9
by @rufaidaumar
ALWASHI
34
©Rufaida Umar
MAMAN MEENAT SUPPLEMENT/SKIN CARE
Yar uwa muna saida kowanne irin supplement na gyaran jiki wanda zaisaki fito fes kamar sabuwar Amarya, yar uwa shin kurajene suka dameki, ko matsalolin jikine kamarsu rama, ko kibace tayi miki yawa kikeso ki rage, bushewar fata ko karancin ni'ima ko budewa ne ko infection? Ko kuma so kikeyi fatarki tayi laushi ki dinga sheki kina haskawa wato kalar madara dai Haj to ki garzago
Yan uwa kusani duk wani supplement da zamu kawo muku sai munyi bincike mun tabbatar da ingancinshi, mun kuma tabbatar da cewa bashi da wata illa ga lfy
Akwai masu cewa sunsha supplement amma har yanzu basuga wani canji ba, to yar uwa kodai an baki fake ko kuma ba'a baki wanda ya dace dakeba, kokuma bakisha yadda ya dace ba, kisani yar uwa kafin ki fara shan supplement akwai ka'idoji daya kamata ace kin kiyaye kuma kin kula dasu matukar kinaso suyi miki aiki yadda ya kamata kuma cikin sauki ***
1. Akwai Supplements na gyaran jiki ciki da waje, munada set na uwargida dana Amare da masu jego
Sannan ga wadanda sokeso jikinsu yayi kyau sosai amma basa son susha supplement to albishirinku muna da kowanne irin mai na gyaran jiki da kuke bukata irinsu lotion, cream, soap, scrubs, face Cream,sun screen, serums concentrate, hair oil, hair cream face mask etc
Muna saida duk wasu nau'in supplement Lotion da kuke bukata, sannan Maman Meenat collection ba anan kadai ta tsaya ba muna saida turaruka kowanne irin na wuta dana jiki, da Airfreshners da air wick, sayen daya ko sari ke dai kawai neme ni a wannan number ***
***
Da fara'arta ta yiwa Inna barka da zuwa duk kuwa da yanda Innar ta ci magani. Bayan ta zauna ne Mamin ta gaida ta jiki a sanyaye, kusan za ta ce ta manta rabon da surukarta ta tarbe ta da irin wannan fuska, iya girkinta shi ne abu na farko da ya siyamata fada a zuciyar Inna.
Afrah da Kausar suka shigo falon da sallama, dawowarsu kenan daga wajen wankin kai. Ganin Inna Afrah ta ƙarasa da sauri ta rungume ta ba ta ko damu da yanayin fuskarta ba.
"Kai amma wannan matar kin shammace ni, jiya fa na gama cewa Mami ni gidanki zan je a can zan yi azumin arfa da sallah."
Inna mai masifar son jikoki sai a sannan ta yi dariya gami da girgiza kai. Ita dai Mami murmushin ta yi itama don wannan ba abin mamaki ba ne a wurinta.
"Inna barka da rana."
Inna ta dubi Kausar cikin rashin fahimtar ko wacece ta amsa, Afrah ce ta ce.
"Lah ba ki gane ta ba ko? Kuma fa mun taɓa zuwa gidanki tare, Kausar ce wacce Hamma zai aura in sha Allah."
Nan da nan Inna ta sauya fuskarta. Sai lokacin ta tuna ashe batun auren ne ma ya kawo ta. Ta ji wani batu a bakin Hajja cewa dole Salma ke yiwa Areef din kan yarinyar.
"Na ji, ku ban waje da uwarku zan yi magana."
Jin haka Afrah da Kausar wacce jikinta ya yi sanyi suka miƙe suka wuce ɗaki. A bakinsu Benazir dake ɗakin ta ji batun zuwan Innar, za ta miƙe ta fita domin gaida ta ne Afrah ta dakatar da ita ta hanyar sanar mata abinda Innar ta ce. Haka ta koma ta zauna don dama kawai tunane-tunanenta take na yadda Mustafa mijinta ya fice a sha'aninta, a wani raɗe-raɗin ma ta ji kamar neman aure yake.
A falo Inna ta dubi Mami dake kokarin zuba mata ruwan roba a kofi tace.
"Salma bar ruwan nan ki saurare ni."
Mami ta ajiye ruwan ta bada hankalinta ga Inna.
