ALWASHI 2

10

by @rufaidaumar

ALWASHI

  ©Rufaida Umar

       35

MAMAN MEENAT SUPPLEMENT/SKIN CARE

Yar uwa muna saida kowanne irin supplement na gyaran jiki wanda zaisaki fito fes kamar sabuwar Amarya, yar uwa shin kurajene suka dameki, ko matsalolin jikine kamarsu rama, ko kibace tayi miki yawa kikeso ki rage, bushewar fata ko karancin ni'ima ko budewa ne ko infection? Ko kuma so kikeyi fatarki tayi laushi ki dinga sheki kina haskawa wato kalar madara dai Haj to ki garzago

Yan uwa kusani duk wani supplement da zamu kawo muku sai munyi bincike mun tabbatar da ingancinshi, mun kuma tabbatar da cewa bashi da wata illa ga lfy

Akwai masu cewa sunsha supplement amma har yanzu basuga wani canji ba, to yar uwa kodai an baki fake ko kuma ba'a baki wanda ya dace dakeba, kokuma bakisha yadda ya dace ba, kisani yar uwa kafin ki fara shan supplement akwai ka'idoji daya kamata ace kin kiyaye kuma kin kula dasu matukar kinaso suyi miki aiki yadda ya kamata kuma cikin sauki ***

1. Akwai Supplements na gyaran jiki ciki da waje, munada set na uwargida dana Amare da masu jego

Sannan ga wadanda sokeso jikinsu yayi kyau sosai amma basa son susha supplement to albishirinku muna da kowanne irin mai na gyaran jiki da kuke bukata irinsu lotion, cream, soap, scrubs, face Cream,sun screen, serums concentrate, hair oil, hair cream face mask etc

Muna saida duk wasu nau'in supplement Lotion da kuke bukata, sannan Maman Meenat collection ba anan kadai ta tsaya ba muna saida turaruka kowanne irin na wuta dana jiki, da Airfreshners da air wick, sayen daya ko sari ke dai kawai neme ni a wannan number ***

***
  Laila tun wayar da ta suka yi da Hajja kan cewa Areef ya kai batun aurensu gaban iyayensa ta kasa sukuni. Jira take ta ji me zai ce, ta kalli wayar da ta saka layin da suke magana a ciki, babu alamar shigowar kowane saƙo. Haka ta ajiye jikinta a sanyaye. Ranar gaba ɗaya bai neme ta ɗin ba sai washegari da rana tana kicin tana girki wayar ta yi ƙarar shigowar kira. Ta ciro ta a aljihun doguwar rigarta ta duba, shi kaɗai ya mallaki layin, hakan yasa ta ɗan duba hanyar shigowar kicin ɗin, sai da ta tabbatar babu mai tahowa kafin ta amsa da sallama. 

  Areef ya amsa sallama da cool voice dinsa. 

  "Barka da war haka, ina fatan ban katse maki wasu uzurorin naki ba?"

Ta yamutse fuska.

"Ba damuwarka ba ce hakan, sannan ban ce tsakaninmu turo saƙonni ba ne kawai?"

Shiru ya ɗan biyo baya daga ɓangaren Areef sai kuma ta ji ya ce. 

"Sorry, won't call again."

"Just text me next time." 

Ta amsa a ɗan zafafe gami da jan numfashi kaɗan, ta ƙara duban ƙofar kafin kuma ta katse shirun da ya biyo baya na ƴan sakanni. 

"Ba ka da abin cewa? Ka katse min abin da nake."

"Dagaske za ki iya zaman aure da ni Laila?"

Ƙirjinta sai da ya buga da ƙarfi, ta ɗan dafe. Ambatonta da Laila yasa ta jin kamar gaba ɗaya sirrikanta ne suka tonu duk kuwa da cewa ba ta mance ita ta sanar da shi sunan ba. Tambayar da ya yi da wani irin sassanyar murya mai tarin fassarori ya ɗan taɓa ta. 

'Idan ace Sameera na raye, za ta iya auren wanda ya yi mata fyaɗe?'  Wani ɓangare na zuciyarta ya jefo mata tambayar. 

