Kuncin zuci
by @bintuuu
Shigansu falon ganin yanayinta yasa Abba cewa "Ku shiga da ita ta huta tukunna" haka Mami ta riqe hannunta suka nufi falonta na sama itada Nafisan while Abba da Faruk suka bisu da kallo zuciyarsu babu dadi...
Ruwan wanka mai zafi Nafisa ta hada mata a toilet din sannan ta fito hannunta riqe da babban towel ta samesu har sannan zaune a bakin gadon Mamin na shafa fuskan Na'iman, sai Mamin ta miqe tace "Ki shiga kiyi wanka Na'ima Ina zuwa" bayan fitanta Nafisa ta miqa mata towel sai Na'ima ta dago kanta tana kallon Nafisan, hawaye Nafisa ta fara sai ta zauna nan bakin gadon ta riqo hannun Na'iman tace "Wallahi he'll pay for this, tun a duniya zasu ga sakamako daga shi har uwarshi" ga mamakinta sai taga Na'iman na hawaye kuma tana murmushi , ahankali tace "Ya sakeni Nafisa, ya sakeni dai" Nafisa was shocked at that moment sai ta rungumota suka rinqa kuka hade da dan dariya tace "Alhamdulillah..Alhamdulillah"
Da Na'ima tayi wankan tayi sallah sai Mamin ta shigo hannunta riqe da cup da kuma plate me dauke da fried egg da slices na bread, dora mata tayi anan kan gadon tace "Kici wannan sai kiyi bacci Habibti" karban plate din tayi ta sauqo daga gadon amma ta kasa ci, dakyar suka tusata taci kadan sannan ta kwanta nan kan gadon Mamin, Nafisa ta rage Ac na dakin sannan Mami ta ja mata blanket suka fita, da farko tunani ne ya hana Na'iman bacci amma da yake ta debo gajiya sosai na mota sai baccin yazo mata babu jimawa..
Sai bayan anyi sallan asuba Mami ta leqota taga har sannan tana bacci, bata tada ita ba ta juya ta fice daga dakin, Falon Abba ta nufa ta iddasa tareda da Nafisa, Faruk, Al'ameen amma banda Abu, fuskanta a hade ta zauna a gefen Abban tana kallon Nafisa, ganin haka sai Nafisan tayi saurin cewa "Wallahi Mami nasha attempting fada muku abinda yake faruwa da ita amma ta hanani, daga baya ma daina fadamin matsalan nata tayi sai in ni na jata da hira" Faruk yace "To in da ta mutu fa?..sai kice da kinsani kenan" hawaye Nafisa ta fara tace "Kuyi hakuri" sai sannan Abba yace "Fada mana meya faru da ita har aka zo gandun nan"...A sannu Nafisa ta fara basu labarin tun farkon zuwanta gidan Na'ima da ta hadu da Bilal din, wani gurin in ta fado abunda ya farun sai Mami ta riqe kai tana fadin "Hasbunallahu wa ni'imal wakil" , Abba ma sauraronta yake cikin tsanaki yana gyada kai, zuwa sannan Nafisa kuka take tana maganan, Faruk sai shafa fuskansa yake zuciyarsa na tafasa, da Nafisa ta fada musu faduwanta akan glass dinnan har taje qauye Mami was more than shock, jikinta har rawa yake tana cewa "Wallahi sai munyi shari'a dasu, duk inda za'a je sai auren nan ya rabu, wannan ba 'yan'uwan ta bane sam" ganin yanda jikinta yake rawa yasa Abba dan riqota yace "Nima zan so hakan Fatima, amma let's focus on sanity din Na'ima first, the girl was broken beyond pieces" kuka Mami fashe dashi tace "Kashe ta suka so yi, kashe ta suka so suyi wallahi" Al'ameen ma sai hawaye, Abba na dan shafa bayan Mamin yace "Mu gode Allah da basu yin ba" Mami ta dago tace "Irin wannan uquban, da tayi suicide fah? kai innalillahi" rai a bace Faruk yace da Nafisa "Wai waye mijin nata ne?" sai sannan Al'ameen yace "Wani ne me zubin mahaukata haka, dan qwaya inka ganshi" Mami tace "Ni tun ranan da mukaje na kallesa hankalina yakasa kwanciya da lafiya Na'ima ke zaune gidanta" Nafisa na share idonta tace "Ta fadamin ya saketa jiyan" Abba ya gyada tareda cewa "Good..saki nawa yayi mata?" ta amsa da "Bata fadamin ba" Mami tace "Ai ko beyi sakin ba wallahi it's over, balle ma yayi" ta sake cewa "Jeki dubo ta ko ta tashi zuwa yanzu" miqewa Nafisa tayi cikin sanyin jiki ta fice daga falon sai Abba ya dauki wayansa yayi kiran doctorn sa da zai zo duba Na'iman.......
