Part 5
by @chefmuaysh
BADAKALA ✍️ Aisha Hamza CHEFMUAYSH
Ta rike ta gam ita kuma burinta ta faɗa ɗakin ta tambaya gwaggo abinda yake faruwa amma an hanata Khairiyya ce tayi dakin kai tsaye a kofar dakin don bata karasa shiga ba ta saki wata razananniyar ƙara ta sulale kasa a sume wasu mata sukayo kanta
Ba ƙaramar bangaza Ayrah tayiwa barira ba tatafi luuu zata fadi tana rike bango ita kuwa Ayrah tayi wuff ta faɗa ɗakin tamkar an dasata haka ta tsaya koda ba'a faɗa mata ba tasan tatace ta ƙare daidai da motsa yatsa ta kasa jitayi duniya take ina take a wannan yanayin bazata iya ganewa ba
Kasancewar ba'a rufe mata fuska ba malam na kanta yana mata addu'a yana sharbar hawaye sai Halima da Inno da wasu mata su biyu duk suna zazzaune a dakin suna matsar ƙwalla
Wani abu taji ya taho mata shi bai fita ba shi bai koma ba ya tsaya mata a wuya yana ƙoƙarin tafiya da numfashin ta daƙyar take jan numfashi
Barira ce ta kuma biyota dakin tana ƙoƙarin janta wai su fita aikuwa nan ta birkice musu tana wani numfashi kirjinta yana sama yana ƙasa koda aka tabata gaba ɗaya ta tafi zata fadi da taimakon halima aka fiddata daga dakin can inda aka kwantar da Khairiyya wata mace na mata fifita nan itama aka kaita aka jera su
Khairiyya ta farfado sai faman lumshe idanuwa take kamar maijin bacci amma ita kuma Ayrah ba suma tayi ba sai wannan numfashi da take kamar zai fita gaba ɗaya
Har aka kammala komai Ayrah bata dawo dai-dai ba Khairiyya kuma ta mike sai kuka takeyi tajawo Ayrah saman cinyarta tana ƙoƙarin wai ta rarrasheta amma abu ya faskara
Fitowa da gawar gwaggon yasa matan gidan mikewa wasu na kuka wasu na addu'a hankali tashe aka fita da'ita
Allahu akbar gwaggo lokaci yayi shiyasa jiya duk take wani iri ashe mutuwar ce ke dukanta
Koyaya rayuwar Ayrah zata kasance ba gwaggo ❓
Wane labari ne gwaggo take son tabata ❓
Gashi ta rasu bamuji komai ba kotaya zamu sani ❓
Menene a cikin akwatin da gwaggo tace na Ayrah ne kuma baida mukulli itace kaɗai zata iya budewa tayaya ❓
Yanzu fa aka fara don ko matakin farko bamu taka ba muje zuwa dai tundaga nan matakin farko muje na biyu uwa uba na uku wato takun siradin BADAƘALA
✍️ na wannan littafin
Da sauri Ayrah tana bangaje mutanen da suka cika kofar gidan ta faɗa ciki Khairiyya na biye da'ita barira ce ta tareta a kofar dakin da mata suke zaune wasu nata matsar kwalla itama bariran kuka take sosai kamar ranta zai fita
Ta rike ta gam ita kuma burinta ta faɗa ɗakin ta tambaya gwaggo abinda yake faruwa amma an hanata Khairiyya ce tayi dakin kai tsaye a kofar dakin don bata karasa shiga ba ta saki wata razananniyar ƙara ta sulale kasa a sume wasu mata sukayo kanta
Ba ƙaramar bangaza Ayrah tayiwa barira ba tatafi luuu zata fadi tana rike bango ita kuwa Ayrah tayi wuff ta faɗa ɗakin tamkar an dasata haka ta tsaya koda ba'a faɗa mata ba tasan tatace ta ƙare daidai da motsa yatsa ta kasa jitayi duniya take ina take a wannan yanayin bazata iya ganewa ba
Kasancewar ba'a rufe mata fuska ba malam na kanta yana mata addu'a yana sharbar hawaye sai Halima da Inno da wasu mata su biyu duk suna zazzaune a dakin suna matsar ƙwalla