"You there?" 

Ya furta har lokacin muryarsa da wani irin sanyin da ta ba kanta cewa na munafunci ne. Ta tabbatarwa kanta da muryar da ma kyawun suffarsa yake yaudarar mata ya haiƙe musu. Yar uwarta ce kawai da ya kasa shawo kanta ya yi amfani da ƙarfi. Tuna haka ta ja tsaki a fili kafin ta amsa.

"Da ba zan iya ba ai ba zan fara zuwar maka da zancen ba. Wai me kake nufi ne?"

"Shikenan, kiyi haƙuri, ban yi tambayar don na ɓata ranki ba. Na faɗawa iyayena batun aurenki. Sun amince min. Sai dai akwai wata ƴar matsala da ban sani ba ko za ki ji daɗinta."

Laila cikin rashin fahinta ta amsa.

"Wace matsala kenan?"

"Ku biyu ne, bayan ke akwai Kausar. Cousin ɗita ce wacce aka riga aka yi zancen aurenmu tun ma kafin.."

"Ya isa haka, sai dai ba na son zama tare da kowa a gidana. Ma'ana, sai dai ka raba mana muhalli."

Areef ya yi murmushi mai sauti. 

"An gama ranki ya daɗe."

Ta ɗan fidda wayar a kunne ta harare ta tamkar yana gani kafin ta maida. 

"Shikenan?" Ta firta cikin soma gundura da sauraron muryarsa. 

"No. Bayan babbar sallah zasu zo tambayar aure. Hakan ya yi?"

Nan ma ta ji faɗuwar gaba ta dai cije ta amsa.

"Allah ya kaimu. Sai anjima."

Daga haka ta katse kiran tana maida numfashi tamkar wacce ta ci gudu. 

"Zan iya kuwa?" Ta yi tambayar a fili, babu mai amsa mata face ita kanta. Babbar wayarta ta ɗauka ta buɗe data ta yiwa Zakiyya dogayen voicenotes na labarin yanda suka yi da Areef tun ranar da ya zo har zuwa yau din. Sai da ta tabbatar ya je kafin ta koma ga Na'eem shima ta aikamasa, daga nan ta maida hankali wajen duba tukunyar dafadukanta,  cikin sa'a ta ga ya dahu ta sauke. Gaba ɗaya jikinta a mugun sanyaye, idan ta tuna batun aurenta da Areef  sai ta ji babu daɗi kamar ta fasa. 
  Tana kammala juyewa ta kai na Gwaggo sauran kuma ta ajiye saman tebur bayan ta miƙa na Daddy samansa. Ta koma ga wacce ta sakawa ƙunshi ta ga har ya kama. Kasancewar sallah ta gabato saura kwanaki kadan a shiga watan babbar sallah yasa ƴan lallen yanzu sun ɗauke ƙafa. Ta taimakawa budurwar ta fidda mata na hannu ta bar ta da cire na ƙafar sannan ta fice zuwa ɗakinsu. 
Zakiyya ta kira ta, bayan sun gaisa da rawar jiki ta ce,

 "Haba Laila, meyasa za ki mare shi? Ba ki yi tunanin kar a je shirunsa jira zai yi ki faɗo gidansa ba tukunna ya shirya ɗaukar fansa? Na kasa yarda wai kin mari guy kamar wannan ya shanye bai yi wani reaction ba."

 "Bai isa ya yi min komai ba, ki kwantar da hankalinki. Kar ki manta fa idan ya shirya nima a shirye nake da shi."

"To ai shikenan." Cewar Zakiyya, nan kuma ta ba ta shawara kan yanzu ne daidai ta sanar da su Gwaggo batun samun mijin. Ta ƙara da fadin,

"Ya dace ko sau ɗaya ne ya zo su gaisa da su Gwaggon. Abin nufi, ya turo wanda zai gabatar madadinsa, kinga zasu fi fahimtar hakan. Ba wai kawai su zo tambaya bayan sallah ba."

Laila cike da gamsuwa ta ce,

"Hakane, zan yi masa text zuwa anjima in sha Allah."

"Yauwa hakan zai fi."

