Chapter -- 02
*** Namii Ƙanin Ajali ****
Page 02
Bayan fareesa ta dawo nace ta fere dankalin ni kuma na tashi na gyara kayan miya nayi jajjage na ɗora fatan dankalin,da kallon tausayi umma take bina, dan tasan dauriya kawai nakeyi nake ƙoƙarin danne damuwata ,sai da nagama na zuba mata a kula na rufe bayan nasa mata wanda zata ci yanzu a kwano,umma tana da ciwon sugar wata biyar kenan da bayyanar sa bayan rasuwar mahaifin mu da ta dinga ciwo yaƙi ci yaƙi cinyewan da har saida muka kaita asibiti suka tabbatar da tana dashi sai dai baiyi nisaba ta kula da magani da kuma kiyaye abincinta,tun daga nan na ƙara ƙaimi akan kulawar da nake bata,haka nake aiki in ɗan ƙulle kuɗina na siyo mata duk nau'in abinci da akace sunaci, daidai ƙarfina...
"Allah yayi miki albarka ya baki ƴaƴa masu jinƙanki kamar yadda kika jiƙanmu, ubagiji ya shiga lamarinki ,ya kare ki daga masu sharri,ya zama gatanki ,sannan a duk inda kike duk hali da ƙuncin rayuwar da zaki shiga kada ki manta akwai allah ,shi kaɗai ne wanda zaiyi miki mafita a duk halin da kike ciki kinji?, a kowani hali kada ki manta da addu'a dan shine gatanki,dan inaji a jikina kina da sauran gwagwarmaya a rayuwarki, kuma zata zo mikine bayan bama raye Allah kawai shine gatanki,dan ni wannan ciwon bazai barni ba sai yakai ni ƙasa,dama shi mahaifinku ya tafi"idanunta suka kawo ruwa da alama kuka zatayi,da sauri nace "haba Umma kiyi hakuri Allah yana tare damu,kuma ita ƙaddara ai ba a guje mata saidai fatan Allah ya kawota da sauƙi,dan Allah kiyi hakuri kar ciwonki kuma ya tashi"
"To Allah yayi muku albarka ke da ƴan uwanki baki ɗaya"Ta faɗa
Na kai hannu na goge mata hawayen "Amin" na faɗa a sanyeye haka umma takeyi duk sanda zaku zauna da ita sai tayi maka nasiha da hannunka mai sanda, cikin dabara irin tasu ta manya, amma wannan karon har tafito fili ta faɗi abin yake ranta anya kodai mit,na kai hannu toshe bakina jin zuciyata tayi wani mummunar bugawa,banyi wata-wata ba wancakali da wannan tunanin.
Da haka muka gama yinin bayan la'asar wajajen Shida saura umma ta kora ni gida dan tun ɗazu take intafi amma naƙi inata yi mata kan keke, Imran ne ya rakani muka tafi har layla,muna isa muka samu kowa na hada-hada aikinsa , ƙofan inna naje nace mata na dawo tayi min sannu tare da tambayata ya jikin umma nace "da sauƙi"
"Yanzu mustafa yake cemin yaji imrana yana gaya miki Hajiya ba lafiya"
" Eh Wallahi amma jikin da sauƙi" na bata amsa
"To allah ya ƙara sauƙi,nace Halima kuma Hajiyar ba Lafiya saiki tafi baki ko faɗamin ba,shi kuma Mustapha ya gama faɗa min kenan kika shigo"
"Nima hankali na nane yayi gaba Wallahi ina sauri ne inje in ganta kiyi haƙuri"na bata amsa
"Shikenan karki damu bari in gama aiki anjima idan anyi magariba zanje na gaida ta"
"To Allah ya kaimu bari in ƙarasa"
"to a huta gajiya "
"Yauwa"na nufi ƙofata
"Ke Layla wato kinje kin maƙale a gidan Hajiya kina cinye mata tuwo ko?"na jiyota tana tsokanar Layla.
