KOMAI YAYI FARKO...

3

by @rahmakabir13

KOMAI YAYI FARKO...

Na

©®Rahma Kabir MrsMG.

Page 3.

Sarac Stars R Pen...✍️

Haka muka ɓata kusan minti ashirin bai biyo bayan kiran dana yi masa ba, dan haka sai na yanke shawarar kiran ƙanwarsa Abida saboda nasan tana gida tunda ana hutun makaranta da yake ita a KASU take karatu tana 300lvl, ta girmeni ma sosai kuma bata yi aure ba. Koda na kirata ta ɗauka sai muka gaisa nace mata.

Abida dan Allah Yaya Umar ya zo nan gida ne?

Eh ɗazun ya shigo amma ban sani ba ko ya fita.

To dan Allah ki sanar da shi bani da lafiya yazo.

Ayya Allah ya ƙara sauƙi bari na duba shi sai na sanar masa.

Ameen nagode ki gaida Hajiya.

Ta amsa mini da to kafin ta kashe kiran, sai na cire Sim ɗina na miƙawa Zainab wayarta ta amsa ina yi mata godiya, tace haba ai bakomai sai ta zauna tana yi mini hira, shuru-shuru Umar bai zo ba har wajen ƙarfe sha biyu na rana, Zainab data gaji da zaman ta miƙe tana cewa.

Bari naje na ɗaura sanwar abinci ƙila inna dafa ki samu ki ci kafin yazo.

To nagode Allah ya bar zumunci.

Haba Farida mun zama ɗaya fa, ki daina yi mini godiya domin Zaman tare ya wuce komai.

Na gyaɗa kai ina murmushi har ta fita ina yaba kirkin Zainab, tunda aka kawo ni ita ce ke ƙoƙarin shigo mini bata taɓa damuwa ba dan ban je wajen ta ba, na san dai in gari ya waye ina leƙawa gurinta mu gaisa kafin in wuce aiki, itama Amarya ce shekarar ta ɗaya da aure amma har yanzu Allah bai kawo rabo ba, tana da kirki sosai dan muna zaune lafiya, da yake kuma kowanne yana da komai a ɗaki sai hira ke fito damu tsakar gida da yamma haka, na sauke numfashi ina mamaki jinkirin zuwan Umar dan nasan zuwa lokacin saƙona ya ishe masa. Zainab ta gama girka jalof ɗin taliya na manja ta kawo mini, ƙamshin dana ji ya cika mini hanci yasa raina ya biya dan haka tana aje mini ko cokali ban jira ta ɗauko mini ba a kitchen, na saka hannu na soma ci, ta fito daga kitchen ɗina tana dariya.

Kai ashe baki jira ni ba to bari na kawo miki ruwa, Allah yasa ya zauna miki karki dawo da shi.

Na amsa da Amin, haka ta kawo mini ruwa ta zauna, ni kuma ina cin taliyar kamar zan haɗa da hannuna dan haɗama, Naji yunwa sosai ga kuma aman dana yi ya galabaitar dani gashi kuma na jima ban ci abinci jalof ba, haka na cinye taliyar ina mayar da numfashi, sai dai kuma ina shan ruwa sai ga amai ya taso mini da sauri na miƙe na shiga toilet na amayar da taliyar, Zainab bata biyo ni ba ta jira na gama na ɗauraye baki na fito falo na zauna, ta shiga jera mini sannu ina gyaɗa kai.

Amma ko zaki ƙara kiran shi ne naga lokaci ya tafi ƙila ƙanwarsa bata same shi a waya ba, ko nasa Hijab naje na kira miki ƙanwar mamanki da kika ce tana nan unguwar.

Bar shi kawai Zainab ƙila wani uzurin ya riƙe shi amma nasan zai zo ki bar maganar Inna Maryam, dan bana son ransa ya ɓaci yaga na nuna ya gaza.

Hakane, to Allah yasa yazo akan lokaci, bari naje nayi Sallah ana kiran Azahar.

To nace mata sai ta fita nima na miƙe naje na ɗauro alwala na gabatar da Sallah a zaune dan jiri nake ji sosai, dana idar na cigaba da zama a gurin na jingina kaina jikin Cushing na lumshe ido ina mamakin rashin zuwan Umar akan lokaci, ban ji daɗin abunda yayi mini ba, ko ba komai ai rashin lafiya babban uzuri ne da zai sa ya aje duk abunda yake yi yazo ya duba ni, shiyasa naƙi yarda Zainab ta kira inna Maryam dan kar rai ya ɓaci saboda nasan halinta da ɗaukar zafi, ba zata ji daɗin yadda Umar ya nuna ko inkula ba, sai maganar ta zama babba ana gutsirata, ina tsaka da wannan tunanin sai ga sallamar Umar ya shigo ɗakin, na amsa ina buɗe ido ya ƙaraso cikin sauri.