Daren ranan bayan isha, Hajiya na zaune a falo tana danna waya Bilal ya shigo, kallonsa ta tsayayi ganinsa adan birkice idonsa ya kada kamar wanda ya zuqi wani abu, tace "Ya dai babana, daga ina haka?" ko gaishe ta beyi ba yace "Abani abinci yunwa nakeji" sai ta kwala kira a shafa, cin abincin Bilal ya rinqa yi babu qaqqautawa, gani haka yasa Hajiyan dake kallonsa cewa "Yau matar taka bata maka abinci bane Babana" sai ya ajiye cokalin yace "Na saketa" cikin shock Hajiya tace "Eh?" cigaba da cin abincin yayi yace "Dazu a asibiti tace in saketa, bansani ba ko ta tafi qauyen by now" Hajiya dake cikin shock har sannan tace "Kai mahaukacin inane da kawai dan ta nemi sakin sai kayi batareda ka fadamin ba, Bilal bazaka barni in huta ba kai kullum" jefa cokalin yayi cikin plate din cikin bacin rai yace "Da Nasir na kamata fa a dakinta" cikin masifa Hajiya tace "Wannan dan iskan abokin naka ko ni in da hali bazai haikemin bane, toh wallahi tun wuri ka maida matar ka shine rufin asirinka, babu me iya zama dakai sai itan, kai kasan kokarin da nakeyi akan tsakaninta da Alhaji kuwa? an fada maka da lafiya qalau ne Alhaji zai zuba ido kana mistreating din ta ne, kana tsammanin nida kai din zai bar mu ne?" qoqarin miqewa Bilal ya fara yana cewa "Gaskiya bazan maida ita ba, i don't even want to see her now" sai ya nufi upstairs zaije dakinsa, da sauri Hajiya ta bi bayansa, anan falon saman ta kamo hannunsa tace "Toh kar ka sake ka fadawa mahaifinka ka saki yarinyar nan in ya dawo daga tafiyar nan" gyada kafada yayi ya shige dakinsa, a daren Hajiya ta tambayi Bilal address din asibitin, da taje bata samu Na'ima ba sai ta wuce gidan Bilal din nan ma megadi ya fada mata babu kowa gidan, bata yarda ba saida ta shiga cikin gidan ta duba, da ta koma gida sai tayi deciding zuwa washegari zata kira Ayuba taji ko Na'iman na can, aikuwa washegarin da sassafe ta kirasa amma sai bata tambayesa Na'ima ba tana jiran taji ko zai mata maganan, sai taji har tambayan ta lafiyan Na'iman yake, nan hankalinta ya fara tashi kuma, Bilal kuwa the following day ya hada ya nasa ya nasa ya tafi Lagos ko sallama beyi da uwar tashi ba...Hajiya na cikin tararradin lamarin Alhaji yadawo gari, bata fada masa a ranan ba sai washegari da safe suna breakfast, farko cewa yayi "Whattt? Bangane ta gudu ba?" Hajiya na hawayen makirci tace "Kamata yayi da qato a daki, kuma da ta tashi guduwan bata nufi Adamawa ba, sai Allah kadai yasan inda taje" cikin tashin hankali yace "Da namiji kuma, anya kinsan me kike fada kuwa Ladi" kuka ta fara tace "Zan mata sharri ne Alhaji, Na'iman nan dai nima 'yata ce, riban me zanci in nayi karya akanta, halin dan yau kawai ta nuna mana, shiyasa bahaushe yace in kaga mutum a rana kawai ka barshi, dame muka ragi Na'ima fisabilillah" sanyi jikin Alhaji yayi yace "Toh yanzun da ta tafin, sakinta Bilal din yayi" ta girgiza kai tace "Shima nemanta yayi ya rasa" yace "Shine baki kirani kin fadamin ba Ladi, wai meyasa a yawancin lokuta kikeson aiwatar da abu gashin kanki ne, Bilal din ya bada cigiyanta ne yanzu?" Tace "Toh ta Ina zamu fara cigiyanta ita ba qaraman yarinya ba, badai duniya bace, taje ta isheta riga da wando, munanan zata dawo ta samomu" ..Kiran Bilal din Alhaji yayi yace duk inda yake ya dawo yanason ganinsa, daga Toh dinda ya amsa kuma sai kashe waya, iyayen sukayi ta kiransa basa samunsa har suka haqura suka zubawa sarautan Allah Ido..da aka kwana biyu sai Hajiya tace yakamata ya kira Ayuba ya fada masa dan sunada hakkin sanin abunda Na'ima tayin, magana dai da taje kunnen Ayuba sai da ya tsinewa Na'ima ranan Alhajin na bashi hakuri, sai magana taje cikin gidansa, sannan gidan Nasiru da iyalinsa, kai har yan uwan nesa sun ji labarin Na'ima ta shiga duniya bayan duk Alkhairyn da su Alhajin suka mata, babban abun ma shine mijinta ya kamata da abokinsa a daki daya, duk yanda Alhaji yaso Bilal din ya dawo qi yayi dan daga baya ma ji sukayi ya koma China...
