AKWAI SILA

Chapter 17-18

by @amanarcool323

💦 AKWAI SILA 💦


BY AMANARCOOL 


YOTA ID/021


*SHIN RAMA CE MATSALARKI? BUSHEWAR JIKI KO KUMA MATSALAR SANYI? TO ALBISHIRINKI, NA ZO MUKU DA INGANTACCIYAR SABAYA DA AKA SARRAFATA DA NATURAL GRAINS, HERBS DA KUMA SPICES, WADDA ZA TA INGANTA LAFIYAR JIKINKU, TA CIKO DA JIKI, SAMAR DA RUWAN NONO GYARAN BREAST, TA KUMA YI MUKU MAGANIN SANYI DA MA SAURAN GYARAN JIKI NA MATA, DUK A KAN KUƊI ƘALILAN. SABAYARMU BA MA SANYA ƘWAYA A CIKINTA, DA TSIRRAI KAWAI MUKE SAMAR DA ITA. SANNAN AKWAI MAGANIN SANYI GA MASU FAMA DA MATSALAR INFECTION KOMAI DAƊEWARSA. AKWAI COMPLETE SET NA GYARAN BREAST, SPECIAL PACKAGE, KU NA IYA TUBTUƁA TA KAI TSAYE KU TUNTUƁE NI AYSHERCOOL TA LAMBOBIN WAYATA ****.


PAGE 17-18


Ya isa ƙofar ɗakin Mama, har zai yi noking sai ya fasa "Me zan ce mata idan na shiga? Taya zan yi mata bayanin abin da na gani jiya?" Ya tambayi kansa, juya wa ya yi ya koma falo ya zauna, dafe kansa da ya yi, yana jin zuciyarsa na yi masa zafi, ƙoƙarin kawar da abin da ya faru jiya yake yi, sai dai tunanin ya ƙi barin zuciyarsa.

Mama ta fito falon, ganin Jiniyo zaune a gurin ya sa ta ƙaraso da sauri ta ce "Jiniyo lafiya kuwa? Me yake damunka ne tun jiya ka kulle kanka a ɗaki? Ni da mahaifinka har mun fara tsorata". 

Ɗago kai ya yi ya kalle ta, ya ce "Mama kin taɓa ganin hallitar mutum gashi dai siffar mutum ce amma zuciyarki ta kasa yarda da cewar mutum ɗin ne?".

Kallon sa ta yi da mamaki ta ce "Kamar ya? Ban fahimci hausarka ba?". Shiru ya yi ya kasa ce mata komai, don bai san ta yadda zai yi mata bayani ba.

"Jiniyo kodai mafarki ka yi ne?".

Ya girgiza kai "Ba mafarki ba ne Mama".

"To me yake damunka? Ka yi mini bayani mana". Ya ce "Babu komai Mama kaina ne ke ciwo"

Kallonsa ta yi da kyau, tasan akwai abin da yake damunsa ba ciwon kai ba ne, ta ce "To yanzu ka tashi ka je ka watsa ruwa, ka zo ka ci abinci kafin Abbanka ya dawo, bai daɗe da fita ba wani uzuri ne ya fitar da shi. Bai musa mata ba ya miƙe ya nufi ɗakinsa, Mama ta bishi da kallo tana girgiza kai.

Tun jiya Dady ya kasa samun nutsuwa, duƙi yake a ɗakinsa hannunsa na riƙe da wata tsohuwar takarda da ya ɗakko ta can ƙasan drawer, rubutun dake ciki ya fara disashewa, kallon takardar yake, kalmomin dake ciki suna suna ƙonar masa da zuciya. A hankali ya ce "Ba zan bari tarihi ya maimaita kansa ba, ko da hakan yana nufin zan zama azzalumi a idon ƴata". Mayar da takardar ya yi inda ya ɗakko ta, ya koma zaman gadon ya zauna.

Momy ta shigo ɗakin tun daga bakin ƙofa take kallosa, ƙarasowa ta yi ta zauna "Alhaji me yake damunka ne? Ina lura da kai tun jiya walwalar ka ta ragu, kamar akwai abin da ke damunka".

Murmushi ya yi ya ce "Babu komai Hajiya, abubuwa ne suka yi mini yawa, ina Shalele ta tashi ne? Ina fatan dai ta wuce school?". "Alhaji kenan, mu bar zancen tunda baka son in sani. Auta tunda safe ta tashi, yau sai 11 za ta je school". Dady ya gyaɗa kai ya ce "Bari na shirya ina son fita da wuri ne, yau ina da baƙi".

