Kuncin zuci
by @bintuuu
Cikin kidimewa Bilal yayi nufin sauqa stairs din sai ya dakata ya juya zuwa dakinsa da sauri ya dauko takalmi saboda glasses dinda suka fashe nan gurin, a rikice ya qarasa gurin Na'iman ya dagota, ganin kamar bata numfashi ne yasa ya dago kansa yana kallon Stella da tayi mutuwar tsaye har sannan, tsawa ya buga mata "Dallaaa ki daukomin Car key" da saurinta taje ta dauko, cicciban Na'iman yayi ya nufi waje da ita, sai da ya kwantar da ita a back seat sannan ya koma cikin gidan da gudunsa ya dauko jallabiya, figan motan yayi bai jira shigan Stella ba ya nufi near by asibiti da Na'ima dake sume har sannan..
Dakyar asibitin suka karbeta ganin injuries din jikinta sannan sukayi emergency da ita, Bilal na tsaye ya kasa zama, addu'an sa daya a lokacin shine Na'ima tayi rai dan be san da wani baki zeyi explaining kanshi gurin mahaifinsa ba..Sai da Na'ima ta dauki two hours me kyau kafin ta farfado, kuka ta rinqa yi nan kwance kan gadon, bayan an ciccire mata glasses din da suka shiga cikin fatarta aka wanke ciwukan tareda saka mata bandage, Allura suka mata sannan suka fito da ita daga dakin ture a gado tana bacci, qarasawa gurinsu Bilal din yayi suka tafi dakin da akayi referring dinta tare wanda ya kasance single room, har asuba Na'ima bata farka ba nurse din da ke kula da ita tana ta zuwa akai akai, Bilal na nan zaune kan kujera a dakin jefi jefi yana kallonta, kiran Stella ne ya rinqa shigowa wayansa babu qaqqautawa yana rejecting, dan ransa ya baci da abunda tayin sosai, Ganin har safiya Na'ima bata farka ba yasashi tafiya gida canjo jallabiyan jikinsa dan ta baci sosai da jini, bayan tafiyansa bada dadewa ba Na'ima ta farka, da farko bin dakin ta fara yi da kallo sai can kuma abun da ya farun suka fara dawo mata kwakwalwa, rufe idonta tayi tanajin hawaye na sauqo mata tana jin wani irin zafi acikin zuciyarta da jikinta gaba daya, tananan kwance nurse din ta dawo tana mata sannu ta duba qarin ruwan da akayiwa Na'iman sannan ta taimaka mata ta miqe ta kaita bandaki, dakyar tayi alwalan bayan tayi sallah nurse din ta sake taimaka mata ta koma kan gadon, tananan kwance Bilal ya shigo suka hada ido, juya kanta tayi other side of the room dan bata son ganinsa ma a wannan lokacin, qarasowa yayi bakin gadon yana kallonta yace "Ya jikin" kuka ta fara yi bata juyo ta kallesa ba, sai da ya gaji da tsayuwa ganin bazata juyo ba yasashi sake fita daga dakin, haka Na'ima ta wuni ita kadai a dakin sai Nurse dinnan ce ta taimaka mata da abinci da rana ganin babu wanda yazo duba yarinyar, sai dare Hajiya da Alhaji suka shigo dakin tareda Bilal, tsayawa a baya Bilal yayi while Alhaji ya riga Hajiya qarasawa bakin gadon yace "Sannu Na'ima, yanzu yake fada mana abun da ya faru" Hajiya ta qaraso bakin gadon itama cikin nuna alhini tace "Sannu daughter, Allah ya kiyaye na gaba, dan Allah ki rinqa kula sosai Na'ima, taya zakiyi mopping baki nutsu kin goge ruwan ba, yanzu badan Allah ya taqaita ba da sai dai wani labarin daban fa" Alhaji na kallon bandage din kafadan nata yace "Ta yaya kika yanke kuma" Hajiya ta saurin cewa "Riqe take da plates din abincin lokacin da hakan ta faru ai" Alhaji ya sake cewa sannu sannan ya zauna nan bakin gadon, abincin da Hajiyan ta shigo dashi ne ta zuba a plate ta