BABBAN GIDA

18

by @nazeefanashe

*BABBAN GIDA….*

New…..

**NAZEEFAH SABO NASHE✍🏽*

BRIGHT PENS.


**I DEDICATED THIS BOOK TO NA’IMA SULAIMAN SARAUTA.**

0803374837.


GODIYA MARA IYAKA DA JIKAR NASHE REAL FANS GROUP… hope wannan karan ma za ku karb’i Babban gida kamar yarda kuka saba karb’ar kowane irin book nawa. Na gode sosai sakamakon Aljanna gareku In sha Allah.🥰



**YOTA ID 004*





Follow this link to join my WhatsApp group: ***



Don samun babban gida daga farko shiga wannan link d’in.



***


18


Zayyad fa ya şaka Kiyya a gaba da tsana da hantara, ta bayan idon iyayen yake mata duk cin zalin da yake mata, kuma ko me iyayenta Za su yi ba zata gaya musu ba, sai dai ta yi ta kuka tana jan ajiyar numfashi. Ga matsalar numfashi da ta dinga samu a kai a kai. Akwai sanda ya rufeta a toilet, aka dinga nemanta amma Zayyad ya fice daga gidan kuma ya b’atar da key d’in. Hankalin kowa ya tashi a gidan banda jama’ar Mommy da suka dinga mata fatan mutuwa ko wani mummunan bala’in ya sameta. Har dare Zayyad bai dawo ba yana dawowa ya dinga pretending as bai San abinda yake faruwa ba. “Ammi, lafiya kuwa?” Ammin ta d’ago jajayen idanunta kafin ta ce “Zayyad, Kiyya ce ba a gani ba.” Zayyad ya waro ido yana furta “Amma an duba ko Ina kuwa?” Ammi ta jijjiga masa kai. “Kuma har toilets…” Numfashin Ammi ya tsaya cak, don kuwa basu duba toilet ba ta mik’e a hanzarce dafatan Allah yasa ba wani abin bane ya sameta a cikin toilet d’in. Toilets Toilets suka dinga dubawa kuma har da Zayyad d’in da ya nuna matsananciyar damuwa a fuskarsa. Ammi ta dawo ta zauna jikinta a sanyaye ta ce “Aina Ma takunu ya’ati bikumullah jami’an..” hawaye ya fara zubo mata. Mk dai ya rasa abinda ke masa dad’i. Zayyad ne ya ce “Am, ina zuwa bari na duba Bathroom d’ina.” Ya yi saurin shiga D’akinsa. Jikinsa a sanyaye yasa key d’in ya bud’e. Zuciyarsa ce ta yi wani irin bugawa kansa ya yi tsawa da sauri ya d’agata ba jikinsa sai rawa yake, don kuwa Sam bai ga alamun tana numfashi ba. Amma na ganinsa da Zakiyya a hannu ta runtse idonta bugün zuciyarta yana sauyawa, ta tabbata ba mamaki shikkenan ta rasa Kiyya. Mk ma mutuwar zaune ya yi har Zayyad ya k’arasa  da ita kusa da su yana furta “Uncle, mu tafi asibiti bata numfashi.” Mk ya zama kamar wani statue har sai da Zayyad ya k’walla k’ara sannan Mk ya mik’e da sauri ya nufi waje Zayyad d’in ya bi shi da ita a hannu a guje. Suka tafi asibiti ba tare da mutanen gidan sun sani ba. 


An sha wuya sosai kafin Doctors su samu nasarar dawo mata da numfashinta. Ido ta kafawa Zayyad da ya rasa nutsuwa, tsoro yake ji kada ta tona masa aşırı. Sak ya yi yana kallon Mk da yake furta “Sannu Barbie, ya aka yi kika shiga toilet d’in Zayya….” “Uncle, bai kamata a mata wannan tambayar ba, kamata ya yi a kira Doctor şu dubata.” Ya yi saurin togace Mk d’in don güdün kada asirinsa ya tonu. Mk ya sauke ajiyar zuciya ya san gaskiya Zayyad ya gaya masa. Yana fita Zayyad ya sauke ajiyar Zuciya yana kallon Zakiyya ya ce “Tona min asiri za ki yi? Wallahi kika sake kika fad’a abinda zan miki sai ya fi duk Wanda nake miki a baya.” Kiyya ta lumshe idonta hawaye kawai yana gangaro mata. Zayyad ya d’an ja hannunta alamar rarrashi a k’asan ransa yana Jin tausayinta sai dai bai San me yasa ba haka kawai yake Jin tsanarta. Murza hannunta kawai yake yi yana Jin wani irin zafin abinda ya mata a k’asan ransa har Mk ya dawo da Doctors bai sani ba. Aka sake duddubata aka saka mata drip sannan ne Mk ya kira Nanna ya gaya mata ta gayawa Jadda şuna asibiti sai su taho tare. Kafin zuwansu har Zayyad ya yi mata wanka tana kwance d’aure da Towel idanunta a lumshe. Ta ji shigowar Mami Sharifa Nanna da Jadda. Ta bud’e idonta a hankali tana kallon Ammi da ta k’arasa bakın gadon da sauri. Jadda Ma da saurin ta isa Tana furta “Sannu Fatima, Sannu Allah ya baki lafiya.” Sai ta saki murmushi ta ce “Ameen Jadda, ai na samu sauk’i ma.” Mami Sharifa ta ce “Amma Barbie, ya aka yi kika rufe kanki a toilet.” Kiyya ta maze ta k’i kallon Zayyad, shi kuwa yana gefe gabansa sai fad’uwa yake ya ji Kiyya ta ce “Na shiga ne, sai sai kuma na fad’i k’ofar kuma ta rufe kanta…” Ko duk jikin Ammi kunne ne ba zata tab’a yarda ba, ta dai yi shiru tana sake nazarin Zayyad da Kiyya. Ta kudirce a ranta wannan karan idan har ta tabbatar Zayyad ne ya rufe Kiyya tabbas zata d’au mummuna mataki.saboda dama kawaici kawai take musu, don Zakiyya y’ar fari ce, bai kamata matsayinta na jinin Fulani ta dinga magana a kan komai aka mata ba.