Ta ce "To shikenan" tashi ya yi ya fara shiri, Momy sai kallosa take yi, tasan akwai abin da ke damunsa amma ya ce mata babu komai, to kodai lamarin Auta ne ke damunsa haka? Haka dai ta shiga saƙe-saƙe a ranta daga ƙarshe tashi ta yi ta fita zuwa na ta ɗakin.

Tana shiga ɗakinta a kwance ta tarar da Joriyya, ta ce "Auta yau kuma ke ce a ɗakin nawa? Hira kika zo yi mini ne? Naga kin kwana biyu baki shigo kin kwanta irin haka ba".

Dariya ta yi ta ce "Eh Momy hira zan yi miki".

"To shikenan ina sauraren ki".

"Momy idan mutum bashi da iyaye, bashi da Momy kenan shi ya haifi kansa ko?"

"To za ki fara ko?" Momy ta ce tana kallon ta

Joriyya ta kuma cewa "Momy to shi wai ina iyayensa suke ne? Nifa ji nake kamar na san shi" kafin Momy ta yi magana Dady ya shigo ɗakin cikin shirinsa.

Ta ce "Yawwa Dady zo ka ji" isa ya yi ya zanuna, ta ce "Dady idan zuciyar mutum nada kyau ana gani? Sannan ana yi mata kwalliya ko? Kuma ana shafa mata mai?".

Dady ya nisa yana murmushi ya ce "Shalele idan mutum nada kyakyawar zuciya ana sani, amma taya za a shafa wa zuciya mai?" .

Tsaki Momy ta yi ta ce "Idan ka biye mata sai ta ɓata maka lokaci da wannan shirmen nata. 

"Dady in sha Allah sai na yi karatu mai yawa, kasan wani abu Dady wallahi ba mahaukaci ba ne, kawai an manta da shi ne". "Shalele ki daina yin surutan nan mana, ki yi shiru". 


"To na yi shirun, amma Dady kaga yadda hannunsa ya yi? Me aka yi masa? Don Allah a siya masa magani, sannan mu tambaye shi ina ne gidan su".

Cikin fusata Momy ta ce "Wai ke bakin ki baya yin shiru ne? Alhaji ka tashi ka yi tafiyarka idan ka biye mata makara za ka yi". Joriyya ta ce "Ni dai tambaya ce kawai na yi, amma sai na yi karatu na zama likita in warkar da shi, ko in zama malama in koya masa karatu da yin magana, ko kuma in zama Momynsa in riƙa bashi abinci kullum".

Tashi Dady ya yi, tare da yi wa Momy sallama ya fita. Joriyya ta ci gaba da zuba wa Momy surutu kamar wata suda, idan ta saki wata maganar sai Momy ta razana, ita har tana murna daga jiya zuwa yau ƴarta ta fara samun nutsuwa ta rage damuwar nan, amma ta lura abin na nan a ranta har yanzu.

*****

"Madam ya dai na jiki shiru tunda kika shigo baki sake fitowa ba?"

"Alhaji baku guri na yi ka gana da ƴar uwarka, ka ga ban san abin da yake tafe da ita ba". 

Tsura mata ido ya yi yana kallon ta, ta ce "Abbin Nihal wannan kallon fa?".

"Na so da ƙaunarki ne ƴammatana" ya yi maganar yana jan kumatunta.

Dariya ta yi ta ce "Ƴammata kuma? A'a sai dai uwar ƴammata". 

Ya ce "In ji wa? Ni Alhaji Kabiru Umar mai nera har yanzu kamar ƴammata kike a gurina, gaki nan shar dake, komai naki a kintse, kullum zam-zam nake jinki kamar..." Da sauri ta rufe masa baki tana faɗin "Haba dai ka yi shiru, mu fa ba yara ba ne yanzu da zaka saki baki kafara ɓarin zance, tunda nake da Nihal ai na wuce zama ƴammata" ta ƙarasa maganar da tana dariya.

"Waya faɗa miki mu ba yara ba ne? Ai ni a yadda nake jina nafi wani sabon angon more wa" ya faɗa yana rugumota jikinsa. Dariya take yi sosai, tasan halin mijin nata idan abin ya motsa masa komawa yake yi kamar wani yaro, ba ta yi aune ba taga ya kashe wutar ɗakin tare da rufe su da bargo.

******

Jiniyo wanka ya yi, ya shirya jikinsa tsaf ya sake fitowa falo, nan ya tarar da Abbansa zaune, tun daga nesa ya ƙurawa Jiniyo ado kamar yana karantar abin da ke zuciyarsa. "Jiniyo" ya kira sunan sa "Tun jiya kake kulle a ɗaki lafiya dai? Baka san na dawo ba ne?".

Murmushin ya ƙe ya yi ya ce "Abba ba na jin daɗi ne, shi ya sa na manta cewar jiya za ka dawo". Mama ta ce "Ƙarya yake yi akwai abin da yake ɓoye wa" .

