The beginning of my destiny
by @zmchubado
*RA'AYIN ZUCI...*
Marubuciya: ZMChubaɗo
*warning ⚠ this is my book and the copyright is mine alone. So Please don't change it for me in any way without my permission don girman Allah🙏*
بسم الله الرحمن الرحيم
CHAPTER: 1
Kaduna State 1:00pm
Juyawar da kaina keyi ya sa na fara ƙoƙarin Jan ƙafafuna waƴanda ke barazanar sagewa a lokacin da na tsinkayi furucin Yusuf Attahiru. firgici da tsoro mai tsanani ne su kai min dirar mikiya, cikin gajeran lokaci naji Zuciyata ta na barazanar tsinkewa.
Da ƙyar nake iya jan numfashi, cikin ƙarfin halin da ya yi mini saura na fara ƙoƙari gaiyato jarumtar da na rasa tun lokacin da na tsaya a bakin ƙofar ofishin Doctor Umar, Nadama da tarin da na sani ne suka dabaibayeni, cikin gajeran lokaci suka kashe tasirin duk wata jijiyar jini dake kai saƙo cikin curin ƙwaƙwalwar dake ɓoye a cikin kaina.
"Innanillahiwainna'ilaihiraji'un"
Na furta a cikin wani gajiyayyen sauti wanda ya yi dai-dai da sakowar hawayen da ke maƙale a tsakiyar idanuna, a haka na bar Asibitin ina kukan zuci da na fili wanda nake ji a raina ba ni da ranar dainawa. "mai ya sa na gurɓata rayuwata da ƙazanta a shekarun da ya kamata ace naci ribar rayuwata?" wani ɓangare na zuciyata ya jefa mini wannan tambayar wadda naji saukarta a ƙirjina tamkar dirar harshashi.
Ƙwallar dake kwaranya a saman kuncina na saka hannu na shafe, ina jin yanda zuciyata ke dunƙulewa tamkar ubangiji bai ƙaddara mata motsawa ba,"Ashe dama halacci ya na rikiɗewa ya koma ƙiyayya?" na firta hakan da busassun laɓɓana, ina jin ciwo mai matiƙar zafi da raɗaɗi na ƙara yin yaɗo a cikin jikina. jin yanayin nake tamkar almara don ban taɓa zaton RA'AYIN ZUCIYAR mutun ya kan tilasta shi ƙin yin halacci ga wanda ya nuna masa ƙauna saboda Allah ba, sai a yau da Yusuf Attahiru ya jefeni da ƙaton dutsen yaudararsa ya daki zuciyata tareda wargaza mini duk wani lissafin rayuwata da na jima ina lisssafawa.Nayi zaton zai canza daga yanda yake a shekarun baya zuwa wani sabon Yusuf ɗin da zai zame mini sanyin idaniya, sannan ya tayani karɓar ƙaddarar da ta sameni, wadda ke ƙoƙarin dai-daita kanta da tsayin kafaɗuna. A she ba haka lamarin zai kasance ba kamar yanda na jima ina fatan kasance ba.
Haƙiƙa nayi kuskure da na yarda da shi a lokacin da bai kamata na miƙa masa ƴarda ta ba. Tabbas wani da na sanin baya ruskar mutum a lokacin da ya dace, har sai wankin Hula ya kai ka ga dare tukunna. A gareni ma hakace ta kasance a lokacin da tsumin gyaɗa ya juye ya zame mini Giya me tsananin wari da hamami, wanda mayen warinsa ya fara walagigi da rayuwata tamkar juyin waina akan tanda!
Shikenan nayi bankwana da farin cikin rayuwata. Fashewa nayi da kuka hannuna dafe da da ƙirjina, yayinda kunnuwana sukaci gaba da dawomin da kalaman da Yusuf ke firtawa akan Aisha Sulaiman ga abokinsa Doctor Umar. ina jin yanda ƙunci da baƙin ciki ke huda duk wata kafa da ke kai saƙon a tsakanin zuciya da gangar jikina. Lumshe idanuna nayi waƴanda suka jiƙe da ruwan hawaye, cikin sarewa na fita da ga cikin Asibitin gabaɗaya ina bin miƙaƙƙen titin da ya mamaye gurin da faɗinsa.
