19
BABBAN GIDA…..
New.
NAZEEFAH SABO NASHE✍🏽
***.
19…
Mommy Hajara ta kafa masa ido, tana jin wani irin tashin hankali yana ziyartar zuciyarta “Me na aikata?” Shine abinda zuciyarta take tambayarta ta ji kanta ya yi wani irin tsawa da ta tuno abinda ta aikata d’in. Me yasa k’addarar zata fad’awa Zayyad? Sai ta ji zuciyarta na wani irin bugu. Ta dinga tuno abinda ta aikata d’in…
Kafin zuwan ranar, abubuwan duniya sun taru sun mata yawa, musamman da taji Labarin Mahmud ya fito zab’e ya tsaya matsayin House of Representatives da dukkan alamu kuma matasa za su bashi had’in kai. Hakan na nufin Nanna zata cigaba da shan gabansu akan dükkan komai. Zata sha gabansu wajen sanya gwalagwalai hawa motoci masu kyau, da sanya manyan laces shadda, da atamfofi da a kullum sune nata burin? Nanna zata cigaba da fita k’asashen waje tana walawa. Me yasa koda yaushe Nanna take sama da su? Anya kuwa idan ta cigaba da kallon ruwa kwad’o ba zai mata k’afa ba kuwa? Me zata yi ta rushe dükkan farin cikinsu? Ta dinga shiga wajen Malamai tana addu’ar Kada Allah ya bawa Mk nasara a zab’en da zai iya, idan har zai yiwu tana son duk wata nasara ta Mk ta zama ta Mijinta, ya zamana Mijinta ne gaba akan komai a gidan. Hakan bata samu ba domin kuwa sanda aka zo sanarwar zab’e sai aka sanar da Mk shine ya lashe zab’en yankinsa. Wannan karan ma burina bai cika ba kenan? Ta furta tana datse leb’enta had’e da zubawa Tv ido, wani irin b’acin rai Yana ziyartar ta. A güjen da Zayyad ya shigo shi ya sake hassalata. Ta watsa masa wani kallo da ya saka shi danne abinda yazo fad’a na murnar lashe zab’en Uncle d’insa da yake. Idanunta sai da suka bashi tsoro don kuwa bak’in cikin ya kasa dannuwa a wannan lokacin. “Gudun Uban me kake ka shigo min da ihu? Kamar kana hauka.” Ya sunne kai muryarsa a hankali ya furta “Mommy kowa yana can yana murna Uncle ya lashe zab’e ke ban ganki ba, shi yasa na ce Bari nazo na gaya miki ko baki sani ba ne.” Ya fad’a yana kallon Tv don ya tabbatar ta gani a tashar da ake nunowa. “Idanunka ya nuna maka na gani ko? To kama gabanka ka bar wajen nan kafin na cusa maka zagi, mara kishin kansa kawai, Ubanka ne ya ci zab’en da kake murna har haka? Shashasha kawai.” Sai ya juya sum sum ya fice. Sosai ta yi hak’ilo wajen daidaita nutsuwarta bayan ta wanke fuskarta saboda hawayen bak’in Cikin da suka cikata sannan ta nufi sashen Hajja inda anan take juyo İface ifacen mutanen gidan. Da wanda suke na gaskiya da wanda pretending suke kamar dai ita.
Da ta shiga da wata irin murna idanunta akan Mk tana furta “Kai Alhamdulillah, bana jin Akwai Wanda ya kai ni farin ciki a wannan wajen, Allah yasa rai ya amfana Uban Zayyad sha alwashi…” Cak Zayyad ya yi tsananin mamakin mahaifiyarsa yana sake girmama a zuciyarsa gani yake kamar mafarki yake, da gaske Mommy kamar wahainiya take, me yasa take irin wad’annan abubuwan. Jin an jashi da k’arfi ya dawo da shi cikin hankalinsa sai ya saki ajiyar zuciya yana kallon Mommy da take matse hannunsa da k’arfi Hakan yasa ya kallo cikin idanunta, sai yaga alamar tana masa gargad’i. Ya lumshe idonsa kawai alamar ya amsa. Sannan ta isa da shi wajen Zayyad da yake ta kiransa a yi hoto. “P.A na, ya na ganka wani sukuku da kai?.” Mk ya furta yana sakarwa Zayyad Murmushi Zayyad ma Murmushin ya sakar masa kafin a hankali ya furta Nothing Uncle.
