BABBAN GIDA

16

by @nazeefanashe

BABBAN GIDA….


NAZEEFAH SABO NASHE✍🏽


***.


16.

Baba Alhaji kuwa bai sake magana ba, sai ma cigaba da danna counter Din hannunsa ya yi, idanunsa kuma a lumshe… Hakan yasa ba wanda ya yi magana a wajen, kowa ya yi tsit Zayyad kuwa ji ya yi zuciyarsa na wani irin zafi, me yasa Baba Alhaji Zai ce haka shi kuwa zai ga wanda Zai masa aure da wannan Aljannar Yarinyar. “Amma dai kamar a adalcin Familyn nan ba a irin wannan auren, idan har Zai yiyu Baba Alhaji a Bari su girma tukun na sai a zartar da hukuncin haka, kada daga baya su zo su ce basa son juna…..” Mommy Hajar ta yi k’arfin halin fad’ar hakan, don bata Jin ko menene zai faru zata bari Zayyad ya auri Yarinyar nan…. “Ke ki ke da goben Hajara? Ki yi fa a hankali Ina lura da duk wani take takenki kwana biyun nan shiru kawai nake miki, na gama magana don haka ku tashi ku bani waje….” Baba Alhaji ya yi maganar da ta saka kowa ya tsorata ganin yarda ya yita a zafin zuciya da Jin haushin Mommyn, sai yanzu kuma wasu mutanen da basu gama gane halin Mommyn ba suka dinga mata wani irin duba, da mamakin Jin furucin Baba Alhaji a kanta. Mommy ta yi shiru zuciyarta na wani irin bugu, tabbas dole ta yi taka tsan tsan da dik abinda za ta yi nan gaba tunda har Baba Alhaji ya fara gane inda ta dosa. Idan har ba so take asirinta ya tonu ba abinda bata fatan faruwarsa. Don haka da sauri ta mayar da fuskar fara’a da walwala ta maye fuskar b’acin ran da take ciki, ta dubi Jadda da itama ta zuba mata ido tun bayan kiran da ta aika aka mata, nazarinta kawai take da son ta gane abinda Maigidanta ya fara ganewa wanda ita bata tab’a lura ba, sai yanzu da takewa Hajaran kallo na tsanaki. “K’in auren Nafisa dai Mahmud ya yi, kada Hakan ya sake ya baki damar cutar da zuri’arsa, na rantse da Allah idan kika yi yunk’urin Hakan Allah ba zai barki ba Hajara, D’in kuwa Mahmud bai cutar da naki d’an ba Banda ma soyayya da Yake nuna masa fiye da kowane yaro a gidan nan, idan kika k’i ji ba zaki k’i gani ba, don haka ki kiyaye.” Jadda ta furta ranta a b’ace tana kallon Hajaran da duk jikinta ya Kama rawa. Sak Hajaran ta yi da numfashinsa kafin ta sauke ajiyar zuciya a hankali ta ce “Jadda, me yasa za ki yi tunanin zan cutar da Mahmud ko jininsa? Har abada babu wannan tunanin a rai na, koda kika ji na yi wancan furucin ganin dukkansu yara ne, basu fuskanci ne rayuwa take ciki ba, amma idan har Hakan ya b’ata miki rai don Allah ki yi hak’uri.” Hak’uri na guda Hajara, ki cire idonki daga kan yaran nan, don na san sarai ke kika cusawa Zayyad k’iyayyar y’ar uwarsa, saboda haka ki san yarda kika yi kika kunce k’ullin da kika k’ulla.” Wannan ne kuma baki İsa ba wallahi…. Hajara ta furta a cikin zuciyarta K’iyayya yanzu ma ya fara mata wallahi in dai Ina rate zan Dai yi taka tsan tsan wajen kautar da hankalinku daga kai na, kai Allah ya d’au ran Baba Alhaji na huta.. a Zahiri kuma sai ta yi murmushi ta mik’ewa kawai ba tare da ta bar wata k’ofa da Jadda zata cigaba da zarginta. Ta fice daga sashen Jaddan tana sake Jin wani matsanancin b’acin rai a k’asan ranta. Ina in dai tana raye Zayyad ba zai auri Yarinyar nan ba.



