KUNCIN ZUCI

Kuncin zuci

by @bintuuu

Sai da taji tashin motansu alamun sun tafi ta qara sautin kukan nata, sai ta kwanta a kan gadon ta dago hannun nata dake nannade cikin bandage tana kallo bata daina kukan ba, Na'ima tayi kuka ta gode Allah wannan daren, dakyar ta tashi tayi sallah, bayan ta idar ta daga hannu sama cikin kuka tana roqon Allah ya kawo mata dauki cikin lamuranta, nan kan sallayan ta kwanta tana addu'an bacci yazo mata ko zata samu sauqi a zuciyarta, shigowan motan Bilal cikin gidan taji sai ta rufe idonta..
Shikadai ya shigo falon dan a sannan ya nemawa Stella hotel dinda zata zauna kafin ta koma Lagos, dakyar ya lallabata ta amince zata koma din, dakin Na'ima ya bude ya ganta nan kwance a qasa, yace "Bakiji na dawo bane", sanin ba damuwarsa bane ya mata illa yasa Na'ima ta miqe zaune, ahankali tace "Sannu da dawowa" tsuka yayi ya juya ya nufi dakinsa, Na'ima na nan zaune taji kiciniyar sa da akwatin Stella ya fice daga gidan, ranan be kwana a gidan ba, can hotel din shima ya kwana..

Washegari da sassafe Na'ima taji bugun qofan falo, tayi saurin yafa veil akan doguwar rigan jikinta ta sauqa falon, Mami tagani tsaye tareda Al'ameen da Abu, fuskan Mami cike da damuwa ta rinqa kallon hannun Na'iman, iso ta musu suka shigo, bayan sun zauna sai Na'iman ta zauna a kujeran dake nesa dasu, Mami ta dafa gefenta tace "Zo nan ki zauna Na'ima" cikin sanyin jiki ta koma kusada itan, sai ta kamo hannun nata tana gani tace "Sannu kinji, a garin yaya kika yanke da langa langan haka" Abu ya dawo kusada Na'iman shima yana kallon hannun yace "Sannu Anty", hawaye Na'ima taji ya kawo idanunta sai ta duqar da kanta ta fara kuka, rungumota Mami tayi tace "It's okay, ki rinqa kula daughter, Allah ya kare na gaba" shidai Al'ameen sai kallonta yake sanin ba haka zancen yake ba amma besan dalilin da ya sa itada nafisan suka boyewa Mamin ba, da Mamin ta saketa tace da Abu "Dauko flask dinnan a mota" ya gyada kai sannan ya fice, sai a lokacin Mami ta rinqa bin falon da kallo tace "Megidan naki ba ya nan ne?" Na'ima ta amsa da "Eh ya fita", da Abu ya kawo flask din sai Mami ta sashi ya dauko plate, anan falon Mami ta zuba wa Na'ima papper soup din da ta taho mata dashi din, suna dan hira ta saka ta a gaba tanaci kadan kadan, Karan shigowan motan Bilal suka jiyo sai Al'ameen ya juya yana kallon kofan falon dan son ganin mijin Na'iman, because he sense that something is wrong a rayuwan Na'ima, daya shigo falon dan stiff yayi ganin mutanen da bai sani ba, madadin ya qarasa su gaisa sai ya wuce direct upstairs ko sannu bai ce musu ba, Mami ta bishi da kallo da dan mamaki, duqar da kai Na'ima tayi tanajin hawayen takaici na zuwa mata, babu wanda yace komai acikinsu sai can Mami ta kalli Na'ima tace "Nafisa ta fada miki zamu koma Abuja?" Na'ima ta gyada kai kawai, Mami ta cigaba "Ai zaki rinqa kawo mana ziyara ko daughter" nan ma hawaye kawai Na'ima take ta gyada kai, sanyi jikin Mami yayi sai ta kwantar da murya tace "Ki daina kukan nan, zamu rinqa yin waya ai, call me if you ever want to talk to someone kinji" sai sannan Na'ima ta bude baki tace "Toh Mami" da haka Mamin ta fara miqewa su Al'ameen ma haka, har bakin motan nasu ta rakasu, Mami ta sake hugging dinta kafin ta shiga motan, Al'ameen yace "Anty nima kinada number na ai ko" Na'ima tace "A'a amma zance Nafisa ta turamin" ya gyada ahankali yace "Allah ya kare na gaba" sannan ya shiga driver's seat, dago mata hannu Abu yayi itama ta daga nata tana murmushi, da haka Al'ameen ya ja motan suka tafi Na'ima najin zuciyarta na karyewa...