Subhanallahi jikin ne kuma?

Na gyaɗa masa kai ba tare da nace komai ba dan baki na yayi mini nauyi, yace.

Tashi muje asibiti Allah ya ƙara sauki.

Nace amin cikin sanyin murya kafin na miƙe na gyara zaman hijab ɗina muka fito ya rufe ɗakin, sai na ƙarasa sashin Zainab na sanar da ita mun tafi asibiti tayi mana a dawo lafiya tare da fatan samun lafiya. Sai muka wuce asibitin Yusuf ɗan Tsoho, muka je gurin wata Nurse 'yar unguwarsu Umar mai suna Hajiya Fati, tana ganina ta washe baki muka gaisheta ta amsa kafin Umar ya sanar da ita abunda ya kawo mu, sai ta ce mu fara buɗe kati tukuna kafin ta kaimu wajen likitan rana, ba musu Umar yaje gurin masu bada kati ya siya aka cike kafin ya bawa Haj. Fati ta kai ɗakin likita, ba jimawa aka ce mu shiga. Bayan likita ya dubani yayi rubuce rubuce sai ya bamu takardan gwaji yaje muje lab a yi mini mu dawo, muka fito Haj. Fati ta ƙara yi mana jagora can Lab ɗin aka ɗiba jinina suka ce mu jira 'yan mintina su gama, muka zauna sai Haj. Fati ta wuce tace da mun dawo mu shiga gurin likita koda da wani a ciki ba matsala, muka yi mata godiya ta wuce sai Umar yake ce mini.

Wlh tana da kirki sosai maƙociyarmu ce ƙawar mamanmu, taso na auri 'yarta Hamida amma naƙi, nace tayi mini girma dan yanzu haka tana ajin ƙarshe a KASU, tafi ƙarfina.

'Hmmm shiyasa ka auri ƙaramar yarinya dan ka cuta mini ba.'

Na faɗa a zuciyata, a fili kuma nace.

Ai da yake matar mutum kabarinsa, Allah bai ƙaddara za kuyi aure ba.

Yace hakane sai kuma yayi shuru ya mayar da hankalinsa wajen wayarsa, haka muka ɓata lokaci har sakamakon test ɗin ya fito kafin aka bamu muka koma wajen likita. Ko da Likita ya amsa ya duba ya saki murmushi yana miƙawa Umar hannu suka gaisa.

Congratulations Abokina, kun samu ƙaruwa dan matarka tana da shigar juna-biyu.

Ya ƙare maganar yana sakin hannun Umar, wanda shima ya mayar masa da murmushi yana yi masa godiya, nan likita ya rubuta mana magani kafin yace idan aman bai tsaya ba mu dawo sannan in cikin ya kai wata uku na fara zuwa awo, to Umar yace ya amsa takardar magani muka fito ya isa Pharmacy ɗin cikin asibiti ya siyo kafin muka yi sallama da Haj. Fati muka kamo hanyar gida.

Kafin mu ƙaraso gida duk abunda na gani na ci sai naji zuciyata ta biya, wani kuma sai naji kamar zan yi amai, a haka na hango wata mai sayar da awara naji rai na ya biya sai na roƙi Umar mu tsaya ya siya min, bai musa ba ya tsaya ya siya kafin muka ƙaraso gida na zauna naci wannan awaran, kuma cikin Ikon Allah sai banyi amai ba, na sha magani na kwanta ina mayar da numfashi, sai Umar yace mini zai fita nace masa to ya wuce, ba jimawa Zainab ta shigo tana yi mini sannu nan na bata labarin asibiti ta shiga murna tana koro mini addu'ar sauka lafiya tare da yiwa kanta addu'ar itama Allah ya bata robon haihuwa, na amsa da amin sai muka cigaba da hira, a hankali bacci ya fara fuzgata ganin haka sai ta yi mini sallama ta fita, ni kuma na sauko kan center carpet na gyara kwanciyata na soma bacci.

Haka na soma laulayin ciki mai wahala, duk abunda naci sai na amayar da shi, sai dai wanda raina yake so shi ne yake zama, wani lokacin haka Umar zai fita da safe ya barni ban karya ba, da rana ma na rasa me zan ci dan kwata-kwata bana son abincin da ni na dafa, matar gidanmu wani lokacin ita ke bani, sai dai ita ba kullun take girki ba saboda mijinta baya zama kuma ba ta da yaro a gabanta shiyasa tafi amfani da kayan zaƙi irinsu comflakes, to duk lokacin data dafa ta bani zanci kuma bana amai zai zauna, da dare kuma nasha tea na kwanta.

