BADAƘALA

Part 6

by @chefmuaysh

BADAKALA ✍️ Aisha Hamza

Kallo ɗaya yayi musu yasan akwai abinda suka kulla tsakanin su don yanda idanuwansu sukayi fiki fiki

Ah aha ya faɗa yana kare musu kallo cikin zolaya yafara furta graduate graduate yan boarding gaba ɗayansu suka saki murmushi Ayrah tace Uncle ai bamu zama ba tukun sai jarabawar ta fito koh

Khairiyya dai taki sakin jikinta abu kaɗan sai Ayrah tadan zunguro ta kafin take dawowa dai-dai gaba ɗaya ya lura da yanayin ta amma bai kula ba suna shirin fitowa gaba ɗayansu saiga Uncle bash ya shigo suka haɗa ido da uncle Sameer sai ya kashe masa ido ɗaya gaba ɗayansu suka saki murmushi

Ayrah da taga sanda sukayi hakan kafin su ankara ta kamo hannun Khairiyya sukayo waje tare suka fito su sukayi gida su kuma su uncle suka wuce quarters ɗinsu suna firar su

A hanya Khairiyya tace nifa Ayrah saina tambaya uncle Sameer wa za'a kashe wallahi don nafara jin tsoron sa ma

Ayrah murmushi kawai tayi sai kuma tace ke daɗi na dake kenan gajen hakuri kila ma bawani abu bane ta faɗa tana sunkuyar da kanta don ita kaɗai tasan a yanzu kuma me take tunani akan uncle ɗin nasu

Haka dai har suka rabu suna firar makaranta Ayrah ta shige gida uniform ta shiga cirewa donta watsa ruwa ko zataji daɗi don yanxu a dakin gwaggo itada ya'yan Inno suke kwana ita tana saman lamisasshiyar katifar da aka sauke daga kan gado su kuma yaran suna saman wadda aka dora don duk sun fara wulakanta dakin da zarnin fitsari Badan Ayrah tana iyakar ƙoƙarin ta wajen gyarawa ba da ko shiguwa baiyi ba

Tunda ta shigo gidan inno ke aikin haɗa botikin abinci wake da taliya mai da yaji bata kawo komai ba har tayi sallah ta zauna tana gyara jikinta zainaba ta leko tana faɗin kizo Inno na kira ko gamawa batayi ba ta mike tafito

Inno ta tura mata bokitik tana faɗin gashinan yau tallah zakije saboda malam bai bamu isassun kuɗin abinci ba kuma dole a nema na dare tana haɗe rai tareda jujjuya idanuwa kamar tsohuwar karuwa

Ko uffan batace ba ta duka ta ɗauka bokitin tayi dakinsu dashi ko abinci ba'a bata ba an haɗa ta da tallah ba yanda ta'iya ta dauko bayan tasaka kayanta tafito rasa inda zata nufa tayi kasancewar ta kwana biyu bata fito tallan ba duk sai taji ta ba daɗi

Tun a kofar gida kuwa aka fara kwalla mata kira cikin ikon Allah bata dade ba takare ta dawo da botikin da kuɗin ta karba tana kirgawa tana Murmushin mugunta

Haka kwana biyu ta sanya Ayrah a gaba akan tallar nan ba yanda ta'iya don sai tayi ma ake bata abinci wani lokacin kuma ta sabe taje wajen Halima taci acan gashi sun daina zuwa makaranta

Yanzu ɗin ma fitowar ta kenan saiga Khairiyya a guje ta fado kanta kaɗan ya rage ta zubar da abincin Saida ta saketa kafin taga ashe tare suke da uncle Sameer

Sanye yake cikin kananun kaya da facing cap da dan ƙaramin glass a idonsa fari nan ta gaishe sa yake tambayar ina zataje tace zata je tallah ne

Tambayar ta yayi abincin na nawa ne ta faɗa masa yace ayi sadakar sa Allah yakai ladar ga gwaggo ba ƙaramin daɗi taji ba aikuwa hakan akayi yabata kuɗin

Nan yake faɗa musu sakamakon jarabawarsu ya fito shi kuma yau zai tafi gida dama shi ɗin bautar ƙasa yazo kuma ya gama sosai suka shiga tashin hankali don ma ya kwantar musu da hankali akan cewar zai dawo kuma su zama cikin shiri sanda zaizo tare zasu tafi ya kaisu makaranta don saima yasamo zai dawo

