WAYE SHI?{Behind the mask}

Chapter fourty two:She was hurt

by @autum17

Lokacin da Samha ta kai shekaru uku, Salamatu tayi tsammanin yarinyar zata zama kamar mama but reverse was the case,bata magana,bata murmushi she rarely cries bata dariya. Idan ana mata magana sai dai taita kallon Mutum kafin kuma ta kauda kai.

Mafiyawanci tafi son tazama ita kaɗai,idan tana wasa mutum yazo wurin ta daina wasar kenan her face was always expressionless.

Idan Mahmah tazo tana mata wasa idan taƙi responding sai Mahmah ta fashe da kuka.

Abun yana samun Salamatu da farko ita da Aliyu sun ɗauka Samha was autistic Saida suka tafi Asibiti sannan suka gano she was actually diagnosed with schizophrenia, wani condition da yake hana mutum sanin ko yana farin ciki ko baƙin ciki,ko yana jin haushi ko akasin hakan it just doesn't allow you to know what emotions you're having.

Hankalin Salamatu ya tashi har da kukan ta,Aliyu was the one who console her cikin kuka tace '' yanzu ya za'ayi insan in tana farin ciki ko akasin hakan? If she's in pain or not, how do I develop the bond of mother and daughter with her Leo?" Tayi maganar wani ƙunci na cika zuciyar ta

Rungume ta Aliyu yayi yace '' we will try'' he said yana shafa bayan ta, kafin ya kalli Dr asking for a solution simply Dr tace sai dai ta dinga zuwa therapy sessions

Godiya suka yima ta kafin Salamatu ta ɗauki Samha da take nan kamar gunki suka tafi.

Along the way Salamatu was helplessly staring at her daughter,she felt weak and heart broken

Lokacin da suka iso gida har Samha tayi bacci hakan yasa Salamatu ta wuce da ita ɗakin su ita da Mahmah ta kwantar da ita ta kwanta gefen ta.

Through out the day she was so moody, lokacin da suka zauna dining sai surutu Mahmah take tana ba Samha labari itako Samha ta kafe ta da ido ko motsi batayi ganin yanda take kallon ta yasa Mahmah dakatawa kafin slowly tace '' Moon,kina fahimtar abinda nake faɗa ko?" Mahmah tayi maganar tana waro mata almond eyes ɗinta,Aliyu da Salamatu ma suka kafe Samha da ido waiting for her response,cire idon ta tayi daga kallon Mahmah ta dawo dashi ga abincin ta batareda tace komai ba, Salamatu ta miƙe ta bar wurin eyes watery she wants to cry, miƙewa Aliyu yayi ya bi Bayan ta. Mahmah ta ajiye abincin ta tana kallon su Aliyu da suka bar wurin kafin tazo ta zauna kusa da Samha ta ɗauki cokalin ta ta fara bata abincin,kamar Samha bazata karɓa ba sai kuma ta buɗe baki slowly ta fara karɓar abincin '' Good girl '' Mahmah ta faɗa excitedly cuz wannan ne karo na farko da Samha ta bari ta bata abinci a baki'.

Bayan sun gama cin abincin Mahmah tace '' Moon,muyi wanke wanke '' Samha bata amsa ba saima ƙarshen rigar ta da take wasa dashi,jawo hannun ta Mahmah tayi suka shiga kitchen ɗin tana wanke wa, Samha na ɗauraya or More like ta zuba ma kwanonin idanu kawai ba abinda take.

Bayan sun gama Mahmah taja ta suka koma ɗakin su,kowa da gadon shi, wardrobe Mahmah ta buɗe ta ɗauko wasu orange colored pajamas guda biyu tazo inda Samha zata cire mata kaya ta samata pajamas ɗin da sauri Samha ta riƙe hannun ta,in a whisper tace '' na iya '' sakin baki da hanci Mahmah tayi tana kallon samha like she couldn't believe the girl just spoke to her. Idan mutum zai kwana yana magana Samha bazata amsa ba, but she just did.

Wata dariyar farin ciki Mahmah tayi kafin ta jawo Samha hugging her tightly, Samha sai numfashi take cuz she didn't like any foam of physical contact kuma Mahmah wasu hugging her way too tight.

Cikin farin ciki Mahmah tace '' ƙara magana inji!" Zare jikin ta Samha tayi ta ɗauki kayan da Mahmah ta bata ta shiga toilet

Dariya Mahmah ta kwashe da shi,she just couldn't believe Samha spoke to her. Bayan ta fito daga toilet ɗin Mahmah ta shiga ta sa nata kayan baccin mai makon da ya fito ta tafi ta kwanta saman gadon ta sai kawai ta hau gadon Samha.

