23
*BABBAN GIDA….*
New…..
**NAZEEFAH SABO NASHE✍🏽*
BRIGHT PENS.
**I DEDICATED THIS BOOK TO NA’IMA SULAIMAN SARAUTA.**
0803374837.
GODIYA MARA IYAKA DA JIKAR NASHE REAL FANS GROUP… hope wannan karan ma za ku karb’i Babban gida kamar yarda kuka saba karb’ar kowane irin book nawa. Na gode sosai sakamakon Aljanna gareku In sha Allah.🥰
***
Don samu da daga farko a shiga channel dinnan.
**YOTA004**
22.
Ta amsa sallamar tana saurin gyara zamanta, shi kuwa Zayyad tsuke fuskarsa ya yi ya d’auke Kai daga kallon Zainab d’in da ta kafe idonta a kansu tana musu wani irin kallo. Zakiyya murmushi ta saki kafin ta furta Amaryar mu, ki shigo mana.” Kamar ba zata shigo ba sai kuma ta shiga ta zauna a gefen Zayyad kamar zata shige jikinsa, har sai da ya d’an motsa kad’an. Kiyya da take kallon komai ta gefen ido kawai ta saki murmushi kafin ta mik’e tana fad’in. “Tunda amaryarka ta zo Bari na je Ya Zayyad, Allah ya k’ara sauk’i.” Wani kallo ya zuba mata, kallon da yasa Zainab shiga wasi wasi, wani kallo ne da ko ita da yake shirin Aure bai tab’a yiwa shi ba. “Kada ki tafi.” Ta tsinci muryarsa da take tattare da alamun bada umarni. Juyowa ta yi don ganin ko da ita yake. Sai ta sakar masa murmushi kafin ta furta “Me yasa zan zauna? Bayan ga Aunty Zee ta zo, Ammi na jira na akwai abinda zan mata…” bata jira cewarsa ba ta saka kai ta fice. “Na baki Umarni, kin nuna min ban isa ba ko?” Ta kalli text d’in kawai ta share ta cigaba da tafiyarta. “Shikkenan, zan shigo anjima, saura kuma ki yi barci.” Wannan karan sai da hakoranta suka fito da murmushi. Da alama ba zata sha wahalar sukurkuta bawan Allahn nan ba. Ta cije leb’enta kawai tana tafe tana wak’arta zuciyarta cike da nishad’i ta shiga parlornsu. Yasmin ta bita da kallo. “Ke kuwa ina kika shige tun d’azu nazo mu kalli Sayyaara, an ce an d’ora a Netflix.” Zama ta yi tana tab’e Baki ta ce “Ke baki da Wata damuwa ne, sai ta kallo Habibti. Ina wajen Yaya Zayyad part d’in Jadda.” Yasmin ta gyara zama tana cewa “Ba zaki gane kalar soyayyar da aka zuba a film d’in nan ba, Ya Allah ka bamu
Mazaje irin wannan mijin na cikin Sayyaara…” “Ya baki dai, kada ki sake sakawa da ni, ni fa nafi son na auri matured mutum ba masu soyayyar yen yen yen d’in nan ba.” Yasmin ta mata shiru kawai ta danna kallon suka fara. Tun Kiyya bata bada hankali ba har film d’in ya tafi da dukkan nutsuwarta don kuwa da gaske soyayyar ake bata wasa ba. Bata san sanda ya shigo ba, kamar yarda bata san sanda Yasmin ta tashi ta bar wajen ba, sai ji ta yi kamar daga sama ya ce “Tunanin me kike?” A razane ta kalleshi, ta ji ta daburce saboda scene d’in da ake nunawa bai kamata a ce tana kallonsa ba yana wajen, Scene ne da ake nuna yarda guy d’in film d’in yake mannawa yarinyar wani zazzafan romancing da Kissing. Wani irin kallo ta dinga hangowa a kwayar idonsa da ya sata saurin janye idonta ta kuma d’au remote d’in zata kashe, ya yi saurin cewa “Kada ki fara Malama…” Ta yi saurin kallonsa a yarda ya yi maganar sai ta ji kamar ba shi ba gaba d’aya muryar ta koma cikin wani irin sanyi ko don whispering ya yi. “Ajiye remote d’in mu yi kallo, dama irin films d’in da kuke kalla kenan ko? Hakan ya nuna aure kike so?” Ta waro ido da sauri kafin ta ce “Ni na ce maka ina kallo, wannan ma Yasmin ce ta ja min nake kalla, ban san ma ina ta tafi ba?” Yasmin gyara zamansa ya wani lumshe idonsa, zuciyarsa ce take harbawa da k’arfin gaske da da hali tabbas a yanzu zai nuna mata kalar wannan soyayyar. “Hot Chocolate pls, Barbie…” Sai da ta sake kallonsa sannan ta mik’e ta nufi kitchen a ranta tana furta “Shegen kwad’ayin tsiya ko me ya sha ba zai sha black tea ba sai Hot chocolate…” Tana mita ta had’a masa ta d’ora a tray ta saka a ranta tana zuwa zata dire masa ta gudu. Tana shiga parlorn idonta ya kai