"Akan wane dalilin ne za ki tursasa yaro auren wacce ba ya so? Ko shi mijin naki ne ya mara maki baya dangane da hakan? Haka aka yi masa? Inace ƴar uwarsa Zayha na so aura masa tun farko amma ya ce ke yake so na kuma yarje masa auren naki? Shi ne don rashin sanin meke maki ciwo za ki yi kokarin cutar da rayuwar ɗanki?"
Mami kanta ya ƙulle, yanzu ta gama fahimtar wanda ke mata wannan iskancin da neman tayar mata ƙura, Hajja Zayha ce. Matar nan ba za ta bar shiga sabgarta ba ashe? Ranta ya ɓaci sai dai ta kai zuciyarta nesa ta gama sauraron faɗan Inna kafin ta soma magana a sanyaye.
"Ki yi haƙuri Inna, ba zan so na yi abin da ranku ba ya so ba. Dangane da Kausar kuwa, ban yi wa yaron nan dole ba. Da kansa ya amince ya ce yana so ya aure ta. Areef ba yaro ba ne da zan mishi dole, tun tashinsa kin san halayensa, ba ya kallon abin da ba ya so ballantana a kai ga amincewa da shi. Ki tambaye shi ki ji, na tabbatar zai fadamaki gaskiya."
"Gaskiya? Gaskiya fa kika ce Salma, yaron da kika gama zarewa idanun ne zai samu bakin faɗa min wata gaskiya? Kin riga da kin masa barazana da tsinuwarki? Shi kuwa wane ɗan neman rashin albarka ne da zai ƙi aminta da zaɓinki Salma? To ba zai yiwu ba. Ke babu inda zan tafi zan jira har ya dawo duk ku same ni a sashin mijin naku zuwa anjima."
Tana kaiwa nan ta miƙe ba ta ko sha ruwa ba ta fice. Mami ta bi bayanta da kallo, ranta a ɓace sosai. Hajja ba za ta taɓa sanin cewa ta girma ba wai? Ita koyaushe burinta ta haɗa gurmi kuma ta kwantar da kai kamar ba ita ba?
Daga haka Mami ta yi ƙwafa, waya ta ɗauka ta shiga neman layin Areef sai dai ba ya shiga. Dole ta haƙura ta bar komai din itama har ya dawo a je gaban Innar tunda Allah ne shaidarta ba tursasa shi din ta yi akan auren Kausar ba.
***
Areef bai ma san wainar da ake toyawa ba don suna tare da Fareed ya yi mishi rakiya wajen wani ɗaurin aure na ɓangaren surukansa. Daga nan kuma suka ɗan zagaya yawonsu yana mai jin ransa wasai haka ya shigo gidan dab da da kiraye-kirayen Magriba. Bai kuma shiga ko'ina ba sai ɓangarensa bayan sun gaisa da masu gadi. A gaggauce ya yi alwala ya gabatar da fita zuwa masallaci. Bai haɗu da Abba ba don yana sahun gaba. Koda ya koma da zummar ɗan miƙewa zuwa sadda za'a yi isha'i ya shiga ɓangaren Mami, ƙarar wayarsa ya katse hanzarinsa, amsawa ya yi ganin Abban ne, sun gaisa yace ya ga motarsa, maza ya zo ɓangarensa tun ɗazu Inna ke zaman jiransa. Ya amsa da toh. Tunani yake a kan dalilin wannan kira na gaggawar, ya fi buƙatar ya kwanta domin ya ƙara samun damar tunani mai kyau ta hanyar da zai ɓullowa lamarin aurensa da Sameera. Ga saƙonta da ya samu a safiyar ranar cewa kada ya sake ya faɗi ainahin sunanta ga iyayensa, ta fi buƙatar ya faɗi sunanta na gaskiya wai Laila. Iya nazarinsa ya kasa gane haɗin sunayen biyu, wato Sameera da Laila da har za'a ce Sameera zai zama nickname din Laila. Ya ba ransa cewar ƙila Laila din sunan wata uwa ce a garesu yasa ake kiranta da Sameera.
Ya miƙe ya cire kayan jikinsa, wanka zai so ace ya yi amma kuma ba ya son tsallake umarnin Abban don haka kawai ya zura doguwar jallabiyarsa maroon mai adon golden a wuya da ƙarshen hannun ya fito.
