2
*KOMAI YAYI FARKO...*
Na
©®Rahma Kabir MrsMG.
Page 2.
Sarac Stars R Pen...✍️
Bayan mamaki daya cikani, tsoro ma ya samu nasa gurbin, dan ba ƙaramin fargaba na shiga ba, da tunanin waye ne yake so ya kashe mini aure dan nasan duk mutanen dana sani 'yan makarantarmu dama waɗanda muke gaisawa a hanya sun san nayi aure, shiyasa na shiga kokwanto akan anya an kirani kuwa.? amma ba zan iya ƙaryata Umar kai tsaye ba duba da na yarda da shi kuma bai dace a zuwan farko nayi masa musu ba, shiyasa nayi shuru da maganar ban ƙara cewa komai ba, na tashi jiki a sanyaye nayi masa sallama na wuce, ya amsa ba tare da nuna wata damuwa ba wanda hakan shi ne ya saka naji kwarin guiwar tafiya. Sai dai na kasa samun sakuni saboda nasan lokacin da nake gida ba ni da samari da yawa, bana kula su domin akan haka aka ɗaura ni har zuwa girmana, ni tsoron samari nake yi sosai saboda ban samu fuskar tsayawa dasu ba, zan iya cewa samari biyu na yi a rayuwata wanda suka iya fitowa suka nuna suna sona a zahiri, sai dai duka babu wanda na samu damar yin soyayya da shi, dan na farkon ma ɗan islamiyanmu ne mai suna Aminu, Kuma a dalilinsa sai da mama ta zane ni ta kuma saka baba ya sauya mini makaranta, Aminu bai haƙura ba ya turo iyayensa niman izini dan da gaske sona yake yi da aure, kuma nima ina sonsa sosai amma sai mama ta zuga baba ya yiwa iyayensa wulaƙanci yaki amsar maganar suka tafi rai a ɓace, dalilin haka yasa Aminu ya ja baya da ni ya haƙura, kuma ba zan mance irin ƙalubalen dana fuskanta ba akan Aminu dan babu irin zagin da mama bata yi mini ba, har cewa tayi yawon iskanci nake zuwa yi ba makaranta ba, sannan ta saka ƙannena su saka mini ido ko zan riƙa kula shi a hanya, bama shi kaɗai ba duk wani saurayi da zai kula ni su faɗa mata, hakan kuma ya ƙara haddasa rashin jituwa a tsakanina da Ƙannena dan ƙanwata Sakina wannan damar data samu sai ta riƙa haɗa mini sharri a gurin Mamanmu, ita kuma babu bincike ta riƙa yi mini faɗa da zagi ko ta haɗa da duka. Dayan saurayina kuma wani ne mai suna Tukur da ya nuna mini so kamar me, amma dole na rabu dashi saboda gujewa ɓacin rai iyayena tunda sun nuna basa so, duk da naso Aminu sosai dan ba ƙaramin shiga raina yayi ba, amma dole na haƙura da shi. Da wannan tunanin na shiga makaranta jikina ba kwari amma ganin ɗalibai a gabana dole na yakice komai na soma gabatar musu da karatu dan bana yarda na haɗa komai da koyarwa, dan nasan muhimmancin ilimi, shiyasa shugaban makarantar yake matuƙar girmama ni duk da ƙaramin shekaruna, saboda ina yin aikina yadda ya kamata.
****
Bayan na dawo gida wajen ƙarfe biyu da rabi, na aje jaka tare da rage kayan jikina na fito falo na shiga kitchen dan ba ƙaramin yunwa nake ji ba, shiyasa cikin sauri na ɗaura ruwa a gas na fara kiciniyar yanka albasa dan ita kaɗai gare ni shima anyi mini gararsa da yawa, na ɗaura sanwar indomie ina tsaye a gun dan na ƙosa ta dahu naci saboda yunwar da yake damuna, a haka naji sallamar Umar, sai na leƙo Falon da mamaki fal a fuskata, na saki murmushi ina amsa masa sallamar tare da yi masa sannu da zuwa ya amsa da.
Yauwa madam kin dawo kenan.?
Wlh kam na shigo, indomie nake dafawa, amma lafiya na ganka ka dawo da wuri.?
Ƙalau, nima yunwa ce ta dawo dani amma bana abinci ba.
Ya ƙare maganar yana ɗaga mini gira, sai na saki murmushi ina cewa.