Samha data lumshe idanun ta,ta buɗe su tana kallon Mahmah that was facing her, murmushi mahmah tayi her white teeth visible,kafin ta maƙale hannun ta a waist ɗin Samha tace '' tare zamu kwana yau'' Samha tayi tsuru da ido jin yanda Mahmah ta wani riƙe ta gam,she doesn't like it.

Amma bayi ƙoƙarin ƙwace kanta ba, haka har bacci yayi gaba dasu.

Salamatu da Aliyu ke suka shigo ɗakin cuz she insisted, saman gadon Mahmah suka fara kallo basu ganta ba, kafin idanun su ya hango ta tare da Samha, murmushi salamatu tayi ganin yanda su biyun suka wani rungume juna hawaye taji suna bin fuskar ta '' It's okay Rosy'' jinjina kanta tayi kafin suka idasa shigowa cikin addu'a tayi musu ta tofa kafin suka juya suka fita.

Haka rayuwa ta cigaba da tafiya, Salamatu trying so hard to bond with Samha,ita kam Mahmah koda yaushe suna manne da Samha,it was hard for Salamatu kafin ya samu Samha warmed up to her,A shekara huɗu Samha ta ɗan fara iya murmushi koshi Murmushin looked forced kamar ba daga ƙasan zuciyar ta bane.

Haka dai suke managing yanzu ya na ɗan magana amma ba mai tsawo ba, kuma har yanzu tafi so ta kasance ita kaɗai

Wannan shekarun ne aka sata makaranta, Mahmah na shekara bakwai ita kuma huɗu, tun daga ranar da ta fara zuwa makaranta aka fara bullying ɗinta but then...komai mutum zai yi mata sai dai yayi ya gama amma babu wani reaction a fuskar ta,iya ka idan ka gama ta kakkaɓe kayan ta tayi gaba.

There was never a reaction, akwai wani yaro mai suna yang katae ya tsani samha shida group ɗinsa kullum sai sunyi bullying ɗinta, bayan su akwai many more amma Samha bata taɓa faɗawa kowa ba,idan taji ciwo kawai zata yi treating kanta ne ba tareda kowa ya sani ba. She was very careful not to let anyone know.

Lokacin da takai shekaru shida,abun ya ƙara intensifying, still she was able to take it, she never complained,she never made a move to retaliate. Mutane suyi ta comparing ɗinta da Mahmah cuz Mahmah gabaki ɗaya appearance ɗinta was like that of a doll very beautiful and alluring ita kuma Samha looked some how,ga wani ƙaton round framed glasses da take sawa that looks bigger than her face. Aside from that Mahmah ta haɗa kyau da ƙwaƙwalwa ita kuma Samha to everyone around she was to slow to understand things Amma ba haka bane,ta zaɓi kawai tayi kamar bata gane abubuwa da sauri ne saboda idan mutum nada ƙoƙari people will be buzzing around you kamar ƙuda she doesn't like crowd.

Sannan Mahmah tana cikin wani top most beautiful girls clique, idan Samha taje wurin zasu ke dinga hantarar ta ne, duk da idan Mahmah ta sani sai sun kwashi yan kallo da mutum

Dan akwai ta da tsiwa,ga tsoro,ga saurin kuka amma kuma akwai nacin faɗa especially idan Samha was involved tana son ƙanwar Tata it's not a hidden fact.

Itama Samha tana son Mahmah sosai ma,cuz tafi jinta comfortable idan suna tare da Mahmah daga ita sai ita, sai mutum na biyu da take ɗan jinta comfortable around itace Salamatu their mom,Amma Aliyu? Ganin sa take kamar wani stranger, Babu wani bond tsakanin su,idan ma ta ganshi sai dai ta bar wurin shi kuma ya ɗauka kawai tana yin hakan ne due to her condition baya Binta Saboda he wants to respect her choice. But she wanted more than that,she wanted him to hug her and Peck her,play with her kaman

yanda yake da Mahmah.

Tafiya take ita kaɗai zuwa wani garden dake bayan class ɗinsu sai ga wasu yara su biyar mata uku maza biyu sun fito daga ɗayan side ɗin sun sha gaban ta,dama sun san zata zo

Wani mai ƙiban cikin su yace '' oh looks who it's!"

In a pretending tone wata tace '' WHO?"

Wata mai blonde hair tace '' it's the loser'' Nan suka haɗu suna bullying ɗin Samha dake kallon su like unimportant elements

Ɗan babban nan dayayi magana ya matso gaba Samha bata yi aune ba kawai ya kwashe ta da mari, mai blonde hair kuma ta ture ta ta faɗi hakan yasa uniforms ɗin ta staining.

Kallon su Samha tayi da foxy eyes ɗinta suna mata dariya calling her names suna zagaye ta, wata mai suna qian luo ta ɗauko wani abu baƙi daga cikin jakar ta tace '' ya kamata muyi mata penti '' sauran kuwa suka yarda excitedly su karɓi abun suka fara yi mata wanka dashi.

