Chapter fourty one:
by @autum17
Aliyu bai karɓi baby'n ba sai da aka mayar da Salamatu a intensive care unit,bayan ta farfaɗo sannan fa,he only took the baby lokacin da zai miƙa ma Salamatu only then did he see her,Nan danan yaji yana ƙaunar ta cuz tana bala'in kama da Salamatu like a carbon copy, miƙama Salamatu ita yayi ta karɓa tana murmushi ga wani irin farin cikin da baya misaltuwa a cikin zuciyar. Shima Aliyu yazo ya zauna beside her hugging both the mother and the baby.
Kwanaki kaɗan Salamatu tayi aka sallame su dan bata da wata matsala. Bayan sun dawo gida Aliyu da kanshi yake kula da su duk da Salamatu tayi insisting ya kawo yan aiki he refused. Ya kira wurin aiki ya sanar da su mutane da yawa sun zo taya shi murna, har da Xue Yao da Shang min they came on a different day. Lokacin da Salamatu taga Xue Yao ta wani tsuke fuska, murmushi Xue Yao tayi tana zama kusa da ita ta karɓi baby'n tare da faɗin '' She's so beautiful '' ƙara tsuke fuska Salamatu tayi tana faɗin '' Masha Allah '' Yar ƙaramar dariya tayi tace '' Kidena haɗe rai Ni dake ba maƙiya bane abinda ya haɗa mu yanzu no longer matters. Nima yanzu inada mai sona genuinely,I don't have to beg for love '' Xue Yao tayi maganar tana riƙe hannun Salamatu da ɗayan hannun ta. Ɗan sassauta fuskar ta salamatu tayi,'' Good girl'' Xue Yao ta faɗa tana maida kallon ta ga baby'n ' nima wata rana zan haifi ya ko ɗa? Da Shang min?' tayi tunanin a ranta tana kallon out side the window.
Ajiyar zuciya ta sauke lokacin da saƙon shang min ya shigo wayar ta,tun da suka shigo ya gaida salamatu suka fita shida Aliyu to God knows where.
Bayan shirun na ɗan lokaci Xue Yao returned the baby ta miƙe tana yi ma Salamatu fatan Alkhair. Salamatu was surprised da Canjin da tagani tare da Xue Yao but she just took it as anyone can change.
Bayan fitar Xue Yao the space became empty for her,her mind wandered back to Nigeria for the first time in a long time.
Yanda ake celebrating kankanin biki in a grand style,yanda mutane nesa da kusa zasu taru wa'yanda aka sani da wa'yanda ba'a sani ba, yanda family members zasu kasance tare da kai...amma anan she's alone it felt oddly different. Banbancin ba kaɗan ba. Wani irin nostalgic feeling ne ya lulluɓeta she felt alone ji tayi tana so ta koma gida. Hawaye ta ji sun cika mata ido,ta kalli yar jaririyar ta dake bala'in kama da ita, abinda ta ɗauko na Aliyu kawai shine shape ɗin idanunsa,his almond eyes. Ƙara rungume ta tayi ajikin daidai Aliyu na shigowa.
'' Rose'' ya kira yana matsowa kusa da ita,zama yayi yana ɗago fuskar ta that was tear streaked, Cikin Muryar kuka tace '' Nayi kewar gida Aliyu,ina so in ganni cikin family and friends,Ina so In yi celebrating wannan abin murna cikin yan uwana Leo, I missed home so much I feel lonely '' ta faɗa in loud sobbs.
Rungumota Aliyu yayi yana buga bayan ta slowly ''its okay Rose'' abinda ya faɗa kaɗai kenan he couldn't say further,shima har ga Allah yana so ya koma cikin danginsa, amma yasan it's impossible.
Suna a haka har bacci ya fara ɗaukar ta,karɓar baby'n yayi ya kwantar da ita tsakiyar gado ya gyara ma Salamatu kwanciya daga gefe ya kwanta ɗayan gefen putting the baby in the middle. This is the only way to escape the pain.
