BABBAN GIDA

20

by @nazeefanashe

BABBAN GIDA…

NAZEEFAH SABO NASHE.


***.

20…



Idonsa ya zuba a kanta, yana mamakin yarda lokaci guda ta canza, a yanzu dai kam ba waccan Zakiyyan Barbiensa mai majina a hancı ba ce, ba rigimammiyar Kiyyansa ba ce. Wata budurwa yake gani mai aji a gabansa ta tattara girarta ta tsuke tana masa wani irin kallo da ya kasa fassara shi. Cak numfashinsa ya tsaya bayan da yaga ta saki wani murmushi kafin ta juya ido ta furta “Morning….” Sai kuma ta juya ta shige shi. Mutuwar zaune ya yi idonsa a lumshe yana shak’ar daddad’an turarenta da ta bad’eshi da shi a wajen. Judging d’inta ta fara yi ba tare da ta sake kallon ko inda yake ba. Zayyad dai yana zaune yana kallon duk wani motsinta, komai nata yana cigaba da burgeshi. Itace ita ce matar da ya dad’e yana nema, ita ce matar da yake so ta maye gurbin duk wata mace a wajensa…. Zuciyarsa ya ji ta buga da k’arfin gaske daidai lokacin da raunatacciyar zuciyarsa ta tunasar da shi girman wancan aibu nasa, bayan haka ma ya san ko zai mutu ya dawo Mommy ba zata bar wancan muradın nasa ya çıka ba. Yana kallo ta taho da alama wucewa za ta yi cikin gıda. Wannan ne damar da kake da ita Zayyad na neman afuwar laifukanka. Ya tuna haka a zuciyarsa don haka cikin husky voice d’insa ya furta “Barbie…..” kamar ba zata tsaya ba sai kuma ta tsaya cak idanunta a cikin nasa. “Zo mana pls!” Ya ce yana gyara zamansa.”Na maka me?” Ta fa’da fuskarta a d’inke kamar bata tab’a dariya ba. Ajiyar zuciya ya sauke kafin ya furta “Pls mana, don Allah.” Shi da kansa mamakin kansa yake, ganin yarda yake kwantar mata da murya. “Ba sai na zo ba, ka fad’i abinda za ka fad’a don Allah. Barci nake ji.” Ya lumshe idonsa ya girgiza mata kai. “Je ki later, za mu yi magana.” Bata sake kallonsa ba ta juya ta fara tafiya da sauri a ranta tana tuna sunan da ta ke kiransa da shi a bayan idonsa. Ya Zalimu. Ko ta ce “Yaya Mugu.” Tuni idanun Zayyad suka cika da wani irin hawaye ba don komai ba sai don hango tsantsar tsanarsa a idanun Zakiyya.


