KUNCIN ZUCI

Kuncin zuci

by @bintuuu

A wannan yanayin ne har lokacin Exams dinsu Na'ima yazo, da kyar Nafisa ta shawo kanta tafara yin karatun, sai ta bata shawaran ta daina yawan zaman gidan, zata rinqa zuwa daukan ta suje makaranta karatu..
Nafisa tayi qoqari sosai wajen ganin Na'ima ta danyi karatu, har yawo tana dan fita da ita in sun fita daga school din dan Na'iman ta warware, kuma Alhamdulillah tasamu tayi exams din da dan nutsuwanta, zuwa sannan Na'ima ta daina yawan fadawa Nafisa abunda Bilal din ke mata she just leave everything as it is sai addu'a..da taje can gidan gaishe dasu Alhaji bata ga alaman yasan taje Adamawa ba dan normal suka gaisa har yana tambayanta school da lafiyan gidan aurenta, which means Hajiya ta boye masa abunda ya faru har sannan.

Ta wayi gari wani ranan Saturday Nafisa ta kirata akan bata da lafiya itama, bata iddasa yin wayar ba Bilal ya shigo dakin sai tayi saurin kashewa, yana tsaye yace "Da wa kike waya" cikin sanyin murya tace "Nafisa" zama yayi bakin gadon fuskansa a dinke yace "I don't like that girl, kar in sake jin kina waya da ita in ba haka ba ranki zai baci" dan juya kanta tayi gefe ta gyada kai sai ya kai hannu ya matse fuskan nata ya juyo da ita tana kallonsa yace "Look at me when I'm talking to you Na'ima" sai tayi saurin gyada kai, kallonta ya tsaya yi da alamun bacin rai a fuskanshi sai tayi saurin bude baki tace "Toh, bazan sake ba kayi hakuri" sai sannan ya sake fukan nata bayan ya miqe sai ya dan duqo yayi kissing kanta, rufe Ido Na'ima tayi har ya fita daga dakin tanajin qofofin tsanarsa na sake buduwa a cikin zuciyarta..Bata bar gidan ba saida ta ji fitan motansa sannan ta shirya cikin light brown abaya da side back dinta ta fice daga gidan, har qofar gidansu Nafisan aka kaita, bayan ta gaisa da megadin ta shiga gidan kanta a qasa ta nufi entrance din gidan ko lura batayi da wanda ke can tsaye a parking space din gidan ba, barin danna wayar tashi Ahmad yayi, ya bita da kallo tana tafiya cikin sanyi har ta shige cikin gidan, shiganta falon ta kusa cin karo da Faruk da yake shirin fita shima, sai yayi baya yace "Sannu Na'ima" itama baya tayi ta gaishesa ya amsa tareda cewa "Ya maigidan naki" ta amsa da "Lafiya" sannan ta bashi guri ya fice daga falon, Mami ta samu zaune a falon tace "Oyoyo Na'ima, shiru kwana biyu bamu ganki ba" tana murmushi ta qarasa sai ga Nafisa ta sauqo daga sama tace "Bobo kinzo" Mami ta juya gurin Nafisan tace "Yauwa zo gashi yi sauri ki kai masa wannan, yana can parking space, kice saqon Mammah ne" da saurin ta amshi ledan da Mamin ke miqa mata tace "Wai har ya tafi?" Mami tace "Yi sauri da Allah kar ya tafin" cikin sauri ta bar falon tana cewa "Ina zuwa Na'ima" gyada kai Na'ima tayi ta zauna a kujera, dan kallonta Mami ta tsayayi bayan sun gaisa sai tace "Na'ima me yake damunki kika rame haka?" tayi murmushi tace "Babu komai Mami" sai Mamin tace "Ko exams din da kukayi ne, kinacin abinci dai ko" nan ma ta gyada kai bata bar murmushin ba, basu dade nan zaune ba Nafisan ta dawo, bayan sun dan taba hira tareda Mami sai suka tafi dakin Nafisan dake upstairs, sai da suka shiga Na'ima tace "Kika ce bakida lafiya kuma sai na ganki garau" dan dariya Nafisa tayi tace "So nake kizo muyi hira karki zauna shiru" murmushi kawai Na'ima tayi suka zauna nan kan gadon Nafisa takawo mata abubuwan ciye ciye.. sai yamma ta koma gida dan tasan Bilal ba wunin gida yake ba, sai da ta dafa masa abinci ta ajiye anan dining area sannan ta tafi dakinta, a wannan daren sai Bilal yace takai masa tea dakinsa, nan kan gadonsa ya ritsata duk a tsammaninsa ko dakinta ne yake sashi ciwon kan, amma duk fitinarsa abu yaci tura, miqewa yayi tsaye yana shafa fuskarsa bai bar kai komon da ya keyi a dakin ba cikin tsawa yace "Damn you Na'ima" baiwar Allah tana kwance akan gadon duk ta galabaita gashinta yayi daddaya akan pillow tana hawaye, fusgota yayi yace "Are you even a woman?" sai ta rufe idonta tana jiran ya mareta amma beyi hakan ba, tsayawa kallonta yayi sai ya hankadata ta fada gadon cikin bacin rai yace "Dauki kayanki ki fitamin daga daki, you witch" cikin sanyin jiki ta tsince kayanta da yayi daddaya dasu anan tsakar dakin ta fice da bedsheet a lullube jikinta, bin bayanta yayi da kallo zuciyarsa na qunaa...