miqawa Na'iman, sai sannan ta dago kanta idonta cike da hawaye ta karba ahankali tace "Nagode" bakin gadon Bilal yazo sai Alhaji yace dashi "Kayi magana da likitocin babu wani internal injuries dai ko" gyada kai yayi yace "Sun ce za'a cigaba da kula da ita tukunna incase of that" Hajiya ta zauna a kujera tace "Allah ya kare na gaba, ki rinqa kula du Allah Na'ima" itadai Na'ima kanta a duqe tana cakulan abincin dake gabanta batace komai ba, ji take komai na duniyan ya fita kanta, sai da su Alhajin suka shafe awa guda a dakin kafin su mata sallama suna qara mata sannu, Hajiya harda fadin zata dawo da safe, Na'ima ta amsa suka fice tareda Bilal din, bai dade ba yadawo dakin still taqi dago kanta ta kallesa, zama yayi bakin gadon yana kallonta yace "Sannu" bata dago ba har sannan idonta cike da hawaye, a nutse yace "Na'ima" sai a sannan ta dago kanta ta kalleshi hawayen na bin fuskanta cikin sanyin murya tace "Yaya dan Allah ka sauwake min" dan stiff yayi yana kallonta sai ta sake cewa "Ka sakeni dan girman Allah" miqewa yayi ransa a bace ya buga tsuka tareda juyawa ya fice daga dakin, kuka me sauti Na'ima ta fashe dashi ranta na quna...Dawowan da Bilal bai sakeyi asibitin ba kenan dagashi har iyayen nasa, dan Alhaji da ya tambayi Hajiya ma cewa tayi an sallami Na'iman ai.
Ganin shiru babu ko abinci da zataci yasata Na'ima karban aron wayan nurse din ta kira wayan Nafisa, jin switch off yasata kiran sufi dan dukansu biyun ta haddace numbernsu a kanta, bayan Sufi ya dauki wayan suka gaisa tafada masa tazo asibiti ne batada kudi kuma, nan take Sufi yace "Ayya sannu Na'ima, ki turo account number'n yanzu, ai bansani ba da nazo, dan yanzu ma haka ina zaria Alhaji ya turani wani aiki, amma in sha Allah zanzo dubaki in na dawo" ta gyada kai tareda yi masa godiya sannan sukayi sallama yana qara mata sannu, through nurse din ya turo mata kudin, dayake ta hadu da mace ta gari sai taje ta ciro mata kudin harda siyo mata abunda take buqata, da wannan kudin Na'ima tayi settling bill na asibitin ranar da aka sallameta, likitan ya tambayeta ina mijin nata ya shige, dan ya kirashi baya dauka, rasa me zatace Na'ima tayi sai kawai tace yayi tafiya, nan likitan ya hau mita, nurse dinda ke gefensa wadda take kula da Na'iman sai kallonta take fuskanta cike da tausayi, da ta tashi tafiya hakuri ta bawa nurse din me suna Amina akan zata dawo mata da kayanta dake jikinta tace bakomai, cikin sanyin jiki ta fito daga asibitin ta nemi abun hawa ya kaita gida..
Isarta gidan bayan megadi ya bata makulli bata samu kowa cikin gidan ba, nan bakin stairs ta tsaya tanajin abunda ya farun na dawo mata sabo, kuka ta fara cikin sanyi jikin ta fara taka stairs din ta qarasa dakin nata, dauko akwatin ta tayi ta fara hada kayanta bata daina kukan ba, sai da ta gama hada komai sannan ta shiga bandaki da nufin tayi wanka, dakyar tayi saboda gudun karta jiqa bandages din da suke bayanta da kafadan nata, har sannan goshinta da bandage din, shiryawa tayi cikin atamfa da babban jalbab brown ta fara cicciban akwatin nata ta fice daga gidan bayan ta bawa megadi makulli, tashan da zata samu motan Adamawa ta nufa aikuwa bata dade ba motansu ya tashi, suna tafe tana addu'an Allah ya dafa mata yakawo mata qarshen wannan iftila'in na rayuwanta.....