Itama ranta a b’ace ta koma cikin gidan, tana jin yarda zuciyarta take fitar da wani irin huci. Ta shiga parlornsu idonta ya fad’a kan Abbi da Amminta. Da sauri ta isa wajensu ta kama su Zuhair ta rungumesu bayan ta manna musu peck a kumatu. Sannan ta sunkuya ta gaishe da Abbin da Ammin. Mk murmushi kawai yake yana jin wani irin farin cikin had’uwar kan iyalinsa, kamar yarda ako da Yaushe  yake mafarkin hakan. “Kiyya, daga ina haka da sassafe?” Tana murmushi ta ce “Na je field Abbi.” Da kansa ya had’a mata tea ya tura  gabanta. Kamar yarda take tun da da bata son Çin abinci yau ma cookies biyu kawai ta d’auka sai ruwan tea da ta kurb’a ta sha berries. Sai ta ajiye cup d’in idonta na lumshewa ta shiga bedroom. A sannan ne Zayyad ya shigo Mk yana ganinsa fara’ar fuskarsa ta k’aru. Sosai ya amsa gaisuwarsa kamar yarda Ammi ma ta amsa masa cike da kulawa ta ce “Zo ka yi breakfast mana.” A hankali ya girgiza kai yana jin kunyarta na sake rub’anya a zuciyarsa. “Ina Azimi Ammi.” Ammi ta kalleshi da mamaki kafin ta ce “Azimi kuma Zayyad? Yau fa Tuesday, kuma ba tsakiyar wata ba balle na ce Ayyamul beed ka ke.” Murmushin ya sake yi yana yin k’asa da kansa ya ce “Na sani Ammi, ina yi ne na godiya ga Allah da ya dawo da Kiyya ina raye sannan ina yi ne don Allah ya yafe min kuskuren da na aikata….” Sosai idonsa ya tara k’walla, jikin Nanna da Mk ya sake sanyi. Sai kawai ta kalli su Zuhair ta furta “Oya, ku je cikin gıda ku gaida Jadda kafin lokacin Islamiyya ya yi.” Zuwa lokacin hawayen da yake k’ok’arin dannewa tuni suka fara zubo masa kamar an kunna famfo. Mk ya shiga shock sosai tun bayan faruwar wancan lamarin bai sake ganin wannan hawayen a idon Zayyad ba, gwara ma sanda Baba Alhaji ya mutu. “Ya İsa Yayansu, komai ai ya wuce, na tabbatar koda ba laifinka ba ne, kuma da yarinta a lokacin iya kad’ai halin daka shiga bayan faruwar hakan, ya İsa ya şaka mu goge aibunka a wajenmu. Don haka a wajenmu dai a yanzu bama tare da wani tabonka a zuciya ka k’addara ma bai faru ba….” Sosai ya ji dad’in kalaman Ammi, ya ji ya samu relief sosai, Hak’ik’a zuciyar Ammi mai kyau ce, da wata ce ba zata tab’a yafewa ba. “Share hawayen Zayyad, Allah ma muna masa laifi ya yafe balle mu y’an Adam.” Ya girgiza kai bayan ya share hawayen a hankali ya ce “Ina son a rok’a min Zakiyya ta yafe min, don naga har yanzu tana min kallon tsana….” Ammi ta jijjiga kai “Zata daina In sha Allah, kada ka damu ka ajiye kowace damuwa ka fara facing shirye shiryen bikinka da ya gabato….” Ai kamar Ammi ta watsa masa garwashi, haka ya ji maganar ta masa dirar mikiya a zuciya. Shaf ya manta da wannan abinda yake jiransa. Gumi ya fara zubo masa Ammi duk tana kula da shi sai dai ta d’auke kai tana jinjina lamarin uwa irin tasa, data fifita soyayyar zuciyarta fiye da farin cikin d’anta. “Tashi ka je ka huta Zayyad, sannan Abbanka ya ce shi zai shirya lefe ba sai ka yi komai ba….” Girgiza Kai ya yi kafin ya furta “Aa Abbi, don Allah kada ka d’orawa kanka wahalar komai.” Abbin ya masa wani kallon da ya saka shi janye idonsa daga kan Abbin, ya kuma mik’e jiki a salub’e ya bar part d’in. Abbi ya saki ajiyar zuciya kafin ya ce da Nanna “Me kika fahimta da lamarin yaron nan.” Nanna ta danne abinda yake ranta don ba zata bawa Mk damar da zai gane ta gane inda Zayyad ya dosa ba. Ina ai sam ba zata iya ba, idan ba so take faccalolinta su had’u su kasheta ba ita da y’arta. Zayyad da Uwarsa take jin yanzu ta haifi duniya saboda matsayin arzikin da ya taka, ta san ko za’a mutu Hajara ba zata tab’a amincewa Zayyad ya auri Zakiyya ba, don haka dole ne ma Zayyad ya hak’ura ya auri zab’in Uwarsa Zainab kuma Yar Aminiyar Uwarsa. Jin ta yi shiru sai Mk kawai ya shanye abinda yake ransa shima. Ya mik’e ya nufi fita. 


Tana dawowa daga raka Mk, ta nufi d’akin Zakiyyat inda ta tarar ta fito wanka kenan. Tana ta aikin shafe shafe. Murmushi Zakiyya ta saki kafin ta ce “Ammi na zo ne?” Ammin ta mata dakuwa tana zama geffen gadon kafin ta ce “Kiyya kin raina ni fa.” “Ammi na san fa kin yi kewata, yauwa Ammi wai don Allah ya aka yi duk mutanen gidannan basu san ina da rai ba, kuma an ce suna zuwa Bauchi biki fa.” Ammi ta ce “Ai duk sanda za su, kwashe duk wani hoto naki nake saka a yi kuma baki ga kema ba na Bari ki zo Nigeria ba? Ni ba wannan ba magana ce ta kawo ni.” Zakiyya ta gyara zamanta sosai tana cigaba da d’aure gashin kanta.  “Zakiyya, bana son irin kallon da kikewa Zayyad, tabbas an san ya yi laifi amma tabbas ba laifinsa ba ne, a lokacin ba shi da k’wanjin da zai sarrafa zuciyarsa wajen yak’i da aikata abinda yake ba daidai ba, ya yi k’arami da yawa don haka Ina son ki cire wancan tunanin nasa na mak’iyi a zuciyarki, tunda na haifeki kaf gidan nan ba wanda bai san kalar k’aunar da yake miki ba, ya kuma shiga tashin hankali musamman sanda ya ji labarin mutuwarki, da k’yar aka samu tunaninsa ya dawo daidai. Don haka zan sake gaya miki Zayyad masoyi ne ba Mak’iyi ba.” D’an turo bakinta ta yi, tana cije leb’e ta ce “Ammi duk abinda ya yi min ya ci buluş kenan?” Tsuke fuskarta Ammin ta yi “Ya ci Buluş Zakiyya, in dai ni nahaifeki ki k’addara taku jarrabawar ce haka ke da shi.” Shiru ta yi idanunta a lumshe tana zubar da hawaye. “Umarni nake baki Zakiyya bana son ki nuna masa ban İsa da ke ba don har ban yazo ya rok’emu mu rok’a masa afuwarki.” Ta yi shiru tana cigaba da jin yarda Ammi take mata nasihar da ta ragargaza duk wata k’iyayyar Zayyad da take zuciyarta ya dawo ma yana bata tausayi. Ammi ta shafa kanta tana furta “Allah miki albarka ya baki Miji na gari.” Ta sunne kanta alamun jin kunya tana sakin murmushi. Ammi ta yi murmushin itama. 