kan screen d’in Tv d’in, bata san sanda ta saki tray d’in ba, Tea d’in ya zube cup d’in ya fashe…. Da sauri ya kalleta ya ga jikinta har rawa yake ta yi saurin juyawa ta shiga kitchen ina sam ba za’a yi wannan abin kunyar da ita ba. A kitchen d’in ma sai da ta murza Key. Zayyad ya dinga kallon k’ofar yana murmushi a ransa ya ce “Ashe dai Akwai kunya a tare da ita, hakan na nuna da bata zubar da tarbiyyarta ba duk da ta tashi a cikin turawa.” Yasmin ya saka ta yi clearing wajen kafin ya fice zuwa Challet. Yasmin ta isa bakin kitchen d’in tana furta “Kiyya ki bud’e mana.” “Ba zan bud’e ba Yasmin, don Ubanki ki kashe wancan banzan film d’in da kika saka.” Yasmin dariya take sosai don itama taga abinda Kiyyan ke gujewa. “Ki bud’e Malama ya tafi.” Zakiyya ta bud’e tana hararar Yasmin ta ce “Munafukar banza, kin cuceni yanzu ba sai ya zata irin kallon da muke yi ba kenan?” Yasmin ta tab’e Baki ta ce “To meye a ciki sai kace wani saurayinki, duk kin bi kin wani diririce…” “Au bakomai ko?” Zakiyya ta furta tana kama baki cikin mamaki, kin ga kuwa abinda nake nufi?” Yasmin ta cilla mata Mop d’in tana furta “Ni banga komai ba wallahi, sai zallar Love, ke wallahi kamar ba rainon turai ba, an fa waye yanzu.” Kiyya ta jijjiga kai tana d’aka mata duka ta ce “Eh, to ya zama lallai na binciki wayarki don lamarinki ya fara bani tsoro.”
Koda ta zo barci, tunanin film d’in ta dinga yi, wani irin feeling da bata tab’a jinsa ba ta dinga ji, shi yaşa sam ba ruwanta da irin wannan kallace kallacen, yau kawai Yasmin ta janyo mata. “Pick the call Malama, wannan wayar take na neman hana ni hira da Lovy.” Yasmin ta furta tana cilla mata wayarta da Zayyad yake ta kira kuma ta k’i d’agawa. Silencing wayar ta yi ta sake jan pillow ta rungume a jikinta tana sakin ajiyar zuciya. Ta yaya zata iya d’aga wayar ta ce masa me? Bata jin nan kusa zata iya had’a ido da shi. “Barbie, pick the call mana.” Ya turo mata text d’in, sai ta dinga jin kamar a kunnenta yak’e whispering mata maganar, ta ji tsigar jikinta ta wani irin tashi, da sauri ta danna Off button ta kashe wayar. Kafin ta runtse idonta da k’arfi tana fatan Allah yasa barci ya d’auketa.
Kwana uku ta yi tana gujewa had’uwa da shi, zuwa lokacin duk wasu shirye shiryen biki sun fara kankama. Kuma kamar yarda Mommy take so haka ya sakar mata kud’i kamar baya so, don ya lura kud’in ta fi so fiye da farin cikinsa.
Ranar ta zama Sunday ne,sai 11:00 suka tashi a gaggauce suka shirya don fita gaishe da Jadda, ta dinga kallon wayarta tana kallon kalolin msg d’in da Zayyad yake turo mata na alamar fushi. Murmushi kawai ta yi kafin a karan farko tun bayan afkuwar lamarin ta mayar masa da amsa da fad’in. “Am sorry, ba zan iya ganinka ba ne, ina jin kunya fa.” 😳 wannan Emojin ya turo mata sai kuma ya ce “Me yasa za ki ji kunyata kamar wani saurayinki? Ko dai?” Ta ce “Ko dai me?” Sai ya turo “Mhmmn, kawai dai pls idan ba wai kina jin feeling a kaina bane to ki yarda mu had’u.” Ai bata san sanda ta sauka daga whatsapp d’in ba. Me Yaya Zayyad yake son ya ce ne? Wata irin kunya ta kamata, daidai lokacin da suka isa parlorn Jadda, da kuma wani karad’i suka mata sallama. Jadda ta ce “To fa! Yau fa ba sarki sai Allah, me ya kawoku? Ku da nace na bawa hutun sati guda?” Zakiyya da Yasmin Suka had’a hannu Suka tafa kafin Kiyya ta ce “Wai har kura ce zai ce kare maye? Ai a wajenki muka koyo surutun…” Idonta ne ya fad’a kan Zayyad da yake zaune yana danna wayarsa a saman kujera, fuskarsa a tsuke bai kuma ko kalli inda suke ba. Jadda ta ce “To Aku sarkin magana…” Kiyya ta ce “Ah to, Hajiya kawai sai na zauna na yi gum da baki, bakina ya fara wari. Yaushe zan zauna na yi jugum kamar wata kurma, ai yarda Ubangiji ya haliccemu da baki da kunne dole mu yi magana…” Jadda ta ce “Ah, wannan dai kin san da wanda kike, da Yayanku kike, shine miskili ka fi mahaukaci ban haushi.” Zakiyya ta waro ido ta ce “Kada ki fara had’a ni fa da shi tsohuwa, ni ba da shi nake ba, ku fa kuke masa kallon miskili, wallahi Ya Zayya…..” kallon da ya mata ne ya sata k’unshe bakın tana dariya. Ya jijjiga kai yana cigaba da danna wayarsa. MSG d’insa ne ya shigo wayarta “Ki iya bakin ki, kada ki saka k’awarki ta raina ni.” Ita sai ya bata dariya ma. Jadda ta ce “Kowa dai ya yi zagi a kasuwa wallahi ya san da wanda yake, wallahi da shi kike kai Yayansu ka ji abinda take fad’a ko?” Ya juya yana kallonta ya ce “Barta Jadda, zan yi maganin wannan bakın nata me shegen sürütun tsiya…” Daga haka ya mik’e ya fice daga parlorn Jaddan, don kam idan har ya cigaba da kallon Kiyya a yanayin shigar jikinta komai ma zai faruwa. “Ki nemi Hijab ki b’oye baiwar da Allah ya miki….” Ya tura mata msg ‘din yana shirin fita murmushi ya yi ganin yarda ta waro ido. Ta fara neman Hijab Tabbas ya bar mata Assignment mecece baiwar da Allah ya bata? Da sauri ta fad’a Bedroom d’in Jadda ta fara kallon kanta a mudubi. Sosai duk wata sura ta jikinta ta bayyana more especially Boobs da Hips ‘dinta. “Innalillahi…” da sauri ta furta tana neman Hijab d’in Jadda ta saka, dole ne dai ta nemi kayan hausawa ta dinga sakawa idan ba so take Ammi ta zaneta ba, don yanzu Ma don tana barci ne shi yasa ta fito a haka.
Zayyad kuwa har ya isa motarsa murmushi yake. Komai na Kiyya burgeshi yake yana jin wani irin zafi a ransa idan ya tuna remain few days a d’aura masa aure da Zainab wacce baya jinta ko kad’an a zuciyarsa.
Ta koma wajen Jadda ta zauna. Jadda tana kallonta ta ce “Ikon Allah ya bakinki ya yi tsit haka? Ai ni ina mamakin yarda Zayyad ma yake d’aga miki k’afa, su su Yasmin ai sun san halinsa…” Yasmin ta ce “Mhmm, ai ni har yanzu bana manta gwala-gwalar Yaya Zayyad, shi yasa har yau baya baya nake da shi, har mamaki nake da ake shirin bikinsa da Zee, duk da Zee tafi kowa shegen surutu a cikinmu… Kai wallahi abin mammaki…” Ta fad’a Tana tuntsirewa da dariya. Shigowar Zee ce ta saka suka yi shiru şuna dubanta. Tana ganinsu a parlorn ta tsuke fuskarta. Jadda na lura da yarda suke zamantakewarsu sam basa shiri da Zainab don haka ta ce “Ke me ye haka ne? Baki ga y’an uwanki ba ne?” Ta turo baki kafin ta ce “Jadda idan na gansu menene? Suna jira ne na durk’usa na gaishe su alhali Nike gaba da su.” Jadda ta jijjiga kai ta ce “Wannan dai ba d’abi’a ba ce mai kyau, Manzon Allah cewa ya yi idan ka shiga waje kaga wani a zaune, Kai ya kamata ka fara masa sallama, bai wani banbance Babba da yaro ba. Sam bana son wannan abinda kuke yi, kuna ji na da kyau ko?kuna y’anuwa ku dinga gaba da juna, eeh gaba mana zance tunda duk sanda kika gansu ina lura da yarda kike had’e rai. To ku kiyayeni idan ba haka ba zan saka Zayyad ya sab’a muku wallahi.” Zainab ta turo baki kafin ta mik’e ta ce “Jadda sai anjima, amma dai su zaki jawa kunne ba ni ba.” Kiyya ta waro ido ta ce “Jaddan ki ke gayawa hakan?” A zafafe ta juya wajen Kiyya don dama tana neman abinda zai had’asu ta ci mata mutunci. “Na saka bakinki ne algunguma? Mai shegen bin maza tun kina yarinya kike binsa shine yanzu ma da girmanki baki fasa ba, saboda kin sha a nonon Uwa dama k’wace shine aikinku, to wallahi in dai akan Zayyad ne na fi k’arfinki yarinya da ke da duk wani tsafi na fulanin uwarki…..” Kiyya ji ta yi ana wani hajijiya da ita, saboda yarda maganar ta mata dirar Mikiya…… “Wancan lokacin ma da kika ga komai ya faru na san tabbas ba haka kawai ba ne akwai abinda kuka k’ulla masa amma wannan karan kam na fi k’arfinki…..” Kukan kura Zakiyya ta yi ta ciri wata side lamp ta maka mata… cikin lokacin kad’an Zainab ta zube ba alamar numfashi a tattare da ita…….
JIKAR NASHE✍🏽