Da sallama ya shiga falon Abban, yana zaune tare da Anti Amarya sai ko Hajja da Inna. Kusan tare ya shiga falon da Maminsa, daga yanayin fuskarta ya san cewa akwai matsala. Ya gaishe ta, ta amsa ba tare da ta kalle shi ba. Koda suka ƙarasa ciki sosai suka zauna, nan ya gaida iyayen nasa. Duk suka amsa.
"Ina ka shiga ne yau?" Cewar Abba.
Ya ɗan shafa kai.
"Na je wata ƴar unguwa tare da Fareed. I'm so sorry My Granny, na bar ki kina ta jira."
Ya ƙarashe da maida akalar zancen ga Inna. Da murmushi a saman fuskarta cike da kulawa da ƙauna ta amsa.
"Kar ka damu Arifullah, zaman ai don kai na yi shi. Batun aurenka ne."
Jin haka ya ɗan ɗago ya dube ta sai kuma ya yi ƙasa da kai. Inna ta cigaba da magana.
"Ka faɗa min gaskiya, akwai wacce kake son aure ne yanzu? Wacce a ranka ka ji ta kwanta maka?"
Babu wacce zuciyarsa ta kawomasa face Sameera, shirunsa ya sa Inna ƙara maimaita tambayar gami da cewa,
"Kar ka ji ɗarr, duk wacce kake so Arifu na maka alƙawarin ita za ka aura. Ba zan lamunce a yi maka dole ba. Idan ma tarihin take so ya maimaita kansa, to zai maimaita amma lallai sai ka auri zaɓinka. Akwai wacce ku ka daidaita yanzu haka?"
Areef ya gane inda Innar ta dosa, bai yi karambanin duban inda Maminsa take ba gudun jawo mata wani abin maganar.
'Damarka ce fa, kar ka bari a tashi a yau ba ka gabatar musu da Sameera ba.'
Wani ɓangare na zuciyarsa ya yi mishi tuni. Don haka ya bude baki ya ce,
"Akwai wacce muka daidaita. Sai dai ina roƙon alfarmar kada a hana ni aurenta, na yi alƙawarin zan auri Kausar itama."
Mami ta dubi Areef, me yaron ke son jawomata? Wace irin magana ce wannan? So ta yi ta tambaye shi, meyasa ya ɓoyemata cewa yana da wacce yake so duk da tarin tambayoyin da ta yi masa har da damarmakin da ta ba shi kafin ta haɗa sa da Kausar, sai dai kuskure ne babba waninsu ya ce uffan ma idan Inna na magana. Don haka ta ja bakinta ta yi shiru, a ɓangaren Hajja kuwa, ji ta yi kamar ta daka tsalle tsabar farin ciki.
"Masha Allahu, Alhamdulillah. Babu damuwa Areef, ka faɗi wace ce ita. Ai na faɗamaka yanda kake so hakan ne zai kasance. Idan ma huɗu ne a lokaci guda ka san muna da kuɗin da zamu auramaka su." Cewar Inna ta ƙarashe da ƴar dariyar da Abba da Hajja har ma da Anti Amarya suka taya ta idan ka cire Mami wacce ba ka gane yanayin da ke saman fuskarta. Hajja na satar kallonta zuciyarnan wasai.
"Laila, sunanta Laila."
Ɗiff, Hajja ta ɗauke wuta. Laila kuma? Wane irin zance ne haka marar daɗin ji? Laila? Ba Sameera ba?
"Laila sunanta?" Faɗin Hajja cike da jin wani irin hargitsi, gaba daya ta shiga ruɗanin da ba ta san ma ta jefo tambayar ba.
"Eh." Areef ya amsa ba tare da ya dubi Hajjar ba.
"A wane gari take?" Tambayar da Abba ya yi kenan.
"Kano."
Inna da Abba suka jinjina kai. Hajja kuwa dai ba ta gama dawowa daidai ba, ta bar zancen da zummar za ta kira Sameera ta ji ko shirinta ne hakan.
Nan dai Inna ta yi na'am ta kuma ba da umarni ga Abba akan lallai idan Baba Dakta ya isa zuwa bayan sallah a tura tambaya gidansu.