A wannan lokacin ruwan hawayen da ke kwaranya a fuskata ya yi ƙarancin da babu wadatar da zai tsawaita zuba, na jima a tsaye sannan na saka hannu na tare ɗan-adaidaita sahun dake shirin wucewa ta gabana.
A wahalce nake ɗaga ƙafafuna har na isa gareshi, sannan na daidaita muryarta wadda ke fita tareda sautin kuka na ce,"Malam Hayin Ɗan-mani za ka kaini."
Kallon tsaf mutunin ke bina da shi tun da ga yatsun ƙafafuna har kan fuskata. Sannan ya nisa ya ce,"ina fatan drop za ki ɗauka don bana ƙaunar shiga wannan unguwar da mutum ɗaya tal." yayi maganar yana ɗauke idanunsa daga kaina
Jan hanci nayi wanda ya ba wa sauran ruwan hawayen dake kwance a idona damar zubowa. Cikin azama na kai hannu na goge su muryata a dakushe na ce,"nawa zan baka drop ɗin?"
"Dubu biyu da ɗari biyar." ya faɗa yana tsareni da idanu don jin ta bakina. Ban ce da shi ƙala ba na shiga cikin Babur ɗin na zauna ina jin yadda kaina ke sarawa.
"Hajiya wani ɓangare zan kai ki a hayin ɗan-mani?"
"layin sarkin dillalai gida na farko daga ɓangaren dama." na faɗa ina kallon titi tareda motocin dake kai komo.
A haka yaja Babur ɗin muka kama hanya, har lokacin ban sauka daga dokin mamaki da baƙin cikin da furucin Yusuf Attahiru ya ɗorani akai ba. Duk yadda na so na daure kar na ƙara zubar da hawaye akan maganar abin gagarata ya yi, sai kawai na kifa kaina a tsakanin ƙafafuna naci gaba da rizgar kuka tamkar raina zai bar jikina. A haka muka iso ƙofar gidan still kuka nake ban daina ba har sai da mai adaidaitan ya juya ya kalleni ya ce,"Hajiya mun iso." sannan na ɗaga fuskata, wadda tai jazur saboda kukan dana jima inayi. na sauke idanuna akan ƙatuwar bishiyar darbejiya da taiwa ƙofar gidan Rumfa da Inuwarta.
Jakar da ke hannuna na buɗe na zaro dubu uku na miƙa masa, sannan na sauka ina ƙarewa ƙofar gidan kallo zuciyata na tsananta bugu. A hankali ƙuncin dake addabar zuciyata ya ke ƙara ninka kansa, Cikin sanyin jiki da na gaɓɓai na ja ƙafafuna ina takawa a hankali na isa jkin ƙofar gidan na tura. Gidane mai girma amma ba sosai ba sai dai yana da wadata irin fasalin ginin masu kuɗin da ɗinnan ne, ɗakuna huɗune ne a ciki sai baban falo da seatroom tareda babban tsakar gida da ɗakin girki. da ga can kusurwar hagu tukwanan ƙasane a jere an shuka furanni a ciki (flower). Babu kowa a tsakar gidan se Inno dake ƙoƙarin Juye Ruwan zafi a Flacks. Dai'daita nutsuwata nayi cikin muryar da ba ta fita sosai na ce,"Assalamu'alaikum."
Inno ta ɗaga kai ta kalleni tareda sakin kofin da ke hannunta a cikin tukunyar Ruwan zafin ta ƙura mini ido hankalin ta a tashe ta na karantar yanayina. A hanzarce ta fito daga ɗakin girkin ta kai hannunta ta shafi gefan fuskata ta ce,"subahanallah! Bilkisu mai ya sameki haka. Ko dai jikin ne ya motsa miki?" tayi maganar cikin tashin hankali.
Nadama ce ta sarƙafe zuciyata yayinda tausayin makomar rayuwata ya fara ƙoƙarin hilata ta, jin'jina kai nayi tareda kawar da idanuna daga kanta, don ba zan iya jurar irin kallon da take mini ba.
