Baiwa ce Return

43-44

by @limzyprincess

Eh ! Kina raina ako dayaushe kinsan da cewa tun kina karama nake tare dake taya yanzu zanbarki?

Koda zaka iya rasa ranka??? Tafurta cikin mamaki

Koda kuwa zan iyayin haka sabida ina sonki  har cikin raina .....yafada yana kallonta

Ahankali tacire hannunta kan nasa tana masa kallon mamaki amman kuma ba shakka batayi shakkan dayafadi haka ba sabida tasan yana da hankali yataimaka musu ba kadan ba tun tana karama yana kula da ita baikuma taba cewa sabida yaga mahaifiyarta batanan zaice zaimata abunda bai kamata ba. Sunkuyar da kanta tayi gurin ne yadau shiru kafin yasata agaba ta cinye taas yanajin alaman akwai wanda zaizo ya dauki kwano ya shafa kanta alaman ta kuka da kanta dasauri yabar gurin zuciyansa a tsorace...

Yana tafiya yana tunani yasan cewa moolah tayi  wayo yanzu amman shin ko tasan mey ake cema so???? ... yana tafiya tayi shiru tana rarrrami da ido  maganan shafiq ne ke dawomata kunne
Ta dauki shafiq matsayin dan uwanta na jini son da take masa ba so bane na wani daban so ke na dan uwa kaman yadda takeson mahaifiyarta haka takeson sa ...
kulle idanuwanta tayi ahankali ba wanda take tunawa sai jalal da fadansa da murmushinsa da yadda yake bacci yyadda suka shaku a kankanin lokaci saikuma ta tuna yadda yamusu hukunci atake ta bude idanuwanta tana kuka mai bacin rai .....

_________

Magani dan sarki sultan yake ma wasu mata biyu agurin magana kansu akasa suna daga kai alaman suna sauraronshi kaman umarni yake basu ahaka yadagamusu hannu suka wuce daga gurin

Ahaka moolah ta kwana tana tunani tashi tayi takalle yadda shanayen suka bata gurin ... ajiyan zuciya tayi tayi shiru tana kallon yadda gurin yake gashi gurin yadau wari ba kadan ba.... daker ta tashi tafara sharewa duk bayanta ciwo yake mata sabida bata saba aikin wahalan nan ba duk da basu da komai amman mahaifiyarta tana kula da ita kuma komai tare suke cikin annushiwa har ma su manta aiki suke......

 Tana gamawa da dau tuluun da take deban ruwan da za taba dabbobin ta je debowa ta debo kafanta yafi a irga .... tana tafiya agajiye take bata ma iya kallo sosai sabida rana ake sosai tayi tafiya mai nisa kafin tadan zauna ta huta ahaka takara tashi sabida tasan wayennnna dogarayin ba mutuncine dasu ba zasu iya mata hukunci munmuna ....... tana kan tafiya kenan kawai ta hango sarki jalal yana  tunkaro inda take . Zuciyantane yabuga ba shiri tayi sauri tashige gefe ta juya baya sabida kota kota batason kallonsa ba kuma son su hada ido bata so zuciyanta yasa ta sanesa sabida abunda yamata ita da mahaifiyarta.....

Sanda taji gurin shiru tayi ajiyan zuciya tajuyo kenan suka hada ido  dashi ...zaro idanuwa tayi cikin tsoro bata taba tunanin yana bayanta ba....

Kallonta yake cikin nitsuwa idanuwansa suna nufi abubuwa daban wanda shi kasan bazai iya fassarawa ba...
lokacin da ta boye ya hangota shiyasa yasak dogaraye su yi gaba su jirasa

Sumar gashinta azube yake har bayan gado moolah irin matane wanda Allah yamusu gashi sosai ga tsawo ga kyau  ga kuka cika yakuna yi baki sosai .... duk da tana cikin wahala amman kyau ta ma kara fitowa yayi ,idanuwanta farare tas ga dan karamin bakinta .... ganin bazai iya deja kallonta ba
Sauke idanuwanta tayi tajuya kanta gefe .

Dan dariya kadan yayi sabida duk abunda takeyi alamane tayi fushi amman fushinta kara mata kyau yayi . Ba abunda yafi basa dariya kaman bakin nata ... bazai irga kwanaki dayayi yamanta ya ake dariya yau da yaganta wani farinciki a zuciyansa ba kadan ba.


Dagowa tayi taga yatafi still yana tsaye yana kallonta wani kallo tamasa ciki da hawaye kallon da take masa tabbas yasan mey yake nufi alamane nacewa batayi sammanin zai iya mata haka ba......

Nayi tunani kai na dabanne musanman zuciyarka nazata zuciyar ta dabanne bazata taba cutar da wani ba kukuma hukunta wani bisa abunda baidace ba amman na kuma yarda cewa duk jinin masaurautar basu da imani kansu kadai suka sani.. bakudamu da kowa ba sai kanki da kuma mulkin ku .

