4
KOMAI YAYI FARKO...
Na
©®Rahma Kabir MrsMG.
Page 4.
Sarac Stars R Pen...✍️
Ga yawan tara miyau dana ke yi, dan har gwangwani na samu na samo toka daga makotanmu ina zuba miyau a ciki, hawaye ne mai raɗaɗi ya shigo fitowa daga ƙwayar idona, na soma sabon kuka har na gode Allah, naji tamkar a duniya Ni kaɗai ce ba ni da kowa ba ni da gata sai wanda ubangiji yayi min, sai nake jin kamar daga sama na faɗo ni kaɗai ne ke rayuwa babu mai jin kuka na balle asan halin da nake ciki. Ga Zainab tayi tafiya bata nan babu wanda nake jin motsinsa a gidan. Haka da rarrafe naje toilet nayo alwala na gabatar da Sallah a zaune, dana idar na shiga roƙar Allah akan ya rabani da wannan cikin ina hawaye, dan a ganina wannan ne kaɗai mafita ta, ban san ya azabtar ɓari yake ba amma wlh naji da hakan zai kasance da ni dana huta, gashi ni ban waye da sanin magungunan zubar da ciki ba, idona ya rufe, kawai fatana a yanzu na rabu da cikin na huta da azabar da nake ciki, naje gidanmu inda nake zaton za a share mini hawaye na amma mama ta koreni, sai na rushe da kuka ina fatan rabuwa da cikin tare da addu'ar koda ace na haihu Allah ya kashe yaron dan ina tausayi abunda zan haifa yazo a irin wannan halin da nake ciki, nasan ba fata mai kyau nake yiwa kaina ba amma ƙuruciya da rashin lissafi dama rashin tsayayyen jagoran da zai tsaya mini shiyasa nake yiwa kaina wannan fatan.
A haka na yini a wannan halin har sai da Umar ya dawo ya same ni, ya shiga tambayata me yake damuna.? Sai na fashe da kuka ina cewa.
Komai ma yana damuwa wlh yunwa nake ji kamar zan mutu, dan Allah idan gidanku suna yin tuwo ka je ka amso mini na ci.
Gaskiya Farida ba zan iya zuwa gidanmu nace a bani tuwo ba dan ina jin kunyar su fahimci ciki gare ki, gwara ki faɗa abunda kike so na fita na siyo miki, kuma dare yayi babu inda zan samu masu sayar da tuwo.
Amma Faruq dan kace a saka mini tuwo naga ba abun kunya bane, saboda a ƙarƙashin inuwar aure muka samu cikin, kuma ribar aure haihuwa ne, saboda da ace zan ɗauki lokaci ban samu ciki ba sai ya zama abun magana.
Sai ya ja guntun tsaki yana cewa shiga ba zai iya zuwa ya amso ba kawai nayi haƙuri, sai ban yi fushi ba nace masa.
To dan Allah idan zaka dawo ka riƙa biyawa ta gidanmu ka amso mini tuwo, kullun da dare shi Mamanmu take dafawa tunda kana da mashin.
To gwara-gwara wannan tunda sun san kina da cikin, In Sha Allah zuwa gobe zan biya na amso miki.
Nace masa nagode kafin na miƙe na dafa indomie fara tas ba komai a ciki sai magginta, na yi shi ruwa ruwa na zo na zauna naci da yaji sai Allah ya taimake ni banyi aman ba, shi ne na samu damar yin bacci cikin salama, shi kuma Umar dama ya riga yaci abinci daga gidanmu. A ranar yadda yaga na galabaita sai ya haƙura bai nimeni ba.
Washegari bayan sallar magariba kamar yadda muka yi da Umar, bai manta ba yaje gidanmu amso mini tuwo amma abin mamaki bai samo ba wai basu gama ba, nace masa to amma raina ba daɗi dan na saka rai sosai, sai ga kira ya shigo wayar Umar ya duba yaga Babanmu ne sai ya ɗaga suka ƙara gaisawa sai yace masa ya bani wayar Mamanmu ce zata yi magana dani, ya miƙo mini na amsa na shiga uwar ɗaka na zauna bakin gado, sai naji muryar Mamanmu ta shiga surfa mini zagi.
Dan ubanki ashe ke matsiyaciya ce baki da mutunci kin raina mijin ki ko, taya zaki aiko shi ya amsar miki tuwo, a kanki ne aka fara laulayin ciki.?
Mamanmu kiyi haƙuri.