Khairiyya tasha kuka da suka rakashi gashi babu mai waya a cikinsu saidai ya basu number sa yace in sun samu waya su kirashi hakan saiya ƙara kwantar musu da hankali

Saida yabasu kuɗi yace su raba kafin yakawo wata katarda yabawa Khairiyya yace idan yatafi ta duba

Sanda tagama karantawa a fili Ayrah na jinta hada hawayenta Ayrah na aikin rarrashi Sosai taji daɗin kalamansa domin ya fada mata ya dade yana sonta kuma kodan ita dole ya dawo Khairiyya hada zazzaɓin ta na kwana biyu na rashin masoyi Abbanta yasha jiyya kafin ta ware

Randa ya cika kwana biyu da tafiya Saida suka samo waya suka kirashi aiko yasha rigima wajen Khairiyya don hada kuka ta sanya mashi dakyar ya shawo kanta

Yau da gobe sai Allah rayuwa ta juyawa Ayrah baya aikinta kenan tallah safe rana dare ba hutu ta rame ta rame abinka ga farar fata idan kaganta kamar wata fatalwa duk kibar nan ta zube sai tsawonta madaidaci da rashin kibar yasa yakara fitowa

Da muguwar gajiya ta kwanta bayan tadawo tallar rana,hakan yasa ko abincin rana bata ci ba juyi take taji ruwa a kanta sharrrr gaba ɗaya ta jike ai a wulkice ta mike tana zazzare idanu don ba ƙaramin tsorata tayi ba kyarma ta gabce mata tana haɗa hakora kasancewar sanyi ne lokacin

Inno ce tsaye itada bawale yana ta kyalkyala dariyar mugunta yana nuna Ayrah Inno da hannunta riƙe da kofi tace ja'ira ai dama tsintacciyar mage bata mage ni wallahi na tsaneki narasa uwar me yasa gwaggon nan ma ta dinga baki wani muhimmanci sai kace wata yar gida kin baje kan katifa kina sharar bacci

Itadai tayi tsuru tsuru tana kallon su don duk a dimauce take wani abun ma ba fahimta takeyi ba, bawale Inno tasa yahau watso mata kayanta tsakar gida wai ta koma dakin girki tunda ba'a girkin a ciki

Hawayene ɗaya na bin ɗaya ga uban sanyin da takeji ta tsugunna ƙasa tana faɗin Inno don Allah kiyi hakuri kibarni in zauna anan ɗin duk abinda kikeso wallahi zanyi maki takai ƙarshe muryarta na sarkewa

Inno ta buɗe baki zatayi magana Ayrah taji an fusgo hannunta tamike ba shiri Khairiyya ce tsaye take ta faman zare idanu tana cika tana batsewa tace ke wacece da zakice ta koma dakin girki wallahi ba zata koma ba

Kallon ƙasa da sama Inno tayiwa Khairiyya kafin ta kyalkyale da dariya tace ai hada su kaza acin maiko kenan ke kuma asuwa wacece ke

Nan fa suka shiga shirga ma juna rashin mutunci duk yanda Ayrah taso hana Khairiyya abin ya gagara karshe ma Saida Inno ta mareta hada hawayenta tana mata Allah ya isa tace da bai isa ba da ubanki bai zauna a garin nan ba ai duk kanwar ja ce keda itan tunda ba ubanda yasan daga inda kukazo ke da ubanki ita kuma bamusan ma daga ina take ba don ina da tabbacin shegiya ce ta faɗa tana nunnu nasu

Kalmar ta ta karshe ce ta daki zuciyar Ayrah ita kuma bamusan ma daga ina take ba don ina da tabbacin shegiya ce

Saitin zuciyarta kawai ta dafe don ba abinda zata iyayi a yanzu dama can kuma ba wani abun tayi ba fisgar hannunta Khairiyya tayi suka nufi hanyar fita ita kuma binta kawai tayi don ji take babu sauran wani kuzari a jikinta ihunn da bawale ya daka ne ya sanya su tsayawa don duk abinda akeyi yananan duke yana finciko sauran kayan Ayrah ɗin

Yanzu ma karo yaci dawani ɗan buhu madaidaici a karkashin gadon yahau buɗewa yana gama fito da akwatin ya ruɗe shine ya tsala uban ihuu

Kanshi inno tayi tana faɗin lafiyar ka kai kuma, kasamagana yayi yana mata nuni da akwatin itama kan akwatin ta nufa tana ƙoƙarin shafata