Zafin k’iyayyar da Zayyad yake nunawa Zakiyya abin har ya wuce duk tunanin mai tunani, tun kowa bai fahimta ba har aka fara gane yar tsamar da take tsakaninsu. B’angaren Kiyya tun abin na damunta har Zayyad ya zama abin tsoro a wajenta, abubuwan da yake mata ya fara shafar karatunta na makaranta, don sam sai ta daina fahimta, kullum a cikin tunani take bata gane komai, da zarar ta ji muryar Zayyad kuwa zaka ga jikinta har rawa yake. Abin ya fara damun Ammi don kuwa ciwon da yake son kamata na Zuciya gaba abin yake madadin samun sauk’i. Kullum a cikin yiwa Zayyad nasiha take Amma kamar sake tunzira shi take, tun bata Jin haushi abinka da Uwa sai ta ji abinda Yake yiwa Kiyyan ya fara tab’a mata zuciya ta fara fita daga sabgarsa. Mk kuwa ba ruwana kulawar da yake bashi bai fasa ba. Har Zayyad ya shiga SS 1 lokacin ya k’ara tashen rashin kunya gashi dama da jikin girma ya daina dariya ya zama d’an gayu na gaske. Duka yaran ya daina shiga sabgarsu ga wata irin shegiyar tsafta da ya sakawa kansa.


Lokacin da suka yi wata third exams a lokacin lamarin Kiyya ya fara bawa iyayenta tsoro, don dai madadin ta d’au first position kamar yarda ta saba wannan karan last position ta d’auka, don kuwa ba abinda take eubutawa a exams Din banda repeating questions d’in da aka rubuta mata. Amminta ta dinga kallon result Din tana hawaye a lokaci guda kuma tana sauraron advice d’in da Principal ta makarantar take basu. “Am definately sure akwai abinda ke damun yarinyar nan. Ya zama dole ku matsa ta ku gano koma menene kafin ya yi sanadin da zai tab’a mata brain, abin ya yi yawa Malamanta sun yi complaining bata fahimtar komai.” Ammi ta ja ajiyar zuciya tana kallon Mk da bai ce komai ba, suka mik’e jiki cike da kasala suka nufi fita daga office d’in. 


Gaba d’aya jikinsu a salub’e yake, hakan yasa Zayyad saurin karb’ar Papers din daga hannun Mk yana furta “Uncle lafiya?” Kamar gaske… Ammi ta furta a zuciyarta ganin yarda Zayyad ya nuna kalar damuwa a fuskarsa. Tana kallon sanda ya saki murmushi da ya gama ganin result d’in. Farin ciki yake ji sosai a ransa, don kuwa ya kasa dannewa a saman fuskarsa ma sai da ya nuna. Ya saci kallon Ammi da ya lura sam yanzu bata fiye shiga sabgarsa, sai ya mayar da kallonsa kan Zakiyya ya ce “Last position kuma Gifted, ya aka yi haka?” Papers Din Amma ta fisge ta yi gaba kawai, tana ji Mk na kiranta amma ko kallonsa bata yi ba, ji take idan har ta cigaba da tsayawa a wajen ba abinda zai hanata marin Zayyad. Mk ya saki ajiyar Zuciya sai ya cigaba da jan Hannun Kiyya da Zayyad da yake gefensa suka nufi mota don isa gida.