Wani abu taji ya taho mata shi bai fita ba shi bai koma ba ya tsaya mata a wuya yana ƙoƙarin tafiya da numfashin ta daƙyar take jan numfashi
Barira ce ta kuma biyota dakin tana ƙoƙarin janta wai su fita aikuwa nan ta birkice musu tana wani numfashi kirjinta yana sama yana ƙasa koda aka tabata gaba ɗaya ta tafi zata fadi da taimakon halima aka fiddata daga dakin can inda aka kwantar da Khairiyya wata mace na mata fifita nan itama aka kaita aka jera su
Khairiyya ta farfado sai faman lumshe idanuwa take kamar maijin bacci amma ita kuma Ayrah ba suma tayi ba sai wannan numfashi da take kamar zai fita gaba ɗaya
Har aka kammala komai Ayrah bata dawo dai-dai ba Khairiyya kuma ta mike sai kuka takeyi tajawo Ayrah saman cinyarta tana ƙoƙarin wai ta rarrasheta amma abu ya faskara
Fitowa da gawar gwaggon yasa matan gidan mikewa wasu na kuka wasu na addu'a hankali tashe aka fita da'ita
Allahu akbar gwaggo lokaci yayi shiyasa jiya duk take wani iri ashe mutuwar ce ke dukanta
Koyaya rayuwar Ayrah zata kasance ba gwaggo ❓
Wane labari ne gwaggo take son tabata ❓
Gashi ta rasu bamuji komai ba kotaya zamu sani ❓
Menene a cikin akwatin da gwaggo tace na Ayrah ne kuma baida mukulli itace kaɗai zata iya budewa tayaya ❓
Yanzu fa aka fara don ko matakin farko bamu taka ba muje zuwa dai tundaga nan matakin farko muje na biyu uwa uba na uku wato takun siradin BADAƘALA ✍️ na wannan littafin
BADAƘALA 🕗
A'isha Hamza✍️ (Muaysh)
Karki bari karku bari kar mu bari abamu labari top 3 Na A'ishatu Hamza wadda kuka fi sani da Muaysh graphics 🤟 🤗 basai na faɗa muku ba littafaine wanda daga jin sunayen su zaka gane cewa na musamman ne
(UMMU OR SALMA) UMMU kO SALMA
(ORPHANAGE HOME) GIDAN MARAYU
(MARYAM’S LIFE) RAYUWAR MARYAMA
Wannan shine account details din mu 👇
3201868037 A'isha Hamza First bank
Ko kuma 9131096058 A'isha Hamza Opay bank
RAYUWAR MARYAMA akan 400 kacal GIDAN MARAYU akan 400 sai kuma UMMU KO SALMA akan 400 ga wanda yake buqatar duka zai biya 1000 instead of 1200 sana zaka tura receipt after payment a wannan number *** ta whatsapp
BADAƘALA 🕗
A'isha Hamza ✍️
Kiran Khairiyya aka aiko a waje ko bata tambaya ba tasan wanene da sauri ta zura takalmanta ga idanuwanta da suka kumbura ta fita
Abbana ta furta can ƙasa saboda shakewar da muryarta tayi alkhairi na ya faɗa yana shafa kanta yace kiyi hakuri kinji yanzu muka dawo daga makabarta nace bari in maki magana nasan kinanan dama ko zakici wani abu na kawo maki
Cikin shagwabe fuska tace ah ah Abbana saidai ko zuwa dare dan anan zan kwana
To alkhairi na kardai ki zauna kiyita kukan nan ki rarrashi Ayrah kinga in kina kuka bazataji daɗi ba koh
Gyada kai tayi alamar gamsuwa sukayi sallama yatafi yana jin soyayyar yar tasa ɗaya tilo ita kuma tajuya ta dawo gidan
Jingine Ayrah take da bango saman tabarma ajiyar zuciya kawai take saukewa sai wasu hawayen da suke ta silalowa tana hadiyar wai abu mai mugun daci
Yan gaisuwa nata shigowa gashi duk wanda yazo ita yake fara tunkara da sunan gaisuwa barira ce ma take dan tare wasu ganin halin da gaisuwaar ke ƙara jefa ta