Lumshe idanu nayi sannan na ƙara buɗesu tar akan Inno wadda har lokacin ta gaza janye ganinta daga kan fuskata, wani irin kallo take min irin kallon dana jima banga irinsa a ƙwayar idon kowa ba sai Ya Zainab. Kallo ne mai cike da tarin ƙauna da tausayi irin na na gaskiya. cikin wani irin yanayi na yi kasa da kaina na ce,"Marata ce ke mini ciwo sosai, har ta kai inaji kamar za'a fizgeta daga jikina ta faɗi ƙasa saboda azabar ciwo haka nakeji" nayi maganar ƙwalla na sake tsatsafowa a idanuna, sai dai har cikin zuciyata banji daɗin ƙaryar da na zuga mata ba, sai dai bani da wani zaɓin da ya wuce yin ƙarya.
Inni ta yi mini abubuwa da yawa na alkhairi ba tareda ta duba girman dangantakar jinin da take tsakanin mu da ita ba, a kalla idan ban sanyata farin ciki ba to bai kamata in zama silar tada hankalinta akan matsalar gidan Aure na ba!
"Idan mararki ce ke ciwo ai bai kamata kiyi kukan da zai kumbura miki fuska irin wannan ba, kamata ya yi kije Asibiti ki nemawa kanki lafiya ko kuma kije kantin sayar da magunguna ki siya kisha." maganar Inno ta katse min gajeran tunanin da na afka, murmushin karfin hali na saki a Raina ina mamakin girman ƙaunar da baiwar Allan nan take mini. Haƙiƙa Ina matiƙar Ƙaunar INNO, ita yayar mahaifinace amma soyayyar da nake mata ba na iya haɗata da kowa a cikin dangina, saboda kasancewarta mai tsananin kirki da hidimtawa zumucin Allah. Inno ta na da wata kalar Golden heart wadda babu komai a cikinta sai tarin alkairi, mace ce mai tsayawa akan lamuran ƴan uwanta duk da cewa Ubangiji bai bata tarin dukiya ta fitar hankali ba.
Ta yi mini halacci a lokacin da na jima da yanke ƙaunar samun wanda zai goya min ba ya a soyayyata. Amma haka ta tsaya tsayin daka don ganin ta sama mini abinda nake buƙata daga iyayena, sai gashi tun ba'ayi nisan kiwo da wucewar yaƙin da ya gabata ba wani sabo yana ƙokarin ɓallewa!
Juyawa nayi saurin yi don ban shirya sauke nauyin da ke ƙirjina a kunnuwan Inno ba, wllh ba na buƙatar in zama silar wanzar da hawaye a kan fuskan macen da ta jefa farin ciki a saman fuskata. A ƙalla She deserve to be happy ko don darajar tarin alkhairan da ta yi mini a shekarun baya.
Mayafin abayar dake ƙoƙarin zamewa da ga kaina nasa hannu na gyara, ba tareda na kalleta ba na ce," Inno banga Hajar ba hala bata nan ne?" na jefa mata tambayar don in shashantar da tunaninta akan matsalata.
"Eh ba ta nan Sun tafi Lere bikin ƴar wan Babansu." cewar Inno.
Zaman Boron dake kafaɗata na gyara sannan na raɓa ta gefanta na wuce can cikin ɗakinta, don a wannan lokacin babu abinda nake buƙata kamar kaɗaici. Ina buƙatar keɓancewa daga ganin kowa, a ganina wannan shine zai sama min nutsuwar da na jima da rasawa a gangar jikina. A wahalce na kwanta a saman gadon dake ɗakin ina jin yanda zuciyata ke dunƙulewa a guri guda, sai a lokacin wasu zafafan hawaye suka fara zarya a saman kumatuna.
Nan take abubuwan da suka shuɗe a shekarun baya suka fara dawo min A lokacin da ban shiryawa hakan ba. Duniyar tunani wadda ba ta buƙatar shiri kafin ta hilaci mutum ta yi mini mamamayar bazata.