Koda ta fito harabar gidan shiru da alama kowa yana mahallinsa a hankali take taku tana sake tuna rayuwar baya duk da gidan an masa canje canje amma still tana tuna duk wani memory na baya. “Ai sai ki tsaya, da kika fito kika bar ni kuma baki dawo ba, tun d’azu nake jiranki mu karya.” Zakiyya murmushi ta yi ganin yarda Yasmin ke zuba mata harara. “Sowie kin ji Habibty, daga wajen training na ji ina son ganin Ammi sai kawai na tafi wajenta.” Yasmin ta zuba mata harara kawai kafin ta ja hannunta. “Kawai dai kin tafi shikkenan kuma Mami ta ce ki zo yanzu.” “To mu je mu gaida mutanen gidan tukun.” Part part na Zawiyya family suka dinga shiga duk inda suka je kadaran kadahan ake amsa gaisuwarsu banda Mommy da ko kallon sashen da suke bata yi ba, ta amsa a ciki ciki tana kallon Mai aikinta ta ce “Idan kin gama ki kira min Zayyad a Challet yazo na bashi list na kayan lefen nan…” Kiyya jikinta a sanyaye ta fito Yasmin kuwa tab’e baki ta yi a hankali ta kama hannun Zakiyya ta ce “Sai ka ce Zayyad d’in son auren yake mun san fa komai. Bari mu dawo daga wajen Jadda na baki labarin bak’ar dagar matar nan.” Duka Zakiyya ta kai mata a leb’e ta ce “Baki da kai, Babbace fa.” Yasmin ta sake tab’a baki suka shiga wajen Jadda. Sosai Jadda ta karb’esu da fara’a ta kama Zakiyya ta zaunar da it daf da ita tana shafa kanta. Ta ce “An tashi lafiya? Jiya kuma madadin ki zo nan mu kwana kawai sai na ji shiru….” “Allah rabani da kwana a gadon tsohuwa….” Ta furta tana Gatsine baki. “Halinki yana nan kenan takwara? Allah ya shiryeki, zuwa yanzu dai na san kin fitar da Miji ko? Ko kema kin tsaya irin ta wannan figaggiyar mai son karatun boko.” Yasmin ta turo baki tana furta “Wallahi ki daina ce min figaggiya kamar wata kaza, to haka kawai nawa nake da za’a dinga min maganar aure.” Zakiyya kuwa shiru ta yi tana murmushi don a duniya idan akwai abinda take jin Kunya to ka mata maganar aure, ita saurayi ko magana ya mata gudu take sawa. A haka ne ake ganinta kamar wayayyia sai dai tsoro ne fal a cikinta. “Ai shikkenan idan baku fitar ba ai na bada ku sadaka.” Zakiyya ta yi shiru kawai. Sun dad’e a wajen kafin su tafi. 


“Kina gaya min, yanzu auren dole za’a musu kenan?” Zakiyya ta fad’a tana kallon Yasmin da ta cikata da labarin yarda Mommy take son yiwa Zayyad auren dole. “Auren dole za’a musu ko auren dole za’a masa? Itafa Zainab in gaya miki sonsa take kamar ta mutu.” “Ai kuwa ta had’u da jidali, masifarsa kad’ai ma ta isheta wallahi. Mutum ko fara’a ba shi da ita, ina kuwa wannan sunan da muke gaya masa Yaya Zalimu, har yau ana gaya masa?” Yasmin ta shek’e da dariya ta ce “Mhmn, ai wa zai sake gaya masa bayan ranar da ya kama mu muna gaya masa ku san hallaka mu ya yi.” Zakiyya ta tab’e baki kafin ta kwanta ta lumshe idonta saboda barcin da take ji.



A hankali ya tura k’ofar sashen Mommyn yana jin yarda gabansa ya ji yana duka, ya san ko me yasa ta kira shi ba lallai ya zama alheri ba. Fuskarta a had’e take sosai ta zubo masa ido tana nazarinsa. “Ka gama da gurin Uwarka Nanna kenan, ka zo ko? Kai ni dai wallahi haihuwa bata yi min rana ba na haifawa Nanna d’a. Dama Jan kunnenka zan yi game da wancan kod’addiyar yarinyar wallahi ba kai ba ita, zan sake jan kunnenka da k’arfin murya wallahi ban amince ka dinga kukata ba, idan kunne ya ji jiki ya tsira, ga kuma list nan na lefe da zaka had’a….”  A saman kansa ya dinga jin furucinta. Zuciyarsa ya dinga jin tana wani irin rawa kamar ma zata fito daga k’irjinsa…… “Bana son ta Mommy, Barbie nake so Kiyya zan aura…Pls Mommy…”



JIKAR NASHE✍🏽