Su Inno kuwa an dukufa wajen murhu wai za'a girka abinci itada wasu daga cikin makota
Saida aka kira sallah laasar dakyar da kalamai masu daɗi barira ta taushi Ayrah kafin suka tashi sukayi sallah itada Khairiyya
Duk abinda take son ɗauka a daki kuwa saidai akawo mata shi waje don taki shiga dakin gani take tana shiga zataga gwaggo duk ta ruɗe ko magana batason anayi mata
Lokacin da aka gama abinci kuwa ko kallo bai isheta ba sunanan saiga Iroro ya shigo da jakansa an biyo shi hada uban kayan tsarabar sa da yazo dasu sai kuka kuwa yake yi yana sabbatu
Shikenan gwaggon mu dama ni hankali na yaki kwanciya tun jiya gwaggo kintafi kin barmu ganin kukan nasa na ƙoƙarin ruda gidan daga waje aka aiko aka fita dashi
Ayrah kam kamar jira take ta ɗora nata marar sauti ta saka kanta cikin hijabi saidai shessheka wanda na kusa da'ita ne kaɗai ke jinsa
Gidan yadan ragu sai masu shigowa jefi jefi Kasancewar anyi sallah isha'i ma sai iya su yan gida aka kuma aikowa kiran Khairiyya ta fita
Leda yabata yace gashinan yabata kuɗi yace da safe kafin yazo idan akwai abinda sukeso sai su siya bayan haka sukayi sallama tadawo cikin gidan
Daƙyar ta samu itada barira suka lallaba Ayrah tadan kurbi ruwan tea tasha saiga shi ance malamansu sunzo yi musu gaisuwa
Dukansu sukazo kuwa sai-dai wanda bazasu iya ganewa ba nan sukayi musu gaisuwa suna bada kuɗi wai ayi sadaka
Ai kuwa duk wanda ya bada kuɗi yana fita Inno zatayo kansu kaɗan ya rage Khairiyya tanka mata barira tahana ta
Ita kam halima idan Inno tayi wani abun saidai tace Allah ya kyauta ta kauda kanta haka suka zauna gidan nan har akayi kwana uku Khairiyya ta koma gidansu saidai kullum nan take yini har bakwai
Gidan ya koma daga Inno don anan take kwana Halima ce ke tafiya gida itada yaranta barira kuma dama katanga ɗaya suke
Ayrah taga jarabawa daga rasuwar gwaggo zuwa a kwana bakwai ɗin don idan Inno ta kawo mata abinci tana cewa ta koshi kamar jira take saita dauke taba yaranta tace dama basu koshi ba ai
Saidai barira da kuma Khairiyya dake ta ƙoƙarin su a kanta ranar da aka kwana takwas Iroro yace bazai iya zama garin nan ba don haka barira ta shirya su tafi Lagos ɗin tare sun dinga zuwa zumunci tunda itama bawani dangi gareta anan ɗin ba
Amma ta kafe tace saidai su tafi da Ayrah don ita bazata tafi ta barta anan ɗin ba ai kuwa nan Inno ta tura malam akan zancen yasamu Iroro ya masa kashedi akan cewar tun Inno na Amarya gwaggon ta bashi Ayrah dondai bai kaita gidan sa ba saidai kullum can take rayuwa sai shida yake ganin yanzu yanada ɗan abin hannu zai ce zai dauketa malam yace bazai yiwu ba domin shi Gwaggo tabawa amanar ta
Iroro dama yasan hakan zata faru kawai dai yayi ne saboda yanda barira tadamu akai dole ya lallaba ta yace zasu dinga zuwa ganin Ayrah ɗin kuma zai dinga mata sako lokaci bayan lokaci kafin ta hakura dan bayan da zatayi kuma bahaka taso ba
Nan yasa ta haɗa duk wani kayanta wanda zata siyar ta siyar na bayarwa ta bada yace idan sunje can zai sai mata wasu abubuwan
