8
by @rufaidaumar
ALWASHI
©Rufaida Umar
33
MAMAN MEENAT SUPPLEMENT/SKIN CARE
Yar uwa muna saida kowanne irin supplement na gyaran jiki wanda zaisaki fito fes kamar sabuwar Amarya, yar uwa shin kurajene suka dameki, ko matsalolin jikine kamarsu rama, ko kibace tayi miki yawa kikeso ki rage, bushewar fata ko karancin ni'ima ko budewa ne ko infection? Ko kuma so kikeyi fatarki tayi laushi ki dinga sheki kina haskawa wato kalar madara dai Haj to ki garzago
Yan uwa kusani duk wani supplement da zamu kawo muku sai munyi bincike mun tabbatar da ingancinshi, mun kuma tabbatar da cewa bashi da wata illa ga lfy
Akwai masu cewa sunsha supplement amma har yanzu basuga wani canji ba, to yar uwa kodai an baki fake ko kuma ba'a baki wanda ya dace dakeba, kokuma bakisha yadda ya dace ba, kisani yar uwa kafin ki fara shan supplement akwai ka'idoji daya kamata ace kin kiyaye kuma kin kula dasu matukar kinaso suyi miki aiki yadda ya kamata kuma cikin sauki ***
1. Akwai Supplements na gyaran jiki ciki da waje, munada set na uwargida dana Amare da masu jego
Sannan ga wadanda sokeso jikinsu yayi kyau sosai amma basa son susha supplement to albishirinku muna da kowanne irin mai na gyaran jiki da kuke bukata irinsu lotion, cream, soap, scrubs, face Cream,sun screen, serums concentrate, hair oil, hair cream face mask etc
Muna saida duk wasu nau'in supplement Lotion da kuke bukata, sannan Maman Meenat collection ba anan kadai ta tsaya ba muna saida turaruka kowanne irin na wuta dana jiki, da Airfreshners da air wick, sayen daya ko sari ke dai kawai neme ni a wannan number ***
***
Yana tsaye a cikin ƴar kyakkyawar bukkar da ke farfajiyar wurin shaƙatawar da ya samu adireshinsa a wajen Laila cewa za su haɗu a nan. Ba shi da tabbacin ko ta iso wurin ko kuwa ba ta ƙaraso ba, ya dai samu wurin ƴar bukkar mafi ƙarancin hayaniya da mutane. Kallon ƴar hanyar da gefe da gefenta ciyayi suka yiwa ado yake, daga tsarin wajen ya fahimci idan dare ne to fa fitilun gefen ciyayin ake kunnawa su ba da haske mai kyau su ƙawata wurin shigowar. Ya nisa ya ɗan kai duba ga mutanen da ke shawagi nesa da inda yake kafin ya duba agogon da ke ɗaure a tsintsiyar hannunsa, uku har da mintuna. Ya ci fiye da rabin awa a wajen. Sauke ajiyar zuciya ya yi gami da duba wayarsa dake hannunsa. Babu saƙonta ko ɗaya balle kuma kira. Ya ɗan juya ya yi taku ɗaya biyu, kafin ya kai ga na ukun ya ji wayarsa ta yi ƙarar shigowar saƙo.
"Ka same ni dab da wurin shiga swimming pool side."
Daga haka ta katse kiran. Areef ya numfasa, tun haɗuwarsu sai a lokacin ya soma jin muryarta. So cool and gentle. Ya dan yi waige ya tabbatar ba a wajen da yake ba ne don haka ya fito gaba daya ya bar ɓangaren, da ɗan ƙaramin board din da ya nuna hanyar zuwa pool din ya gano wajen. Daga can gefen ginin da ya yi wurin akwai kujeru hakanan akwai bishiya da ta lulluɓe wurin. Areef ya ƙarasa, bai ga kowa a zaune wurin ba sai wata matashiyar budurwa da ba ɗora ƙafa ɗaya kan ɗaya, sai ko jakarta da ke saman kujerar. Hankalinta kwance tana latsa waya, jikinsa ya ba shi cewar ita ce Sameerah. Ya ƙarasa har gaban teburin ya na dubanta, cikin tausassan muryarsa mai amon sauti irin na dakakken namiji ya yi mata sallama. Laila ta ɗago bayan ta runtse idanu ta ambaci sunayen Allah, ƙirjinta na harbawa don ta sani a yau dai sai ta fuskanci makashin ƴar uwarta Sameerah. Ba kuma yau ɗin ce ranar haɗuwarsu ta ƙarshe ba, mafarin kenan. Ta cikin gilashin idanunta ta dube shi, duk yanda shaddar da ya sanya da baƙar hula suka haska shi, ba ta ga ɗigon hasken ba face duhu da tsantsar tsanarsa. Ba kyawun fuskarsa da ma kwantacciyar sumarsa ta gani ba da ta kalle shi face wani ƙasurgumin mugun mutum wanda yake baƙiƙirin a zuciyarta, mai ɓoyayyiyar fuskar da ba kowa ya sani ba.