*****
Ranar suna Aliyu yayi ma Salamatu Abinda batayi tsammani ba, kamar yanda ake celebrating suna a Nigeria haka shima yayi,ya gayyato mutanen Nigeria dake zaune a China,suma yan china'n he invited them yasa sukayi shiga irin ta yan Nigeria both Igbo and Hausa. Yanda ake a Nigeria wasu na tare da mai jego wasu kuma tsakiyar gida suna dafa abinci hakan ne ke faruwa yanzu ma. Babu wani banbanci the only difference is family
Salamatu tayi farin ciki beyond words.... Mutane sai celebration ake ga drinks and foods of all kind. Xue Yao itace ƙawar mai jego da wasu yan Nigeria da Salamatu bata sani ba,Shang min ƙawar baban baby. Abun
ya ƙayatar sosai. Ga raguna guda biyu da yasa aka yanka just for the naming
Lokacin suna aka mayar ma da baby sunan maman ta amma ana kiranta da Mahmah,Anci an sha anyi hotuna da yawa anyi nishaɗi kafin kowa ya watse.
Koda dare yayi gidan was back to its normal self shigowa ɗakin Aliyu yayi wurin ƙarfe 10:00 yaga har Salamatu ta canja musu kaya sun kwanta.
Bayi Aliyu ya shiga shima yayi wanka ya sauya kaya sannan ya hau gadon,ya fara kallon fuskar baby'n shi kafin matar shi. Wani irin so da ƙaunar family'n nashi of a different level yana ƙara ratsa duk wani gaɓa da jijiyoyi yana jikin shi.
Ahankali ya kai hannun sa ya shafa fuskar ta,buɗe idon ta tayi and their eyes met. Miƙewa zaune tayi ya jawo ta ya zaunar saman cinyarsa yana shafa gashin ta,tana wasa da yatsun ta tace '' Thank you so much, this is the best gift I could ever ask for '' tayi maganar tana kallon fuskar sa kamar yanda shima yake kallon ta, murmushin sa ya kasa ɓoyuwa slowly in a whisper yace '' your appreciation is my biggest happiness Rose ina matuƙar ƙaunar ki,bana tunanin i will survive if anything happens to you Rose '' yayi maganar yana haɗe hannayen su haɓar sa a kafaɗar ta.
'' I love you too '' she replied kafin ta juyo placing her lips on his it was a short sweet kiss.
Lumshe idanun sa Aliyu yayi kafin ya kwantar da ita on her side ya kwanta ɗayan gefen the baby in the middle.
**************
Aliyu ya cigaba da zama gida yana kula da Salamatu acewarsa sai tayi arba'in kafin ya koma aiki,
Daga lokaci zuwa lokaci yan wajen aikin su ke kawo masa ziyara, wani ɗaki dake ɗan nesa da nasu ya gyara sosai yasa akayi decorating ɗin komai na ciki pink with Barbie princess theme ya cika shi da kayan wasa kala kala irin na yara for the baby. Kullum shi yake komai safe da dare da ƙyar yake bari Salamatu tana wani aiki,idan baby'n ma ta fara kuka Aliyu was always the one to take care of her,kawai bai son Salamatu ta takura. He was so so....!!
Bayan Salamatu tayi arba'in Aliyu ya koma bakin aikin sa kamar yanda ya faɗa, amma lokacin break nayi zai dawo gida till break is over,Babu wanda bai san da wannan ba a company'n har ake kiran sa da 'worry wart dad' sai dai yayi murmushi yace '' bazaku gane ba''
********
Rayuwa ta cigaba da tafiya har Mah-mah ta iya tafiya,yanzu ta iya yan ƙananun maganganu, Salamatu da bata zuwa ko'ina ke koya mata magana da Hausa, yarinyar tana da saurin ɗaukar abu ga shegen wayo,
Lokacin da takai shekara biyu ta iya tafiya ta iya magana *coherently* Aliyu insisted sai dai ta koma ɗakin da ya gyara dan ita,she was disturbing their moment acewarsa 👀
Aiko bayanda Salamatu ta iya dole Mah-mah ta koma ɗayan ɗakin. From time to time Salamatu ke zuwa tana duba ta cikin dare. Bayan tafiyar ta Aliyu ya kanai maye Salamatu wai ta dena kula dashi attention ɗinta nakan baby.dariya tayi tace'' toh ai Saboda baby can't take care of herself...'' Aliyu ya katse ta da faɗin '' Ai nima ban iya kula da kaina '' yayi maganar yana marairaice fuska stylishly romancing her kafin labari ya ɗau route...