Anan na nabar laylan harda husna,a tsatsatsaye muka gaisa da matan gidan, na ƙarasa ƙofata bayan na ɗanyi kaye-kaye na hura wuta na ɗumama tuwon da miyan na sa ruwan wanka na nayi su layla sunyi na su a gidanmu , na fito nayi alwalar magariba na shige ɗaki , bayan na shirya nayi sallah ban tashi ba sai Isha,akan daddumat ina lazimi Bature ya shigo ya sameni ,wuceni yayi ya zauna akan kujera na ɗago kalleshi na mishi sannu,bai amsani ba ya fara ƙoƙarin ɗaiko Radio, haushi ya kamanu dan haka nace
"wato bayan tuwon da na samaka shine ka koma kaje yanka a cikin na ɗumame ko?, to kada ka sake gobe ka tambaye ni ɗumame da safe"
Cike da hargowa koma ince borin kunya yace "auuuw nida gidana ,na kuma bada kuɗin cefane sannan a samin doka akan abinci,za'a bani iyakan yanda zanci to baki isa ba"
Miƙewa na yi na naɗe sallayar na kalle shi nace "oh tohh aifa, su megida anji jiki ,kai yanzu har kana da bakin ɓaɓatu akan abincinnan nawa ka bayar ɗari biyu ko? "na ɗan nisa nayi murmushin takaici sannan naci gaba da faɗin,"tsakani da allah me ɗari biyu zaiyi a abincin rana kawai ma, balle kuma har dare, harma da safe kane mi ɗumame, kayiwa kanka hisabi mana bature,da har kake wani cewa kai da gidanka za'a maka doka, haka masu gidan suke" na sauke maganar saboda numfashina da nakeji yana min wani iri,na buɗe baki zan cigaba naji abunda yasa maganar komawa da kanta batare da na shiryawa hakanba
"Yanzu ni halima kike cemin bana ciyar dake saboda yau kin cika min hamsin kuɗin cefane iye?, wato duk ƙoƙarin da nakeyi abanza kike gani ko?ba damuwa lokacinki ne,dan kin samu nema watama tana ko kamar hakanne a bata tayi cikonma bata samu ba" mamaki daskaraddani ni yaushe na ce haka ,kuma idan hakanma na faɗa ai ba ƙarya nayi ba tunda watarana ba ya bayar da ko hamsin ɗin da yake maganar nayi mishi ciko balle ɗari biyu,kuma a ɗari biyunne yake batun ciko a wannan tsadar kayan,kai Bature yana kashe ni da mamakinsa,kalan na yau kuma kenan?,jin maganganunsa yana shirin samin kaina fara juyawa yasa nayi waje na barmasa ɗakin ,to wai ni dama haka auren wanda kake so ɗin yake ko kuma ni ce banyi sa'a ba , kai haka ne ma,baga wasila ba ƙawata ce sanda aka kawo ta gidan basiru da bulala mahaifinta ya rakota ɗakinta amma har yau shekara goma Sha baka jin kansu kamar ba auren kiyayya ba har yaransu biyar yanzu,na jinjina kaina tare ina ba kaina tabbacin auren soyayya ita take zama na ƙiyayya, sai yau na tabbatar da maganar da kaka na ya gaya randa da za'a kawo gidan bature, muryarsa ta dawo min raɗau a cikin kunne na kamar yanzu yake gayamin,
"Makudina" ya kirani da ɗaya daga cikin sunayen da yake kirana dashi wani lokaci,ban amsa ba kaina yana ƙasa yayinda hawaye yake bin fuskata,yace"Abdallah kike so ko?" Ya ɗan ja fasali kafin ya cigaba "to an bakishi,abu na farko da nake so naja hankalinki akai shine haƙuri dan zan iya ce miki shine gini mafi ƙarko a cikin zaman aure musamman aure irin naki na soyayya,dan auren soyayya baya ƙarko,musamman irin naki da akayi turka-turka, bazan ɓoye miki ba zaki gamu da abubuwa da yawa a cikin zaman aurenki waɗanda bakiyi tsammani,bawai ina nufin auren soyayya ba'a samun kwanciyar hankali bane amma yana wuya ya ɗore,dan yakan juya ya zama ƙiyayya mai muni,a yayin da auren ƙiyayya yakan zama soyayya,duk da shima yana da nashi illar musamman gaku yaran wannan zamanin, sannan mijin da kika ɗauko ba irin wanda akeyiwa wannan son bane, akwai abubuwa da dama amma ga wannan inaso ki sashi a kanki dan watarana ko bana raye zaki tuna,a ƙarshe ina horonki da yi haƙuri! Kiyi haƙuri!! Dan shine ginshikin aure dan ba'a sanin halin juna sai an zauna shi kuma zaman aure ba zaman tsuguno bane,zama ne wanda ake so sai mutuwa kinga kuwa sai ansa haƙuri,a ƙarshe ina miki fatan alkhairi da zaman lafiya Allah ya baku zuri'a masu albarka"daga haka yamin addu'a sannan yace na"sallame ki kuje ku Kaita"....
A lokacin gani nake faɗa kawai yakeyi ni inda Bature meye matsalata a duniya,amma taya za'ace ka auri wanda bakaso kuma ku zauna lafiya,ban ɗauki maganarshi da muhimmanci ba, amma na basu waje na musamman a cikin ƙwanyata na ajiyesu......