To yunwar me yake damunka in ba na abinci ba, dan na ganka ba yadda kake, bari na ƙara sanwar indomie sai mu ci tare.
A'a ni a ƙoshi nake dan daga gidanmu na fito, ki sauke indomie ɗin ki zo ciki dan gaskiya a buƙace nake dake.
Ya ƙare maganar yana miƙewa ya shiga uwar ɗaka, sororo nayi ina kallonsa har ya shige mamaki ya gama cika ni, wai da rana tsaka yake wannan maganar.? sai na koma kitchen ɗin na rage gas na fito nabi bayansa dan ina buƙatar ƙarin bayani saboda ban gama fahimtar inda ya dosa ba. Ko dana shiga na same shi ya cire kaya yayi ɗai-ɗai a gado yana kallona.
Wai dan Allah da gaske kake yi ne ko wasa.? naga yanzu ma ukun rana ake magana, ni wlh kunya naji.
Ki aje kunyar nan dan babu haramci, kuma ki daina ɓata mini lokaci.
Ya ƙare maganar cikin gimtse fuska, ganin haka yasa na aje wasan nace masa.
Bari na kammala indomie naci wlh ba ƙarfi a jikina.
Farida ina wasa dake ne, bana son raini, ki zo yanzu idan kuma kin yarda Mala'iku su tsine miki Bisimillah.
Hmmm kawai na iya faɗa na koma kitchen na kashe gas na dawo uwar ɗaka, na zame kayana na ɗaura fallen zani na hau gadon zuciya a takure sam babu daɗi, na fahimci Umar kansa kawai ya sani bai damu da duk halin da zan shiga ba matsawar buƙatarsa zata biya. Haka ina ji ina gani na zama tamkar gunki ya gama biyan buƙatarsa ya sauka ya shiga toilet na bishi da kallo hawaye yana cika mini ido, har yau na kasa sabawa da wannan abun, haka na miƙe jiki ba ƙarfi dan har wani jiri nake gani saboda azabtar yunwa, na ɗaura zani wanda a lokacin Umar ya fito yana dubana.
Ina zaki je.? Ai bamu gama ba saura ɗaya.
Kallon ƙasa-ƙasa nayi masa idanuna suna kawo ruwan hawaye, ga kirjina da yake yi mini katsa mai zafi alamar ulcer na ya motsa, jikina yana ɗan rawa kaɗan na ce cikin dakiya.
Dan Allah ka bari naci abinci, yunwa nake ji.
Cin abinci da najasa a jikinki, kina dai so ki ɓata mini lokaci ne kawai amma ba zamu wuce minti biyar ba zuwa shida, Haba Farida ya kike abu kamar ba wayayyiya ba.
Ya ƙare maganar yana zama a gefen gado, ban iya ce masa komai ba na nufi gadon jiki a saɓule na zauna, sai ya jawo ni jikinsa yana shafa mini suma, daga haka ya lallaɓani ya sake sauke mini wani gajiyar, kaina har ciwo ya fara yi mini ina ganin dishi-dishi, ya mike ya bar ni a kwanci ina zubda kwalla wanda bana zafin da jikina yake yi mini bane sai na mahaukacin yunwa da nake ji, dan kamar ya kwashe mini hanjin cikina nake ji, ina kwance ya yi wanka ya fito yana goge jiki.
Ki tashi ki yi wanka kar la'asar ta wuce ki dan an soma kiran Sallah.
Hmmm nace masa na yunƙura da kyar na sauko na ɗaura zani na shiga bayi a dudduƙe saboda bazan iya tafiya a miƙe ba dan yunwa, shi da yace ba zamu wuce minti biyar ba sai gashi mun ɓata kusan rabin awa ana abu guda, na sharce hawayena na cigaba da wanka tare da gasa jikina sosai, na ɗan ji dama-dama dan haka na fito na zura doguwar riga na koma kitchen dan samawa kaina mafita, haka naci wannan indomie ɗin ban tsaya ɗunɗumawa ba, bayan na gama na kora da ruwan sanyi kafin na dawo falo ma gabatar da Sallah, dana idar ina bisa kan sallaya Umar ya dawo daga masallaci ya kalleni yana gyara links ɗin hannun rigarsa.
Ni zan fita sai na dawo.
To a dawo lafiya, amma me zan dafa Kaga jiya shinkafa muka ci da mai da yaji, wlh ni na gaji da cin abinci da yajin nan ina tsoron ulcer ɗina ya tashi, ka siyo mini kayan miya mu dafa ko taliya da miya ne, idan mun samu kifi ko nama duk ina so.