"Can i seat?"
Ya furta cike da dakiya ba tare da ya dube ta ba, jinsa yake very guilty, ya mata laifuka masu tarin yawa, ya ga ta masa kwarjini ainun ba don komai ba sai don rigar laifin da ya kasa yakice shi, wanda ya hana shi ganin kyawun duk wata sutura da zai sanya. Da yatsunta uku ta masa alamar ya zauna ɗin, koda ya zauna ta saka hannu ta zare tabarau ɗin idanunta. Kallon juna suka yi cikin idanu, sai dai kallon bai je ko'ina ba kowannensu ya kauda fuska kusan lokaci guda. Ga Areef, daga yanayin sauyin launin idanunta zuwa ɗan jaja-jaja ya kasa jurewa kallon yana jin kansa a mai laifi matuƙa, gaba ɗaya fatar fuskarsa ta yi ja, ga wani gumi da ya tsastsafo a goshinsa da tafin hannuwa. Ya ɗan sauke ajiyar zuciya. Ƙamshin turarukansu ya cakuɗe wuri guda. Aka rasa mai ƙarfin halin maganar, can kuma ya nisa ya yi ta maza.
"Fatan na sameki lafiya?"
Sai lokacin ta yi wani murmushi na zallar takaici. Ta maida gilashinta don ba ta so ma hawayenta ya zubo. Haidar, darajar yaron kaɗai zai ci a yau da ba za ta ɗura masa ruwan ashariya ba. Ta yi gyaran murya kafin ta soma magana kai tsaye ba tare da ta ɗauke idanunta daga kansa ba wannan karon.
"Zuwanka ya nuna ka shiryawa sharuɗɗana, koda dai nasan ba wai tsorata ka yi ba don mai hali na akuyanci irin naka ba zai ji ɗarr da komai ba. Duk da haka ka kyautawa kanka da ma mutuncin iyayenka da ka tako ka kawo kanka nan. Hum."
Laila ta ɗan numfasa gami na ƴan daƙiƙu, shi kuwa a hankali ya ɗaga ƙwayar idanunsa ya dube ta. Ba haka ya tsammaci ganinta ba, cikakkiyar mace mai aji wacce da kallo ɗaya za ka san ba gidan talaka ta fito ba. Sai ya ji zafin hakan a ransa, abinda zai sauya rayuwarta ɗaya ne, idan har a baya a marar gata ya santa, to tabbas mummunan hanyar da tunaninsa ya ba shi, ita ta bi. Ba kuma laifin kowa ba ne face shi da kansa, shi da ya ruguza mata rayuwa kamar yanda ta faɗa. A fuskarta yana karantar irin zafinsa da take ji har da tsanar da ta masa, ya kuma yi amanna da ace za'a ba ta makami da iznin aika shi lahira, shakka babu da ta aiwatar da hakan.
"Zamu yi aure bayan sallarnan, za kuma ka ɗauke ni ka kai ni har gaban iyayenka matsayin zaɓinka."
Ta ƙarashe tana mai fidda gilashinta ta mishi ƙuri da idanunta da ke nuni da tsantsar tsanarsa. Shi ma ita yake duba, bai tsammaci hukuncin mai mugun sauƙi ba ne har haka, sai ya ji zuciyarsa ta nutsu da hakan. Ba tare da tunanin komai ba ya amsa yana dubanta.
"Idan har na aureki za ki yafe min?"
Ta kauda idanunta daga nasa, a ƙasan ranta ta ce, 'Me kake ci na baka na zuba Areef? Yanzu za'a fara wasan ai.'