data koma falon sai da zuciyarta ta buga ganin Bilal tsaye, fuskar nan a hade yace "Su waye su?" muryarta na dan rawa tace "Maman Nafisa ce" ya nuna ta da yatsa yace "Idan na sake ganinsu a gidan nan ko banzar kawar kin nan, sai na illataki Na'ima" ta gyada kai tareda cewa "Kayi hakuri", dan tsayawa kallon hannun nata yayi sannan ya juya rai a bace ya koma dakinsa...
Komawansu Nafisa Abuja ba qaramin ta ba lafiyan Na'ima yayi ba duk da tana waya dasu, bata da aiki sai kuka akai akai yanzu kuma, in ta tuna babu inda za taje taji sanyi nan ma sai kuka, gashi Bilal ya dawo mata da sabon uzzurawa, idan bai daketa yau ba to gobe tasani sai ya daketa, kiranta yake da mayya a duk sanda ya daketan, akwai ranar da har allura ya danneta yayi mata dan kawai yasamu biyan buqatarsa, amma Na'ima na kwance kamar ta mutun haka ya kasa tabuka komai akanta, zuwa wannan lokacin Na'ima ta daina magana sai ido, kana ganinta kaga mai cutan depression, haka Bilal zai ta masifa bata iya ko bashi hakurin ma sai hawaye da kuma binsa da ido, in ya daketan ma sai kukan zuci da kuma kallo da ido, qirjinta yayi ta hawa yana sauka kamar me ciwon zuciya..
Ranan wata asabar Bilal yazo gidan da Nasir, dakinta ya shiga ya sameta kwance akan sallaya as usual, yace "Ki fito ki gaisa da Nasir, and cook something quickly" dakyar  ta miqe tareda gyada kai ta gyara hijab din ta sai Bilal ya tsaya kallonta, ta gefensa ta zo ta wuce ya bita da kallo har ta sauqa, Nasir na ganinta ya fara murmushi yace "Sannu Amaryanmu" ci kanka batace ba ta wuce kitchen ya bita da kallo, sai da takawo masa ruwa asannan Bilal yana zaune a falon shima, ciki ciki tace "Ina wuni" bata jira amsan sa ba ta koma kitchen ta fara aikin dafa musu spaghetti, data gama ta kai nan dining ko magana batayi musu ba ta haye sama cikin sanyin jiki Bilal ya bita da kallo, sai dare Nasir ya tafi...
Amma abun mamaki..Washegari bayan Bilal ya fita sai ga Nasir a gidan, da Na'ima ta bude kofa suka hada ido sai ya fara mata murmushi, juyawa tayi adan tsorace ta koma falon ya biyota ciki tareda cewa "Bazaki min iso ba amaryarmu" tace "Sannu da zuwa" sai ta wuce kitchen ta dawo hannunta riqe da ruwa, kafin ta ajiye akan glass table din sai ya kamo hannunta, a firgice ta kwace tayi baya sai ya miqe yana kallonta yace "I'm here to save you Na'ima, trust me" juya kanta tayi gefe tace "Banaso" bai bar kallontan ba yace "Trust me, zan rabaki da Bilal but i need only one thing in return" sai sannan ta kallesa ta sake cewa "Ka fita Dan Allah" ganin ba fahimtarsa zatayi ba yasashi fara kokarin kamota sai tayi saurin daga riganta ta ciro qaramin wuqa, a firgice ta nunashi da wuqan tace "Ka fita ko in caka maka" ganin yanda hannunta ke rawa yasa Nasir yin murmushi yace "Okay" sai ya juya ya fita, yardar da wuqan tayi hawaye na kawowa idonta ta yi saurin saka key a kofan falon...
