AKWAI SILA

Chapter 21-22

by @amanarcool323

💦 AKWAI SILA 💦

BY AMANARCOOL

YOTA ID/021

SHIN RAMA CE MATSALARKI? BUSHEWAR JIKI KO KUMA MATSALAR SANYI? TO ALBISHIRINKI, NA ZO MUKU DA INGANTACCIYAR SABAYA DA AKA SARRAFATA DA NATURAL GRAINS, HERBS DA KUMA SPICES, WADDA ZA TA INGANTA LAFIYAR JIKINKU, TA CIKO DA JIKI, SAMAR DA RUWAN NONO GYARAN BREAST, TA KUMA YI MUKU MAGANIN SANYI DA MA SAURAN GYARAN JIKI NA MATA, DUK A KAN KUƊI ƘALILAN. SABAYARMU BA MA SANYA ƘWAYA A CIKINTA, DA TSIRRAI KAWAI MUKE SAMAR DA ITA. SANNAN AKWAI MAGANIN SANYI GA MASU FAMA DA MATSALAR INFECTION KOMAI DAƊEWARSA. AKWAI COMPLETE SET NA GYARAN BREAST, SPECIAL PACKAGE, KU NA IYA TUBTUƁA TA KAI TSAYE KU TUNTUƁE NI AYSHERCOOL TA LAMBOBIN WAYATA ***.

PAGE 21-22

Baki buɗe Momy ke kallon Dady, Dady kuma na kallon Joriyya dake ƙoƙarin kwanciya a ƙasa. "Shalele" ya faɗa da ƙarfi, fasa kwanciyar ta yi, ta ɗago da kanta ta kalle shi ta ce "Na'am Dady".
"Me kike ƙoƙarin yi ne?"

"Dady birgima zanyi irin yadda Anty Teema ke yi idan..."

"Shalele!" Ya daka mata tsawa "Ke daina wannan wasan ba na so, ka da na sake ganin kin kwatanta yin irin haka".

Shiru ta yi ta ɓata fuska kafin ta ce "To Dady addu'ar me za'a yi mini? Ko don in daina jin tausayin mutane ne? Dady kasan wani abu? Jin zafi nake idan na ga mutum yana wahala".

Sai a lokacin Momy ta yi magana "Auta wai ke bakinki ba zai taɓa yin shirun ba ne?". Joriyya ba ta ce ƙala ba, ta bar falon ta haura sama, tana shiga ɗaki ta kulle ƙofa, zama ta yi a gefen gadonta, hawaye na taruwa a idonta "Me ya sa mutane ba sa ganin abin da nake gani ne? Bana son ganin mutum a cikin damuwa". Ta faɗa tana duƙar da kanta tsakanin cibiyoyinta.

Bayan tafiyar Joriyya Momy ta kalle Dady ta ce "Oh ni Shafa'atu ina ganin abin da yafi ƙarfina, ji mini wata lukutar masifa da take ƙoƙarin gayyato ma kanta. Alhaji bori fa take wasan yi". Dady kasa magana ya yi yana jin yadda gabansa ke faɗuwa, wani irin tsoro da fargaba na shigarsa, ya miƙe a hankali ya nufi ɗakinsa zuciyarsa cike da tunani iri-iri.

Jiniyo ne kwance a ɗakin abokinsa, idonsa a rufe, wani tuƙuƙin baƙin ciki yake jin yana taso masa tun daga tafin ƙafarsa zuwa cikin ƙirjinsa, zuciyarsa na yi masa zafi mara misaltuwa, buɗe idonsa ya yi yana furzar da isaka mai zafi, ya kalle abokansa Salim da Yasir ya ce "Gayu wallahi ni ne zanyi ajalin wancan wawan mahaukacin, wai har ni Jory za ta ce wa banzan can yafi ni hankali? Ni? Ni Jiniyo? Impossible, sai na ƙara koya masa hankali, idan ma da sauran hankali a tattare da shi sai na yi sanadiyar da zai rasa shi gabaɗayaa. Zanyi masa abin da zai ƙara zama silar ɓarkewar haukarsa!" Ya ƙarasa maganar cikin ƙunar rai.

Salim ya ce "Jiniyo this is sad and frustrating for us, taya za'a yi mahaukaci ya riƙa baka matsala irin haka? This is embarrassing for us".

Yasir ya ce "I'm not happy about that, tabbas wannan abin kunya ne a gare mu, dole ne mu ɗauki matakin da ya dace akan wannan lamarin, kamar mu za a zo wa da wannan rainin hankali?".

Jiniyo ya dube su da idanunsa da suka canza launi ya ce "Me ya kamata muyi masa wanda zai sa jikinsa ya gaya masa?". Salim ya yi wuff ya ce "Kamata ya yi an jima da isha mu same shi muyi masa ɗan banzan dukan da sai ya kasa tashi, mu canza masa kamanni ta yadda idan ta gan shi ba za ta yi marmarin sake ganinsa ba".

Yasir ya ce "Good job Salim, that’s a suggestion this is how we should handle him." Cike da gamsuwa suka yi na'am da wannan shawarar.