Washegari kulleta yayi a gidan, hakan kuma bai tada mata hankali ba ta cigaba activities dinta a gidan, ashe dai tafiya Bilal yayi dan sai da Na'ima tayi sati biyu cikin gidannan bai dawo ba, da ya dawo ma bai kulata ba, haka ya rinqa kulleta a gidan kullum in zai fita, ranar da Nafisa tazo gidan sai Na'ima ta leqo ta window takira sunanta Nafisa tadan hade gira alamun confusion tace "ki budemin mana" hawaye Na'ima taji yazo idonta tace "ya kulleni Nafisa" ran Nafisa inyayi dubu ya baci ranar, sai ranar Na'ima ta fada mata kulletan da yayi shekarun baya, zama Nafisa tayi anan varenda'n taqi tafiya, sai da Na'ima tayita roqonta sannan ta tafi...Dare sai ga Bilal din ya dawo a bugensa abun mamaki sai bai kulata ba har sannan, washegari tayi masa breakfast tana serving dinsa yana nan zaune a dining chair din yana sipping tea kawai aka fara banging kofa da karfi, da sauri Na'ima ta ajiye serving spoon din hannunta ta nufi kofan ta bude Bilal na kallonta..Nafisa ce ta shigo ranta a bace ta dan ture Na'iman sannan ta qarasa cikin falon tana kallon Bilal fuskarta bayyane da bacin rai, Na'ima tayi saurin kamo hannunta tace "Nafee muje sama" sai ta fincike hannunta ta qarasa gurin Bilal dake sipping tea yana kallonta har sannan , cikin daga murya tace "Anya kai musulmi ne Bilal, bayan dukan har kulle ta kakeyi kamar akuyar ka, wai kai wane irin dabba ne nikam" ajiye cup din yayi yana kallonta with shock, ganin haka Na'ima tayi sauri shiga gaban Nafisa tace "Nafisa ki tafi dan Allah" sai Bilal yace "No barta ta gama then I'll show her waye dabban nida ita" cikin hargagi Nafisa tace "Wooohh..Lallai Bilal da kasan ba kowacce mace ake tabawa akwana lafiya ba" miqewa yayi, ganin haka cikin sauri Na'ima ta tunkuda ta zuwa kofan fita tace "Get out Nafisa" ran Nafisa a bace tace "Ki barshi ya tabani yagani in beyi kwanan cell ba wallahi ban cika yar Wadzani baaa" tsayawa kallon Nafisan yayi, ta cigaba da magana rai a bace "Wawa mai gwada qarfinshi akan mace, kai har wani jan wuya ka dauki kanka" Na'ima tayi mata tsawa "Enough Nafisa, ki fita daga gidan nan, meye hakan kikeyi?" Nafisa na kallonta tace "Na'ima ni zaki kora daga gidan ki akan Bilal?" ranta a bace ta amsa da "Ki tafi banaso" hawaye Nafisa ta fara sai ta juya ta fice daga gidan..juyawa tayi zata qarasa gurin Bilal kawai ya dauki mug din tea ya wurgo mata ya bugeta a kafada tayi saurin kai hannu gurin, rai a bace yace "So you're going around telling people I'm a monster" kuka ta fara tana girgiza kai, yace "Zan nuna miki ni monster'n ne Na'ima" ya qarasa maganan tareda nufota...