Kyallin hasken ranar dakin ne yakai ma akwatin har take ƙoƙarin dalle musu idanuwa daga kofar fitan da suka nufa wani irin burki Khairiyya taci tare da juyowa tadawo kan inda Inno suka dukufa kallon akwatin

Ita kuwa Ayrah ko a jikinta domin tasan da zamansa saboda shegen binciken ta tun gwaggo na da rai ta hanata taɓa shi domin itama bata taɓa fito dashi daga buhun ba saidai ta taɓa gwaggon tace karta buɗe ta maida shi amma yanzu haka maganganun gwaggon ne suka shiga dawo mata akan akwatin

Akwai sakon ki a kasan gadon nan kinsha tambayar menene a ciki ban faɗa miki ba yau ɗin ma ba faɗa mikin zanyi ba don Nima bansan menene a ciki ba

Amma nasan abu ne mai muhimmanci ki adana shi karkiyi wasa dashi gadonki ne duk randa kikaji kina sha'awar sanin wani abu dangane da wannan akwatin nasan zaki iya kokarin gwada buɗe sa amma babu makulli a jikinsa kece zaki nemo

Nannauyar ajiyar zuciya ta sauke tare da hawaye Masu dumi na tunawa da abokiyar firarta gwaggon ta kuma mai matukar kaunarta domin bata taɓa jin maraici ba sanda gwaggon na raye duk da wahalar da Inno ke sanya ta batasan ma menene maracin ba sai yanzu

Inno ce keta faman shafa akwatin kasancewar da yar ƙura a jikinsa amma hakan bai hanashi kyalli ba bawale ya katse ta da faɗin Inno wannan fa zinare duba kiga yanda yake kyalli tuni ya ƙara hargitsa ta Inno mai shegen son abin duniya

Bawale ya ciro rigarsa yahau goge sa Inno nakara kai hannunta kawai daga dan gefe sukaga jar danja takawo ai a guje suka nemi tserewa har suna bangazar juna Ayrah dai tayi sagale tana kallon ikon Allah 🤔

Khairiyya ce tafara dawowa don hada ita akayi wajen ganin abinda basu taɓa gani ba basu daddara ba suka ƙara komawa kan akwatin wasu numbers ne 1 to 0 daga kasansu kuma A to Z ne suka bayyana ajere kamar keyboard idan ka kalla sama kuma zakaga alamar ********** har guda shida alamar security ne a wajen amma ba zaka taɓa sanin dasu ba yanzu ma don sun kawo hasken ja ne da Inno ta shafa wajen

Nan fa aka shiga kallon kallo Khairiyya tace wa Ayrah menene wannan Ayrah tana ƙara lekowa don taga da gaske dai wutar yake kawowa ko kuwa don su a ganinsu wannan jan data kawo wuta ce wai

Ayrah dai batace komai ba don itama tafara shiga rudanin don gwaggo bata mata bayanin komai dangane da akwatin ba duk da zata iya cewa bata gama jin zancen ta ba bacci yayi awon gaba da'ita

Cikin rashin Sa'a Inno ta kuma shafawa wai taji koda zafi aikuwa nan take number ɗaya tahau kamar irin ana saka security ganin haka yasa bawale ma ƙara taɓa guda kamar wasa Inno ta danna last number da zai cika shida

Duk wanda yake cikin dakin Saida ya firgita don ita inno da akayi wurgi da'ita bata ƙara sanin inda kanta yake ba wata irin ƙara akwatin yayi daga wajen password din kuma yana danna warning tashin hankali wato dai akwatin wuta gareshi kana saka password ba dai-dai ba saidai kaji wuta taimaka mugun kamu

Ai daga ranar ba'a ƙara ganin bawale ba cikin gidan ita kuwa Inno jiyya ta kwanta don ba ƙaramin jiki ta jiba Ayrah kullum idan dare yayi kowa yayi bacci saita jawo akwatin tana ƙare mata kallo amma koda wasa bata taɓa gigin gwada password ɗin ba bare taga yanda Inno taji jiki

Khairiyya dama ranar tazo ne ta sanar ma da Ayrah uncle Sameer sunyi waya yace Abbanta yake son magana dashi suka nema waya aka hadasu yake masa zancen ansamu makarantar da zasu ci-gaba su shirya very soon zaizo Amma bai faɗa musu lokaci ba

Da murnarta tazo faɗa ma Ayrah ta iske abinda yake faruwa karshe itama tunda ta tafi bata sake dawowa ba saboda akwaita da shegen tsoron mutuwa don a lokacin ita mutuwa kawai ta hango ba ƙaramar razana tayi ba