Sun ɗan jima suna tattaunawa sannan suka yi sallama. Fitowa ta yi zuwa ɗakin sana'arta, Budurwar har ta tafi don daman sun yi sallama. Gyarawa ta yi ta rufe sannan ta koma ta ɗebi abincinta ta haɗa da coke mai sanyi da ruwa ta nufi ɗakin Gwaggo Samha. Ta iske ta soma cin  nata abincin. Ƙarasawa ta yi ta zauna a gefenta. 

  "Sannunki ƴar kirki, ina nan ina zuba santin girkinki. Masha Allah, Kubra tana burgeni da ta tsaya tsayin daka wajen koyar da ke aiki, sam ba ki da son jiki ga saurin ɗaukar abu."

Laila ta yi ƴar dariya. 

 "Kai Gwaggo, toh kodai na sakamaki matashin kai a bayanki ne?"

Dariya itama Gwaggon ta yi tana ƙarasa haɗiyar naman ragon da ya dahu luguf a abincin kafin ta amsa.

"Ai idan ma aka yi hakan ba ki yi laifi ba. Ke dai Allah ya maki albarka, ya kawo maki miji nagari."

Ta sunkuyar da kai kaɗan tana murmushi, hakan da ta yi ya sa Gwaggo murmusawa itama. 

"To da alama wannan karon akwai daddaɗan labari kenan?"

Laila ta gyaɗa kanta. 

"Alhamdulillah, ko kefa? Ai aure ba ya hana karatu. Waye shi?"

Da sanyin murya ta amsawa Gwaggon,

"A can Katsina iyayensa suke, ya fi zama dai a ƙasar waje inda yake gudanar da kasuwancinsa. Zai shigo kafin sallarnan ma ya gaisheku."

Gwaggo jin haka ta faɗaɗa fara'arta. 

"Masha Allah, labari mai daɗi. Ke kar fa ki kashe ni, ga daɗin girki ga na wannan labari naki."

Dariya Laila ta yi gami da jan istigfari. 

"Kai Gwaggo, kisa kuma?"

"Eh mana, yanzu kinga bayan sallarnan saurayin Haseena zai zo tambaya, da ace nakin ma kun fahimci juna ai da an yi mai gaba ɗaya kawai. Allah ya tabbatar mana da alheri."

Laila ta yi shiru, ita ba ta fiye son haɗa sabga da Haseena ba don haka murmushi kawai ta yi ta amsa amin din Gwaggo a zuciya. Ita alherin da take nema a auren ai bai wuce ta yi nasarar jefawa Areef  bomb din da zai tarwatsa zuciyarsa ba. Ya rayu kamar matacce. Wannan shi ne babban farin cikinta. 

Bayan ta kammala ta aikamasa da text na cewa ya dace ya turo wanda zai zo madadinsa cikin kwanakin da suka rage  
a shiga watan babbar sallah. 
 
  "Ok." Ita ce amsar da ya aikomata a gajarce. Ta ji zafin wannan ok din amma ta danne kawai. 

 ***
   KATSINA

 Areef a gaggauce ya amsawa Laila saƙonta sakamakon chaji da kansu ya dauki chaji suna ta haɗa lissafin abubuwan da ya dace su shigo da su a wannan karon don faɗaɗa kasuwancinsu kamar yanda suke so har a garin Kano. Abinda ba ta sani ba dama shi da Fareed da ma wasu ma'aikatansu biyu suna kan hanyar shigowa Kano don zuwa ganin filin da aka nemar musu na gina branch dinsu a can. 
   Sun kammala komai ya shigo ofis dinsa ya fidda coat din da ya saka ya bar ta cikin. Zama ya yi gami da ɗaukar gorar ruwa ya sha. Jinginar da kai ya yi jikin kujerar yana so ya ɗan samu relief daga ciwon kan da ya matsa mishi a kwana biyun saboda rashin hutu. Fareed ne ya shigo da sallama hannunsa riƙe da wasu takardun. 

   Buɗe idanu kawai Areef ya yi yana dubansa. 

   "Again?"

Dariya Fareed ya yi ya zauna bayan ya dire takardun saman teburin.