Rayuwan Na'ima gidansu Nafisa har sannan dai gatanan ne, yau tayi walwala kadan, gobe ta wuni cikin kunci tana kuka, lokacin da Abba ya kirata ta masa bayanin abubuwan da suka faru kasawa tayi saboda kuka, hakan ya famo mata abubuwa da dama a zuciyarta, sai cikin hira da lallami Mami ke sanin abubuwan da suka farun a sannu, Ahalin gidan suna iya kokarinsu na ganin sun kyautata mata, har rige rigen kyautata matan suke, kowa nason ganin ya saka murmushi a fuskanta amma abu ya ci tura, dakyar Na'ima ta fara fita falon gidan ana hira da ita, gashi nan dai ta warke sosai amma wannan kuncin har sannan yana tare a zuciyarta, Mami da Nafisa duk sun shiga damuwan ganinta hakan, ganin haka Abba yayi shawara da Mamin batun kaisu makaranta itada Nafisan ko karatu zai debe mata damuwan, dan sosai Na'ima tayi sanyi kamar ba ita ba, watarana haka zata rinqa kuka cikin dare ita kadai tanajin zuciyarta babu dadi, gashi dai bata dana sanin tahowan da tayi amma har sannan zuciyarta ta kasa samun nutsuwa...da Abban ya kirasu ya fada musu zai nema musu gurbin karatu a oxford, Na'ima taji dadi na cewa zata bar qasar, and she can't wait for a fresh start in England....Faruk da Nafisa ne suka je Kano karbo results din nasu ita da Nafisan, daman tun kafin su tafi Abban yayi waya sai basu sha wahala ba.....
Sai da Bilal yayi 8 months a China kafin ya dawo gida, wanda sai da Alhajin da Hajiya sukaje, dawowan ma a firgice yayi ta dalilin wani bala'i da ya fada masa, aka wayi gari an sace Stella a qasar kuma duk wani zargin batan nata is pointing directly at him, sai da aninan Alhaji suka kai qasa sosai kafin ayi belin Bilal, wanda dawowarsa qasar ne ya fara neman Na'ima ido rufe, kuma sai a sannan yace da Hajiya zai maida auren nasu, murmushi kawai tayi a lokacin tace "Kayi latti Bilal, ai danace ka maida ta tun farko din ka dauka ban san me nakeyi bane? ni banason ta dawo ma, Yanda ta dau lokaci har haka ma ka hakura da itan kawai, dan zuwa yanzu bariki ta zauna mata sosai" be ce komai ba Hajiyan ta cigaba "Dan ni bansan ya zanyi ba in yarinyar nan ta dawo yau, na dawo daga rakiyarka Bilal, gwara ma ka fada masa nima baka fadamin batun sakin ba duk ranar da Na'iman ta waiwayi gida, dan ko jahili yasan babu aure a tsakanin ka da Na'ima yanzu"....
Bilal bai hakura ba ya cigaba da neman duk wata hanya da zai same ta, har Abujan yaje bayan ya samo address din gidansu Nafisa amma baiga alamun Na'ima na rayuwa a gidan su ba, sai after a month ya samo link na cewan Nafisa na tare da Na'iman suna karatu a Oxford amma kuma ya rasa in da zai samu direct contact din Na'iman, sai ya fara bibiyan Nafisa sosai, handles dinta na social media kowanne bi yake yana neman ta inda zai ga ko da wani qaramin clue da zeyi Linking dinsa to Na'ima..A ranan da ya tabbatar da inda suke zama a London ne ya turawa Nafisa message through Instagram dinta, ranan kuma be kwana a Nigeria ba yayi booking din jirgi sai london, he spend weeks going to their apartment before that fortunate Day da Na'iman tazo diban kayansu....
Toh Jama'a....Menene manufar dawowan Bilal cikin rayuwan Na'ima?
Shin Bilal yana da tabbacin Na'ima zata dawo garesa da duka this time around?
Shin me Ahmad zeyi bayan yaji abubuwan da suka faru a rayuwan sanyin idaniyan tasa?
Wane mataki ze kai na ganin ya kawar da duk wani qalubalen da zeyi masa katanga da Na'ima?
Shin kuna ganin wani gumurzun ne zai faru da Na'ima tsakaninta da Laila kaman yanda ta sha fama da Stella?
Menene manufar Faruk akan Na'ima?
Ku biyo ni Bintu Musa, zan warware muku komai a sannu..
Karku manta nace "A Love that stood a chance amidst chaos ko" Toh yanzu soyayya da ruguntsumin zasu soma....
Vote and follow my account please