Part 7
by @chefmuaysh
BADAƘALA
✍️ A'isha Hamza
Sai daku 🤟 yan amana
Saida ya gama saka layin a sabuwar wayar da aka aiko mashi da'ita saiga sako ya shiga nan take yayi duk abinda aka umurce sa ba tareda bata lokaci ba
Video call aka kirashi aka ce ya haska matar dake kwance domin shi baya ganin ainihin wanda yayi kiran wayar domin ya rufe camera shi sana baya magana saidai ya turo sako
Abinda akace yayi yake yi Saida ya gama nuna matar aka yanke wayar ba dadewa kuma saiga wani sakon ya shigo ta wayar, ƙara tashi yayi ya fita yana buɗe kofar yaci karo da ƙatuwar jaka a bakin ƙofa
Again saiga wani sakon dilin ya shigo ya ƙara karantawa sai ya fara yan juye juye baiga kowa ba kawai ya duka ya ɗauki jakar ya fice daga wajen baki ɗaya Saida ya fito wajen gaba ɗaya ashe hotel ce babba an rubuta SHAUBAN HOTEL
Saiga wata jibgegiyar mota tasha gabanshi aka buɗe ya shiga aka tada shi kanshi baiga fuskar su ba domin duk a rufe take da facemask Sai uwayen bindugu a hannusu kowa ya rike tashi ga wata a kugu yar karama
Dai-dai wani kofar gida suka direshi har sauri yake ya fita domin ba ƙaramin kaduwa zuciyar sa keyi ba dama Allah Allah yake ya gama musu aikin su yadawo gida dama shegen son kuɗin sa ne ya kaishi
Inno na zaune tsakar gida Ayrah ta fito sanye da doguwar hijab tace zataje gidan su Khairiyya tajita kwana biyu shuru batasani ba ko batada lafiya ne
Inno tace Allah raka taki gona ko meye ma na gaya man sai kace dama ba kinsaba gantalinki yanda kikaga dama ba
Shiru tayi kawai tawuce don tasan hali yanzu dinma tana raga mata me don tace itafa dama tana zargin Ayrah ɗin yar aljanu ce tundaga siffarta ga kuma akwatin da yayi mata mugun ja har ya sanya ta ciwo ance mallakin Ayrah ɗin ne daganan tafara shan jinin jikinta da Ayrah ɗin
Dan yanzu har dakin gwaggon tabar mata baki ɗaya kuma ko katifun duka tabar mata ita kuwa Ayrah hakan ba ƙaramin daɗi yayi mata ba duk da wani lokacin kasancewar ta ita kaɗai ya kansa ta tashi tayi ta kukan rashin gwaggon cikin dare saidai tayi nafilfili tareda yiwa gwaggon addu'ar rahama
Tafiya take tanata yan tunane tunane har tana neman wuce gidan su Khairiyya ɗin kafin ta maido hankalin ta da sallama ta shiga gidan nasu suna zaune tsakar gida itada Abbanta da gudu Khairiyya ta tare ta wai tayi missing dinta
Kafin ta shiga gaisheda Abban Khairiyya ɗin fita yayi yabar musu gidan dan yasan in suka haɗu Shikenan ba saura in suka fara labari ba kamar Khairiyya taji labari
Khairiyya tace da yau zanyi ta maza inzo wallahi sosai tabawa Ayrah dariya wai zatayi ta maza tazo sai kace gidan yaƙi
Zancen gizo dai baya wuce na koki Khairiyya tace dama ranar fa da nazo in faɗa maki uncle Sameer ya kira sunyi waya ma da Abbana kuma ya amince zamu tafi yanzu ma da kika ganmu zancen mukeyi
Ayrah tace to Alhamdulillah gaskiya naji daɗin labarin nan yanzu shi uncle Sameer din yaushe zaizo Khairiyya ta taɓe baki alamar damuwa tace wallahi bai faɗa min ba kuma na kagara in Ganshi ma
Murmushi Ayrah tayi tace to Sarkin rigima ai tunda yace zaizo to zaizo dinne nan Ayrah taci abincin rana don ba yanda Khairiyya batayi da'ita akan ta tsaya sai dare ba tace Inno zatai mata faɗa