Sai yamma liqis suka isa, ta tari mashin yakaita har qofar gidan kawunta Ayuba, tana shiga gidan su Umma dake abincin dare suka dago kai suna kallonta har Anty Amarya dake zaunen itama, Kamal yace "Hajiya Na'ima sauqan yaushe" Na'ima bata amsa ba ta tsugunna tana gaishe da matan kawun nata sunata bin fuskanta da kallo, miqewa Anty Amarya tayi ta qaraso gurin Na'iman tace "Na'ima meya sameki haka" Umma tace "Ni sai naga kamar duk ta fita hayyacinta ma" Anty Amarya na kallon Na'iman tace "Jeki daki ki huta tukunna" gyada kai tayi ta nufi dakin Anty Amarya suka bi bayanta da kallo..
Ranan Na'ima har shidewa take dan kuka gurin fadawa musu abunda Bilal din yake mata, ahakan tana kasa fadan wasu abubuwan ma, Umma dake tsaye bakin kofa ta riqe baba tace "Wai dama dan giya ne yaron nasu daman, innalillahi wa'inna ilaihi rajiun dama karuwan har lasisi ne dasu haka a kanon" Anty Amarya da ke Jin ranta duk a bace tace "Kiyi hakuri Na'ima in Sha Allah komai yazo karshe bari kawun naki ya shigo" Na'ima ta gyada kai bata bar kukan ba, sai dare Ayuba yadawo kasancewan yaje wani qauye nan kusa saro kayan miya, bayan ya gama cin abinci matan nasa suka sako masa magana, cewa yayi su kira masa Na'iman, da taje dakinsa har sauqe masa riganta kadan tayi dan yaga kafadan nata, sannu ya rinqa mata yace taje zai kira Abdullahin yaji komai, aikuwa daren ranan sai ga kiran Hajiya a wayan Ayuba tace tana kan hanyan zuwa nan da kwana biyu dan maganar bata Alhaji bace ita tasan komai, zatazo suyi magana, cikin ladabi Ayuba ya amsa da "Toh Allah ya kawoki Hajiya, dama ai kece uwa dole komai zai zamo da saninki" da haka sukayi sallama, cikin kwana biyun nan Anty Amarya tayi ta bawa Na'ima qarfin gwiwa sosai, da kanta take dafawa Na'ima abinci sannan ta tusata a gaba taci, Ranan da Hajiya ta iso gidan, nan tsakar gida Umma ta shimfida mata tabarma sai nan da nan take da ita kuttu kamar ya kashe Anty Amarya, fitowa Na'ima tayi ta gaisheta sai taqi amsawa ranta abace "Ni ban cancanci gaisuwa gurinki ba Na'ima karma ki gaisheni, sai yanzu na tabbatar baki daukeni uwa ba" Anty Amarya ta tabe baki, Umma tayi saurin cewa "Haba dai Hajiya ai kaf duniya Na'ima batada uwar da ta wuce ki yanzu, riqon da kika mata ai ko yar cikin ki iya kaci" Hajiya ta tabe baki tace "Ita ai batasan da hakan ba, shi dan yau dama kai dai kayi masa komai dan Allah kawai"...Kiran Ayuban Hajiyan tayi cikin sauri yadawo gidan, nan zaure aka shimfida musu tabarma Hajiya ta hau masa bayanin qanzon kurege, sai da ta shafe awa biyu tana magana Ayuba na fadin "Hakane" "Hakane" "Ayi hakuri Hajiya" "Na'ima bata kyauta ba" maganganu iri iri dai marasa dadin ji..Da Ayuba ya tashi shiga gidan Hajiya bata bishi ba tananan zaune ya shige yabarta..