*** *** *** ***
*_14 January 2019_*
_Kafin Aurena da Yusuf Attahiru._
_A nitse ya yi parking a harabar gidan a cikin ɗaya daga cikin rumfunan ajiye motocin da aka ƙawatar harabar gidan da ita, ya jima a zaune cikin motar sannan ya fito fuskarsa a sake, sanye yake da farin yadin filtex wanda haskensa ya bawa farar singlet ɗinsa damar nuna kanta a fili, kansa babu hula, sai tarin sumar kansa mai sulɓi wadda ke fitar da natural ƙallinta ga duk wanda ya ɗora idaniyarsa akansa. Sosai yadin ya zauna a jikinsa tareda fallasa kyawun chocolate skin ɗinsa a fili ba tareda hijabi ba._
_Cikin nutsuwar da ta zame masa ɗabi'a ya nufi ƙofar da zata sadashi da cikin gidan, a zaune ya sameni ina gyara ganyen ogun da Mama za ta haɗawa Baffah miya da shi, tun kafin ya yi sallama mayataccen turarensa na Baccarat Rouge 540 Extrait ya kai ziyara hancina._
_Gabana ne ya yi wata irin faɗuwa, duk sanda yazo guri muddin ina zaune a gurin sai naji irin wannan yanayin a tareda ni, tamkar wadda aka ɗaurewa jijiyoyin jiki hakanan sai na kasa ɗaga kai na kalleshi tamkar wadda aka dasa a gurin haka nake ji a jikina._
_Ɗan murmushi ya yi tareda harɗe hannayensa a ƙirjinsa yana ƙare mini kallo, ya jina a haka sannan ya ce,"Assalamu'alaikum."_
_Wuƙar da ke hannuna na ƙara damƙewa ba tareda na kalleshi ba na miƙe na tattara ganyen da komai na shige kitchen ina maida numfashi. Da idanunsa ya yi mini rakiya har na ɓacewa ganinsa sannan ya wuce zuwa falo, a zaune ya samu Mama ta na karanta jaridar Daily trust, ganinsa ya sa ta wadata fuskarta da murmushi ta ce,"Lallai yau ina da babban baƙo kaine a gidan nan da yammacin nan?"
Murmushi ya yi sannan ya yi ƙasa da kai ya kasa cewa komai._
_Ganin haka ya sa mama cikin zolaya ta ƙara cewa,"Welcome, distinguished Engineer na san wannan zuwan na Baffa ne ba nawa ba, barin ns kira maka shi tunda ni kallon suruka kake mini." ta faɗi hakan tana ƙoƙarin miƙewa amma ya yi saurin dakatar da ita ya ce,"no Mama gurinki nazo, ina so ne muyi magana."_
_Shiru mama ta yi ta na karanyar yanayinsa sannan ta ajiye jaridar a gefanta ta ce,"ina jinka Engineer Lfy dai ko?"_
_Sai da ya sauke numfashi mai zurfi sannan ya ce,"It's about Bilkisu."
Jin ya ambaci sunana ne ya sa Mama ta ƙwala mini kira na shigo falon, na zauna a nesa da inda ta ke zaune nayi shiru bance komai ba._
_Ajiyar zuciya ya ƙara saukewa sannan ya fara magana cikin sanyin murya ya ce,"Don Allah ina so ki yima maganata kyakkyawar fahimta Mama, na san ke uwace mai jajircewa akan lamuran duk wani makusancinku. Wannan dalilin ya sa nazo da kaina ba tareda na shigo da tafinta a tsakanin mu ba, don Allah don darajar manzon rahama mama karki matsawa Bilkisu akan abinda ba ta da ra'ayi akansa. ke uwa ce na tabbata ba zakiso abinda zai samar da gurbin damuwa a zuciyar ɗiyar da kika haifa ba, idan da hali don Allah ki tayata karɓar zaɓin zuciyarta muddin zai zama silar yayewar baƙin cikinta. Tunda ta nuna cewa ba ta ra'ayin Aurena zai fi alheri a barta ta aurin wanda zuciyarta ta zaɓa, ina da kyakkyawan yaƙini cewa Yusuf Attahiru zai samar da farin ciki a a rayuwata da zuciyarta ma gabaɗaya. Irin farin cikin da mu kanmu a nan gaba zai saka mu alfahari." Yaya Abdulƙadir ya firta haka cikin tattausan sauti wanda ke cike da tarin girmamawa a gareta_