A zaune suka samu Baba Alhaji akan babbar daddumar da ya saba zama da safe kamar wannan lokacin. Ya amsa gaisuwar Nanna yana k’are mata kallo, a idanunta ya hango damuwa don kuwa ba haka ya saba ganin yanayinta ba. Sai dai ya share bai tambayeta ba don kuwa ba huruminsa ba ne. Ya mik’awa Zakiyya hannu da take jikin Nannan idanunta har sun d’an kumbura. “Amaryata, zo mana, ya aka yi kin dai d’auko mana first position d’in. kamar yarda kika saba ko?” Zayyad ya dinga danne dariyarsa kamar zai ce ta d’auko Last position dai, sai ya danne maganar yana kallon Nanna da ta sake damk’e papers d’in a hannunta. Mk dai bai ce komai ba sai ajiyar zuciya yake a hankali, ya kalli Nanna ya ce “Ku je gida, ki bata maganinta.” Kamar jira take ta mik’e da Kiyya a jikinta suka nufi part d’insu. “Zayyad, follow them.” Mk ya fad’a yana kallonsa. Zayyad sai ya ji abin wani irin, ya fara tunanin me Uncle d’in zai ce da har sai ya ce ya bar wajen. “Baka ji me na ce ba ne?” Ganin yanayin uncle d’in yasa ya mik’e da sauri ya nufi waje har yana jin kamar ya fad’i. Mk ya sunkuyar da kai ya rasa ta yarda zai yiwa Baba Alhaji bayanin abinda yake ransa. “Ina jin ka Mahmudu, na san dai ko baka fad’a ba, tabbas akwai matsala, gaya min me ya faru?” Mk ya yi k’asa da kansa kafin ya ce “Baba Alhaji, don Allah ka min alfarmar na tashi na bar gidan nan…..” Yanayin kallon da Baba Alhaji yake masa yasa shi yin shiru bai k’arasa sauran maganar ba, dama ya san da k’yar idan zai amince masa, sai ya ji kwalla ta cika idonsa. Baba Alhaji ya janye idonsa daga kaifaffan kallon da yake masa kafin cikin wata irin Murya ya ce “Menene hujjarka na barin gidan nan Auta? Ashe ba zaka iya yi min alfarmar ko bayan babu raina ka cigaba da zama da Jinin Bintu ba, kada ka manta da halaccin Jaddanku a kanta shin baka san idan har ka ce zaka bar gidan nan zata iya zaton da ba ita ta kawo ka duniya ba?” Mk ya runtse idonsa abinda yasa tuntuni bai bijiro da wannan buk’atar tasa ba kenan, yana Jin nauyin Jadda don bai San fassarar da za ta yi masa ba. “Me ya sake samun Zakiyyan?” Baba Alhaji ya furta idonsa cikin na Mk. Idonsa ya lumshe kafin ya bud’e ya fara bawa Baba Alhaji labarin abinda suka tarar a makarantar su Kiyya, da bayanin da Principal ta yi musu. Sai da ya gama tas sannan Baba Alhaji ya jinjina kai ya ce “In dai wannan matsalar ce tazo k’arshe da izinin Ubangji…” Mk ya yi saurin kallonsa murya na rawa ya ce “Baba Alhaji, me za ka yi?” Murmushi Baba Alhaji ya saki ya ce “Ba abinda zan yi auta sai addu’a, amma ina raye ba zan bari Zumuncin Ahli na ya watse a banza ba, Saboda dalilin mutum d’aya, wannan dalilin Ba zai saka ka bar cikin gidan nan ba Zayyad, ka tashi ka je zan samu Sheih Abdalla a fara yi mata rubutun neman kariya daga ita har Zayyad d’in.” Mk ya mik’e yana ji a ransa kamar hukuncin Baba Alhaji bai zauna masa ba sai dai ya bar abin ransa, tabbas kuma Zayyad na gama secondary school zai saka ya bar k’asa nan ya yi nesa da gida ya je karatu can k’asar waje.


Hannu bibbiyu a kumatu ya samu Nanna, idanunta a lumshe sai dai sai zubar da kwalla take. Ya dafata yana furta “Haba Nanna ta, me kenan zan gani? Ki yi hak’uri in sha Allah ko mai yazo k’arshe.” Nanna ta yi saurin bud’e ido ta ce “Ya yarda mu bar gidan nan?” Mahmud ya jijjiga kai “Ya dai ce zai d’au mataki, bana son ki sake magana don Allah Nanna.” Sai ta ji zuciyarta ta k’ara karyewa ta kamo hannunsa duka biyun ta ce “Ina jin tsoro Habibi, bana son komai ya samu Kiyya.” Murza hannunta ya shiga yi a hankali kafin ya ce “Ba abinda zai faru Nanna sai Alheri In sha Allah….” 



Sosai Baba Alhaji ya dage da karb’ar musu addu’oi da tofin Alkur’ani, amma Mommynsa ta saka shi a d’aki ta ce “Ko an bashi ya daina sha, a zatonta a asirin da yake jikinsa na farrak’un zasu karya,ita kuwa ba zata so haka ba, so take ma ta k’ara uzzira abin. Don haka idan an bashi baya sha, Barbie dai an samu kanta sosai.


Don watarana suna kwance da Nanna, sai Nanna ta ji ta ce “Ammi, in gaya miki wata magana?” Da Saudi Nanna ta ce “Gaya min Barbie….” Sai Kiyyan ta ce “Ina jin tsoro fa Ammmeey, Ya Zayyad ya ce idan na fad’a….” Sai ta danne Bakinta da hannunta wannan karan jikinta har rawa yake ta lumshe ido. Hankalin Nanna ya tashi ta mik’e zaune ba shiri ta ce “Ba za ki gaya min ba?” Kiyya ta lumshe ido murya a wahale kamar wacce aka shak’e ta ce “Ina rannan, da kika ji k’amshin turarensa a jikina har kika ce Uban me na yi masa da turare? To wallahi ba wasa na yi da turaren ba….” Nanna ta waro ido ta ce “Ina jin ki, ta yaya turaren ya shigo jikinki to?” Ta girgiza kai da sauri kafin ta ce “Ya ce fa kada na fad’a idan na fad’a……” Ammeey ji ta yi jikinta na wani irin b’ari bata san sanda ta janyo Kiyya ba ta janye rigarta ta ja pant d’inta ta shiga dubata dükkan gabban jikinta rawa suke, bata fatan abinda take tunani ya kasance……




JIKAR NASHE✍🏽