Dawowan Bilal ya rinqa banging kofan jin ta a kulle, cikin sauri taje ta bude masa beyi wata wata ba ya dauke ta mari yace "Banyi warning dinki akan rufemin kofa ba" tana dafe da kumatun nata tace "Kayi hakuri" yace "Ub*n meyasa kika kori Nasir a gidan nan dazu da yazo nemana" da mamaki Na'ima ke kallon Bilal, ransa a bace yace "Ki bani amsa before i wound you, gidan ub*nki ne nan din" ta girgiza kai tace "Ban kores..." sai ya sake dauketa da mari yace "Dama na lura da karban da kika masa jiya, yaushe raini yafara shiga tsakanina dake Na'ima?" Ta sunkuyar da kai batace komai ba, ransa ne ya qara baci na shirun da tayi kawai ya finciko gashinta ya jata cikin falon, jefa ta yayi nan tsakiyar falon yace "Zan sauke miki rainin da kikeji dashi ne Na'ima" tana kallonsa ya fara kiciniyar cire belt dinsa, sai ta kwanta kan tiles din hawaye na kawowa idonta tana jiran saukan dukan a jikinta...

Kwance Na'ima take kan gadon dakin ta fuskanta yayi jaa sosai saboda kuka, miqewa tayi ta nufi madubin dakin ta bude drawer, razor ta ciro tana kallon kanta a madubi, sai ta kai hannu ta tattaro gashinta da nufin yankewa, tsayawa tayi tana kallon kanta a madubin sai ta jefar da razor din ta dafa mirrorn tana kuka, sake bude drawern madubin tayi ta dauko takardar da Nafisa ta bata wancan ranan, by then ta riga ta haddace address din a kanta, juyawa tayi ta nufi wardrobe din ta, ta janyo akwati sannan ta fara ciro kayanta tana zubawa aciki har sannan bata daina hawaye ba, bayan ta gama hadawa sai ta zauna tana kallon akwatin zuciyar ta na tsinkewa, jitayi an bude kofan falon sai ta miqe da sauri ta saka akwatin cikin wardrobe ta fita, dasakarewa tayi a bakin stairs ganin Nasir tsaye falon yana mata murmushi yace "Hi Na'ima" juyawa tayi da gudu ta nufi dakinta ya biyota da gudun shima, kafin ta saka key a kofan ya banko ya shigo yana cewa "What is wrong with you Na'ima, inason in miki abunda dolon mijin ki yakasa miki shine kike guduna" jikinta na rawa tace "Dan Allah ka fita, ka rufamin asiri dan girman Allah" yana kallonta kamar tsohon maye yace "Kin dai ga matsayina a gurin mijikin jiya ai ko?..to ko ki nutsu ko yau ma hakan ta sake faruwa" sai ya fara takowa gareta tayi baya, cikin kwantar da murya yace "Na'ima i won't hurt you, wallahi tun ganin farko dana miki nake sonki, bazan cutar da ke ba i assure you" a wannan lokacin kan Na'ima kullewa yayi ta rasa ma ta ina zata fara kubuta daga hannun wannan azzalumin, addu'a kawai take jerowa a zuciyarta sai ta nufi toilet da gudu, da sauri Nasir ya kamota ya dauketa, kiciniyar kwace kanta ta fara sai taga ya kwantar da ita anan kan gadon, kokuwa suka farayi Na'ima na kuka, beyi wata wata ya yaga rigar jikinta, white padded bra din ta ya bayyana, a daidai wannan lokacin Bilal ya turo kofar dakin ya shigo duk suka juya suna kallonsa, daskarewa Bilal yayi nan tsaye yana kallon Nasir dake kan Na'ima a gadon, saurin miqewa Nasir din yayi alamun tsoro ya bayyana a fuskarsa ya dan qarasa gurin Bilal din yace "Listen man...she wanted it" naushi Bilal ya kai masa saida yakai qasa, ya sake