_Ajiyar Zuciya Mama ta sauke tareda furzar da wata zazzafar iska daga bakinta. A nitse ta ɗaga idanunta waƴanda ke ɓoye cikin farin gilashin ƙara ƙarfin gani ta ce,"ko ɗaya ba ja nake da zaɓin da tayiwa kanta ba Abdulƙadir. tunda ita ce za ta zauna da shi ai banga abin ja'inja a ciki ba sam, sai dai kamar yanda ka ce ni uwa ce, wannan matsayin nake ƙoƙarin riƙewa da duk wata power da ke tattare a cikin jimlar. Ba na so na ka sa playing role ɗin da ya dace a rayuwar Bilkisu,wannan ya sa nake ƙoƙarin nuna mata abinda ya kamata ace ta fahimta, amma ba komai tunda haka ƙaddarar rayuwarta ta zo dashi, ni ba zan ja da yin Allah ba tunda shine mafi sanin abinda ke ɓoye" ta faɗi hakan tana sauke dubanta akai na._
_Ɗan murmushi Yaya Khadir yayi har lokacin kansa ya na ƙasa ya ka sa ɗagowa ya kalleta, sai da ya numfasa sannan ya yi jarumta ya kalli Mama ya ce,"wani kuskuren iyaye ne ke fara samar da gurbinsa a rayuwar ƴaƴansu Mama. Furucinki har yanzu ya na nuna rashin goyon bayanki a taraiyar Bilkisu da Yusuf, don Allah karki zama irin uwar dake ɓoye ɓacin ranta a bayan kalamanta. Yin hakan zai iya jefa rayuwarta a cikin gararanba da walagigin rayuwa, wanda mu ba zamu so haka ba."_
_"ko ɗaya ban riƙe hakan a zuciyata ba Abdulƙadir, har cikin raina nake mata fatan alkhairi. Ka roƙeni in bata damar da ta rasa kuma na amince zanyi hakan meyasa kake kokwanto?_
_"Ba na kokwanto akan maganarki Mama. Amma yin hakan shine maslaha idan da halin don Allah ki bata damar ta, irin damar da ko wacce mace ke samu a ƙarƙashin inuwar Uwa. Bilkisu ita ma mace ce, a ƙalla ta na da ƴancin zaɓawa kanta abokin rayuwar da take ganin ya dace da ita. Mudɗin ta na da sanya ran zai riƙeta da amintacciyar soyayyah, wadda za ta isheta na iya tsahon rayuwarta."_
_Ɗa ga kaina nayi da sauri a lokacin da ya kai ƙarshen maganarsa, cikin sa'a idanuna ya faɗa cikin nasa. saurin janye idanunsa ya yi daga kaina zuciyarsa na wani irin harbawa._
_Shiru ne ya ratsa gurin na tsahon mintina uku, kowa da abinda ya ke saƙawa a cikin ɓoyayyiyar zuciyarsa sannan ya katse shirun ta hanyar cigaba da cewa,"kiyi haƙuri idan na firta kalmar da ta sosai miki rai a kalamaina" ya firta hakan cikin sanyin murya yana murza mukullin motar da ke tsakanin yatsun hannunsa_
_Tausayinsa ne ya cika zuciyar Mama,saboda ita sheda ce akan irin son da ya jima yana yimin tun kafin na zama mutum, don haka sai ta yi shiru ta kasa cewa komai na tsahon lokaci. Jin shirun ya yi yawa ne ya sa na ɗaga kai na kalleshi._
_a lokacin da kalmarsa ta ƙarshe ta samu gurbin dedaita kanta a kunnuwa na, sai dai ko da wasa banyi gigin neman ƙwayar idonsa a wannan lokacin ba, saboda na san hakan ba zai taɓa za me mini alkairi ba._
_Yau ɗaya! ADULƘADIR ALIYU LERE ya taka mahimmiyar rawa a rayuwata don ganin ya sama mini damar da na jima da cire ran samunta a gurin mahaifiyata. wannan ƙokarin da ya yi min ya isa ya baiyana girman mahimmancin da nake dashi a cikin rayuwarsa, na tabbata ya yi duk abinda ya yi ne don ya samar da Farin ciki a birnin zuciyata kamar yanda na jima ina fatan samu._