Randa aka cika kwana goma suka tafi kamar ranar akayi mutuwar abin ya dawo musu don sun sha kuka itada Ayrah dakyar aka rabasu ko rakiya Ayrah kasayi musu tayi
Gida yazama ba kowa daga ita sai Inno makarantar su kuwa anfara jarabawa don ma akwai interval shiyasa bata rasa duka ba shima daƙyar uncle Sameer ya lallaba ta take zuwa zana jarabawar
Inno kuwa ta gaje gidan gwaggon da masifa tacewa Malam wai dama can yayi musu kaɗan tunda su biyu ne duk abinda za'a raba sai ya Bama Iroro kuɗin kawai ita kuma ya gyara musu wannan itada yaranta don dama yafi nasun kyau shima daki biyu ne su Ayrah ne kawai basa amfani da dayan
Ai kuwa hakan akayi tasa aka dauke katifar ƙasa aka maida ita saman gadon ta saman gadon aka dawo da'ita ƙasa aka kwaso mata kayanta daga wancan gidan gaba ɗaya bayan an gyara mata ɗayan dakin aka maidasu ta siyar da wasu don ita mutuwar gwaggon ma daɗi tayi mata
Shi kuwa malam abin yana damunsa ba kamar yanda gwaggon tace tana nemansa shi kuma baixo ba idan yana zaune saidai yayita hawaye shi kaɗai amma Indai yana tareda Inno Shikenan sai ya manta da batun ma
Satinsu biyu ana uku suka gama jarabawar itace tafara fitowa sai wasu daga cikin yan ajin nasu tana tsaye saiga Khairiyya ta fito tana Murmushi ta nufeta saboda farin ciki ta faɗa kanta tana faɗin Ayrah munkusa tafiya boarding
Duk yanda taso ɓoye damuwarta hakan ya gagara wasu siraran hawayene suka shiga silalowa ta idanunta
Tuni Khairiyya tasha jinin jikinta ta saka hijabinta tana goge mata tana faɗin don Allah Ayrah ki daina kukan nan banajin daɗi ko kaɗan wallahi kinga Nima saiki sani kuka
Kalaman gwaggo ne suka shiga dawowa kwanyarta gwaggo tace ke yanzu Ayrah ko makarantar aka samo miki a birni tafiya zakiyi kenan kibar gwaggon ki
Ayrah ta zaro ido tana faɗin kai ni na isa gwaggo in tafi in barki ai tare zance yasama mana makarantar da zamu iya zuwa tare suka saki dariya
Murmushin da batasan dalilinsaba ta saki sai ta shiga goge hawayenta kamar yanda Khairiyya keyi suka nufi office ɗin uncle Sameer domin Ayrah tace suje suyi masa godiya kodan karfafa musu gwuiwar da yakeyi akan karatun
Ohh shiit ya akayi kuka bari ya kubuta karku ɓatamin aiki na na shekaru mana dana dade inayi yadanyi shuru kafin ya cigaba ya kuke so inyi da Oga tsaki yaja kafin yace nabaku nan da awa ɗaya ku kawo shi da rai ko babu idan yaki tsayawa ku harbeshi kawai
Dafe kirji sukayi gaba dayansu da jin furucinsa na ƙarshe kokarin magana Khairiyya take yi Ayrah ta fisgo ta suka bar wajen
Jin alamun mutum yasa shi katse wayar yana lekowa saidai baiga kowa ba amma hankalin sa bai kwanta ba zama yayi yana nazari saiga sako ya shigo wayarsa
Sanda ya gama karantawa ya saki wani shuumin murmushi tare da faɗin ka shiga hannu tare da mikewa saidai kafin ya fito kadan ya rage suci karo Khairiyya na gaba Ayrah na bayanta
Kallo ɗaya yayi musu yasan akwai abinda suka kulla tsakanin su don yanda idanuwansu sukayi fiki fiki
Muje zuwan yan amanar chef ku ci-gaba da farin ciki da karatun wannan littafin namu mai daɗi ✍️🤸🤸