Suna komawa gıda Ammi ta sakata a d’aki tana dubanta ta ce “Kiyya, gaya min gaskiya, kin san dai k’arya babu kyau, musamman baa so ka yiwa Mahaifiyarka k’arya, ko menene zai faru da ke, ni ya kamata ki samu ki gayawa bana son ki dinga b’oye min komai. Zayyad ne ya kulleki a toilet ko?” Kiyya ta runtse idonta kafin ta d’aga kai. “Amma Ammi, pls kada ki gaya masa ni na gaya miki, ni na yafe masa tunda dai Brother na ne, kuma ni Ina son sa bana son yake Jin haushi na.” Ammi ta cije leb’enta kafin ta ce “Me yasa zan kyaleshi ne ya cıgaba da cutar min y’a?” “Ki yi hak’uri Ammi, idan kika masa magana, zai adding more akan abinda yake min…” Ammi kawai ta ji hawaye na son zubo mata, Ashe haka aure a gidan yawa yake? Haka dole Tana ji Tana gani ta bar abin a ranta, bata yi magana ba ba don Zayyad ya fi k’arfinta ba, sai don gani da take a duk sanda ta yi masa fad’a kamar tana sake ingiza shine ya ci zalin Zakiyyan. Don haka bisa tilas ta kudundune abin ta ajiye a zuciyarta. 


Ranar da Zayyad ya gama J.S.C.E. Wata irin murya yake yi kamar Wanda aka ce ya gama secondary school gaba d’aya. Mk ma murna yake Taya shi sosai don Zayyad d’in ya Kama Kansa ya ajiye duk wata shiririta da ya fara, musamman Mk ya had’ashi da Sheikh Abdallah, sai dai a zahiri Zayyad ya nutsu amma bad’in akwai bad friends da suke tare da shi suke kuma k’ara zugashi ta hanyar k’wanzarta surarsa da irin yarda kuşan matasan y’an matan school d’in duk suka mato a kansa, don haka a School ba abida ya dameshi gwara kan y’an mata yake sosai da sosai. 


Mk ya duk yaran gidan şu shirya a je School d’in su Zayyad Taya shi murnar gama Js section lafiya. Ammi ta shirya Kiyya cikin wasu Riga da wando masu Kyan gaske. Aka mata 2 Babies a kanta da ya k’ara fito mata da Baby face d’inta, ta yi kyau sosai kamar ka sure ta ka gudu. Haka kawai tun safe take cewa Ammi zuciyarta na bugu. Ammi ta saka hannu ta ji itama yanayin bugün, tsoro ya kamata ta dai danne abin a ranta ta yiwa Zakiyya addu’oi ta bata ta sha, sannan ta ce Abbinta ya kula da ita sosai.