_yanzu kam na fahimci dalilin zuwansa gidan mu. Haƙiƙa duk yanda nake tunanin yaya Khadir ya wuce zato da tsammani na, tunda ga shi duk tsaurin da Mama take da shi akan al'amuran rayuwata cikin ɗan ƙaramin lokaci ya yi nasarar sauyata._
_wannan alfarmar da na samu ta silar sa ita ce ta zama silar siya masa babban matsayi a idanuna, albarkacin haka ya sa na ɗaga kai na kalleshi da kallon mutunci a karo na farko a rayuwata tun bayan haɗuwata da Yusuf Attahiru. saɓanin kallon da na jima inayi masa a shekarun baya, wanda babu komai a cikinsa face zallar ƙiyayya mara misali._
_Wllh duk sanda zan ɗaga ido na kalleshi ji nake tamkar shine dalilin da ya sa mama ba ta son alaƙata da wanda nake so. Amma a yau sai na fahimci na tabka babban kuskure da na bari zuciyata ta ginu da ƙiyayyar mutum Mai daraja irin Yaya Khadir, jikina ne ya yi bala'in sanyi ban san lokacin da na ɗaga kai ina binsa da kallo na musamman ba.Wani irin kallo nake masa wanda yasha ban-ban da irin kallon da na saba jifansa da shi a duk lokacin da ƙaddara ta hadamu a guri guda, kallo nake masa mai ɗauke da tarin abubuwa masu yawa wanda ke da alaƙa da saƙon zuciya, a yanda nakeji a wannan lokacin baki ya yi Kadan ya iya siffanta yanda nake jin girman yaya Abdulkadir, ƙimarsa da mutumcisa ne suka ninka kansu a cikin duk wani lungu da saƙo na zuciya da ruhina_
_A nitse ya miƙe cikin nutsuwar da ta zame masa abokiyar rayuwa ya nufi ƙofar fita daga falon, ba tareda ya yi kuskuren sake kallon fuskata a karo na biyu ba, kai tsaye ba na ce ya barmin abin tunawa ba. amma juyawarsa a wannan lokacin ta haifar da abubuwa masu wahalar mantawa._
_"ina ganin lokacin barinki falon nan yayi Bilkisu. Saboda ba na so zuciya ta ɗebeni in aikata miki abinda zai zame miki abin tunawa a duniyarki na tsahon har abada, kamar yanda ki ka samar min a tawa duniyar wanda ba lallaine na iya mantawa cikin sauƙi ba. wato Bilkisu har kinyi wayon da za ki kai ƙarata gurin Abdulƙadir akan Namiji ko?" Mama tayi min tambayar cikin jin ciwon abinda na aikata._
_Jikina ne ya yimatiƙar sanyi a lokacin da furucinta ya kai mini farmakin ba zata. Hawayene suka fara kwaranya a saman fuskata, zanyi magana ta yi saurin ɗaga mini hannu taci gaba da cewa," kin buƙaci in baki damar da kika jima da cire ran saminta, sai gashi a yau kin sameta ta sanadin mutumin da kika jima kina gudun tsira daga gareshi. ni na san waye Yusuf Attahiru tun kafin na haifeki kizo wannan duniyar, sai dai bani da sanya rai sosai akan zai baki abinda kike buƙata a rayuwarki na har abada. Amma duk da haka ina miki fatan alkhairi, Ubangiji ya sa hakan shine alkhairi." mama tayi maganar cikin sebaitaccen yanayi mai wahalar fassarawa_
_Jikina har lokacin a mace yake cikin rashin guzari da karfin gwiwa na ɗaga Kai na kalleta, ganin yanayin da fuskarta ta nuna ne ya sa naji na karaya. nan take naji rauni akan abinda na aikata Yana barazanar tarwatsa min zuciya_
_Kai tsaye ba zance ban fahimci inda magan-ganunta suka dosa ba, sai dai har lokacin na kasa samawa maganar muhalin da ya kamata ace na sama mata a cikin raina. banƙi ba wata ƙila in tuna hakan a nan gaba a lokacin da rayuwata tayi min kyau kamar yanda nake fata._