Sai da tayi sati tana kiran Nafisa wayan baya tafiya duk hankalin ta ya tashi da hakan gashi violence din Bilal na kullum daban, abun sai ya hadewa Na'ima har ya zamto bata cin abinci akai akai, tana cikin wannan halin ne wani taro ya tashi a school din nasu na wa'inda suka gama, burin Na'ima a wannan lokacin ta gamu da Nafisan su shirya dan ita kanta tasan bata kyauta ba, all that Nafisa did was out of love, tasani ranta ne ya baci har tayi abunda tayi, da suka hadu a wajen taron ne Na'ima tayi saurin nufan ta sai Nafisan ta dauke kai ta kai waya kunne, sanyi jikin Na'ima yayi sai ta nemi guri ta zauna tana kallonta jefi jefi, sai da aka tashi tayi sauri zuwa gurinta tareda riqo hannunta, rai a dan bace Nafisan tace "Ni ki sakeni, na rantse ko kasheki mahaukacin nan zeyi bazan sake cewa qala ba" Na'ima tace "Dan Allah kiyi hakuri wallahi nayi hakan ne dan ki tafi saboda nasan zai iya dukanki Nafisa" dan dariya Nafisa tayi tace "Bilal fa sai ranan na gane da hankalinsa, ba kowa yake duka ba wato, kinsan Allah bazai iya duka na ba, duk dama jikina rawa ya fara daga baya amma shima na hango shakku a idonsa" Na'ima tace "Nidai kiyi hakuri" sai tace "Kiyi hakuri kema, nasan ban kyauta ba amma wallahi raina ne ya baci dan ko Mami batasan na fita ba" dan murmushi Na'ima tayi, Nafisa ta cigaba "Kiyi hakuri Dan Allah, dan nasan ya dakeki bayan tafiya ta" shiru Na'ima tayi sai hakan ya tabbatar wa Nafisa hasashen ta, tace "Allah ya kawo miki sauqi cikin lamuranki Na'ima, Allah zai kawo qarshen Bilal a sannu, watarana komai zai wuce" sai Na'ima taji zuciyarta ta karye dan ita dai kullum tunaninta shine yaushe ne lokacin wucewan komai din zai zo, dan ta gaji....
Ba'a rufa kwana biyu da haka ba Stella ta dawo gidan, ranan da ta iso Na'ima kadai ta samu a gidan, sai da Na'ima ta tsorata da ganin kallon da take mata dan kusan bangajeta tayi a bakin kofar ta shiga ciki, ganin haka yasa Na'iman tabarta anan falon tayi saurin komawa dakinta ta saka key...sai bayan Isha Bilal ya dawo gidan a sannan stellan tana kwance a dakinsa, direct dakin Naima ya wuce sai yaji a kulle, ransa a bace yace "Uban meyasa zaki rufemin kofa" cikin sauri ta bude kofan yace "I need tea" ta amsa da Toh, da haka ya wuce nashi dakin Na'ima ta sauka zuwa kitchen din, bata dade da shiga ba ta jiyo ihun Stella daga dakinsa alamun duka Bilal din ke mata, dan fitowa tayi falon sai taji kamar ta fita compound saboda dan tsorata da tayi, tananan tsaye Stella ta sauqo falon, saurin matsawa gurin dining area Na'iman tayi sai taga ta nufi kitchen ta fito hannunta riqe da wuqa ta nufe ta gadan gadan, da qarfi Stellan ta nemi caka mata wuqan sai tayi qara ta riqo bakin wuqan da bare hands dinta, tura wuqan Stella tayi da dukan karfinta tana harin cikin Na'iman tace "Yau sai nayi ajalinki, wallahi sai na kasheki" duk yanda wuqan yake tsaga hannun Na'iman bata sake shi ba, Kiran Bilal ta rinqa yi da qarfi, aikuwa ya fito da saurinsa beyi wata wata ba ya saka kafa ya kwashe stellan anan falon, ji kake tim ta buga kanta da tiles, da gudu Na'ima ta nufi kitchen ta kulle kofa hannunta na zuban jini ba qaqqautawa, dankwalinta ta ciro a gigice ta kulle hannunta nata, daga nan tsaye cikin kitchen ta rinqa jiyo bala'in Stella tana qundumo duk zagin dayazo bakinta, da mamaki Na'ima ta Jiyo Bilal na fadin "Baby tayaya zan bari ki kasheta, I'm sorry na dakeki cikin fushi ne but I'm sorry" Stella na kuka tace "Wallahi sai ka rabu da yarinyar nan Bilal ko duk muyi mutuwan kasko" Na'ima na hawaye tajiyo Bilal yace "Ni banaso ki rinqa tada hankalinki akan yarinyar can, she's nothing to me, now let go to my room mugama maganan acan" Stella tace "Ni bazan zauna a gidan nan yarinyar nan tana nan ba" yace "It's alright muje duk inda kikeso to" da haka suka fice daga gidan Bilal bai bi takan Na'ima ba, bayan taji fitan motan nasu tayi sauri fitowa tana kuka ta nufi dakinta da gudu, hankali a tashe ta dauko wayanta ta kira Nafisa, tana dauka tace "Dan Allah kizo yanzu, zan mutu wallahi jinina zai qare Nafisa, ta yanka ni" ta dayan bangaren Nafisa ta miqe daga cin abincin da sukeyi itada Mami da Al'ameen sai duk suka tsaya kallonta, tace "Ina zuwa yanzu" da haka ta fara kokarin barin gurin Mami tace "Baby meya faru?" cikin tashin hankali tace "Na'ima ce Mami, cewa tayi inje yanzu" da confusion Mami tace "Me ya faru?" da gudu Nafisa ta nufi upstairs Al'ameen dake gurin ya bi bayanta tareda Mamin, da mayafin ta a hannu ta fito da gudu Mami ta riqeta tace "Ke ki nutsu ki fadamin me ya faru da Na'iman" tace "Nima yanzu zanje in gani" fita sukayi compound din tare Al'ameen ya karbi car key din hannun Nafisan ya shiga driver's seat, sai da suka tada motan Mami ta leqo kanta tace "Ki kirani in wani abun ya faru Nafisa, zan kira ma"....