Kwana biyu da zuwan Ayrah kuwa saiga Abban Khairiyya yayi sallama da Malam sun dade a waje kafin ya shigo ya saka zainaba ta kira masa Ayrah
Idar da sallah ta kenan ta maghrib domin bata dade da dawowa daga tallah ba saiga zainaba ta shigo kiranta inji baba, don har Saida hankalin ta yadan tashi don tana gudun kar ace Inno tace tayi mata bata ne a kuɗin ta
A dakin Inno ta sameshi waje tasamu ta zauna Inno kuwa nata faman aiko mata da harara bata ƙara dubanta ba tunda ta kalleta sau ɗaya tayi ƙasa da kanta
Baba ne ya katse shurun da faɗin mahaifin ƙawar kine yazo akan batun makaranta nutsuwa tayi sosai don ta riga ta sakawa ranta ba lallai ne Inno tabari a tafi da'ita birni karatun ba
Ya ci-gaba da faɗin yace ki shirya nan da kwana uku sunyi waya da malamin naku zaizo kuma kwana ɗaya zaiyi ku wuce saboda haka na kiraki inji ko akwai abinda kike buƙata
Kamar wasa haka Ayrah taji zancen baban domin batayi tunanin abin zaizo mata cikin sauƙi haka ba saiga Inno ta ware tana faɗin to malam Nima dai na soya mata aya mai gishiri da gyada idan zata tafi
Hawayen da take ƙoƙarin maidawa ne suka silmiyo mata da sauri tasa gefen hijab ɗin tana gogewa Inno ce ta kamo ta tana faɗin meye kuma na kuka Ayrah keda zaki tafi cika burinki na zama loya ake ce musu koma menene oho
Ba ƙaramin daɗi Ayrah taji ba duk da bata da tabbas ɗin kulawar da Inno ɗin take nuna mata ta Allah da Annabi ce amma ita koma menene dai hakan ya wadatar da'ita
Randa akayi zancen kuwa bacci saidai barawo don tana sakawa da kullawa ne akan tafiyar da zatayi ta wani ɓangaren kuwa batajin daɗi kasancewar ba gwaggo mai tayata farin cikin da take ciki
A zahiri Khairiyya tafi Ayrah nuna farin cikin tafiyar su birni karatu amma a gaskiyar zance Ayrah tafita farin ciki kawai ita mai ɓoye wasu abubuwan ne badan komai ba saidan tanada taka tsantsan akan duk abinda ta sanya a gaba
Yau din ma Khairiyya ce ta tashe ta daga bacci ko gari bai karasa waye ba saboda farin ciki nan take faɗa mata Abbanta yace zaije yimata siyayya anjima cikin gari Ayrah ta tayata murna amma a kasan zuciyar ta tanajin babu daɗi don tasan ita ba wanda zai mata siyayyar
Suna zaune kuwa saiga yaro ya leko wai Nuhu mai shagon caji yace Ayrah tazo da kamar bazataje ba don batasan akan me zai aiko kiranta ba Khairiyya ta matsa mata akan suje suji menene
Da yake basu da nisa sai gashi sun iso kuwa nan yake faɗa mata Iroro ne ya kira waya wai anason magana da'ita zo kaga farin cikin da Ayrah ta shiga kamar zata hadiye wayar da aka bata don an musu flashing ne ance bari ya kira
Kamar jira kau suke wayar tana shigowa ko ringing ba'a bari tayi ba suka daga sallamar barira ce ta katse su ai kuwa cikin zumudi Ayrah tafara gaishe ta sun dade suna waya har suka fara kuka daga can barira kema Ayrah albishir ɗin tanada juna biyu ba ƙaramin daɗi Ayrah taji ba itama take sanar mata da zancen makarantar da zasu wuce jibi don gobe ne uncle Sameer zai zo
Daga karshe Iroro ya amshi wayar yake tambayar ta lafiyar yan gidan duk tace suna lafiya yace to tanada wata buƙata tace masa ita kiran da sukayi ma taji lafiyar su ya wadatar da'ita
Yace mata ai yasan yan makaranta da buƙata saboda haka zai tura ma Nuhu mai chaji kuɗi zai faɗa mata abinda zai siyo mata canjin kuma a bata tayi murna sosai ta shiga jera masa godiya kafin barira takara karbe wayar suka gaisa da Khairiyya ma kafin sukayi sallama
