RIKITACCIYAR ALAƘA

19

by @diamondbhatool3

19

Bayan kwana biyu da maganar CEO da Hajiya ne suka yanke shawarar gabatar da al'amarin ta sama, sun kuma ƙudiri aniyar komai ya kasance cikin ƙanƙanin lokaci kafin su Dada su farga, Hajiya ba ta ba wa CEO damar sanar da Imaan ba, ta dai ce ya bar hakan a hannunta, su  Uncle ɗinsa kuma suka je nema masa auren Imaan ɗin a wurin Abba wanda dama shi ma ya san da zuwan nasu don Mami ta riga da ta sanar da shi komai. A take kuwa ya amince yana mai farin ciki maras iyaka don ganin cewa, wani babban nauyi da ya gagara sauƙewa na gab da sauƙa, abun da ya fi faranta masa ma shi ne, Uncle ɗin CEO ya ce ba sa so bikin ya wuce wata guda, ke nan dai har a zo bikin Dada ba za ta sani ba bare ta ce za ta hana, haka uwar son zuciyar ma ba za ta sani ba bare ta lalata komai.

Kasancewar yau juma'a ce da wuri suke tashi a wurin aikin nasa yasa Imaan fara harhaɗa kayanta da wuri,  bayan sun gama komai ita da  Jamila suka fito kasancewar yau za ta je unguwar su Jamilah ɗin da yake a can take kitso. Bayan Imaan ta yi kitso ta koma gida ne Mani ta ce ta shirya Hajiya na nemanta.

Haka kawai ta tsinci kanta da bugawar gaba, tsintar kanta ta yi da furta "Hasbunallahu wani'mal wakili, la ilaha illa anta subhanaka inni kuntu minaddhalimina" a sukwane ta shirya cikin wani material ɗin ta ɗinkin doguwar riga da ya ɗan sha ruwa ta saka hijabi ruwan shuɗin sararin samaniya, turare kaɗan ta mulka sannan ta yi wa Mami sallama ta wuce  gidan Hajiya.

Sosai Hajiya ta tarbi Imaan, duk da cewa ba sabon abu ba ne samun tarba mai kyau a gidan amma sai take jin na yau ɗin banbaraƙwai, ajiyar zuciya take sauƙewa kawai tana nanata addu'a cikin ranta.
A hankali Hajiya ta ɗebe ta da taɗi har ta sake. Sai bayan la'asar tukun Hajiya ta ja ta cikin ɗaki ta zaunar da ita bakin bed sannan ta sanya idanuwanta cikin na Imaan ɗin, a hankali ta ce
"Imaan"
Imaan ta amsa tana kawar da nata idon gefe don yadda kaifin idanuwan Hajiyan ke affecting ɗin ta a yau.
"Ni na saka Maminki ta aiko min ke, kin yi mamaki ko?"
Ba ta samun damar furta komai ba sai ta gyada kanta.
"To ba komai ne ya sa nace ki zo ɗin ba sai wata muhimmiyar magana da nake so mu yi, wacce ba na so kowa ya sani"

Gaban Imaan ne ya fadi tana jin bugun zuciyarta na ƙaruwa cikin ranta tana tambayar wacce irin magana ce wannan Hajiya za ta faɗa mata.
Hajiya tace "Imaan, ke, Ni, Maminki da kuma Abbanki, mu kaɗai ne muka san irin rayuwar da kika yi a baya, kike yin ta a yanzu kuma muke hasashen in ba a ɗauki wani matakin ba cikinsa za ki ci gaba da rayuwa."
Shiru ta yi ta ja numfashi sannan tace "Sannan kuma, mun yi magana da Maminki ta ce akwai saurayin da yake son ki ƴar'uwarki ta yi ƙarfa-ƙarfa yanzu haka suna tare ko?"
A kunyace Imaan ta gyaɗa kai
"Amma ke ce babba ai?" Hajiya ta faɗa tan jijjiga kai "ba wannan ba dai, shekarunki sun kai a ce a yanzu kina gidan aurenki Imaan,  shekaru ashirin da ɗori?"
Wani irin yawu Imaan ta haɗiye da ƙyar sai zazzare idanuwa take, cikin ranta tana fatan inama a ce Hajiya ta bar wannan zance don kuwa ba shi da wani fa'ida.