"Kai fa kana nema ka zama ragon maza, mene ne abin tsorata da ganin documents din nan, photocopy ne na details na shipping ɗin ɗazu wanda already mun kammala."

Areef ya ɗan murza idanunsa da hannu. 

"Ok."

Faeeed da ya zuba masa idanu kaɗan ya ce.

"Akwai wani abu ne? Kwanakin nan wani iri nake ganinka."

"Ba komai, kaina ke takura min kwanakin nan. Amm..dama ina son nace maka akwai inda za ka yimin rakiya idan muka shiga Kano."

Da ɗan murmushi Fareed ya ce,

"Laila?"

Areef ya buɗe idanunsa gaba ɗaya yana kallonsa, Fareed bai bari ya tofa ba ya dara gami da amsawa.

"Yes na ji komai a bakin Abba. Ka samu matan aure har biyu at once. Ya faɗa min da tunanin ma na ji, a rashin sanin Abba, ni ne ƙarshen jin batun Laila."

Ya ƙarashe da ɗan watsawa Areef ɗin kallon da ke nuni da rashin jin daɗin hakan. Areef ya shafi sumar kansa yana ɗan murmushi. 

 "Ka gafarce ni, abin ne ya zo bagatatan, amma trust me, ina da niyyar sanar da kai."

Jinjina kai Fareed ya yi,

"Farin cikin ka samu matan aure ba ma mata ɗaya ba ya kore komai fa. Yaushe ku ka haɗu har abin ya yi wannan nisan?"

Ya ƙarashe tambayar da yanayin mamaki. 

 Murmushin Areef ya ƙara yi, ya tunano abin da ta aikomasa ɗazun. 

"Wata ce, na shirya baka mamaki ne yasa na ja bakina na tsuke. Za ka gan ta very soon in sha Allah."

"Dakyau, naku na manya daban yake, biyu a lokaci guda."

Girgiza kai kawai Areef ya yi har a lokacin da murmushi saman fuskarsa. 

"Allah ya shirye ka."

Fareed ya yi dariya shi ma.

"Cewa za ka yi Allah ya tabbatar da alheri. Bari nima Hayateena ta sauka lafiya na kawomata abokiyar zama."

Murtuke fuska Areef ya yi,

"Are you serious? Aisha za ka yi wa kishiya? Da wuri haka?"

Fareed ya miƙe yana ɗan ɗaga hannu alamar ya yi saranda.

"Maida wuƙar, wasa nake yi. Amma ban yi maka alƙawarin da ita ɗaya zan rayu ba."

Daga haka ya fice yana ƴar dariya, Areef ya girgiza kai kawai. Fareed akwai tsokana. 

 ***
  Mami tana zaune tare da Mardiyya da Maryama sun yi shiru suna sauraronta tana labarta musu batun auren Areef da ya taso har mata biyu lokaci guda. 

 "Tirƙashi! Yanzu Areef duka-duka nawa yake da zai haɗawa kansa cakwakiyar mata biyu at once fisabilillahi fa?"

Cewar Maryama tana duban Mami da Mardiyya. 

 Yamutse fuska Mamin ta yi 

 "Aikuwa haka nan zai zauna da su tunda ya yi ƙaurin baki tun a farko. Yadda ba za su hana shi zaɓinsa ba kamar yanda suka ce, haka nima ban ga wanda zai saka ni mayar da hannun agogo baya dangane da aurensu da Kausar ba in sha Allahu. Ku bi shi kawai da addu'a amma fa ni sam yarinyar tun ma kafin na yi tozali da ita, na ji zuciyata ba ta aminta da ita ba."

"A ƙyale shi ya yi Mami, ƙila rabonsa ce tunda kika ji yace a baya ma ba shi aka so ta aura ba a gidansu. Yanzun kuwa tunda kika ga hakan ta faru, to hakan ya fi alheri. Ki tuna fa wahalar da aka ci a kansa a baya kafin yanzun ya amince zai yi auren nan Mami, a bar komai a hannun Allah kawai. Don't stress yourself please." 

Faɗin Mardiyya cikin son kwantarwa da Mamin hankali.