Wani ajiyar zuciya na sauke tare da wani ƙaƙƙarfan kuka da ya ƙwace min,duk abinda ya faɗa na gani ko ince ina kan gani,tunda ba rabuwa mukayi ba hali kuma kullum sabo nake gani,to amma ai ga kawata zaliha taci soyayya da Dan ladi kafin suyi aure har yanzu kuma bayan sunyi aure shekaru ba ɗaya ba suna nan ba matsalar komai sai Wanda ba'a rasa ba ,kenan dai nice banyi dace ba kamar yadda yace ba mijin da za'a mishi wannan soyayyar bane,haka nayi ta karatun wasikar jaki bansan adadin lokacin da na kwashe ina wannan kuka ba balle zamana a wajen daga dai karshe na miƙe na nufi ɗaya ɗakin da nake ajiyar sauran tarkace na da kujeruna dan ɗaya ɗakin kujera ɗayace a ciki mai zaman mutum ɗaya,shi na shiga na kwanta akan ɗaya mai cin mutum uku...
Washe gari ....
"An tashi lafiya, yau bamu gaisa ba" naji muryar hama akaina dago kaina nayi daga yankan tuwon da nakeyi zanyi dumame na kalle ta nace
"Ahhh hama kece barka da safiya an tashi lafiya?" na amsa mata da dan murmushi a fuskata ,
"Lafiya lau ya me jiki ashe umma jiki ya motsa?"
"Eh da sauƙi alhamdulillah,ina baban kasuwa?"
"To Allah ya ƙara dauƙi,baban kasuwa sun fita da babanshi"
Nayi ɗan murmushi da zama min al'ada nace"sarƙa uban rikici"tayi dariya.
Hama itace matar da muke dan yi sosai da ita a gidan , ba wai dan ina gaba da sauran ba ko bama hira ba , nidai kawai bana shiga abunda ba ruwana duk wacca tazo kofana ta kawo gulma har tayi gama iya kaci idan na ainun ince ta yi hakuri ko kuma Allah ya kyauta, idan kikayi kuskuren fadan abunda ban fada ba kikace na fada , to kin shiga goma dan bana daukar walakanci ko munafurci ko kadan ,sanin Halina yasa ba mai sako ni ,badan Basa maganata ba....
Maganar hama ta katse min tunani Jin ta fadin ...
"Jiya bakya nan munci uwar sabada ni da hassana ta hada munafurci, wai Iyalli>wato kakarta ta gurin uwa,wai mayya ce ita take turomin makaranda da suke damuna shiyasa duk maganin akeyi ba sauki ,ita take cinye min yaya shiyasa nake ɓari magana kala-kala dai ta dingayi,daga ƙarshe magana ya dawo kunne na,aiko nace sai ta nuna min inda ta ganta tana maita hmmmmmm atakaice dai Sale>wato mijinta , shiya bani hakuri kuma yau zamuje ofis Yan sanda ayi tsakani kafin magana ta mutu"...
Hmmmmmm.... Na sauke ajiyar zuciya mamaki na kusan kasheni, Atohhh mamaki ya kasheni mana inba haka ita lyalli ba a garinnan take ba balle ƙauyen take ma ba a kusa yake ba balle ince hassana tana da inda zata samo labarinnan bana jin tanada wani a garinma dan badan rasuwar kakan ita hamar ba, har mukaje mata gaisuwa ba, bata taba zuwa ba amma tsabar faɗe-faɗe irin na hassana ta faɗo abunda zaisa a ɗaure ta har igiya tayi rara , koda yake ba abun mamaki bane saboda zaiyi wuya magana ta tashi, kiji hassana bata ciki ,yau badan sale ba mutum ne ba mai son fitina ba ay da ta shiga goma sha takwas(18) dan shari'ar maita ba abu mai sauƙi bane ,tabbas hama tana da iskokai masu zafi ma kuwa dan gaba ɗaya halittar juye takeyi ta koma abun tsoro kuma tabbas tana yawan bari dan da ƙyarr cikin baban kasuwa ya tsaya,kuma yanzu haka ma wani cikin da ita, wanda shikam ALHMDLLH ana sa rai dashi dan ko cikakken laulayi batayi , sai kwaɗayi da yake sata.......
To masu karatu pls a daka ce ni , mu haɗu a page nagaba na har kullum amdy tejj pls vote for me kuma ayi comment dan bani kwarin gwiwa.....
Magana ta what's app *** na gode!!!!!!!!!