Cikin bacin rai yafara kwala kiran Na'ima, tayi saurin fitowa ya nuna ta da yatsa yace "Fito ki tattara kayanki ki koma dakin mijinki, wato kina tsammanin zan goyi bayan rashin mutuncin da kike musu ne ko, Ashe ke nan har dambe kikayo da 'yar'uwar mijin naki sannan kika taho" Umma tace "Bangane ba Malam" ya kalli Umma cikin bacin rai yace "Toh Na'ima dai 'yar uwar mijin nata ce taje gidan shine tsabar kishin bala'i sukayi dambe har abun yakoma kanta yarinyar ta ci galaba akanta ta turata ta fado daga benen" ya juya ya kalli Na'ima da ta shiga shock yace "Ke yanzu duk riqon amanan da mutanen nan suka miki sai kice bakyasan nasu Na'ima, maimakon ki riqe gidan mijinki sai ki tsiro da wani halin daban kenan, to wallahi ni Ayuba bazan lamunci rashin da'a ba, ki dauko akwatinki ga Hajiya can tana jiranki zaku koma tare" kuka Na'ima ta fara, Anty Amarya na tafa hannu rai bace tace "Ke duniya..Allah ka rabamu da son zuciya" sai ta kalli Malam cikin Ido tace "Wallahi Malam kaga hakkin yarinyar nan, shi kadai sai ya hanaku kwanciyar kabari" atare Umma da Ayuba suka bude baki suna kallonta, Umma tace "Abida lafiyanki, yarinya tayi ba daidai ba shikenan uban nata bazai ganar da ita ba" cikin bacin rai Ayuba yace "Abida ki tafi gidanku sai na nemeki, dan bazan zauna da matar da kemin fatan rashin gamawa da duniya qalau ba" Anty Amarya na kuka tace "Wallahi Ayuba bakada zuciya me kyau, Allah wadai da halinka, mutanen da basu dauke ka a bakin komai ba shine zaka bata lahirar ka dominsu, inace shekarun baya daka je sai daganan muka rinqa hada kudi muka tura maka sannan kasamu kudin motan dawowa ma, sai yanzu dan ta zo ta baka wasu aninai da basu taka kara sun karya ba zaka maida marainiyar Allah'n nan gidan mashayin dan nasu, wallahi sai kayi bayani a gaban Allah" cikin bacin rai Ayuba yace "Ki fita ki barmin gida Abida, 'ya kuma tawa ce, abunda ya dace inyi shi zan aiwatar akanta" tsugunnawa Na'ima tayi nan tsakar gidan tana kuka Umma tace "Sai hakuri Na'ima, kowama hakurin nan yakeyi, ke naki hakurin ma tare yake da kudi, Allah na tuba yau ko yanka namanki sukeyi ai kya zauna, wataran sai labari duk ze wuce" Anty Amarya kasa magana tayi wa Umman saboda takaici ta shige dakinta...da kuka Na'ima ta sake dauko akwatinta Ayuba ya rakata har bakin motan da Hajiyan ke hakimce a baya, wani kudin ta sake cirowa ta miqawa Ayuban tace ya qara akan wanda ta basa yayi cefane, godiya ya rinqa yi yana ba Hajiyan hakuri "Ku cigaba da hakuri Hajiya Allah ne kawai zai baku ladan hakan, yaron yau ne ka haifesa amma ba ka haifi halinsa ba" ...A hanyarsu ta komawan babu wanda yayi magana cikin ita da Hajiyan sai da sukayi nisa Hajiyan ta fara zazzaga bala'i Na'ima ta kwantar da kanta a jikin window tana hawaye aranta tana ayyana "Yau ta sake fahimtan ko mutuwa tayi ba damuwan kowa bane a kaf danginta, Yayun ubanta sun nuna mata sunfi son duniya akanta, qanwar uwarta bata sake waiwayanta a rayuwa ba, gidan mariqan ta kuma son zuciya da son dansu ya rufe musu ido, mijin nata ma kilaki ta fita a wajensa.....yau tagane in ta mutu ba faduwar kowa bane, yau tagane bayan Allah batada wanda zai tsaya mata a rayuwa kuma..