Wani hawaye ne ya kwaranyo daga kan kyakkyawar fuskar Imaan, a yanzu ne ma kuwa take jin wani yanayi maras daɗi dangane da rayuwarta, sof course ya kamata a ce tana da abokin rayuwa a yanzu, to amma tana da kyakkyawan yaƙini kan cewa hakan ba za ta taɓa faruwa ba matsawar Ihsan da Dada na numfashi, idan kuwa har sun amince ta yi aure to ta tabbatar mijin ba irin wanda ya dace da ita ba ne, amma ai aure lokaci ne, don haka nata bai zo ba da ta yi"

"Kin yi shiru Imaan, akwai wanda kuke tare ne a yanzu?"
Cikin jin nauyin Hajiya da ta kasance kamar uwa gare ta tace "A'a" tana jijjiga kanta.
Numfashi Hajiya ta sauke tare da sakin wani murmushi.
"To Alhamdulillahil, dama abun da nake son ji ke nan"
Gaban Imaan ne ya yi wani irin bugawa jin abun da Hajiya ta ce, tsananin mamaki ne ya mamaye ta har sai da ta ɗaga ido ta kallo Hajiyar, jinjina mata kaj Hajiya ta yi kana tace "Ƙwarai kuwa Imaan, na ji daɗin jin hakan, yanzu dai ki kwantar da hankalinki, akwai yaron yayan Alhaji sunansa Sulaiman, ba zan ce Miki komai a kansa ba, amma dai abun da na sami shi ne yana so ya aure ki..."
Saurin katse Hajiya ta yi da faɗin "Aure kuma Hajiya?"
Hajiya ta jinjina kai "ƙwarai kuwa Imaan"

Cikin rawar Murya tace "A'a Hajiya don Allah ki rufa min asiri wallahi..."
Hajiya ta katse ta da faɗin "Ai rufin asirin ke nan Imaan, aure ne kawai zai ƴantar da ke daga uƙuba da son zuciya irin ta Dada",
Cikin kaɗewar hankali tace "Amma Hajiya"
"Shhhh" Hajiya ta ɗaura yatsarta kan lips ɗin Imaan kana tace "Don't say anything Imaan, mun riga mun yi magana da Abbanki, Mami duka sun amince kuma sun nuna farin cikinsu, idan har kina son farin cikinsu ina jin za ki amince, don su ma rashin ta cewa yada suke zuba ido suna ganin abubuwan da ke faruwa da ke, ba wai don ba son ki ba ne sai don an fi ƙarfinsu"

"Imaan lokaci ya yi da ya kamata ki nutsu, ki yi aurenki ke ma, ki auri mijin da zai kasance garkuwa gare ki, wanda zai tsaya Miki kan al'amuranki"
Shiru Imaan ta yi yayin da bugun zuciyarta da kuma numfashinta ke fita da sanri.
"Ba za a tilasta Miki ba, za a ba ki dama ku fahimci juna da mijin amma a sirrance, don Allah Imaan, kada ki bari wannan magana ta bayyana a cikin gidanku don hakan na nufin rushewar komai ciki kuma har da farin cikin iyayenki da mu masu ƙaunarki, ga waya nan zan ba ki, Sulaiman ne da kansa ga siya ya ce a ba ki, za ku yi magana, don Allah ki nutsu, mutumin kirki ne sulaiman na kuma tabbatar Miki ko nan gaba ba zai wulakanta ki ba, zai tsaya Miki kan al'amuranki, yana da mata ɗaya, amma hakan ba damuwa ba ne Imaan, don matar tasa gaba ɗaya ba ta da hali, ke dai ki taimaka masa don ya samu kwanciyar hankali domin shi ma akwai tasa matsalar."

"Kar na cika ki d maganganu, Magrib ta kusa, bari na ɗauko Miki wayar."
Miƙewa HaJiya ta yi ta janyo wata ƙatuwar leda ta miƙa mata, mamaki ne ya bayyana kan fuskar Imaan, ita da za a ba wa waya me ye wannan babbar ledar? Ta tambayi kanta.
Tunaninta ya katse ne da maganar Hajiya "Ga wannan, wayar tana ciki, abubuwan cikin kuma shi ya ce a ba ki, ki daina saka waɗannan suturun please "
"Hajiya ki bar su wurinki kawai, ko na tafi da su ba amfani zan yi da su ba kin sani"
"A'a, dole ko tafi da su, ki dai yi yadda za ki yi ki adana su ko Mami kada ki nunawa don ta san da su."
Gyada kai Imaan ta yi tana faɗin "To Hajiya, na gode Allah ya saka da alkairi "
"Amiin Yarinyata, ki tashi ki wuce, ga wannan, ki hau abun hawa"
"A'a Hajiya" Imaan ta faɗa a kunyace "akwai kuɗi a wurina"
"To ki ajiye wannan ɗin ko ki sadakar"
Zaro idanuwanta tayi waje kana ta amsa tana faɗin "Na gode Allah ya saka da Alkhairi"
"Mu je in raka ki"
Tare suka fita har compound ɗin gidan tukun suka yi sallama Hajiya ta koma ciki.