Samha zaune tayi bata ko motsa ba,sai da qian luo tazo ta taka hannun ta,it was painful but her face remained expressionless,hakan bai ishe su ba suka rufe ta da suka, Mahmah dake zuwa da clique ɗinta ta hangi Samha zaune tsakiyar su while they bully her, suma sauran abokan ta were surprised duk da sun ɗan ji daɗi they hated the girl.

Ƙarasawa wurin Mahmah tayi tana kallon abinda ake yiwa Samha idanun ta suka ciki da ƙwalla,aiko idanun ta suka rufe yaran nan su biyar ta kamasu ta dinga dukar su kamar an aiko ta sai ihu suke.

Ita dai Samha still tayi zaune she didn't move and she didn't look like she was going to

Saida Mahmah tayi ma yaran nan jage jage,sun jigata kafin mutane suka ankara aka zo raba su. Jan Samha tayi suka bar wurin while people murmured among them selves. Su kuma ƙawayen ta tunda ta fara dukan yaran nan suka ga idan har aka zo zata iya kifewa dasu suka sulale suka bar wurin.

Wani empty class suka shiga, Mahmah ta rufe class ɗin tazo ta fara yima Samha ihu, Samha ta dinga Binta da ido,'' don't give me that shitty look damn it!!!!" Mahmah ta faɗa cike da ƙaraji,ga hawaye na bin fuskar ta kamar ita akayi ma wa, sauke idon ta samha tayi slowly tace '' I'm sorry '' wani irin mugun kallo Mahmah tayi mata kafin ta tako ta zo ta tsaya kusa da ita, ta riƙe fuskar ta in her palm suna kallon juna tace '' Moon,you have to stand up for yourself,it doesn't matter ko kina da feelings or not,dole idan ana maltreating ɗinki ki rama, idan ke baki jin zafi muda muke tare da ke it hurts us! Idan baki tsaya ma kanki ba Ni body would stand up for you! A Duniyar nan Ni body has the right to step on you ko su maida ke punching bag pls Samha!" Mahmah ta ƙarashe maganar in a pleading tone dan tasan Samha saurare take kawai but she won't heed.

Banko ƙofar akayi,wani senior yayi musu alamar su biyo shi, Mahmah tana so ta tambaye shi ina zasu the cold glare he shot her yasa tayi gum da bakin ta.

Sai kuma ta riƙe hannun Samha suna tafiya every now and then yana ɓoye Samha bayan ta, wannan gesture yasa Samha jin wani irin tururin ƙauna ya daki zuciyar ta more than before.

Office ɗin principal aka kawo su,there uwayen yaran da Aliyu ne zaune sai kuma yaran ƙarasowa ciki sukayi kallo guda Aliyu yayi musu yaji ranshi ya ɓaci who did that to his children?

Miƙewa yayi ya fara bala'i akan me wa'yannan yaran za suyi ma ya'yan shi haka,dan yasan har tunda aka kawo ƙarar su,and the way the looked, bullying ɗin su akayi.

Aiko suma sauran iyayen yaran suka tashi suna zubo nasu jawabi wuri ya kacame da hayaniya, quietly Samha taja hannun Mahmah suka fita cuz she didn't like noise,daga ƙarshe dai barin office ɗin principal sukayi kowa ranshi a ɓace.

Aliyu samun su yayi suna jira bakin motar shi da sauri ta ƙarasa, amma maimakon yayi takan Samha wurin mama ya fara zuwa though she looked fine,hakan yayi ma Samha zafi not because she was jealous but it was obvious a wurin shi,she was always the last. Sauke idon ta tayi daga kallon yanda yake duba Mahmah if she was injured

'' lafiya ta lau,pa Samha was the one bullied '' sai lokacin Aliyu ya kalli inda Samha take,she was looking at another direction,ƙafafun ta haɗe wuri ɗaya kayan ta duk jirwaye gashin ta looked like a bird's nest. Miƙewa yayi yazo Wurin ta zai mata magana juyawa tayi ta fara tafiya tana faɗin '' I'm fine '' daga haka bata sake cewa komai ba sai juyawa da tayi ta tafiyar ta.

Bayan tafiyar ta Mahmah ta kalli Aliyu ta ɗan ɓata fuska tace '' she's hurt '' tayi maganar tana kallon bayan Samha, shiko Aliyu yayi mamaki and he felt guilty Taya akayi Mahmah ta gane Samha was hurt not him? Mahmah ta ƙara faɗin '' You should have attend to her first '' tana gama faɗar haka ta bar wurin towards Samha,shafa goshin sa ALIYU yayi he felt anxious kafin ya shiga motar shi ya bar wurin,idan ma yace su tafi baza su bishi ba

Slowly take tafiya har Mahmah caught up to her,riƙe hannun Samha tayi tana faɗin '' I'm sorry moon'' batareda ta kalle ta ba tace '' meya sa kike ban haƙuri?" Shiru Mahmah tayi,she was speechless. Locker room suka tafi suka canja kaya kafin suka wuce aji.