binsa yana kai masa duka ta ko ina, miqewa Na'ima tayi akan gadon ta gyara riganta tana kuka da qarfi ta rasa me ma zatayi a wannan lokacin, da Nasir yaga Bilal na neman illatashi sai ya samu dakyar ya miqe ya hankada Bilal din ya fita falo da gudu, bin bayansa Bilal din yayi kafin ya riskeshi ya fice through kofan gate, komawa cikin gidan Bilal yayi yana wani irin huci kaman zaki, Na'ima da zuwa sannan ta biyosu falon taga ya shigo yana huci, kafin tace komai Bilal yasa kafa ya kwasheta ta fadi nan kan tile goshinta ya fashe, da kafa ya rinqa harbin cikinta yana huci yana cewa "F*ck you Na'ima..Damn you...kin hanani kanki zaki baiwa wani" dukanta kawai Bilal keyi kamar ba mutum ba, tun Na'ima na gani har komai yazama duhu a idanunta, sai sannan ya fincikota bai bar hucin ba yace "I'd rather kill you akan wani ya sameki" gani yayi Na'ima tayi luuuu kamar babu rai a jikinta, jijjiga ta yayi still yaga bata motsi, ai da sauri ya azata a kafada ya nufi compound din gidan da ita, hankali a tashe yasata a mota sai asibiti, yana driving din ya dauko bottle water ya tittila mata a fuska duk da haka bata motsa ba, the same asibitin da ya kaita rannan ya sake kaita yau ma, amma likitocin emergency sukaqi karbanta akan sai Bilal yazo da takarda, sa'a yayi Amina ta shigo part din, ganin Na'ima kwance yasata tabi bayan likitan, ba'a dau lokaci ba tadawo tasaka Bilal din daukan Na'ima ya shiga da ita, sai azahar Na'ima ta farka nan ma suka mata alluran bacci ganin yadda duk ta galabaita, da suka kaita dakin da zata huta, sai Bilal ya tsaya nan bakin gadon yana kallonta fuskanta da duk ya kumbura, juyawa yayi ya fita zuciyar sa na quna, sai yamma yadawo dakin, zuwa sannan Na'ima ta farka har Amina ta sake bata kaya ta saka ganin na jikinta a yage, ita kadai ya samu a dakin dan Amina ta fita wani aiki lokacin, ta dago fuskanta tana kallonsa idonta daya yayi suntum, gefen bakinta duk ya kumbura, yanayin fuskan nata duk me imani in ya kalleta sai ya ma ta hawaye, qarasowa bakin gadon yayi yace "Ki fadamin dalilin da ya kai Nasir dakinki" sai ta sauqar da kanta tana hawaye batace komai, ganin bazata amsa ba yasa shi juyawa sai tayi saurin riqo rigansa tana kuka sosai tace "Dan Allah, Dan Allah ka sakeni Yaya, mutuwa zanyi in na koma gidanka" tsayawa kallonta yayi sai yace "Qauyen zaki koma" tayi shiru ya sake cewa "I'll give you space Na'ima, but kisani duk inda zakije you'll come back to me, And i'll be waiting, kije qauyen mugani" bai dena kallonta ba ya sake cewa "Kije na sakeki saki DAYA" fashewa tayi da kuka me qarfi, Amina da ta shigo a lokacin tayi saurin cewa "Amma baka da imani kai dinnan, a gadon asibitin zaka mata wannan sakamakon" kusan bangajeta Bilal din yayi ya nufi kofa, tana hawayen ta qaraso gurin Na'iman tace "Ina iyayenki ne wai Na'ima" bata daina kukan ba tace "Dan Allah ki aramin kudi zan je gida" Amina na kallonta tace "Meyasa bazaki fadamin abunda ke faruwa bane Na'ima" sai tayi shiru bata daina kukan ba, Amina ta sake cewa "Dubu shida ne dani a account dina yanzu haka, zai kaiki gidan kuwa" Na'ima tayi