Abba ya ce "Idan ma akwai abin da zai damuwar yarona nasan akan ƴar yayarki ba ce, da ina da ikon da zan cire masa son yarinyar nan da na yi".

"Haba Abban Jiniyo ƴar uwarsa ce fa, taya za ka hana shi ya so ta?" .

"Yi mini shiru Munira, tun da aka haifi yarinyar nan yake nuna mata so da kulawa, amma da ta buɗa ido ta fara wayo babu wanda take hantara kamar shi, ina kiyaye da ita ko gidan nan ta zo da Mamanta ba ta kula shi, akan me zan so yarona ya fara shiga damuwa akan yarinyar da ba ta san yanayi ba?".

Tsam Jiniyo miƙe ya fita daga falon gabaɗaya, ya ja motarsa ya bar gidan.

Mama ta ce "Abban Jiniyo bai kamata kana wannan maganar ba, Joriyya fa kamar ƴa take a gurink..." "Bana son jin komai daga bakin ki, ai ba za ki bari a yi magana ba" . Ya katse ta yana gama faɗar hakan tashi ya yi ya ba ta guri.


Dady ne tare da baƙin sa suna tattaunawa akan harkar kasuwanci su da tsare-tsaren shigo da kaya daga waje, ɗaya daga cikin su ya ce "Alhaji wannan sabuwar yarjejeniyar da muka ƙulla da su za ta amfane mu sosai". Dady ya gyara zamansa ya ce "Ina so komai ya tafi bisa tsari, ba zan yarda da asara ba, mun sha darasi a baya, yanzu ba zan lamunci a sake maimaita abin da aka yi mana a baya ba".

"In sha Allah babu wata matsala da za ta kuma faruwa a yanzu, da mun san akwai matsala ba za mu koma gayyato ka cikin tafiyar ba" Dady ya yi na'am da maganar sosai, suka ƙarasa tattaunawar sannan suka yi masa sallama tare da barin ofis ɗin. Suna fita suka kalli juna suka yi murmushin da suka ɗai suka san ma'anarsa.


Joriyya na zaune a class tare da ƙawarta Safina, Malam Musa na yi musu darasi amma ba ta fasa surutun da take yi ba, kallon sa take tana dariya ƙasa-ƙasa ganin yadda yake yi musu bayani kamar baya jin daɗin jikinsa, cikin ƙasa da murya ta ce "Safina kin ga Musa yau kamar wanda aka hana shi shayin safe, sai layi yake yana lumshe ido kamar yadda Indiyawa ke yi a film".

Safina ta girgiza kai ta ce "Ke dai ba za ki daina surutu ba? Joriyya ka da ki jawo mana duka fa".

"Surutu fa yanzu na fara, Safina kin san bashi da lafiya hannunsa ke ciwo" . Joriyya ta ce tana lumshe ido

Safina za ta yi magana kenan suka ga Malam Musa na kallon dole ta yi shiru.

Da aka tashi daga school ɗin, direba ya zo ɗaukar Joriyya, kai tsaye gida ya nufa, babu za to ya ji Joriyya ta ce masa

"Tsaya ba wannan hanyar zamu bi ba, ka wuce ta can baya nan nake son mu bi".

Ya ce "Amma Shalele ga hanyar..."

"Don Allah kabi inda na buƙata, zan ɗan tsaya ne wani guri" ta katseshi

Direban bai sake magana ba, ya juya akalar motar zuwa inda ta buƙata, tun daga nesa ta hango shi zaune a cikin bolar, rana na dukansa. karensa na gefensa, hannunsa ya ƙara kumbura, fuskarsa ta yi duhu, idanunsa sun zurma sosai, bakinsa ya bushe, sai hamma yake yi alamar yunwa yake ji, tasa direba ya tsaya daidai bakin bolar. A firgice ta fito daga cikin motar tana faɗin "Subhanallah". Ta matsa kusa da shi hawaye har sun fara zuba a fuskarta ta ce "Me ya ƙara kumburar maka da hannu haka? Me yasa ba wanda yake taimaka maka ne? Yanzu dama haka kake fama da hannun? Da gani ma yunwa kake ji?". 

Mahaukacin ya ɗago da kai a wahale, ya kalle ta da idanunsa da suka yi zurfi, bai ce komai ba. Hawaye suka ƙara zubu mata, ta rufe fuskarta da tafin hannunta tana kuka. "Ba haka ya kamata rayuwar mutum ta kasance ba" ta faɗa cikin muryar kuka.

Direban ya tsaya daga nesa yana kallon ta, zuciyarsa cike da fargaba.


Amanarcool
***