Abunda na iya faɗa kenan ina share hawayena, ta cigaba da yi mini faɗa har ta gama ta kashe wayar, na sauke numfashi ina jin jikina yana rawa saboda bana son tashin hankali, ban yi mamakin abunda mama tayi mini ba domin koroni da ta yi jiya ya tabbatar da zata yi mini abu fiye da haka, kawai dai babban damuwata me yasa mama take yi mini haka.? kamar ba itace ta yi naƙuda ta ba, ni nasan a tsawon rayuwar da muka yi tare da ita ina matuƙar kiyaye ɓacin ranta, ina tsoron nayi mata laifi, kullun cikin takatsantsan nake amma duk da haka ban fita ba, haka na gama kukana na share hawaye, na shiga toilet na wanke fuskanta na hau gado na kwanta ko cire kayan jikina banyi ba na rufe ido, daga haka bacci ya ɗauke ni ba tare dana ci komai ba.
....
Tun daga wannan abun da Mamanmu tayi mini ban sake gigin niman wani abu a gurinta ba, na cigaba da lallaɓawa ina maneji, matar gidanmu da ta dawo ta cigaba da taimaka mini da abunda zanci, in dai tayi girki zata saka mini kuma ikon Allah inna ci bana amai, a hankali laulayin ya fara raguwa mini amma kuma ƙaunar tuwo yana nan a zuciyata.
*****
Bayan mako guda, wajen ƙarfe biyar na yamma na farka daga bacci sai Naji jikina yayi ƙarfi, na tashi ta shiga toilet na ɗauro alwala nazo na gabatar da Sallah, na idar kenan sai ga yaron Inna Maryam yazo, ya shigo da sallama na amsa ina murmushi.
Abul-Khairi sai yau zan ganka a gidana, to nayi fushi.
Kiyi haƙuri Anty wlh makaranta ne yasa ban samu zuwa ba, yanzu ma muna dawowa mamanmu tace nazo na gaishe ki.
Ina amsawa, su Inna suna lafiya?
Lafiya lau.
To madalla, bari na duba sauran cin-cin na baka, duk da diddigi ya rage kaƙi zuwa ka amsa akan kari.
Murmushi yayi yana sunne kai cike da jin kunyata, shi ne ɗan farko a gurin Inna Maryam yaron yana da hankali, sam bayi da rawar kai, ko da yake sun tsaya sosai akan tarbiyyarsu daga boko sai islamiya babu damar wasa ko yawo, na kawo masa cin-cin da sauran diblan, ya amsa ya fara ci na dauƙo masa ruwa, haka muka zauna ina tambayarsa makaranta da Karatunsa yana bani amsa, gabda sallar magariba ya yi mini sallama zai tafi.
Nagode Abul khairi, dan Allah ka cewa inna in tayi tuwo ta aiko mini da shi, kuma ka gaishe ta.
Ya amsa da to kafin ya tafi, ni kuma na rufe ɗaki na koma uwar ɗaka dan nayi alwala.
Wajen ƙarfe takwas na dare sai ga Abul khairi ya kawo mini Tuwon, na amsa ina godiya sai ya tafi, na dauƙo plate a kitchen na zauna a carpet jikina yana rawa saboda ɗokin cin Tuwon, miya daban haka ma kulan Tuwon daban, na zuba Tuwon sannan na zuba miyar wacce naji tana gafin kuka da daddawa, da yake nasan girkin gidan gandu suke yi dan suna da yawa, saboda inna tana da kishiya kuma gidan gado ne suna da yawa, dan haka ban yi mamaki ba ganin irin miyar da aka kawo mini wanda ko nama babu, haka na zauna naci ina siɗe hannu dan ba ƙaramin daɗi yayi mini ba nayi gatsa ina godewa Allah, nasha ruwa sai na miƙe na adana sauran a kitchen da nufin da safe shi zan ɗumama naci.
Washegari wannan tuwon naci da safe ina murna, Umar kuwa bai ma karya ba ya fita. Da rana sai ga aike daga Inna Maryam ta sake aiko mini da alalen gwangwani guda shida an zuba manja sosai da yaji a gefe, na amsa ina godiya cikin farin ciki, sai na ɗauko kulolin tuwon jiya na bawa ɗan aiken ya wuce, na zauna na miƙe ƙafa ina ci daɗinsa yana ratsani kamar ana kaɗa mini kunne, a haka Umar ya dawo ya same ni, shima sai ya zauna yaci alalen yana faɗar ya bashi sha'awa, bayan mun cinye ne yake tambaya ta inda na samo shi, sai nake faɗa masa Inna ce ta aiko mini, yace ta kyauta dan shima yaji daɗin alalen.
Haka muka cigaba da tafiya kullun Inna sai ta aiko mini da tuwo da daddare da rana kuma ta aiko mini abinci kamar alalen ko shinkafa da mai da yaji da salad, watarana Kuma shinkafa da miya da nama a ciki, ko kuma doya da miya ko da mai da yaji, na dai fahimci ba abincin gidan su bane siya take yi ta aiko mini, kuma duk in ta aiko mini da abincin rana tare da Umar muke cincewa in dai yazo ya samu ko anyo aiken akan idonsa, wani lokacin baya isanmu amma haka nake haƙura muci kuma babu kunya yaci yasha ruwa, shi bai siya mini ba amma yana cinye wanda aka kawo mini, tuwo ne dai baya ci dan yana ci daga gidansu. Ba zan taɓa mance alkhairin Inna Maryam ba dan ta taimake ni a lokacin da nake niman agaji, na tabbatar Allah ya amsa kuka na ne ya kawo Inna Maryam cikin lamarina.