saurin gyada kai, sai tace "Bari na ciro miki cash amma tukunna ki bari sai kin gama karban treatment dinki sai ki tafin" nan ma gyada kai kawai Na'iman tayi, fita Amina tayi taje ta ciro kudin sannan ta kawo mata, bayan ta karba tayi godiya sai Aminan tace "I'll settle the bills, amma yanzu ki jira muga yanayin jikin naki tukunna" Na'ima ta gyada kai, fitan Aminan taji zuciyarta na zafi ta dafa hannunta a wajen tana kuka, kawai takai hannun ta cire drip din ta miqe dakyar ta fice daga dakin, cikin sa'a bata hadu da Aminan ba ta fice daga asibitin, lokacin da fitan gari ya fara duhu amma magrib batayi ba, haka ta tari mashin tace ya kaita tashan da zata samu motan zuwa Abuja, da ta isa tashan sai ta nemi inda ake saida face mask dan daman hijabin jikin nata ta janyo har gurin hancinta, bayan ta siya ta nufi gurin motocin amma sai yaron motan yace mata kudin ta baze kai ta shiga motan ba, cikin sanyin murya tace "Ka taimakamin Dan Allah" yace "Yayata ga Daf can ta lodo kayan kamfani , itama Abujan ta nufa, kije ki biya dubu ukun ki zasu kaiki, ga mata can suna hawa ai" ya qarasa magana yana nuna mata Daf din ta juya tana kallon yanda mutane ke hawa bodin harda mata...
Haka ta biya kudin Daf din wani ya taimaka mata ta hau bodin ta samu guri gefen wata mata ta zauna, a wannan lokacin Na'ima ji take ko keke akace tahau ya kaita Abujan zataje...da magriba suka kama hanya, iska kam sun shata a Express way dinnan amma haka ta jure tanajin kamar bazasu isa ba, karfe biyun dare suka isa saboda gudun da motan tayi dan saurin isar da kayan da ta debo kar su baci, da sauran 2k din jikin nata ta tari taxi ta fada masa address din gidansu Nafisa, sai karfe uku taxi din ya sauketa a kofar gidansu Nafisan, ta daga kai tana kallon babban gidan nasu dayafi na Kano alatu, Hawaye ne taji ta kawo idonta ta nufi gate din tafara knocking a hankali, tayi knocking yafi a qirga kafin megadin ya fito cikin magagin bacci yana kallonta yace "Daga Ina?" rasa abunda zata ce tayi ganin haka ya sake tambayanta, tace "Gurin Nafisa nazo" sai yace "Kece wa?" tace "Sunana Na'ima", ce mata yayi ta tsaya sannan ya shige cikin gidan, bin layin tafarayi da kallo ganin ko ina gidan arziqi ne da wuta tas, can aka bude gate din Nafisa ta fito tareda Faruk, sai ta dan tsaya tace "Na'ima?" sauqe face mask din fuskanta Na'iman tayi, ai da gudu Nafisan ta taho ta rungumota ta fara kuka, sai sannan Na'ima ta fashe da kuka itama, Faruk sai kallonta yake yakasa magana, sai Nafisa ta dago tana kallon raunukan fuskan nata tace "Muje ciki" ta kama hannunta suka shiga, a nan compound suka ga Mami da Abba sun fito suma, Mami da saurinta ta qarasa ta kamo Na'iman, ganin raunukan fuskanta yasa Mamin ta fara hawaye tace "innalillahi wa inna ilaihi rajiun" sai kawai ta rungumeta sosai a jikinta, Abba ya dafa bayan Na'iman shima, Faruk har lokacin was in shock to see Na'ima like this..kuka Na'ima ta rinqa yi a jikin Mami, Nafisa na shafa bayanta tana kukan itama, sai can Mamin ta saketa tareda kama hannunta suka shiga cikin gidan Abba da Faruk din suka rufa musu baya....