Zuwa ranar Monday, ban samu zuwa aiki ba saboda bani da lafiya, Umar ya kira shugaban makaranta ya faɗa masa, sai yayi mini addu'ar Allah ya bani lafiya yace ba matsala in na samu sauƙi sai na zo, dan haka na ƙara miƙe ƙafa ina kula da abunda ke ciki ne. Babban abunda yake bani mamaki yadda naga Umar baya ɗokin abunda zan haifa, shi bai ce baya son cikin ba bai kuma ce yana so ba, na kasa gane inda ya dosa dan haka ni kaɗai nake kiɗa da rawata, baya tayani rainon cikin iyakarsa yace mini sunna, bai damu daya siyo mini irin kayan kwaɗayi ba, dan ko na ce ya siyo cewa yake yi bai da kuɗi, haka zanyi haƙuri na mayar da maitata, kuma a haka bawai ya fasa matsa mini bane da kusanta ta dan sai abun ya ƙara yawa saboda ance daɗin mai ciki daban yake, kuma ikon Allah duk abunda yake yi bai sa cikin ya samu matsala ba, sai dai ya barni da ciwon jiki ga rashin kuzari dan bana samun cin abinci sosai, haka nake lallaɓawa.

******

Bayan mako guda.

Na koma makaranta, sai dai in naje bana da kuzarin koyar da yara, sai yawan amai dan ko ƙamshin turare na shaƙa wanda bai yi mini ba sai na dawo da abunda naci, sannan ga yawan kwanciya da bacci, haka dai na lallaɓa har na ƙare mako guda a haka, shugaban makarantar yaga ba zan iya aikin da suke so ba, sai yace ya bani hutu na koma gida har na haihu dan gaskiya ba zan iya yin aikin ba, kar karatu yara ya samu matsala, ban musa ba nayi masa godiya ya bani albashina na watan daya wuce na baro makarantar ina jin ba daɗi dan na saba da fita, zaman gidan ba zai yi mini faɗi ba. Tun a hanya na siya taliyar Hausa da kayan miya a cikin kuɗin na dawo gida nazo na yi dafadukan taliyar manja, haka na zauna na cinye shi tas ina lashe plate, Alhamdulillahi ya zauna banyi mai ba, sai na adana sauran kuɗin da niyyar in mamanmu ta aiko a amsa kuɗin zubi na bata dubu biyar, sai na aje sauran kuɗin ina kashewa kaɗan-kaɗan kafin ya ƙare, babban farin cikina ma shugaban makarantar yace zan samu albashi duk wata amma fa dubu biyar zasu bani tunda na tafi hutu, Naji daɗin wannan karamci da suka yi mini da yake babban makaranta ce na kuɗi shiyasa basu yanke mini albashi gabaɗaya ba, duk da ba aiki zanyi a watannin ba.

....

Washe gari bayan Umar ya fita wajen tara na safe, na sauko daga gado na kwanta doguwar kujera dan har na karya da tea, yanzu ma gajiya nayi da kwanciyar na fito falo, ina tsaka da tunani sai ga ƙanwata Sakina ta shigo da sallama, na tashi na zauna ina murmushi.

Sai yau zaki zo, ina su Laurat da Usman.?

Ni kaɗai na zo, kin san baba ba zai bari mu zo ba saboda makaranta, yanzu ma yace karna zauna saboda na samu zuwa islamiyan yamma.

Babanmu kenan yana ƙaunar karatu, da fatan duk kowa lafiya.

Alhamdulillahi, mama ce ta aiko ni nazo na amsa kuɗin zubi tace ki bada dubu takwas ɗin duka, saboda zata bayar da gudunmawar biki da sauran kuɗin.

Waye zai yi aure?

'Yar ƙawarta Haj. Hadiza kin san dai irin gudunmawar da suka bayar a auren ki, to dole ne ta yi nata ƙoƙarin wajen fita kunya.

Hakane, to Allah ya sanya alkhairi, amma na taɓa kuɗin sauya dubu bakwai da ɗari biyar.

To sai ki bayar haka inna je zanyi mata bayani. Wai Anty naga kinyi wani mugun haske ne kamar wata Baturiya, amma kuma kin rame sosai, ba kida lafiya ne.?

Cewar Sakina tana ƙare mini kallo, murmushi nayi nace.

Aiko banda lafiya amma da sauƙi Alhamdulillahi.

Allah ya baki lafiya, ɗauko kuɗin na tafi kar nayi laifi gurin baba.