Tafada cikin fushi tana zubda hawaye tana kallonsa... kafin tafara ja da baya ta gudu ta bar gurin


Goshinshi ya rike yana jin yadda gansa ke juyawa da maganan moolah ..... meyasa takasa fahimta cewa duk abunda yayi yayine sabida ya kubutar da ita sabid ayabata sauki a hukunci yasan muddin mahaifinsa yayi hukunci yasan tabbas hukuncin kisa ne.. shikuma bazai iya rasa taba babu shakka yana so.. so na hakika wanda shi kansa baisan lokacin da yakamu da ita ba.

Kuka moolah ta cigaba da yi bayan tabar gurin.
______
Gurin sauraniya kuma wanda ake cema uwa ga jalal
Wato wanda tarikeshi tun bayan rasuwan mahaifyarsa (sarauniya amah )gyara zama tayi kafin tasakamasa ido tana nazari baimasan tana kallonsa ba yana cikin tunani shiru yake yana kallon wani guri na daban ya jingina kansa akan kujeran dayake zauna na masarauta bayan kafan sa kuma yamikeshu tare da hada hanneyensa a kirjinsa...

Taba hannunsa tayi jalal!
kafin yajuyo ahankali ya amsa
Jalal mey yake saka tunanine kwana biyu duk kaman ba kaiba?

Dasauri ya girgiza kai alaman babu ....
saikuma yajuya yariko hannun mahaifinsa ... nakasa warware lamarin nan...

Wani lamari???

Inasonta ! Inasonta! Sarauniya inasonta ita kadai nakeso nayi yadda zancire sonta azuciyata tunda nasan mahaifina bazai taba yarda ba amman nakasa ... naka sa daurewa naganta cikin wannna damuwan da wahala ...tana son mahaifiyarta baikamata mahaifiyarta tazama baiwar nikh ba ...

Yau dana ga idanuwanta naga so amman kuma naga nadama dakuma taimako a idanuwanta.......

Mamaki take tana kallon sarki jalal dama tasan haka zai faru tasan jalal yanason moolah ba kadan ba amman kuma taya zata bollowa lamarin nan ... tasan cewa tabbas idan sarki mulk yaji wannnna lamarin bazai taba bari ba bazai taba bari ba....
Shafa kansa tayi tana mai basa hakuri
Amman jalal kai fa yanzu sarki ne zakuma ka iya zantar da ko wani irin hukunci abi ...

Mahaifina kuma fa??? Bazaiyuba sabida inason mahaifina banason nabata masa rai tun ina karami shiyakula dani bayan ke yasoni na hakika taya zan butul cemasa naki bin umarninsa?

Shiru tayi tana nazari bazata iya jure ganin danta jalal awannnna yanayin ba... karka damu jalal zanna mafita karkadamu


FADAR SARKI MULK
Kasan da cewa dan ka jalal yanan da barinka da kunya??? Sarauniya maha tafada

Kaman yaya? Sarki mulk ya tanbayeta

Murmushi tayi kafin ta dago ido takallesa ... ashe baiwar da ya ma hukunci haryanzu yana sonta kuma ya da alama idan bakayi wani abuba zaka rasa danka ...

Dasaurki sarki mulk yajuyo yana ganinta

Jalal din?

sarki jalal sai yabaak kunya a idon masaurautar nan na moulk... kasan da cewa dokan da kakafa cewa babu soyayya tsakanin jinin sarauta da bayiii??

Ni aganina danka jalal baikamaci kujeran nan ba sabida zuciyansa bakaman naka bane zuciyansa tayi sanyi daiwa kakalla dana sultan zafin ka yake dashi kuma yana iya aikata komai amman jalal yaasaka so agaba.. wani kallo sarki mulk yamata dasauri tayi shiru kafin kuma ta dan hareresa kasa kasa takara da cewa

Toh danka zai karya dokan nan ... idan kuma ya karya mey zakamasa hukuncin mey zakamasa babu... tunda shi yanzu yazama  sarki yana kuma yin haka mutuncin ka yazube a duniya gabaki daya.



Tashi sarkii mulk yayi cikin bacin rai dasauri ta riko hannunsa ta danyi murmushi karka tada hankali sarki mulk idan da zaka barmin wannnna nizan maganceshi nakuma maka alkawari sarki jalal saidai ya aura yar jinin masaurautar badai baiwa ba...

Juyawa yayi kafin yadaga kai . Duk yadda za ayi ki tabbata kin dau hukunci dawuri kada kibari jalal yasan da abunda zaki aikata kuma ki aikata cikin gaggawa ... jalal shine dana danafiso badon komai ba sabida yanamin biyayya kuma yana tausayine banaso musamu matsala tsakaninmu dashi ... bai tantanci baiwa ba kuka bazai taba auran baiwa ba koda bayan rainane...

Murmushi tayi tana dariyan mugunta ta gefe.