Bayan sallar isha da ƙyar ya tashi daga cikin bolar ya koma kangon nan ya kwanta yana fitar da numfashin azabar da yake ji a hannunsa. Karensa ya fita, nesa da gurin suka yi parking ɗin motarsu, a hankali suka ƙarasu gurin cikin sanɗa, yana kwance sai gani ya yi an haske shi da fitar wayar dake hannunsu. Ya sa hannunsa mai lafiya yana kare fuskarsa. Jiniyo ya ƙarasa inda yake suna ci gaba da haske masa fuska da fitilar waya, duƙawa ya yi ya cusa masa wani abu mai raɗaɗi a cikin bakinsa, ya sa salatif ya liƙe masa baki. Shure-shure ya fara yi yana jin raɗaɗi da azaba na ratsa masa baki kamar ana yanka shi da reza. Cike da rashin imani Salim ya duƙa yana ɗauke sa da mari tare da matse hannunsa mai ciwon. Zabura ya yi ya fara ƙoƙarin tashi zaune, cikin ƙita da mugunta Jiniyo ya mayar da shi kwance yana ƙara matse hannun daya kumbura yana walƙiya. Mimmiƙewa ya fara yi yana kakari, Jiniyo ya ce "Ai baka ga komai ba tukuna, sai na yi ajalinka" Ya faɗa yana miƙewa tsaye, babu imani balle tausayi suka fara dukan shi da sandunan da suka zo da su, duk inda suka samu a jikinsa duka suke yi. Wani bugu da Jiniyo ya yi masa a ido sai da ya miƙe zaune da ƙarfi, da ƙafa Yasir ya mayar da shi kwance. Sai da suka tabbatar da sunyi masa duka ba na wasa ba, kafin suka ƙyale shi, Jiniyo ya fito da sabuwar reza a cikin aljihunsa, ya damƙi hannunsa mai ciwon ya yi masa yanka uku manya, sannan ya miƙe. Nan take numfashinsa ya ɗauke gabaɗaya, ganin ya daina numfashi ya sa suka fice gurin da gudu, motarsu suka shiga tare da janta da ƙarfi. Jiniyo ya lumshe idonsa yana jin zafin zuciyarsa na raguwa.

Bayan kamar minti goma da tafiyarsu Karensa ya dawo bakinsa ɗauke da ledar abinci, gabansa ya zo ya ajiye ledar, sai dai duk da duhun da ya mamaye gurin ya lura da rashin motsin sa, zagaye shi ya fara yi yana kuka. Sai dai shiru bai motsa ba, da ya gaji da kukan ya zo kusa da shi ya kwanta.

Hasken ranar da ya fara fitowa ne ya dake kumburariyar fuskarsa, a hankali ya fara motsa jikinsa da yake a kumbure, hannunsa mai ciwo ya ƙara kumbura ga busashen jinin da ya bushe ya ƙara mannewa da fatar gurin, idonsa ɗaya ya kumbura sosai. Ciwon da ke ratsa jikinsa ba zai iya bayyana shi da baki ba, ajiyar zuciya yake saukewa kaɗan, idanunsa suka fara buɗewa a hankali. Ji ya yi kamar ƙwayar idonsa ɗaya za fito tsabar azabar daya ji a gurin, ƙoƙarin motsa bakinsa yake son yi ya kasa saboda salatif ɗin dake manne a gurin, cikin azaba ya saka hannunsa mai lafiyar wanda shima ciwo yake masa a yanzu sakamakon dukan da a ka yi masa, cire salatif ɗin ya yi daga bakinsa yana zubar da yawo, abin da suka tura masa a baki tuni ya narke masa a ciki. Iska ya furzar mai zafi yana nishi da ƙyar, cikin ƙarfin hali da jarumta ya tashi zaune yana jingina jikinsa da ruɓaɓɓen ginin dake gurin. Kallon hannunsa ya yi yaga yadda hannun ya ƙara hawa, ga yanka a cikinsa, ya runtse idonsa hawaye masu zafi na zuba a gefen fuskarsa. Dubawa ya yi baiga karensa ba, ya miƙe da ƙyar yana tangaɗi, fuskarsa a kumbure ya fita waje yana jan ƙafarsa dake yi masa ciwo sosai, bakin bolar nan ya je ya zauna ya tsurawa hanyar da motar su Joriyya ke biyo wa.

Misalin ƙarfe tara Dady ya je har gida ya samu Malam Nura. A ƙofar gida ya same shi zaune yana karatun da ya saba a nutse, cikin tsafta da kamala. Dady ya fito daga motar shi ya nufe shi. Malam Nura ya saki fuska ganin Dady, da sallama ya isa gurin, Malam Nura ya amsa yana miƙa masa hannu suka yi musabaha suna gaisawa cikin mutunci, Dady ya zauna akan tabarmar dake shimfiɗe a gurin.

Malam Nura ya ce "Alhaji yau kai ne da kanka a ƙofar gidana?".

