“SANADIN ƘADDARATA”

Page-25

by @zahratulqalam51

*FASAHA WRITER'S ASSOCIATION*
     (*F.W.A)*©✍️
     ⭐⭐⭐

Ƙungiya masu aiki cikin salon hikima da fasaha gurin juya tunanin al-umma, kaifin alƙalumansu ya zarta takobi ©✍
___________________________________________________



بسم الله الرحمن الرحيم.
اللهم صلي وسلم على نبينا محمد. 




❁ 𝐒𝐀𝐍𝐀𝐃𝐈𝐍 Ƙ𝐀𝐃𝐃𝐀𝐑𝐀𝐓𝐀 ❁ 




Free book📓



By


*Aisha G Umar*
_*🌹𝑍𝑎ℎ𝑟𝑎-𝑡𝑢𝑙-𝑄𝑎𝑙𝑎𝑚🖋️*_




Page2️⃣5️⃣





"Babu abun da za ki ce min Sadiya! Shikenan burinki ya cika, kin raba ni da ɗana, tun jiya na ke kiranki amma ba kya ɗauka, saboda ni shegiya à wurinki na haifa miki ɗa kin aure ko?!".

Bakin Sadiya ne ya fara rawa idonta ya cika da tsoro, a hankali ta samu damar cewa, "a ah Baaba ba..." Baaba ta katseta da cewa, "to wallahi baki isa ba, ba zan haifa ɗa ki ki ci ribarsa ba!" Tana faɗi ta kashe wayar. A hankali Sadiya ta sauke wayar a kunnenta, idonta ya fitar da ƙwallah. "My Sadi?" Ta ji kiran Faruq, da sauri ta share hawayenta, tana amsawa....

NURIYYAH. 

'Yan uwa da su ka zo biki sun koma saboda komai ya ƙare. Ina zaune a garden riƙe da wayata a hannu, ban san ina na shiga ba, tun ɗazu wayar ta nuna min wasu rubutu, wanda ban gane musu ba, na yi ta ƙoƙari in gyara amma hakan ya ƙi yiwuwa. Ina cikin haka na ji zuwan mutum wurin. Saurayin da na ke kallonsa da Abba ne, wanda na ke jin su Asma'u suna kiranshi yaya Sayyid. 

"Can I sit?" ya faɗi yana kallona da murmushi, da mamaki na ɗagamishi kai alamar me zai hana? Sannan na furta, "Ina wuni?" Kamar ba na so, sai da Sayyid ya zauna sannan ya ƙara cewa, "lafiya ƙalau. Ko zan iya sanin me yasa fiskar kyakykyawa ya kasance cikin damuwa?", Kaina da na maida akan wayata na ɗago ina dubansa.

"Faɗa min mana kyakkyawar ƙanwata" kamar ba zan yi magana ba sai na ce, "daman wayata ce ta ke da matsala, tun ɗazu na rasa gane mata". "Ohh sorry na gani?" Miƙa masa na yi kamar yadda ya ce. Babu wani ɓata lokaci ya gyara min sannan ya miƙa min, amsa na yi cikin farin ciki ina yi masa godiya, ya murmusa ya ce, "Nuriyyah ko?" Na ɗaga masa kai alamar eh, ya ƙara cewa, "kin san sunana?" "Yaya Sayyid" na faɗi kamar yadda na ji su Asma'u na bashi girma, sai na tashi ina shirin barin wurin.

"Ba kya son hira da ni ne ki ke son tafiya ki barni ni kaɗai kyakyawa?" Ban amsa masa sai sake msa fiska da na yi jin sai ce min kyakykyawa ya ke, "to zauna ki yi hira da yayanki mana" a hankali na koma na zauna, nan ya fara jana da hira, tun ina amsa masa ɗaiɗaya har na sake muna magana, yadda ya ke ba ni wasu labarai na ban dariya ni kuma ina murrmushi har da fitar da haƙora, saboda ganin kamar shi mutum ne mai sauƙin kai da son raha.

Mun ɗau lokaci ka na daga baya na tashi na barshi a wurin, bayana ya bi da wani irin kallo yana sakin murmushi cikin nishaɗi, "I love this girl!" Ya furta a saman laɓɓansa. 

DARE.