"Mene ne abin damun kai Mardiyya? Ai babu shi, aure ne ya je ya yi Allah ya sa alheri ne. Kiran da na yi muku don ku zo ku yi tsarin abinda kuka ga ya dace, mun yi magana da Alhajinku, komai ya damƙa shi a hannun yar uwarsa, na.."

"Wace yar uwarsa kuma?" Maryam ta katse Mamin ranta na suya don tun kan a amsa ta hasaso ta. 

Murmushi mai ciwo Mamin ta yi ta ce,

"Wa kuwa ban da uwarku Zayha? Ai ya na ta wuƙa da naman shirye-shiryen komai ciki har da na lefe kuwa. Ya ce Areef ɗanta ne ba ɗana ba. Idan da kara wai ya dace na bar komai a wurinta, shirin da na kira ku domin mu fara, a kan yar uwarku kuma kanwarku Kausar ne, na san dai bikin ba zai wuce farkon shekara ta musulunci ba in sha Allahu. Sai ku san me za ku yi."

Mardiyya da Maryam duk ransu babu dadi, abin ba haka suka so ba. 

"To ke Mami shiru kika yiwa Abban? Fisabilillah don me za'a tauyeki haka? Auren nan na gani dai ba shi ne na farko a ɗakin nan ba, ko na Adda Diyya da nawa babu wacce ya damƙawa ragamar, nasu kawai ido da ƙananan shawarwari, sai yanzu da ya zo kan Areef?"

Maryam na kai wa aya itama Mardiyya ta amshe zancen,

 "Matarnan fa ba don Allah take lamuranta ba Mami. Ni kam da za ki ji shawarata da kin ƙara rarrashin Abba ko batun lefen ya damƙa mana."

Taɓe baki Mami ta yi.

"Ku na abu kamar baku san halin ubanku ba, to ku ji ni dakyau, babu abinda ban ce ba, ƙarshe da na nuna ku ne zaku haɗa lefen cewa ya yi ai idan ma ɓangaren kayayyakin mata ne, to fa Fadila ce kan gaba tunda kasuwancin ta ke bugawa sosai. Ya ce na bar masa zancen ma kar na ɓata masa rai. Haka na ja bakina na rufe."

Wani ashar Maryam ta saki sannan ta ce,

"Fadila? Ƙanwar ƙanwarmu Fadila ita ce Abba zai ba ragamar lefen Areef? Ya san irin burin da na cima bikin yaron nan idan ya tashi?"

"Aikuwa ba zai yiwu ba gaskiya Mami, idan Hajja ita a nata wautar ba zamu iya tunkarar Abba idan ya yanke hukunci ba to ba ta yiwa kanta adalci ba."

Mami dai ta ce kar su kusa su ambaci sunanta gaban Alh Sada, suka ce sun ji. Nan aka bar zancen aka shiga kuma maganar auren Benazir da suke tunanin an yi sakin kawai Baba Dakta ke ɓoyewa tunda yace a bari ko mene ne za'a ji idan ya shigo Katsina. 

  Koda Alh Sada ya dawo da magriba suka risƙe shi har falonsa, da baiwar iya magana ta Mardiyya ta shawo kansa ya amince da damƙa mata ragamar haɗa lefen mutum ɗaya don a cewarsa ya riga da ya furtawa Hajja ba ya so ta kawo wani abu. Furucin bai yi musu daɗi ba sam sai dai ko babu komai sun sani wannan yaƙin zai faranta ran Maminsu. Maryam ta dora da faɗin ya dace ya dinga ba da dama garesu sisters kan wasu sha'anin ba wai iyaye ba saboda hakan ma zai ƙara haɗa mishi kansu. Abba ya yi na'am da shawarar Maryam yana mai jin nishaɗi da hakan. 
 Da wannan suka komawa Mami, sosai ta yi mamakin yadda suka shawo kan nasa kuwa. Fara'arta ta faɗaɗa ta ce to lallai su haɗa na Kausar, a bar ita Laila can Hajja ta ji da ita. A cewarta ai so so ne, amma kuma son kai ya fi. Suka yi dariyar furucinta. Sun yi amanna Mamin tana kaunar Kausar sosai, sun kuma kula yarinyar ba ta da hayaniya sam, ga biyayya ga umarnin Mamin. Sam ba ta da rawar kai. Fatansu ta ɗore har bayan auren. 