Gaba ɗaya takejin zuciyar ta wasai don dai-dai gwargwado kiran su bariran ya rage mata kaso mafi yawa na damuwar da take ciki ga kuma abinda za'a haɗa mata na tafiya makarantar
Da yamma kuwa saiga kaya niki niki nuhu mai shagon caji yakawo mata su Inno anga abin duniya akabi aka ruɗe dukda ta debi kayan da suka kai rabi hakan bai hana dan akwatin da baba ya siyo mata cika ba hada yar Ghana must go dinta
Saida Inno tayi mata gyada da aya aka daka mata yaji taje wajen Halima ta faɗa mata game da zuwa makarantar itama hada yan kuɗi tabata a hannun ta tace ta rike tasayi wani abu
Saida aka gama shirya komai Inno tace to malam gaskiya Ayrah dole ta tafi da wancan bom ɗin nata don bazata bar mana masifa a cikin gida
Duk yanda yaso ya nuna mata ba buƙatar haka ga wanda zaije makaranta amma tace sam bata gamsu ba itadai atafi da akwatin nan
Ayrah ita bata damu ba saboda haka ta canja shirin kayanta tasaka akwatin can kasan kayanta kafin ta ɗora wasu dukda ba wasu kaya ta ɗauka ba saboda ance musu da sunje za'a basu uniform da cheeks na makaranta
Rana bata ƙarya dai don uncle Sameer yazo amma sai randa zasu tafi yazo gaba ɗaya sun shirya, Ayrah kam zainaba ta rakota hada baba ma gidan su Khairiyya
Khairiyya kuwa ta rike Abbanta sai kuka take kamar wanda za'a kai gidan Aure daƙyar ya lallaba ta yace zai dinga zuwan musu visiting
Napep suka tara suka tafi tasha suka hau motar zuwa Kano direct tunda Ayrah take bata taɓa barin garinsu ba har taje wani waje hakan yasa tunda motar su ta tashi taketa faman yan kalle kalle ita kuwa Khairiyya baccinta tasha sosai
A hanya da aka tsaya ne uncle Sameer ya siyo musu doya dakwai kowa da nata Ayrah dai kaɗan taci don duk wani iri takejin ta tarasa dalili ita kuwa Khairiyya tass ta cinye tasha lemun daya siyo musu
Wayar uncle Sameer ce tafara ringing murmushi yasaki kafin ya daga kiran da alama babu abinda akace daga ɗayan ɓangaren saidai shi da yace sir mun kusa isowa kuma ya yanke wayar
Ayrah dai ta kalleshi kaɗan kuma ta juya tana yan tunane tunanen ta na duniya
Sosai sungaji lokacin da suka iso Kano suka fito kowace daga gani bata saba doguwar tafiya ba don duk a jigace suke
Bakin titi daga gefe suka fito yasanya yan dako suka dauko musu kayan su wata bakar motace ta faka kusa dasu tasha uban tinted glass baka taɓa ganin na ciki
Gaba ɗaya Khairiyya ta tsure sai raba idanu take ganin motar ta buɗe kanta yasa ta nema zubawa da gudu don dai rikotan da uncle Sameer yayi sai tadawo bayansa ta labe
Ƙoƙarin shiga yake Ayrah kuwa sai kallon ikon Allah take, ganin duk a rikice suke yasanya yace musu wannan motar gidansu ce zai kai su su huta zuwa jibi zasu wuce makarantar
Daƙyar yasamu Khairiyya dai ta nutsu Saida ya shirya musu kayansu a cikin bayan motar su kuma suka shiga ciki suka zauna sai yan dube dube suke kamar ya satosu
Mai tukin ne da fuskarsa take a rufe yadan kallasu ta mudubi kafin yace sir wacece surukar tamu ne anan
Toh mutanen chef kuce inbani babu ku a comment 🙌 Please ku cigaba da bibiyar labarin nan inshaa Allah kamar yanda kukeji dadinsa a gaba ma tafi daɗi