlorn ta zube a wajen saboda galabaita. Mk da ya sako kai zai fita ya yi turus yana kallonta tana numfashi da k’yar. Bai san sanda ya isa wajen ba ya d’agota yana kiran sunanta. “Kiyyana open your eyes, menene Fad’uwa kika yi?” “Yaya Zayyad ne ya sata Kneel down…” Yasmin ta fad’a idanunta yana ciko da hawaye don itama zuwanta wajen kenan. Mk ya furta “What? Zayyad kuma?” Don shi duk abinda ake bai sani ba, Nanna bata gaya masa ba, ganin tana buk’atar taimako sai kawai ya sunkuceta ya yi ciki da ita da sauri yana k’walawa Nanna kira. Nanna gabanta yana fad’uwa ta fito a guje tana kallonsa da Kiyya a hannu. Waro ido ta yi, bai mata magana ba kawai ya saka Kiyya a saman cinyarsa ya fara bata taimakon gaggawa amma numfashinta sai wani irin d’aukewa yake. Da sauri Nanna ta ce “Don’t waste our time, mu tafi asibiti kawai Habibi…” shawararta ya bi ya mik’e da sauri suka nufi kai ta asibiti. Yasmin ta koma wajen Mammynta ta gaya mata Sharifat ta girgiza kai ta mik’e ta nufi wajen Jadda ta gaya mata. Jadda salati ta saka ba shiri ta dinga kiran wayar Mk sai dai ba amsa don shi
garin sauri ma bai san ya bar wayar a gida ba. Sharifa ta ce “Jadda wannan karan fa ya kamata a tsawatarwa Zayyad wallahi, abin ya yi yawa kada kawaicin iyayenta ya janyo a cutar musu y’a fa.” Jadda ta dinga girgiza kai, koma menene Sharifa yau zan kawo k’arshen wannan iskancin na Zayyad Baba Alhaji zan je na samu na gayawa.” Ta fad’a tana mik’ewa ta nufi parlorn Baba Alhaji.
Da kallo Baba Alhaji ya dinga bin Jadda kafin ya furta “Zayyad kika ce yana dukan Zakiyya? Na zata duk gidan nan ba wacce ya fi so sama da ita.” Jadda girgiza kai ta yi tana furta “Yanzu fa abin ya canja salo Baba Alhaji, ba yarda kake tunani ba ne shi kuma nasa girman da iskanci da fitsara da miskilanci yazo masa kana masa magana yana gaya maka duk abinda yaga dama ba shakka bakomai.” Baba Alhaji ya shiga girgiza kai bayan Jadda ta gama gaya masa irin abubuwan da Zayyad yake yiwa Zakiyya… “A duk inda yake a sanar masa ina neman sa.” Daga haka ya cigaba da laziminsa. Jadda ta mik’e ta fice don ta san ran Baba Alhajin ba k’aramin b’aci ya yi ba, daga yanayin fuskarsa ta san ko wani hukunci zai yiwa Zayyad ba zai zama mai sauk’i ba….
Mk ya dinga kallon Doctorn jin abinda ya ce masa. “Gaskiya sai kun kula sosai da lafiyar zuciyar yarinyar nan idan ba haka ba akwai matsala babba….” Nanna tana hawaye ta ce “Zuciya fa ka ce Doctor? Wani irin zuciya kuma na shiga uku ni Nanna?” Doctorn ya girgiza kai a hankali yana shafa kan Kiyya data fara barci a saman cinyar Mk da ya rasa bakin magana a duniya baya jin akwai abinda yake so sama da Zayyad da Kiyya, shi yasa ya tsorata da jin abinda Nanna ta dinga gaya masa game da Zayyad da irin cutarwar da yake yiwa Kiyya, me zai saka Zayyad ya canja haka a lokaci guda? “Ku je gida da ita, a cigaba da kula da k’ok’arin kiyaye duk abinda zai saka ta fiirgita kafin mu ga abinda Allah zai yi, idan kuma Akwai hali za ku iya kaita k’asar waje don a dakatar da abin kafin ya zama wani issue babba.” Ajiyar zuciya kawai Mk yake saki don kuwa ya shiga shock fiye da zaton Nanna, don sai ita ta d’au Kiyyan ma suka tafi k’arshe ita ta yi driving.
Suna zuwa gate yara suka ce Baba Alhaji tun d’azu yana nemansu. Don haka Mk ya ce Nanna ta je da Kiyya gida shi Bari ya k’arasa wajen Baba Alhajin.
Ba wanda babu a parlorn da alama taro ne babba ake yi. Baba Alhaji yana zaune fuskarsa a d’aure tamau kamar yarda ta Zayyad ma take a tsuke sai cizar leb’e yake. D’in kuwa Babansa ne ya gama zane shi duka na sosai har sai da aka ceceshi. Baba Alhaji yana kallon Mk ya ce “Auta, ya jikin Amarya ta.” Mk ya d’an saki murmushi kafin ya ce “Jikin Amarya sai dai addu’a da sauk’i ma, ciwon zuciya ne yake k’ok’arin kamata….” Jadda da wasu daga cikin mutanen wajen suka saka salati. Baba Alhaji ma ya jiya juya ya kalli Zayyad da ko kallon inda suke bai yi ba, sai ya girgiza kai ya ce “Allah ya bata lafiya, amma zan bar muku wasiyya ko bayan raina ina son wannan ja’irin yaron ya auri Zakiyya………”.
Z
JIKAR NASHE✍🏽
Masu tambayar complete
Wallahi littafin nan ba complete da akwai nima da tuni na manta na baku shi yanzu nake gyara shi nake mayar da shi online. Na gode da soyayyar da kukewa Babban gida.🙂

Ba wanda babu a parlorn da alama taro ne babba ake yi. Baba Alhaji yana zaune fuskarsa a d’aure tamau kamar yarda ta Zayyad ma take a tsuke sai cizar leb’e yake. D’in kuwa Babansa ne ya gama zane shi duka na sosai har sai da aka ceceshi. Baba Alhaji yana kallon Mk ya ce “Auta, ya jikin Amarya ta.” Mk ya d’an saki murmushi kafin ya ce “Jikin Amarya sai dai addu’a da sauk’i ma, ciwon zuciya ne yake k’ok’arin kamata….” Jadda da wasu daga cikin mutanen wajen suka saka salati. Baba Alhaji ma ji ya yi hankalinsa ya tashi, sai idanunsa ya sauka akan Mommy Hajara da mamakinsa sai yaga wani irin farin ciki take, ya juya ya kalli Zayyad da ko kallon inda suke bai yi ba, ya mayar da kallonsa kan Mommy Hajara sai ya girgiza kai yana murmushi da shi kad’ai yaşan ma’anarsa ya ce “Allah ya bata lafiya, In sha Allah zata warke sumul kamar bata yi ba, amma zan bar muku wasiyya ko bayan raina ina son wannan ja’irin yaron ya auri Zakiyya…. Kuma bana fatan a canja min magana ta…….” Mommy da Nanna duk suka d’ago a firgice suna kallon Baba Alhajin.