Tunda Inno taji sauƙi bata sake marmarin koda shiga dakin ba ƙarshe ma yaranta tadawo dasu dakinta tace saidai su gwamutsa anan bata shirya rasasu ba don tace bom ne a ɗakin

Malam kuwa yasan da zaman akwatin domin shima gwaggon ta faɗa masa akanta amma ta tabbatar masa data Ayrah ce saidai ba ƙaramin mamaki yayi ba jin wannan zancen na abinda yasamu Inno

Aiko bayan sati ɗaya da yan kwanaki malam ya tabbatar domin bawale ne yazo da wasu abokansa marassa ji daya basu labarin abinda yafaru sukace karya ne saboda mugunta kuwa yace suzo su gani

Badan Ayrah taso ba ya sanya tafito musu da akwatin ba yanda Inno ma batayi dasu ba sukaki ji wai wallahi ko aljanine a cikin akwatin yau sai ya fito wanda yafi cika bakin kuwa aka ce ya shafa yana shafawa hada wani dakewa ganin numbers sun fito amma a zahiri fa a tsoracen shima yake nan ya shiga dannawa Saida bawale ya lura zai saka ta karshe yace ya jira ya fita inno kau daman tuni tabar gidan sai Ayrah dasu baba da sauran abokan masu cika baki

Koda ya saka number karshe takara buga wata ƙara wanda basu suka saka ba ma wani hada sakin fitsari don idan tayi ƙara kamar bom ɗin ya tashi yanda Inno ta faɗa shi kuwa wanda ya danna akwatin saida hankali ya fara dawowa jikin mutane kafin akaga inda akayi cilli dashi don shi ba'a san ma sanda ya warke ba don ya dade yana jiyya

Ayrah kuwa ko a jikinta domin abin ma ya daina bata tsoro sai mamaki bare yadda Baba yakara jaddada mata cewa akwatin mallakin ta ce domin da'ita aka bawa gwaggo ita akace kuma gadonta ce

itadai batason zancen ko kaɗan ma na wai wasu suka bada ita shiyasa abin bai cika damunta ba ma

Zumbur ya mike daga kan kujera yana zare idanuwa yana kallon matar dake kwance saman lallausan gadon matashi ne da bazai wuce 25 years ba a duniya

karin ruwa ne a jikin matar sai tulun magunguna da allurai a bedside daga gefe A shekaru bazata wuce 38 ba amma a yanayin yadda kowa zai kalleta za'a iya cewa takai shekara arba'in da wani abu saboda daga ganinta akwai wahala tattare da'ita

Agogon hannunta ya duba karo na biyu yaga da gaske hasken warning take kawowa hannunsa har kyarma yake wajen ciro waya daga aljihunsa bugu ɗaya kamar jiran kiran nasa akeyi kuwa ya furta Boss agogon hannunta na buga warning bamuji me akace daga can ɓangaren ba saidai ajiye wayar da yayi gefen kujerar da yake zaune

Numfashi take hankali kwance ruwan na shiga a hankali kamar yanda aka saita shi wani kiran ne ya shigo wayar yayi saurin dagawa iya abinda yace shine ok boss angama

Fita yayi daga dakin ba jimawa ya dawo hannunsa rike da wata leda ya buɗe sabuwar waya ce a ciki da layika guda biyar duka MTN ne nan take ya kashe waccan wayar da yake amfani da'ita da farko ya karya layikanta

Kallo fa ya koma sama nidai bangane ba amma idan akwai wanda ya fahimta ya sanar damu🤔

Tofah ana wata ga wata nan kuma ina muka ɓullo ❓

Waye wannan saurayin dawa kuma yayi waya ❓

Shin wacece wannan matar da take kwance a wahalce ❓

Shin kuna tunanin da nakeyi kuwa wannan wane irin akwati ne mai jan mutane har su suma ❓

Gashi dai ance mallakin mutuniyar ku ne Ayrah 🤔

Tofah menene yasa Ayrah bata son zancen da ake mata na wani yakawo wa gwaggo ita kuma bata damuwa da son sanin komai dangane da kanta ❓

Nidai abin na daure man kai bansani ba ko kuma haka

BADAƘALA ce ta gaske anan na lura

To yanzu munshigo cikin matakin farko tsundum fa amma kafin muje ga na biyu akwai aiki domin cakwakiyar tanada yawa

Ina ganin addu'o'in ku Nagode sosai Allah yabar tare da alkhairi

Sai daku 🤟