Dady ya dubi shi cikin yanayi na damuwa ya ce "Na zo ne akan batun yarinyata ne, kwana biyu bamu gane ma kanta, shi ne muke tunanin ko akwai matsalar shafuwar aljanu a tare da ita, akwai wani mahaukaci da tunda ta fara ganinsa gabaɗaya ta rikice, da farko mun ɗauka tausayinsa ne take ji, daga baya sai muka ga abin ya fara wuce gona da iri. Shi ne nake son ka taimaka mana da addu'a. Saboda ina zargin mahaukacin nan kamar ba mutum bane aljani ne, kullum bata da batu sai na shi, gabaɗaya ta bi ta susuce akan shi".

Malam Nura ya jinjina kai ya ce "Babu damuwa in sha Allah zamu yi abin da ya kamata, gidan zan je ko kuma nan za ka zo da ita?".

Dady ya ce "Idan babu damuwa ina son mu je yanzu, idan kuma kana da wani uzuri ne sai mu bari zuwa anjima da yamma sai na aiko a ɗauke ka" 

Malam Nura ya ce "A'a muje yanzu, anjima da yamma akwai in da zani". Dady ya yi murna sosai da hakan, Malam Nura ya naɗe tabarma ya kai cikin gida sannan ya fito, mota suka shiga direba ya ja motar suka wuce. A rantsatstsen falon saukar baƙin Dady aka sauke Malam Nura, nan aka kawo masa lemu da ruwa. Dady ya wuce ciki, bai ɗauki lokaci ba ya dawo falon hannunsa riƙe dana Joriyya. Da sallama ya shigo, Malam ya ɗan bi ta da kallo yana nazartarta. Risinawa ta yi cikin sanyin murya ta gaida Malam, ya amsa mata cikin sakin fuska, Dady ya dubi shi cikin yanayin damuwa ya ce 

"Gata nan Malam, lokaci ɗaya muka kasa gane ma kanta, gabaɗaya ta birkice, don Allah a ɗan duba mana ita ko da wata matsalar" Malam Nura ya jinjina kai sannan ya fara yi mata karatu tare da karanta addu'oi. Ya ɗauki dogon lokaci yana karatun, ita dai Joriyya kanta a ƙasa tana sauraren ikon Allah, zuwa can Malam Nura ya kalle ta na ɗan lokaci kafin ya girgiza kai ya dubi Dady ya ce "Alhaji yarinyar nan bata da komai, babu wani shafar aljanu da yake damunta, wataƙila ta sakawa ranta tsananin tausayin shi ne shi ya sa take yin haka, sai dai akwai al'amari mai girma a tare da wannan ƴar taka wanda na kasa fahimtar ko mene ne, amma in sha Allah nan kusa ko mene ne zai fara bayyana".

Dady ya girgiza kai cike da damuwa yana dafe kai ya ce "To yanzu babu wani taimakon da za ka iya bamu ne? Saboda tana yawan ambaton shi, tana yawan magana akan shi, tun hakalinmu baya tashi har abun ya fara ɗaga mana hankali. Sai ta riƙa ce mana wai shi ba mahaukaci bane, ta san shi, mantawa aka yi da shi, sannan kuma tana yawan ɗaga hankalinta akan shi, dalilin haka ya sa muke zargin ba mutum bane aljani ne yake zuwar mata a suffar mutane".

Malam Nura ya girgiza kai ya ce "Gaskiya ba aljani bane, tabbas mutum ne, kawai dai akwai wani al'amari mai girma tsakanin wannan bawan Allah da Joriyya, amma na kasa fahimtar komai, kuma ina son ku kwantar da hankalinku, ku sani lafiyar ƴarku ƙalau, sai dai akwai wani abu da yake fizgarta zuwa gare shi".

Joriyya ta kyaɓe fuska tana ƙoƙarin yin kuka ta ce "Yawwa Malam gaya musu dai ba aljani ba ne mutum ne kamar kowa, kuma ba mahaukaci ba ne mantawa aka yi da shi".

"Ka ji ko Malam, kaga irin wannan surutun ne bana son tana yi" Dady ya faɗa yana nuna Joriyya. Malam Nura ya ce "Yi haƙuri Alhaji in sha Allah za ta daina, idan na koma gida zanyi mata wani rubutu sai ka aiko a karɓa mata" Dady ya jinjina kai yana yi masa godiya, sannan ya yi masa alkhairi, bai so karɓa ya tilasta masa ya karɓa dole. Suka fito harabar gidan Dady ya sa a mayar da shi gida. Sannan ya kama hannun Joriyya suka koma ciki, suna shiga falon ta zame hannunta daga na Dady ta dafe ƙirjinta, Dady ya ce "Shalele lafiya dai?".

"Dady"

"Na'am Shalelena"

"Mu je mu duba shi, bashi da lafiya, Dady yunwa yake ji bai ci abinci ba!".

"Yi mini shiru babu in da za muje, kuma kika sake zancensa sai na kai gurin Na'ima in nisanta ki da ƙasar nan kowa ma ya huta" yana gama faɗar haka ya wuce da sauri ya bar ta a gurin. Yana ƙoƙarin haurawa sama ne ya ji ƙarar faɗuwar abu, juyowar da zai yi yaga Joriyya zube a ƙasa numfashinta na fita da sauri. 


Amanarcool
***