A ranar barci gagarar Mommy Hajara ya yi, ta dinga tufka tana warwara kafin zuciyarta ta amince da shawara guda da ta dinga bawa kanta, bata san abinda zata aikata zai juye kan d’anta ya zame masa bak’in cikin da har abada ba zai daina tuna shi ba.
Ta d’aga waya da sassafe ta kira mai aikinta, da suke ta gyaran gida saboda walima da aka shiryawa Mk, za’a gudanar da ita a yammacin ranar. Shiru Kuluwa ta yi idanunta a kan Uwargijiyarta tana jiran jin umarninta. “Wannan karan Kuluwa bana son shirme, kuma aikin Ina son ki aikata shi a sanda kika fuskanci uwar yarinyar nan bata gida, so nake da zarar an aikata shi burina ya cika, bana son kowane kuskure Kuluwa, a wannan karan ina son ki kawo k’arshen abinda yake raina game da Mk da y’arsa da Matarsa, ina son na dasa musu wani bak’in ciki da har abada ba zasu manta ba….” Kuluwa ta jinjina kai kafin ta furta “An gama Uwar d’aki na.” Murmushi Hajara ta yi kafin ta mik’a mata wani k’ullin magani. “Bayanin yarda za’a yi amfani da shi, yana ciki Kuluwa bana son a Samu kuskure.” “Ranki ya dad’e nasara tamu ce In sha Allah.” Kuluwa ta amshi maganin tana jijjiga kai. “Tsaya Kuluwa na sake jaddada miki, wallahi bana son kuskure, idan har kika aikata abinda na saka ki daidai, ina tabbatar miki da cewa kin gama aikin bauta a gidan nan, zan çıka miki jaka da makudan nairori da zasu yanke miki duk wani talauci da kike ciki. Ina son ki sani bana son surutu, duk yarda aka yi kika bari abin nan ya fito to ina tabbatar miki sai kin yi nadama irin wacce baki tab’a yi ba a duniya.” Kuluwa ta jijjiga kai. A hankali ta fice daga sashen jikinta na rawa.
Mommy Hajara na zuwa nan a tunani ta yi saurin furta “Na shiga uku, me yasa Zayyad?” Hakan da ta yi ya ja hankalin jama’a kanta, musamman Nanna data kafa mata ido, tana nazarinta. Jikin Hajara ya fara rawa tana kallon yarda Kiyya ta sandare uwa Gawa. Murya na rawa ta ce “ Amma kamata ya yi ku kaita asibiti da sauri ko?” Wani irin abu Nanna ta had’iye kafin ta ce “A wannan karan wallahi duk abinda ya samu y’ata ba zan hak’ura ba…..” Hajara ta runtse idonta tana jin yarda zuciyarta take bugu sosai…
Mu huta daga tunanin baya, mu dawo labari…….