A fili kuwa ta amsa mishi da faɗin,
"Yafemaka ko rashin yafemaka wannan ra'ayina ne ba wai naka ba Sir. That's for me to decide. Yanzu..."
"Yes, i will marry you. Na shirya hakan Sameera, zan aureki a kowane yanayi na tsinceki. A can baya ma..."
"Ya isa haka, ban buƙatar jin komai daga bakinka please. Tunda har ka shirya aurena, to bari ka ji kaɗan daga sharuɗana. Aure ne na sirri a wurin yan uwana. Ma'ana, bana so wani ya gano ko waye kai da zan aura, kama daga zuri'ar da ka fito, ko kuma sunan kai kanka ma. Bana so. "
Daga kallon da ya mata da mayun idanunsa ya fahimtar da ita da magana bakinsa sai dai ba ta ba shi damar yi ba ta ɗora.
"Ba ka da hurumin sanin dalilina na yin hakan, muddin dagaske ka shiryawa duk abin da na zo maka da shi ɗin, to kawai ka aure ni."
Ta ƙarashe da jin ciwo da haushin kanta, kamar ita wai ta tsaya cewa makashin ƴar uwarta ya aureta. Ta ja tsaki a ƙasan ranta. Ta ji sadda ya sauke ajiyar zuciya sannan a tausashe ya ce.
"Ai na amince da sharaɗinki Sameera, ban zo Kano ba sai da na shirya zan yarda da dukkanin abin da kike so na aiwatar matuƙar bai saɓawa Mahaliccinmu ba. Na shirya zan aureki, na kuma yarda ba zan bayyana kaina ga iyayenki ba. Zan san ya zan yi na ɓoye kaina garesu har zuwa lokacin da kika ce na bayyana ɗin. Idan kin ba ni dama zan iya neman wata alfarma?"
"Ina ji."
"Za ki ba ni nan da kwana uku na shiryawa yanda zan ɓullo da batun auren tunda kin fi so a yi a ɓoye. Ni kuma zan nemi wanda zai zo madadina amma da sunana. Bayan an ɗaura auren sai na ji daga gareki yanda za'a yi? Sannan babu laifin sanar da nawa iyayen?"
Ta yamutsa fuska gami da ɗan ɗaga kafaɗu.
"Ba matsalata ba ce wannan, idan ka ga dama ka sanar ko kar ka sanar. Batun na ba ka kwana uku ka je na ba ka week ma. Mu'assalam."
Tana kai wa nan ta maida gilashinta ta miƙe gami da ɗaukar jakarta. Kallonta ya ke sadda ta soma takawa da zummar barin wurin, daidai sadda ya miƙe tsaye ta juyo ta dawo, bai yi aune ba ya ji saukar yatsunta biyar a kuncinsa. Ɗif wasu ƴanmata dake can gefe guda suna ɗaukar hoton milkshakes din da waiter ya diremusu suka yi suna binsu da kallo, haka nan wasu ma'aurata dake can gefe da ma wasu samari biyu da suke kokarin shigewa wajen swimming pool, dukkansu hankalinsunya karkata gare su. Areef wanda ya yi mutuwar tsaye kawai yana dubanta ba tare da ya ce uffan ba, duk da ya kawo fiye da hakan ma kafin zuwansa su haɗu, sai dai bayan haɗuwarsu da yanda suka tattauna cike da nutsuwa ya kautar masa da tunanin haka kan iya faruwa. Ita kuwa daga haka ba ta yi wata-wata ba ta juya ta bar wajen. Haka kawai sai ta ji wani ɗan sanyi a ranta. Bai damu da ƴan maganganun da ke tashi a wajen ba ya kwashi wayoyinsa ya bi bayanta. Ba zai tantance yanayin da marin ya haifar masa ba don bai masa daɗi ba, bai kuma ba sa haushi ba.
Koda ya hau motarsa dake parking space din wajen, fitowarsa titin ya iske ta tana tafiya don fita babban titi. Ji ya yi ba zai iya wuce ta ba don haka ya ɗan tsaya a gabanta. Laila wacce tsayuwarsa ta sanya ta dole ta ɗan dakata ta dube shi.
Gilas ya sauke.
"Ki yi haƙuri na ɗan fitar da ke a nan, naga da ɗan zurfi kuma ba napeps."