OK nace kafin na miƙe na koma ɗaki na zare ɗari biyu canjin taliya, sai na kawo mata dubu bakwai da ɗari biyar ta amsa tana ƙirgawa.

Kin san dokar kuɗi ne dole a ƙirga.

Ai da yake na saba cuta dole ki ce haka.

Na faɗa ina gimtse fuska, ta miƙe tana mele baki.

Ni dai ba haka nake nufi ba karki yi mini sharri. Hmmm su Anty Farida rowa, ko ruwa baki bani ba, aiko inna je gida sai na faɗawa mama.

Dama halinki ne ki haɗani da ita, dan haka ba zai dameni ba, dan ba yau kika saba yi mini sharri ba.

Sakina bata kulani ba ta wuce kitchen ɗina ta gama buɗe-buɗenta bata samu abun ci ba, sai ta ɗauko ruwa ta sha ta fito tana cewa.

Ni na wuce sai anjima.

Ki gaida kowa da kowa sai na zo.

To tace mini ta fice, ni kuma na koma na zauna ina tunanin yadda zan cigaba da zama ba kuɗi a hannuna, tunawa da na yi da awara sai na dauƙo ɗari biyun nan na fita na suyo na Naira ɗari a nan kusa damu, guda biyar har da gyaran ɗaya aka bani, na dawo naci nasha ruwa na kwanta.

....

Bayan kwana biyu, amai ya dawo ga bana cin abincin kirki, tuwo nake son ci amma bansan inda zan samu ba, ga Umar ko na faɗa masa cewa yake sai dai nayi haƙuri bai da kuɗin siyan garin masara saboda na gwada yin Tuwon semo da miyar kuka amma cikina bai son Semo, jiya na dafa naci amma sai da na amayar da shi, yanzu ko warin Semo bana so, haka dole na haƙura da amfani da shi, na fara tunanin inda zan samu Tuwon masara miyar yauƙi, sai kawai gidanmu ya faɗo mini a rai dan kullun tuwo muke yi da daddare saboda Babanmu yana so, kuma tun bama so suka zo muka saba da ci, dan haka sai na shirya na saka Hijab na fito na rufe ɗaki na kama hanyar gidanmu, duk da jikina babu ƙarfi amma haka na jure tunda zuciyata tana son naje naci tuwon ba za a rasa sauran na dare ba, ban duba nisan dake tsakanin gidana zuwa gidanmu ba, tun daga Kwanar Mai Shayi har zuwa Sabon Garin Tudun-Wada na miƙa a ƙafa, dan bani da ko sisi da zan hau mota, kuma bani da wayar da zan kira gida nace a kawo mini shiyasa na yanke shawarar naje kuma dama nayi kewar gida, ya dace ace na je, dan tun bayan biki da kwana goma da muka je da daddare muka gaishesu ban sake komawa ba. Haka na riƙa jan ƙafa ina layi kamar wacce kwai ya fashe mata a ciki, ina yi ina kuka da kyar na ƙarasa gidanmu ina share hawaye, na shiga na sallama sai naji Mamanmu tana kan keken ɗinki dan sana'arta kenan, na ƙarasa ɗakin na shiga na zauna ina gaisheta ina tara miyau a bakina dan na kasa haɗiyewa, sai naji mamanmu taja tsaki, sai na miƙe na fita na zubar na dawo na zauna, sai take ce mini.

Yanzu me ya fito dake daga gidanki.?

Babu komai kawai dai bana jin daɗi ne.

To shi Umar ɗin yasan kin zo.?

Eh tare muka fito shi ya wuce gidansu ni na tawo nan, Dan Allah baku rage sauran tuwo ba yunwa nake ji.?

Kin ga Farida maza ki tashi ki koma gidanki ki zauna a ɗakinki bana son iskanci.

Ta ƙare maganar fuskarta a haɗe, jiki ba kwari na miƙe hawaye yana zuba a Idona na share, ko sai anjima ban iya faɗa mata ba na ƙara kamo hanya a ƙafa ina yi ina hutawa, mutane sai kallona suke yi wasu matan da suke wucewa haka suke ce mini sannu, damin duk wanda ya ganni a wannan halin yasan bani da lafiya ina jin jiki, haka na koma gida na kwanta a carpet ina murƙususu ina juyi dafe da marata kamar zan mutu saboda azabar yunwa, dan tun safe banci komai ba sai amai dana yi, dan ko ruwa nasha sai na dawo da shi saboda a lokacin tuwo rai na yake so.

Jinjina ga ko wace Uwa, idan kaga Uwa tana iko da 'ya'yanta kalleta kawai. Allah ya bamu ikon farantawa iyayenmu yasa 'ya'yanmu suma su faranta mana. Ameen

Rahma Kabir ce.