Tsit parlorn ya yi kowa yana kallon Kiyya. Jadda ma idanunta ne kawai suke zubar da hawaye tana tuno abinda ya gabata. “Zo ki zauna Zakiyya.” Har a lokacin jikin Mommy Hajara rawa yake, sai dai zuciyarta a cike take da bak’in cikin wannan lamari. Baba Babba ne ya gyara zama, don tun bayan rasuwar Baba Alhaji ya zama shine mai zartarwa a gidan Zawiyyan, a yanzu kuma a jajirce yake wajen yin hukunci na gaskiya, koda ba da son matarsa Hajara ba. Don duk wani bak’in halinta ya bayyana. Ya ja ajiyar zuciya yana kallon Nanna da ta yi k’asa da idonta don ta san dole ne ta amsa duk wata tuhuma da za su mata yau. “Nanna, me yasa kika b’oye mana gaskiyar zance? Ki ka ce Zakiyya ta mutu alhali ba haka bane.” Nanna ta runtse idonta tana d’auke Hawayen da suke zubo mata. Murya cike da rauni ta ce “A wannan lokacin hakan ne kawai abinda ya dace na yi Baba Babba, ba ni da zab’in da ya wuce haka, ina gudun rasa Zakiyya ba kuma na san a cigaba da irin abubuwan da aka dinga yi.” Jadda ta girgiza kai kafin ta furta “Yayansu, duk wata tashin tashi na ta wuce haka don Allah, ko waye a mahallin Nanna, iya abinda zai aikata kenan a tunani na, yanzu ba gashi komai ya wuce ba, don haka don Allah a bar maganar haka, a farko nima na ji haushi, amma da maimartaba sarkin Bauchi ya yi min bayani sai na ji zuciyata ta samu nutsuwa na kuma gamsu da dukkan hujjojinsu abinda ya Riga ya wuce ya wuce har abada, a kuma yafi juna don Allah, sannan zan yi jan kunne da babbar murya koda wasa kada wancan abinda ya farun ya sake faruwa don idan hakan ta faru a wannan karan bana ji zan yiwa kowa Uziri wallahi. Magana ta wuce Zakiyya ta dawo shikkenan fak’at..” Daga haka ta yi shiru. Jama’ar parlorn ma shirun suka yi, sai y’an mata da suke ta kallon Zakiyya suna murmushi nan kuma kowa ya fara rungumeta ana sake sabuwar gaisuwa. Wani irin farin ciki ya dinga lullub’e Zakiyya, har kullum da son faruwar hakan take kwana take tashi a zuciyarta sai gashi Alllah ya cika mata burinta. Idanunta ne ya sauka a kansa, ta ga yana kallonta yana murza goshinsa. Wani abu ta ji ya tsaya mata a wuya kafin ta zuba masa harara ta kuma d’auke idonta tana cije lips d’inta. Hajara ce ta lura da kallon ta ji wani abu ya tsaye mata, koda yake a yanzu ba sai an matsa ba zata sake jaddada batun auren Zayyad da Zainab. Sai ta ji sanyi a ranta ta san ko me za’ayi Nanna da Mk ba zasu bawa Zayyad Zakiyya ba, tunda sun san da saka ranar y’ar Uwarsa a kansa. Ya zama dole a wannan lokacin ta b’oye k’iyayyar Zakiyya a ranta, don ta san yanzu kowa zai zuba mata ido ne, ga furcin Jadda da ta tabbatar ba zata d’agawa duk wanda ya yi shirin wargaza musu zumuncinsu ido ba, zata tabbatar ta d’au k’wakkwaran mataki a kansa. Sai ta had’iye zilamarta ta kalli Kiyya tana furta “Zakiyya, don Allah ki yafe abinda ya wuce….” “Na kashe wannan maganar…” Nanna ta furta a hankali da sauri ba don komai ba bata son tuno abinda ya Riga ya wuce. Sai Hajara ta yi shiru tana janye sauran furucin nata. A haka kuma duk aka watse. Yasmin da ta kasance Sa’a ce ga Kiyya y’ar wajen Mammy Sharifat ta damk’e hannun Kiyyan suka fita daga wajen…
B’angaren Ammi suka nufa cikin farin ciki da annashuwa. A Bedroom d’in Ammi ranar suka kwana ita da Yasmin. Bayan sallahr Asuba Kiyya ta shiga wanka sannan ta zura Sport wear ta fice daga bedroom d’in don zuwa motsa jiki kamar yarda ta saba. Cak ta tsaya daidai lokacin da ta shiga field d’in ta hangoshi yana nasa training d’in. Zuciyarta ta ji tana wani irin tafasa kamar zata juya sai kuma ta taka ta nufi inda yake……
JIKAR NASHE✍🏽