***
   BAYAN KWANA BIYU...

Laila tun safe ta tsinci shigowar saƙon Areef kan cewa za'a shigo gidansu a ranar kamar yanda ta buƙata a je din. Duk don ta nunawa su Momi Fannah kamar tana son wanda zai zo din ta shirya masa abinci da abin sha saboda ta sanar musu daga Katsina zai zo. Tunani take ta yi waye wannan da Areef din zai turo madadinsa tunda hakan ta zaɓa? Ta kasa ba kanta amsa a ƙarshe ta share batun. Koda ta kammala komai Abbas ɗan Momi Fannah ya taya ta kai komai ɗakin saukar baƙi ta koma zuwa falo ta yi zamanta. Momi Fannah  a fitowa ta ganta ta kama baki.

"Laila, ba kika ce baƙonki ma tafe ba?"

Cike da rashin fahimtar me Momi Fannah ke nufi ta amsa da eh.

"To shi ne za ki zauna babu ko wanka da shiri? Ba dai haka za ki tarbe shi ba?"

Sai ta wayance da ɗan yaƙe ta ce,

 "Dama zama na ɗan yi don na huta kaɗan Momi, bari na je na shirya." Ta kai ƙarshe tana ƙoƙarin miƙewa. 

"Au to, yanzu na ji batu."

 Daga haka Laila ta fice zuwa ɗakinsu, Haseenah na falon ta baza takardu tana karatun jarrabawa ta yi mata sallama Haseenah ta amsa ba tare da ta kalle ta ba. Itama ciki ta shige don yanzu ta tattara lamarin Haseenar ta watsar a gefe. 

  Kamar jira yake ta shiga sai ga text dinsa, ta buɗe tana hararar wayar kamar shi ta gani.

  "Your address please."

Ta ja tsaki kafin ta aika masa da cikakken adireshin gidan don ba ɓatacce ba ne, sunan street dinma sunan Daddy Mu'az me. Ya ƙi yi mata bayanin wanda zai zo itama gani take bai kai ta dinga watsa mishi tambayoyi ba don haka ta yi burus.

 Daga haka ta shiga wankan dole saboda kaucewa magana. Shiryawa ta yi cikin wani lallausan swisslace ruwan toka mai adon black and yellow flowers. Ɗinkin ya zauna ɗabas a jikinta ga wani adon stones da aka yi wa gefe ɗaya na gown din inda aka bi bakin leshin har ƙasa.

   Ta fiddo mayafinta yellow ta yafa. Kwallinta da man leɓenta na gado su ta zizara a ido da bakin daga haka ta fesa turare mai sanyi. Sallama aka yi, muryar Faruk da Abbas ta ji har suna rige-rige wurin fadin "Anti baƙonki ya zo, yana sittingroom"

   Ƙirjinta ya buga, ta karanto sunayen Allah kafin ta amsa musu da toh tana zuwa.  Wayar ta ɗaga ta duba, babu ko kiransa balle saƙo, kenan ya sallame ta. Ajiyar zuciya ta saki ta kashe ƙaramar wayar ta adana ta can cikin kayanta, riƙe da babbar ta fito hannunta, Haseena ta bi ta da kallon mamaki amma ba ta ce uffan ba har ta gifta ta. Laila ta zari flatshoe dinta a shoe rack dinsu ita da Haseena ta fito. Sai da ta soma biyawa wurin Momi Fannah da take zaune a dakin Gwaggo suna taɓa hira ta musu sallama suna yaba kwalliyarta sannan ta fice zuwa ɗakin saukar baƙi. 

  Sallama ta yi kafin ta tura kanta saboda jin muryoyin Ilham da  Faruk wanda tasan zai hana a ji sallamarta. Wanda ta gani zaune ya yi matuƙar kaɗa hanjinta. 

 "Kai ne?"

Ta furta a gigice har su Faruk suka dube ta.