Kuka sosai Na'ima takeyi har lokacin tananan zaune aqasa cikin dakin nata duk ta hada zufa, zuwa sannan dankwalin duk ya jiqe shima da jini, a haka ta Jiyo horn kamar tsayuwan motansu Nafisan, dakyar ta qarasa falo aikuwa aka turo kofan da sauri su Nafisan suka shigo, da gudunsu suka riqota Na'ima na kuka tace "Kasheni zatayi wallahi, Nafisa kukaini asibiti" da gudu Nafisan na kuka ta nufi dakin Na'iman dan dauko mata dankwali, dan gashinta ya ware gaba daya a firgice take, cikin tashin hankali Al'ameen yayi sake kamota yace "Innalillahi, muje mota Anty" yana riqe da ita suka tafi motan Nafisa ta biyo bayansu, nearby asibiti suka nufa da ita basu sha wahala ba aka karbi Na'ima suka wuce dakin dinki da ita, bayan angama har allura likitan ya mata, Al'ameen ne ya fita siyo magungunan da likitan ya rubuta, da likitan ya gama sai yayi ta mata fadan ta rinqa kula dan ce mishi sukayi langa langa ne ya yanke ta, bayan sun koma gidan, Nafisa tace da Al'ameen ya zauna nan falon zatakai Na'iman daki, gyada kai yayi tareda miqa musu ledan maganin yace "Allah ya qara sauqi Anty, Allah ya kiyaye na gaba" Na'ima ta gyada kai tareda da masa godiya suka wuce dakinta, sai da Nafisa ta kwantar da ita a gadon ta tsaya tana kallonta tace "Na'ima Ina addu'an Allah ya baki qwarin gwiwan barin wannan trapped rayuwan" shiru Na'ima tayi sai Nafisa ta nufi madubin dakin ta ja drawer ta dauko paper da biro, nan bakin gadon ta zauna tayi rubutu a takardan ta miqawa Na'ima, miqewa zaune Na'ima tayi ta karba sai ta ga address ne rubuce ajiki, Nafisa na hawaye tace "Zamu koma Abuja qarshen satin nan, aikin da yakawo Abba Kano ya kammala, wannan shine address din gidanmu na can, I'll be waiting for you har zuwa lokacin da zaki samu courage din barin wannan quntacciyar rayuwar Na'ima" fashewa da kuka Na'ima tayi tace "Nafisa ya zanyi, duk inda zanje sudin 'yan'uwana ne" itama tana kuka tace "Wallahi koda bahaushe yace hannunka baya rubewa ka yasar, saidai beyi tsutsa ba Na'ima, dole ka yanke, ai bazance ki bar 'yan'uwan ki ba inda cikin lumana kuke zaune, yau inkin mutu ba damuwar kowa bane cikinsu, why can't you see that ke da babu duk daya ne a wajensu" kasa magana Na'ima tayi har sannan tana kuka, ganin hakan yasa Nafisan miqewa ta fice daga dakin bata daina kukan ba itama..fita falon tayi tana goge idanun ta Al'ameen ya miqe yace "Ta samu baccin ne" Nafisa ta gyada kai tace "Eh mu tafi, Mami na ta kirana" da haka suka fice daga gidan har sannan Na'ima na zaune kan gado tana kuka mai tsuma zuciya....