"Ba ni da buƙatar hakan."
Kamar ya ce wani abu sai kuma tunanin kar ya ɓallo wani ruwan kawai ya fasa, ita tuni ta gifta shi ma ta cigaba da tafiyarta. Ya dan bi ta da kallo, zai so sanin kalar rayuwar da ta gudanar bayan mummunan ƙaddarar da ta afkamusu da ita. Ajiyar zuciya ya sauke kafin ya ja motarsa ya bar titin. Ta ɗan kalli bayan motar tasa, fara ƙal mai baƙaƙen gilasai tinted.
"Allah ka sa komai da na tsara ya tafi daidai."
Ta furta a fili, ba ta yi aune ba wani napep ya taho daga inda take nufa ya ɗan tsaya saitinta.
"Hajiya ina za ki je?"
Ta faɗi sunan hall ɗin da ake event din kamun Khadija.
"Hau mune faka-faka."
Ya furta har ta ɗan dube shi, kasancewar sauri take ba ta ko tsaya ciniki ba ta faɗa ya ja don babu nisa sosai da unguwar da suke.
Suna isa ya sauke ta, za ta fiddo kuɗin kawai ta ga ya ja yana faɗin.
"Ki bar shi Hajjaju, an biya ni haƙƙina."
Ya bar Laila da sakin baki kan ta yi ƙwafa, Areef, shi ne mai wannan aikin.
"Wuta bal bal." Ta furta a fili sannan ta nufi wajen taron ta shige bayan ta bada gatepass ga security.
***
A gajiye liƙis suka koma gida, ta tabbatar yara sun yi wanka sun saka kayan bacci kafin ta shige ɗakinsu don Gwaggo tuni ta yi bacci. Ita ta yi wanka ta yi sallah da nafila sannan ta kira Mama ta whatsapp suka gaisa. Fadi take,
"Yaushe za ki dawo Mama?"
Dariya Mama Kubra ta yi.
"Ki yi addu'a komai na treatment dina ya tafi lafiya, na dawo ina taku da ƙafafuna in sha Allah. Ni dai fatan da nake Allah ya fiddo maki miji nagari, karatu ba zai hana aure ba Laila."
Laila ta ji zuciyarta ba daɗi, da ace Mama Kubra ta san duka shirinta ta tabbatar sai ta ɓata rai sosai.
'I am sorry Mama, hakan kadai zan yi na samu nutsuwa.'
A fili kuwa ta amsa.
"Mama ko yau na samu wanda nake so in sha Allahu zan cikamaki burin nan. Koda auren zai kama bayan sallah indai ya kwanta min na maki alƙawarin zan yi."
"Alhamdulillah." Mama ta maimaita sau uku har abin ya sa Laila mamaki.
"Mama duk a kan nace zan yi aure? Ashe ba da son ranki zan yi karatun ba?"
Ta ƙarashe da ƴar shagwaba. Dariya Mama Kubra ta yi.
"Laila kenan, ina so ki yi karatu, amma ba zan ɓoyemaki ba, abubuwa da dama sun saka yanzun na fi kaunar na ga kin zauna a dakin mijinki, zaman aure. Koda karatun ne ma ki yi daga can hankalina zai fi kwanciya."
Ajiyar zuciya Laila ta saki.
"Allah ya cikamana burikanmu."
Mama Kubra ta amsa da amin.
"Ki kwanta ki huta, gobe kinga kuna da sabgogin biki. Ki gaida min yar uwarki Haseenah."
Nan suka yi sallama. Madadin ta samu ta yi baccin, sai bacci ya ƙaurace mata, tunanin yanda suka yi da Areef take da ma batun aurensu, ga kuma Mama fa ƙaramata wani tunanin, wata zuciyar na ba ta shawara, kodai ta haƙura da ɗaukar fansar nan ne ta yi auren da zai faranta ran Mahaifiyarta? Wata zuciyar kuwa ta yunƙuro da nata, inaa ba zai yiwu ba. Ba ta ga abin da zai karyamata alwashin da ta ci ba muddin tana raye da ikon Allah.
Da haka ma ta watsar da tunanin baki ɗaya gudun kar ya hargitsa mata lissafi ta yi addu'o'inta ta kwanta.
***
KATSINA