Na ƙare maganar cikin zolaya, ya kalleni yana taɓe baki yace.
Hmmm kukan jin daɗi kike yi, amma wata ma abincin da kike ci take nima ido rufe, dan haka ki dafa abunda ya samu.
Yana gama faɗar haka ya juya ya fice, girgiza kai nayi ina mamakin wannan lamarin, ace ayi ta cin abu ɗaya ba sauyi, ni dai na gaji, daga shinkafa da wake da mai da yaji sai farar taliya da mai, ko ɗan waken semo, shi kenan girkin dana ke yi ko indomie, aiko ya dace ace na sauya girki dan wlh har marmarin miya nake yi dan tun satin farko da aurenmu rabon da na ci, da ina da kuɗi tabbas da sai dai ya dawo yaga na girka abunda nake so. Na sauke numfashi ta miƙe ina naɗe dadduma nace a fili.
To Allah ya kyauta.
Kana na aje sallayar na koma kitchen Dan na haɗa ɗanwaken semo.
.....
A haka tafiyarmu ta soma miƙawa har muka cika wata guda da aure, abubuwa suna daɗa sauyawa wanda a farko ina tunanin zai gyara amma abu sai gaba yake yi, ya zamana kusan kullun Umar sai ya dawo da rana ko da yamma ya kusance ni sannan hakan ba zai hana shi cikin dare ya ƙara nima na ba, sannan da asuba ya ƙara, a hankali ya soma mayar dani sex machine, gashi ni kuma na kasa sabawa duba da babu wani gamsuwa dana ke samu face shan wuya, sannan ga bana cin abinci mai kyau dan ya tabbata Umar ba irin mazan nan bane masu jure cefane, dan ƙiri-ƙiri ya mayar da abincinmu komai da mai da yaji, Allah yasa ma anyi mini garar yaji mai yawa dan 'yan uwa babanmu da suka zo daga Shanono ne suka haɗo mini shi, sannan a dai-dai wannan hali da nake ciki gas ɗina ya ƙare dama daga gidanmu ne aka cika mini shi, Kuma daya ƙare Umar ya nuna bai da halinsa, sai yaje ya ciko galam da kalamzir na zuba a risho ɗina na fara amfani da shi, gashi tukunyar gas ɗina har biyu amma Umar bai da niyyar zuba mini gas, kuma ikon Allah ba aje ko ina a shima kalanzir ya ƙare, sai ya zamana in ba wutar nepa ne suka kawo wuta ba, to bani da abun yin girki, dan duk saurina akan na yi girki da wuri to sai dai na haƙura har sai in nepa sun kawo wuta kafin zan dafa abincin a electric ko rice cooker, musamman in zan dafa wake dan yayi saurin nuna, haka zan dafa shinkafa da wake na soya mai ko albasa babu dan wanda aka kawo min na gara ya ƙare, har na saba da wannan cimar daga satin dana tare a gidan Umar zuwa yanzu da muka yi wata gida, gashi ina da chronic ulcer Amma haka nake yin juriya da yunwa har sai nepa sun kawo wuta, in kuma sun ɗauke ban gama ba to haka zan aje girkin har sai sun dawo da ita, kuma ni bani da murhun gawayi dan iyayena basu siya min shi ba saboda a ganinsu gidan masu kuɗi zani, shiyasa ma suka siya mini kayan 'yan gayu na amfani.
Nan da nan sai gashi na rame na ƙara haske sosai, kwata-kwata banyi cikar ɗaki da amare ke yi ba, wani lokacin haka zan dafa abincin na kasa ci saboda na gaji da cin mai da yaji, ƙarshe haka zan kwana ina ɗame-ɗame da yunwa. Rayuwarmu sai ta zama na maneji wanda zance har rayuwar gidan iyayena yafi mini daɗi dan muna cima mai kyau bama irin wannan ƙarma-ƙarmar, amma duk da haka ban sare ba duba da rayuwa yau fari ne gobe baƙi kuma bana tunanin zamu dauwama a haka tunda nasan wata ya ƙare Umar zai samu albashinsa, sai dai zuwa kwana biyu shuru kamar an anki bawa garinsu ba albashi, tunda da an biyashi zan gani a cefanen gidan, dan haka sai na tambaye shi akan batun albashinsa, Umar ya kalleni yana murmushi.