Suna zuwa wajen taron idanuwa suka dawo kan Kiyya. Ba don komai ba sai don zallar Kamanni da ta yi da Indians. Y’an makarantarsu kuwa suka rufeta şuna yaba irin kyan da ta yi musu a ido. Saboda ta shiga ran kowa a makaranta don yarinya ce mai barkwanci da fara’a. Zayyad ya dinga kallon abokansa da suke maganar Zakiyya. “Wallahi nan gaba Allah ne kad’ai ya san irin Karon da yarinyar nan zata dinga had’awa a titi. Subhanallah Zayyad Allah ya yi halitta a wajen Kanwar nan taka….” Zayyad ya zabga musu harara yana tsaki kafin ya ce “Wani karo anan? Ku kuna tunanin tana da Kyan da zata saka karo…” Wata Beb d’in Zayyad da yake ji da ita ta ce “Aa fa Zayyad, Banda son zuciya yarinyar nan kaf Zawiyya ba na biyunta…” wani abu ya ji ya caki zuciyarsa. Ransa a b’ace ya ce “Har Ni Mihibba?” Ta d’aga mata kansa with full confidence don ita a tunaninta Biological Sister d’insa ce. Ya cije leb’ensa yana Jin ransa na masa zafi. Muhibba ita yafi so a duk y’an matan da suke kawo masa farmaki, amma yau ita ta bud’i baki take kuşhe shi take cewa wata ta fishi kyau. Maganar Ta fi kowa Kyau a ZAWIYYA ya zauna wa Zayyad daram a zuciya. Ya dinga hararar Zakiyya ransa yana k’una a ransa ya ce “Ya zama dole ya yi maganin Yarinyar nan. Hakanan ya dinga hotuna da kowa amma banda Kiyya, jikinta ya yi sanyi sosai ta yi lamo a jikin Amminta da duk abinda ake take lura. Zuciyar Zakiyya ta cigaba da tsananta bugün da take. Haka aka tashi taro Nanna ta tuna zata gidan wata cousin d’insu. Don haka ta mik’awa Kiyya Jakarta ta ce “Mu je Mota, gidan Aunty Hamida Za mu.” Kiyya ta d’an turo baki kafin ta furta “Ammi zan bi Mammy, sai na zauna a wajenta kafin ki je ki dawo…” gaba d’aya Kiyya ta d’aureta a gaban Sharifa, Sam ba zata iya cewa ba zata barta ba, haka nan zuciyarta bata amince da barin nata ba. Ta d’an girgiza kai a hankali tana furta “Bari gobe na je kawai, tunda ba kya Jin da’di.” “Sai kuma aka ce ni ba zan iya kula da ita ba ko me Nanna?” Nanna ta girgiza kai tana furta “Ba haka ba ne…” “To yaya ne?” Sharifat ta fad’a Fuskarta na nuna alamun b’acin rai. Nanna ta saki silent murmushinta Tana furta “Shikkenan gata nan zan je na dawo, Barbie take care.” Zakiyya ta sakar mata murmushi har da jan hannunta ta yi kissing d’insa, idonta kamar zata zubar da k’walla. Gaban Ammi Nanna ya buga da k’arfin gaske, ta dinga Jin wani irin sanyi na shiga jikinta, sai dai kunyar idon Sharifa ya hanata yin komai, ta juya nata jikin a salub’e ta bar wajen, tana d’auke k’wallar da take son zubo mata, gabanta kuwa bai fasa fad’uwa ba.


Sharifa irin iyayen nan ne, da basu damu da me yaro yake aikatawa ba. Don haka ko bayan da suka dawo gajiya ce sosai a jikinta ta zuba musu abinci ta ce su ci su je su yi wasa amma ta yi warning d’insu Banda zuwa part d’in su Mommy. Suka d’aga mata kai ita kuma ta shige bedroom d’inta ta ware Ac ta hau biyan bashin barcin da bata yi ba.. har yaran suka gama cin abinci suka fice babban field d’in gidan yin wasa bata sani ba.


Ammi gabanta ne kawai yake fad’uwa gashi gidan Hamida da Nisa don can d’an ladi nasıdi ne, kuma from unguwar su Northwest zuwa Danladi nasidi ba k’aramin Nisa ba ne da wajen. Har Sun kai bakın gate ta ji zuciyarta ta yi wani irin bugawa da sauri, bata san sanda ta ce drivern “Mu koma Baba, na fasa zuwa.” Ta furta muryarta na rawa, don ta tabbata akwai wani abu da zai faru koma ya faru. Ta dinga rok’on Baba ya yi sauri sai dai duk saurin da zai yi tafiyar ba kad’an ba ce.



A bakın gate Baba ya tsayar da motar, bata san sanda ta fice ba ko bari ya shigar da motar bata yi ba, ta shiga cikin gidan hango su Yasmin şuna wasa ba Kiyya ya sata k’arasawa da sauri tana fatan Allah yasa Kiyya Barci take. “Yasmin ina Zakiyya?” Yasmin ta d’ago kafin ta ce “Ya Zayyad, ya zo ya tafi da ita d’akinsa….” Idanunta ta ji şuna rufewa bayan Jin furucin Yasmin bata san sanda ta nufi part d’in Mommy ba don ta San tunda aka ce d’akinsa to Ana nufin d’akin Mommy tunda nata part d’in a rufe yake. Shiru ba kowa part d’in ta k’arasa bakın k’ofar Zayyad Tana kiran sunan Kiyya, Jin shiru yasa ta shiga cikin d’akin….. Zuciyarta ta buga da k’arfin gaske kafin ta kurma ihu tana furta “Wayyo Jadda, Wayyo Jadda Kiyya Jadda Jini ne yake fitowa kin ga…..” ta furta idanunta yana fad’awa cikin na Jaddan da ta kafawa Zayyad ido. Jikinsa kawai rawa yake idanunsa a lumshe hawaye na zubowa daga cikinsu..




JIKAR NASHE✍🏽