Masifa Hajiya ta rinqa yi driver na bata hakuri tana fadin "Ke yanzu kaf duniya ba gidan Bilal din bane gatanki da zaki sa kafa ki tafi qauyen naku, banda rashin godiyan Allah ma ace baki rasa ci ba, baki rasa sha ba, har makaranta gashinan kinayi amma sai ki kasa hakurin zama da jinin mu Na'ima, dan cikin Alhajin kike gudu" ci kanki Na'ima batace ba tanata hawaye....
Sai dare suka isa Kano, har kofar gidan Bilal din suka ajiyeta Hajiya na sake cewa "In kin ga dama kiyi hakuri in kinga dama ki cigaba da tunzurashi yana miki illa" nan ma Na'ima batace komai ba taja akwatinta ta shige gidan, zuwa sannan ta daina kuka a abayyane sai na zuci kuma, ko abinci takasa dafawa taci haka ta kwanta nan kan gado batare da ta chanja kayan jikin ta ba..
Bata dade ba nan kwance taji shigowan motan Bilal din, can taji an turo kofan dakinta bata juyo ba balle ta kallesa, still tayi shiru tana kwance ta yi pillow da hannunta tana kallon gini, qarasowa yayi gurin gadon yace "Kin dawo kenan" bata amsa ba ya sake cewa "You think you can escape me Na'ima? you must be kidding yourself" miqewa zaune tayi sai sannan hawaye ya kawo idonta ta kallesa takasa magana ma, yana kallon cikin idonta yace "You're bound to me Na'ima, I've grown addicted to your presence, duk inda zakije sai kin dawo gareni" ya juya ya fice daga dakin yabarta zaune tana swallowing maganar tasa, kamar an mintsineta tayi sauri miqewa tabi bayansa nan falon qasa ta sameshi a tsaye yana danna wayarsa ta tsaya bayansa tana kuka tace "Dan Allah ka sakeni" saurin juyowa yayi yana kallonta ta sake cewa "Ka rabu dani inje inyi rayuwata" ransa ne ya baci yace "Bar gabana ko in illataki" bata matsa ba ta hade hannayenta guri daya tana kuka tace "Idan ba tare aka halittomu ba dan girman iyayenka ka sake...." bata qarasa ba ya kai mata maruka a fuska, tananan tsaye taga yana qoqarin ciro belt dinsa, tsayawa tayi bata motsa ba ganin ya nufota da belt din zai daketa kawai ta rufe idanunta hawaye na zuba sanin dukan farkon ne wanda yafi zafi a ko yaushe.... Nan ne mafarin abubuwa da dama a cikin rayuwan Na'ima, a sannu ta fara shiga depression, mantuwa, da kuma firgita ita kadai, wani irin rama ce ta fara shiganta sanadin damuwan, zuwa makarantar nata ma yakoma sama sama, Nafisa tayi fadan har ta gaji ganin mutuwar tsaye Na'iman keyi, ga final exams dinsu da ya tisosu gaba wanda Na'ima batasan ma me akeyi ba, zuwa sannan in Bilal yazo gareta ma bata yunkurin hanashi sanin bazai iya tabuka komai ba sai riqe kansa da kuma duka, har lokacin Bilal ya kasa aiwatar da komai akan Na'ima wanda hakan ba qaramin kulle masa kai yake ba, baya tashi jin ciwon kai sai yaje gareta, gashi babu abunda yake so irin ya kusance ta amma abun ya gagara, kullum da haushinsa da kuma dukan da yake mata yake barin dakin nata, bayan ya fitan haka zata miqe tana hawaye ta maida kayan ta jiki..