Asma'u ce ta ce da ni mu je mu gaida Hajiya Kaka, ban ƙi ba na bita domin na ɗan ga canji kaɗan a wurinta, duk da ba na son haɗuwa da yaya Abba ko kaɗan. Ko da mu ka isa a ɗakinta mu ka tadda ta, gaisuwa cikin girmamawa na yi mata, itama Hajiya Kaka ta amsa min cikin jin daɗi, ta ɗora da cewa, "Nuriyyah zo ki matse min kaina kamar na ranar na ji daɗinsa sosai" cike da murna na miƙe na ce to Hajiya Kaka, sannan na zagaya ta bayanta na fara yi mata.

Murmushin jin daɗi Asma'u ta yi, saboda ta ji daɗin amincewar da Hajiya Kakar ta yi da ni. Asma'u da Hajiya Kaka na ta hira nima ina sanya musu baki jefi-jefi, sai na ji sallamar Yaya Abba. Ko da jin haka na turnuƙe fiskata, duk da kuwa zuciyata na bugawa, amma sai na daure.

Asma'u ta gaishe shi ya amsa yana tambayarta sai kuma ya juyo ya dubeni ya kuma duban Hajiya Kaka, "Kakata yanzu wannan gajerar ce ke matse miki kai da guntayen hannunta?" Murmushi Hajiya Kaka ta yi ta ce, "au ita Nuriyyar ce ka ke kira gajera? Wato jiya da na ji ka kira da ita ka ke kenan?" Kafin ya yi magana ni na ce, "yauwa Hajiya Kaka, ki yi magana, ban san me na tsarewa yaya Abba ba ya maida ni gajera".

Na faɗi ina sake ɓata rai, murmushin ƙasan zuciya ya yi, sannan ya miƙe, Kaka da Asma'u kuwa sai dariya su ke yi. Kallon Asma'u na ke yi da mamakin me ya sata dariya? Sai na ji muryar Abba ya sake cewa, "Hajiya Kaka duk share gajerar nan ma, ni fa tea na ke kwaɗayi yanzu", "kai dai ka riga da ka yi gadon nan, kullum da dare sai ka sha tea, to ni dai ba zan tashi yanzu in haɗa maka wani tea ba" cewar Hajiya Kaka, Abba ya murmusa ya ce, "ni dai a taimaka min".

"Yaya Abba bai kamata ace kai ba ka iya haɗa ko tea ba!" Na faɗi ina murmushin mugunta, saboda na Jo daɗi da maganar Hajiya Kakar, kallona ya yi ya ce, "ni fa ba abun da na iya, amma ke ba kin iya ba? Je ki haɗa min da kanki!" Da sauri na ɗago bayan na dakata da ga abun da na ke yi, na kalleshi na ce, "ni ni kuma? A ah". Hajiya Kaka da Asma'u da suke jin abun da mu ke cewa suna murmushi, Kaka ta ce, "eh ki je kawai ki haɗa masa, ba yayanki ba ne?".

Haka nan na sauka daga kan gadon ina kallonsa da haushi, shi kuma ya kashe min ido sannan ya ce "malama gajera idan kin gama ki ijje min a falo, kada kisa min gishiri a maimakon suger dai, in za ki sa sugern ki sa kaɗan ka da ya yi yawa, kuma kisa min a flasks kada ya yi sanyi", "to ai na ga kamar ka iya ma, ka haɗa da kanka mana!" Cewata ina turo baki, Abba kuma ya ce, "I'm waiting" Yana faɗi ya bar ɗakin yana girgiza kai cikin nishaɗi.

Kallon ya raina min wayo na bishi da shi sannan nima na bar ɗakin don yi masa abun da ya ce, duk da ba na so amma ya zan yi tun da a gaban Hajiya Kaka ya faɗa. Asma'u da Hajiya Kaka kuwa hira su ka cigaba da yi na Kaka da jika, Asma'u har tana cewa Kaka ta bata tatsuniya.

Ni kam ko da na je na duba kayan haɗin shayi, bai wani ɗau lokaci sosai ba na kammala, kamar yadda ya ce ban sa mishi suger sosai ba, bayan na sa a cikin flasks ɗin na taho falo don na ijje masa, amma ban same shi ba, Sayyid na samu, da murmushi na gaisheshi tare da zama a kujerar, ina tambayarsa aikin da ya ce min ɗazu yana son ya ci nasara a kai, shin ya samu nasarar? Shima da fara'a ta jin daɗi ya ke sanar da ni eh ya samu.