Bayan sun dawo gida babu ɗayan su daya faɗi abinda ya faru a makaranta including Aliyu, rather sun ci abincin su silently Amma not a heavy silence.

Kwanaki sun cigaba da tafiya while Salamatu, Mahmah da Samha suka cigaba da growing closer, Samha da Aliyu their relationship became more *detrimental*

Salamatu was so close to her children da idan suna su uku komai tare suke,dafa abinci, wanke wanke da sauran su. Cikin kwanakin ne kuma Aliyu ya kawo wani mai suna cheng xiao wanda zai ke dinga laundry da na shukoki ruwa tunda Samha ta ganshi taji ta tsaneshi,wani irin mayataccen kallo yake Binta da shi and sai ya dinga sa kaya matsatstsu,she hates him to the core a zuciyar ta. Amma a fili she was indifferent.

Haka kuwa yake aikin shi cikin kwanciyar hankali,ga respect,ga kwantar da kai ga girmama na gaba dashi,a ɗan wannan lokacin yayi winning ɗin trust ɗin yan gidan but not Samha,ya kuma yi studying ɗin kowa ya gane, Mahmah akwai tsiwa da ƙarfin hali ga nacin tsiya,she wouldn't be an easy victim for his motive Amma Samha? Idan za'a kashe mutum gaban ta baza ta ce uhm ba,hakan yasa ya fara targeting ɗinta. Yar ƙaramar dama yake nema once ya samu ya biya buƙatar shi zai yi gaba.

Bayan sati biyu suna zaune a parlor dukan su saboda weekend ne Samha tazo ta tsaya gefen Salamatu dake kallon cartoon tare da Mahmah,Aliyu daga ɗayan gefen a little fat,sai Mahmah kwance ƙasa. Dukan su hair style ɗin su two steps da ya sauko har kafaɗar su.

Ganin Samha kusa da ita yasa salamatu yin murmushi ta miƙa hannu ta jawo ta tace '' kina buƙatar wani abu ne?" Jinjina kanta tayi,hakan yasa Aliyu da Mahmah dawo da attention ɗinsu kanta, murmushi salamatu tayi kafin ta zaunar da ita saman cinyar ta tace '' faɗa min'' ƙasa da kanta samha tayi bayan shuɗewar kusan 5mints tace '' ina so in koyi martial arts, taekwondo '' daga nan bata sake cewa komai ba.

Da sauri Mahmah tazo ta tsaya kusa da ita tace '' nima zanyi '' Aliyu ya juyo disapprovingly yace '' babu wanda zai yi wani martial arts can '' yayi maganar strictly, Salamatu ta ɗan juyo ta kalle shi but bata ce komai ba, Samha tayi ƙasa da idon ta kafin tace '' but i want to '' share ta yayi kamar bai ji ba. Shiru tayi batace komai ba kafin ta miƙe ta bar wurin walking slowly, Salamatu bata ji daɗin abinda Aliyu yayi ba, miƙewa tayi ta bi bayan Samha Mahmah ma tabi Bayan su.

'' why doesn't he love me '' tayi maganar ma kanta in a whisper tana tsayawa bakin window

Salamatu ta ƙaraso ciki ta zauna bakin gadon tayi gyaran murya, kamar Samha zata share sai kuma ta juyo alamar tazo Salamatu tayi mata,zuwa tayi kanta ƙasa ta zauna kusa da Salamatu '' meyasa kike so ki koyi martial arts Moon?" Inji Salamatu gently, Samha dake kallon wani wuri tace '' Nothing '' Salamatu bata ƙara cewa komai ba cuz tunda Samha ta bada wannan reply ɗin that's the end of the conversation, Mahmah CE ta banko ƙofar ɗakin excitedly tace '' pa ya yarda'' ɗan kallon ta Samha tayi tace '' how?" Mahmah in a carefree attitude tace '' I convinced him,kin San yana sona he can't turn me down '' ita Mahmah tayi maganar bada wata manufa ba amma maganar ta daki zuciyar Samha,ke nan ita Aliyu bai son ta? Ajiyar zuciya ta sauke feeling so sad, Salamatu ta jawo ta ta rungume ta, though Bata San abinda ke gudana acikin zuciyar ta ba,but she felt she needed a hug.

Kwantawa sukayi su uku Samha a tsakiyan su, their hands wrapped around her,hakan yasa baƙin cikin abinda Aliyu yayi mata vanished just like that.....