*Bloordale village*

A cikin kwanaki soyayya mai ƙarfi ta ƙullu tsakanin JK da kuma Shahada wacce ta riga ta koma gidansu, sosai JK ke nuna mata kulawa haka ita ma a nata sashen ba ta wasa da al'amarinsa, lokaci bayan lokaci idan sun yi waya ta kan bayar da saƙon gaisuwar ga AK, haka kawai take jin tausayinsa ba kuma wai don ta san wani abu dangane da rayuwarsa ba ne, a'a kawai dai yanayin yadda yake ne yasa ta fahimci akwai wani abu tattare da shi. A ɓangaren AK kuma kullum al'amarinsa ƙara ta'azzara yake don ko aiki ba kullum yake fita ba, yana zaune shi kaɗai a kan makeken gadonsa yana aikin na tunani, zabura ya yi ya miƙe zaune, kamar wadda ya tuna wani abun ya sauko daga kan gadon ya fara zagaya ɗakin, tunanin mafita yake kan al'amarin yarinyar nan da ta tsaya masa a rai da ruhinsa, tabbas ya yadda soyayya azaba ce amma kuma ya ƙudiri a yau ɗin nan ba gobe ba ya samarwa kansa maslaha ga rayuwarsa don tsira da hankalinsa da yake neman gushewa saboda ita.

"Shin ta ina zan fara?? Ta ina zan fara?"
Ya furta cikin yanayi na nazari kafin ya ce "Nigeria zan koma, ba tare da sanin kowa ba, zan je Azare ko kwana nawa zan yi sai na nemo ta, i know Jahaan will be there for me"
Samun wuri yayi ya zauna yana jinjina kansa i tare da yin amanna da shawarar da ya yanke wa kansa.
Zuciyarsa ce ta gargaɗe shi da faɗin "Idan kuma ita ma kamar kai ne fa? Wato zuwa tayi kamar yadda ka je?"
Kansa ya langwaɓar gefe tare da sakin wani zazzafan huci yana dunƙule hannunsa tare da naushin isa. A hankali ya furta "Then sai in je in ɗauki CCTV footage na wurin da muka haɗu, though it has been a long time amma la'alla na samu idan suna ajiya"
"Idan kuma ba sa yi fa?"
Kansa ya dafe da dukkan hannayensa yace "I know her face, her smile, and her look! Zan bi jiya ko nawa ne a zana min hotonta! Of course, hotonta will work wurin nemanta. Amma ta ina zan fara?"
Ya ƙarashe cikin Muryar da ke nuna tsantsar karaya, da sauri zuciyarsa ta ba shi amsa da "Ta ko ina ma! I'll publish the image a newspaper, zan bayar da tsagwaron kuɗaɗe ko da nawa ne ga wanda ya samo min yadda take"

Mikewa yayi zumbur tare kai wa iska naushi yana murmushi, that'll work in Sha Allah! My dream girl, I'm here coming to your rescue, zan ceto ki daga hannun ko ma waye kike, zan zo gare ki da zuciya ta da kuma ruhina! Ki jiraye Ni!" Wani irin yanayi y tsinci kansa, take ga ji duk wata damuwarsa kamar ta kau har wani irin sanyi yaji yana ratsa shi.

A ɓangaren Imaan bayan ta koma gida ba ta bi ta kan kowa ta adana ledar da ta taho da ita tukin ta nufi ɗakin Mami, so take ta ji maganar daga bakin Mami amma Mamin ko a fuska ba ta nuna mata da ta san wani abu da suka tattauna akai ba sai ma tambayarta ya ta baro Hajiya, daga nan ta mike ta je don gabatar da sallar Magrib da aka fara kiraye-kirayenta.

Bayan ta idar da Sallah ne ta janyo ledar ta fara fito da abubuwan da ke ciki, abayoyi ne masu ɗan karen kyau guda biyar sai waya keypad ƙirar Itel wacce ke cikin kwalinta, kayan ta fitar daga ledar ta saka su cikin jakar kayanta sannan ta dawo ta zauna, buɗe wayar ta yi, tana kunna ta taga ta kawo ashe dai an riga an yi charging nata. Bayan ta gama kunnuwa taga har SIM akwai a ciki, ajiyar zuciya ta sauƙe sannan ta sanya wayar a meeting mode, wato vibration ta yadda ba za a ji ko da ringing ɗin ta ba.

Jin sallamar Abba yasa ta fita ta masa sannu da dawowa ta amshi ledar hannunsa da ke ɗauke da shinkafa da kuma kayan miya, ajiyewa tayi daga nan ta hau girki, sai wuraren Isha ihsan ta dawo daga school, da kallo kawai Imaan ta bi ta sannan ta haɗa wutar girki.