Waye yace miki ina aiki? Na dai ƙare Karatuna amma ina da gyaran paper Guda biyu yanzu haka sune nake zuwa makaranta dan yin karatunsu.
Ya ƙare maganar yana miƙewa ni kuma ina ƙare masa kallo kamar wacce ta warke cutar makanta, sai na tsinkayi maganarsa yana cigaba da cewa.
Bari na samo kamu ki dama mana daga nan zan siyo ƙosai mu haɗa da shi.
Humm na iya ce masa ya fice ya bar ni da maɗaukakin mamaki, dan a sanina babanmu yace yana aiki a asibiti kuma ya ƙare Karatunsa dan fannin Likita ya karanta, haka na cigaba da juya maganar a zuciyata ina mamakin wannan lamarin har ya dawo ya cim mini ban miƙe ba, ya bani Kamun daya siyo a can saman unguwarmu na miƙe jiki ba kwari na saka ruwa a kettle dan akwai wuta a lokacin, yana tausa na dama masa nasa sugar na fito falo na aje masa, bai ce mini komai ba ya fara sha tare da ƙosan daya siyo, ya gama sha ya rage mini ya miƙe yana ce mini sai ya dawo ya fita, na bishi da a dawo lafiya, na rafka uban tagumi dan tsoron Allah yasa na kasa kwakkwaran motsi dan mamaki ne kaɗai ya kakkaɓe kuzarina, ban dawo hayyacina ba sai da yunwa ta fara nuƙurƙusata na miƙe na isa inda ya bar mini sauran koko a jug, na buɗe tare da yamutse fuskata dan gaskiya ko a gidanmu bana shan koko saboda ulcer, sai na dangwarar da kofin na soma tunanin da anyi mana albashi da tabbas na ci gumi na, dan sai na siyo kayan tea da kwai na mayar da baƙin miyau, wai abunda nafi ƙarfinsa yanzu shi ne yake niman gagara ta. Na fuzzar da iska daga bakina na zauna a Cushing ina jin ƙosawar Monday ta yi na samu albashina, da yake yau Asabar ba makaranta dan mun samu hutu dama gabda aurenmu muka yi jarabawa, saboda Asabar muke zuwa NCE ɗinmu shiyasa ma har na samu damar zuwa koyarwa, Alhamis da Juma'a kuma ina zuwa sanawiyya nan Tudun-wada a makarantar Alƙalam acedamy, shima sai shekaran jiya na samu na cigaba da zuwa, saboda babanmu ya kirani a waya akan na koma makaranta baya son ina wasa. Babansu yana matuƙar bawa ilimi mahimmanci boko da islamiya shiyasa yake kashe mana kuɗi akan haka. Amai dana ji ya taso mini shi ne ya sani na miƙe da sauri na faɗa toilet ɗina na soma kelaye shi, abu kamar wasa sai gashi yana niman zama babba, dan sai da nayi amai sau uku, tun ina da kuzarina har ƙarfinsa ya ƙare, haka na fito falo na kwanta a three seater Ina mayar da numfashi.
Nan naji muryar maƙociyata tana yi mini sallama a ƙofar ɗaki, na amsa mata sai ta shigo tana ƙare mini kallo.
Farida baki da lafiya ne?
Eh wlh amai ma na gama.
Ikon Allah, ina wayarki na ɗauko ki kira mijinki.
Aiko ba ni da waya.
Na bata amsa a taƙaice dan Tecno ɗin daya bani ta lalace ta daina kawowa, sai ta fita ba tare da ta bani amsa ba, ba jimawa kuma ta dawo da wayarta ta miƙo mini.
Kisa Sim ɗinki sai ki kira shi bai dace ki zauna haka ba.
Na amsa ina yi mata godiya sai na miƙe na isa inda na aje sabon Sim ɗin daya siyo mini na fito na zauna, ta taimaka mini muka saka a wayarta sai ta siya mini katin MTN daga Account ɗinta, muka soma kiran layin Umar, sai dai nayi masa kira sama da goma bai ɗaga ba, sai na soma tunanin ko yaƙi ɗagawa ne saboda kar nace masa ya siyo mini wani abu, haka na daure ban nuna damuwa akan fuskata ba dan bai dace na bada ƙofar da matar gidanmu zata fahimci yanayin halin da muke ciki ba.
*Akwai cakwakiya fa ku dai ku bini a sannu.*
Rahma Kabir ce....