Lokacin da Mahmah ta kai shekara biyu da watanni kamannin ta da salamatu were more clear, gata kyakkyawa,kowa ya gani sai ya maganta dan dama Aliyu yakan fita dasu every weekend,hakan yasa salamatu ƙara jajircewa wurin yima ta addu'a. enrolling ɗinta akayi a wani private school, mai uniforms riga fari sai pleated skirt baƙi,ranar da ta fara zuwa ta birkice akan ita bazata zauna ba,sai kuka she turned the school upside down sai guje guje take daga nan zuwa can ita ala dole bazata zauna ba gida take so,yara irin ta sai dariya suke mata but she didn't care
Sai da aka kira Aliyu yayi mata jan ido sannan ta nutsu amma fa taƙi tayi karatun.
Lokacin da Aliyu yazo ɗaukar ta bayan an tashi sai uban surutu take zubawa kamar ba ita ce take kula da safe ba, murmushi kawai Aliyu yayi yana girgiza kansa
It intensified lokacin da suka haɗu da Salamatu sai ta katse ta kafin tayi shiru.
Daga nan bata sake cewa komai ba sai da aka zo dining kowa nacin abinci suddenly ta ajiye cokalin ta tana faɗin '' Papa kashan abinda ya fayu a makalanta?" Salamatu da Aliyu suka dawo da kallon su kanta,kafin su bada amsa ta cigaba da faɗin '' wani yayo yayi kashi a wando kuma...'' ajiye cokalin ta Salamatu tayi tana hararar Mahmah tace '' yima mutane shiru!" Shiru mamah tayi tana xaro almond eyes ɗin ta, Aliyu yace '' ai da kin bari ta cigaba '' yar hararar sa Salamatu tayi tace '' muna cin abincin ko?" Yace '' eh mana'' girgiza kanta Salamatu tayi ta kalli Mahmah data nutsu tana faɗin '' makarantar da kike kukan baxaki zauna ba taya akayi kika san abinda ke faruwa?" Tana turo baki Mahmah tace '' ai ajin mu ɗaya kuma bayan shi akwai wata yalinya itama tana ta kuka sai kuma wata yalinya itama tana ta wasa da amincin ta duk ta ɓat...''
'' yi shiru kici Abincin ki'' inji Aliyu ganin surutun bazai ƙare ba. Ɗaukar cokalin tayi ta fara wasa da abincin maimakon taci,tashi Salamatu tayi tabar wurin,Aliyu was the one who cleared everything ya gyara ma Mahmah jiki bayan sun gama cin abincin
Aliyu was a perfect wife material gashi very romantic. Soyayya suke gwada ma juna ba kaɗan,familyn su, su uku and it looks perfect.
Mahmah na cika shekara uku aka haifi Samha,itama kamar yanda akayi celebrating ɗin bikin Mahmah haka Aliyu ya ƙara tarkato mutane akayi wannan yarinya taci suna Samha. Dama lokacin hutune, dan haka Aliyu ya zauna gida shida Mahmah suna kula da Salamatu da baby, kullum Mahmah na tare da Samha cuz she loves the baby so much..,Ga baki ɗaya Samha tafi kama da Aliyu abinda ta ɗauko na Salamatu kawai shine foxy eyes ɗinta, Salamatu na bala'in son yarinyar hakan yasa na take kiran ta da 'moon'
Lokacin da hutu ya ƙare za'a koma makaranta, Mahmah ta aza rigima akan sai dole an barta ta tafi da Samha,da ƙyar da wayau aka samu akayi convincing ɗinta TA tafi makarantar.