Lokacin Abba ya iso falon, kallona da Sayyid ya yi, sai kuma ya haɗe fiska, bai yi magana ba sai da ya zauna akan kujera sannan ya dubeni ya ce, "me ki ke yi anan har yanzu!?" Ya faɗi da ɗan ƙarfi ba wasa. Ni kuwa da na ke kallonsa tun da ya iso ya zauna, ban ce komai ba na tashi zan wuce, saboda yadda ya yi min maganar ban ji daɗi ba, ya shiga har cikin raina, duk da kuwa yadda ya ke min magana a baya, amma wannan ya tsaurara.

"Abba kafin ta tafi bari ta sa mana tea ɗin tukunnan. Ƙanwata zuba min shayin kin ji?" Sayyid ya yi maganar yana gyara zama, murmushi na yi masa na dawo zan sanya masa tea, har na kai hannuna akan flasks ɗin, sai kuma Abba ya yi saurin ɗauka, na ɗago ina dubansa ya ce, "jeki ni zan zuba!".

Wucewa na yi ina mamakinsa har cikin raina, ko gajerar ma bai kirani ba bare na san tsokana ya ke min, a sanyaye na wuce ɗakin Hajiya Kaka. Abba sauke numfashi ya yi sannan ya zuba musu tea ɗin, bai san me yasa ya yi mata magana haka ba, shi kam Sayyid bai yi tunanin komai ba, amma ya so da Abba bai hana Nuriyyah sanya musu shayin ba.

Ko da na isa ɗakin Hajiya Kaka na samu ta yi barci, ita kuma Asma'u ba ta nan, wato ta koma sashin Momy kenan. Har zan wuce sai Hajiya Kaka ta kira sunana, "Nuriyyah" da sauri na amsa don na ɗauka barcin ta ke yi, "dama ba barci ki ka yi ba Hajiya Kaka?".

"Tashi ta yi ta zauna sannan ta ce, "eh ban yi ba tukunna ina zaki je?" "Zan koma sashin Momy ne" ki bari sai gobe, yanzu zo ki kwanta a nan dare ya yi sosai", ta faɗi tana nuna min gefenta, mamakin maganar na ta na yi, sashin Momy duk a gudan ne amma kuma ta ce na bari sai gobe? Ban sake cewa komai ba na je na kwanta a gefenta kamar yadda ta ce, itama murmushi ta yi min ta juya ta kwanta, na ji daɗi a raina da na samu wannan damar a fiskar Hajiya Kaka, ko ba komai yanzu na gane babu tsanata a ranta.

WASHE GARI.

"Hajiya Kaka ban gane me ya ke faruwa da ke ba kwanan nan, idan ban manta ba tun ranar da aka gane ba yarinyar nan Nuriyyah ta yi satar sarƙar Fatima ba, shikenan ki ka sake mata fiska, yau kamar gani na yi a sashinki ta kwana, bayan kuma na san da ba ki sonta," cewar Mama tana kallon Hajiya Kaka da ta jingina da kujera.

Ɗagowa ta yi ta dubi Mama ka na ta ce, "Hajja Mama da ma can ba sonta ba ne ba na yi, amincewa da ita ne ban yi ba, to yanzu kuma na amince saboda zaman da ta yi a gidan nan ban ga wani mugun abu daga gareta ba, gaskiyar Raham..." "Hajiya Kaka! Yanzu kema tsakani da Allah biyewa Rahama za ki yi? Kin amince da 'yar tsintuwa kenan? Shikenan ku cigaba da ba ta dama, ni dai ina kan baka ta, kuma ina mai tabbatar muku sai kun yarda da ni nan gaba!". Faɗin Mama cikin takaici, ita dai babu abun da zai sa ta yarda da wannan tsintacciyar, sauke numfashi Hajiya Kaka ta yi ta furta, "toh Allah yasa mu dace"......

Ni kam ko bayan da na koma sashin Momy shiryawa mu ka yi mu ka wuce makaranta, bayan mun dawo, ina zune a falon Momyn yaya Sayyid ya shigo, ko da mu ka gaisa ya zauna yana tambayata ina Momy zuwa ya yi ya gaisheta, "laa tana sashen Hajiya Kaka fa, ba ka ganta ba?" Cewata ina kallonsa, wayan cewa ya yi ya ce, "Ban ganta ba da ya ke daga waje na ke ne shiyasa" ya faɗi sannan ya zauna akan kujerar, dama ba wai zuwa gurin Momy ya yi ba, don kawai ya ga Nuriyyah ne.