"Ku je da shirinku, don na ga yanzu zai wahala a je tambaya a dawo hannu wayam! Akan je ne a yi mai gaba ɗaya. To idan har sun aminta, kar a jira komai."
Abba ya yi dariya.
"Shikenan Innarmu, yanda kika ce hakan za'a yi in sha Allah. Batun ita Kausar fa?"
Abba ya tambaya yana duban Areef, a sanyaye Areef ya ce.
"Dama na amince zan aure ta Abba."
Har ajiyar zuciya Mami ta saki, ko babu komai bai watsamata ƙasa a ido ba. Sai dai dole ya amsa mata tambayoyinta. Nan aka tsaida magana cewa itama Kausar din, Abba zai kira ya yi magana da magabatanta zuwa bayan sallah a nema mishi aurenta. Da haka kiran sallar isha'i ya tashe su.
***
Hajja na zuwa sashinta ta dannawa Laila kira. Koda ta ɗaga dannar zuciyarta ta yi ta amsa sallamar Lailar.
"Sameera, kun yi da Areef ya sauya sunanki ne zuwa Laila?"
"Yes, Laila ne ainahin sunana Hajja. Sameera nickname ne saboda sunan kakata wacce ta haifi ubana na ci."
Ajiyar zuciya mai karfi Hajja ta sauke da har Laila ta ce
"Lafiya?"
Ta yi ƴar dariya cikin jin daɗin abin da ya faru din ta ce.
"Alhamdulillah, farko na yi zaton wata ce Areef ya gabatar gabanmu zai aura, ashe ke din ce. Nasan za ki komai daga bakinsa. Mun tsallake wannan siraɗin."
Shiru Laila ta ɗan yi sannan ta amsa da mata da ok. Daga haka suka ajiye wayar.
***
Ita kuwa Mami koda Areef ya shiga wurinta bayan sallar Magriba ɗakinta ta ja shi.
"Wace ce Laila? Meyasa ka min ƙarya?"
Tambayarta ta ƙarshe ta tashi hankalin Areef, ya dube ta da sanyin jiki ya ce.
"Haba Mami, ta ya ya zan maki ƙarya?"
Ta kauda nata idanun a kansa, ta sani ba halinsa ba ne ƙaryar, amma kuma yau da gobe ai babu abin da ba ya sauyawa, ba'a shaidar ɗan yau ma.
"Ka yimin ƙaryar babu wacce kake soyayya da ita. Areef da na zaɓa maka Kausar tilasta maka na yi kan sai ka amince da aurenta?"
"A'a."
Ta ma rasa me za ta ce don haka ta yi ƙwafa.
"Shikenan, yanzu tun yaushe kake tare da ita Laila din?"
"Mun ɗan jima tare sai dai a farko na bar ta saboda mun ɗan samu saɓani, haka kuma akwai wanda ya nemi aurenta a danginsu sai dai Allah bai nufa auren zai yiwu ba. Dalili kenan da yasa ban kawo zancenta ba sai yanzu. Ina neman afuwa."
Mami ta girgiza kai.
"Shikenan, ka dage da neman zaɓin Allah daga yanzu har zuwa lokacin da aka ce za'a je neman auren. Allah ya zaɓamaka abinda ya fi alkhairi. Kana iya tafiya, zan sa a kawomaka abinci."
Areef ya dube ta, bai gamsu da cewar ta haƙura ba amma haka nan ya amsa da toh. Mami ta bi shi da kallo bayan fitarsa, ji ta yi karon farko ta tsani yarinyar mai suna Laila. Areef bai taɓa yi mata ƙarya ba, amma yau ya mata. Ta kasa aamincewa da zancensa. Ba ta son auren ta dai tabbatar an fi ƙarfinta ne kawai.
***
Abba ya ajiye wayar da ya gama amsawa ya dubi Anti Amarya wacce girkinta ne a daren.
"Ikon Allah, kin ji wai Alh Affan zai zo babbar sallah a garin nan tare da iyalinsa?"
Anti Amarya ta jinjina kai.
"Tirƙashi! Idan ya zo kuma ya ji batun auren Areef da har mata biyu babu ɗiyarsa Nihla fa? Me za ka ce masa?"
Nan da nan yanayin fuskar Abba ta sauya yana duban Anti Amarya ba tare da yace uffan ba, itama ta ja bakinta kawai ta yi shiru.
***
KANO