_Wani kyakkyawan murmushi Mama ta samar a tsakanin laɓɓanta, wanda ke nuni da gaskiyar yanayi da take ciki. ta jima tana juya girman alaƙar dake tsakanina da Yusuf Attahiru, wadda ta sauyani daga Bilkisu mai Sauƙin kai zuwa wata new Stubborn Bilkisun._
_Lallai ta yarda Yusuf yana da matiƙar mahimmanci da tasiri a cikin duniyata. Sai dai har yanzu ta kasa gano hujjar da ta sa na fifitashi fiyeda nagartaccen namiju irin Abdulƙadir wanda ya ginu da soyayyata tun ina tsumman goyo. A nitse ta miƙe tana takawa bisa shimfiɗaɗɗen kafet ɗin da ya mamaye falon da taushinsa. ba tare da ta ƙara bi ta kaina ba ta raɓa ta gefena cikin nitsatsen takunta, irin takun dake baiyana ƙarfin gwiwar da take tare dashi akan hukuncinta. A haka ta ɓacewa ganina gaba ɗaya._
_A kasalance na sauke idanuna waƴanda nai mata rakiya da su, ina tufka da warwara akan zaɓin da nayiwa kaina. Lumshe idanu nayi cikin ɗaurewar kai akan yanayin da na karanta a kan fuskar Mama, sai dai har lokacin zuciyata ta gaza karɓar abinda nayi katari dashi kwance a tsakiyar idanunta._
_"ya Allah."_
_na firta cikin gajeran sauti wanda ke baiyana raunin Zuciyata a fili. Sai dai ba na jin zan sauka da ga kan zaɓin da nayiwa rayuwata, wanda nakeji a raina zan samu yalwataccen farin ciki a tareda shi na har abada!._
_Miƙewa nayi da wani irin ƙarfi a lokacin da na tabbatar da cewa ƘARSHEN WAHALA ta ya zo, har ban san lokacin da wani kyakkyawan murmushi ya ratso ta tsakanin siraran laɓɓana ba. Kai tsaye ƙofar fita da ga falon na tunkara cikin walwalar da na jima ban yiwa kaina a do da ita ba._
_Duk inda na ɗora ƙafata sai Mama ta yi min rakiya da idanunta, waƴanda nake jin tasirinsu a ilahirin jikina, a haka na kammala aiyukan dake kai na, sannan na koma ɗaki cikin maɗaukakin zumuɗin jiran kira daga Yusuf, mutumin dake da matsayi mai girma a zuciya da ruhina._
_Hmmm A tunanina duk wanda ya ji tarihin alaƙata da Yusuf Attahiru, dole ne ya jinjinawa zaɓina wanda nake ganin shine dai-dai dani. So guda ɗaya ne tak! kuma na miƙashi gareshi babu ranar canzawa._
_Kafe wayar dake hannuna nayi da idanu ina kallon lambar wayarsa cikin maɗaukakin shauƙi, a irin ƙaunar da nake masa wllh ko filo yace inyi da ramin kunama zanyi hakan, saboda yanda nake gudin karya umarninsa, wata irin ƙauna zuciyata ke masa irin wanda babu ita a zahiriya sai a duniyata ni ƙaɗai._
_Faɗaɗa murmushin da ke kan fuskata nayi ina ji a raina tamkar fuskarsa nake kallo, a wannan lokacin babu abinda nafi buƙata kamar jin sautin muryarsa wanda nayi kewa na tsahon lokaci. a ƙalla idan na kira shi zai rage min kaɗaicin rashin ganinsa wanda ya jima da kassara nutsuwar zuciyata!._
_Yawun da ya taru a bakina na haɗiye da ƙyar sakamakon jazabar ƙaunar dana afka. cikin ƙoƙarin son na haɗa kalaman da zan firta masa idan ya amsa kirana, ina buƙatar in zaiyana masa yanda nakeji a tareda shi, da kuma adadin yanda nayi kewar sa._
_Lema naji a saman kuncina wadda ta alamta min cewa kuka nakeyi, kai na tsaye na danna masa kira cikin ƙaguwa da zumuɗin jin muryar da ke saukar da nutsuwa a cikin ruhina._
_Wannan kiran da nayi shine ya zama silar faruwar abubuwa masu tarin yawa a rayuwata......!_
***
Miss🌙
#Share
#comment
#Ra'ayinzuci
Love u all