Dama karatun alqur'ani na ke yi a cikin wayata, don haka na cigaba da kayana. Sayyid kallonta ya ke yi yana murmushin da ya ke ji har cikin zuciyarsa, so ya ke ya yi mata magana, ya sanar da ita ya kamu da sonta, amma kuma kamar ana ci je shi. "Ƙanwata i want to talk to you". 

Tsayawa na yi sannan na juyo ina kallonsa na ce, "ina jinka yaya Sayyid" sai da ɗan shiru ya gifta a tsakani ka na ya ce, "me ki ke karanta a school?" Sai da na yi Jim cikin nishaɗin burina na ce, "doctor!" "wow, zamu samu doctor kenan? Shikenan sai ya zama doctor Sayyid and doctor Nuriyyah", ɗan zaro ido na jin daɗi na yi na ce. "Yaya Sayyid kai ma doctor ka ke son zama?" "Ba ma na ke son zama ba, ni doctor ne", Sayyid ya faɗi.

Murmushin da bai yanke a fiskata ba na ciga da yi ina kallon yaya Sayyid, shi kuma shiru ya yi cikin dauriya ya ce, "kyakykyawar ƙanwata, dama abun da na ke son ce mi ki shine". Maida hankalina garesa na yi sosai da alama abun da ya ke son ce min yana da mahimmanci, Sayyid ya sake cewa, "shine...I'm...i...i...".

"Assalamu alaikum", sallamar Abba ya tsaida Sayyid daga abun da ya ke son faɗa, dukkanmu mu ka juyo muna amsa sallamar Abba. A ɓangaren Abba kuwa wani irin ƙullutu ya ji ya dakar masa ƙirji ko da ganinsu, kamar jiya haɗe fiska ya yi sosai, kamar wanda ba ya dariya. Nima haɗefiskana yi ko da ganin yana son sa ke yi min abun jiya, don ban manta da zafin kalmar da ya faɗa min ba, duk da ba wani babban abu ba ne.

Sai da Abba ya gama kallon Nuriyyah sannan ya juya gun Sayyid da idonsa ke kan Nuriyyahr sannan ya ce, "abokina mu je ko?" Duk da Sayyid ya so ya isar sa saƙonsa amma sai ya tashi ya amsa da toh su ka fice, kamar jiya ma Abba bai san me yasa ya ji rashin daɗin yadda ya ga Nuriyyah ta sakewa Sayyid ba, 'to ma me yasa hakan zai dameni? Mtsewww' ya yi maganar a zuciyarsa yana jan tsaki.


Ni kam gyara zama na yi akan kujerar da na ke zaune, na bi ƙofar da kallo bayan sun fita, "me yaya Abba ya ke nufi da ni ne? Bayan tsokanar ma da ya ke min kuma me yanzu ya ke nufi? Ko ma dai ki share shi Nuriyyah, dama ai ba shiri ku ke ba" na faɗi a fili sannan na tashi nima.

SADIYA.

Tana zaune kusa da Faruq fiskarta ɗauke da tsoro da fargaba, domin tun da ta ji Baba ta kira Faruq sannan yanayinsa ya canza ta san ba lafiya ba, bakinta na rawa ta ce, "Dear menene Baaban ta ce?" Ta yi tambayar da tsoron amsar da zai ba ta. Sai da ya ja numfashi cikin rashin daɗi ya ce, "Baaba ta matsa akan sai na koma kusa da su, har tana faɗa min maganganu marasa daɗi wanda ba ta taɓa faɗamin ba"....


Last page
___________________________________________________

Hehehe, Sayyid fa ya kamu da love ɗin Nuriyyahr mu, sai ga kuma wani yanayi da mutuminmu Abba ke shiga idan ya ga Nuriyyah da Sayyid, hhh to kuna ganin Sayyid zai samu damar fitar da abun da ke rashin kafin ya koma? Shin Abba zai fara gane yana sonta ne tun yanzu ko kuwa sai gaba?.

Hajiya Kaka dai ta koma ɓangaren Momy akan Nuriyyah, ita kuma Mama ta faɗi wasu kalamai akai, to kuna ganin maganarta na wata rana sai sun yarda da ita nan gaba, zai tabbata?

Toh ga Sadiya kuma Baaba ta takurawa Faruq akan su koma kusa da ita, sgin kuna ganin za su koman?.

Mu kasance a next page don jin yadda za ta kaya?




_*🌹𝑍𝑎ℎ𝑟𝑎-𝑡𝑢𝑙-𝑄𝑎𝑙𝑎𝑚🖋️*_