Zuwa wani lokaci cikina yayi kwari, sai inna ta daina aiko mini da abincin musamman data ga yadda jikina yayi ƙarfi, saboda ina zuwa gidanta mu gaisa, kuma Alhamdulillahi gaskiya laulayin ya ragu sosai dan a yanzu cikina yana cikin wata na shida, har na cigaba da zuwa makarantar NCE kuma mun yi jarrabawar ƙarshe, dama shekara biyu ne Karatun kuma tun ina gida na fara, sai na mayar da hankalina da zuwa Sanawiyya da yake nan tudun-wada kusa na unguwarsu Umar, kullun in mun tashi gidansu nake zuwa na jira Umar anan, har sai ya dawo sai mu tafi gida tare a mashin ɗinsa, to duk lokacin dana isa gidan da rana dai-dai lokacin an gama abincin rana ko an gama ci basa taɓa yi mini tayi, gashi girki suke yi lafiyayye mai daɗi dan ko a ido kaɗai ka gani sai ranka ya biya, amma basu taɓa cewa ga naki ba a matsayina na sirikar gidan, a yadda na fahimcesu in dai baƙo ba'asan da zuwansa ba to da kamar wuya a bashi abinci, amma kuma ni da suka san duk Alhamis zuwa Lahadi ina zuwa makaranta sun san da zan zo, kuma wani lokacin saboda sauri ko karyawa bana tsayawa yi haka nake fitowa sai dai na bige na siyan awara da pure water, da wannan tunanin na isa gidan da sallama sai na hango cikin falon suna cin abinci, sai kawai na zauna a korido ina mayar da numfashi, matar babansu Hajiya ta buɗe murya tana cewa.
Farida ya zaki zauna anan ki ƙaraso ciki mana.
Hajiya wlh na gaji ne bari na huta zan shigo. Ina wuni.
Na ƙare maganar ina gaisheta ta amsa kana yaran gidan suma suka miƙo mini gaisuwa ina zaune a gurin, dan gaskiya ba ni da matsala da su a lokacin suna girmama ni, daga haka sai na juya baya na cigaba da kallon bishiyar gwanda ina mamakin wannan halin nasu, sun san daga makaranta na fito ba daga gida nake ba balle su ce a ƙoshe nake, a'a ba za'a bani ba tunda basu saka ni a waɗanda za a girka dasu ba, na tabbatar ƙila da mahaifiyarsu Umar tana raye ba zata yi mini haka ba saboda ina da labarin kirkinta. Hmmmm shiyasa ma na yi Branch anan korido dan kar in shiga in ga abunda raina zai biya, dan mai ciki ba a rabata da ƙulafuci, ko ƙamshin dake ziyartan hancina kaɗai ya ishe ni balle ace na kai ga gani. Sai dai in nayi sa'a babansu yana gida ranar weekend suna bani, to idan an zuba masa nasa abincin yaci ya rage sai yace a ajewa matar Umar in ta dawo makaranta sai taci, haka zasu bani suna yi mini bayanin abunda Alhaji yace sai dai nayi murmushi na amsa na ci, in ko bai rage ba to haka zan yini ina fama da yunwa babu mai bani abinci, ga Umar wani lokacin sai bayan sallar magrib yake dawowa mu tafi gida, to in zamu tafi ne sai suke zuba mana Tuwon dare a kula malmale biyu na Semo mu tafi da shi gida, kuma koda mun koma gida Umar ne yake ci saboda ni bana son semo, ƙarshe sai dai nasha tea na tusa da biredi ko na dafa indomie, shiyasa tunda na fahimci yanayinsu kenan sai na koyawa kaina juriyar yunwa, sai nake yiwa kaina dabara tun daga gida na ci na ƙoshi yadda ko da rana tayi bazan galabaita ba. Fitowar ƙaramin yaron Hajiya matar babansu da kwano yasa na dawo daga gajeran tunanin dana shiga, ya tsaya a gabana yana yi mini gwaranci na saki murmushi ina kama kumatunsa, sai dai miyauna ya gama tsinkewa daga ganin kalar abincin da yake kwanonsa, shinkafa ce fried rice taji Mai ga Kuma tsokar naman kaza a ciki, ɗan cikina ya motsa sai na miƙe cikin sauri dan naji kamar sun gama cin abincin na shiga falo na wuce ɗakin Abida na yada zango, Alhamdulillahi cikina yanzu ya fara saba wa da yunwa dan haka ina jurewa har sai Umar ya dawo kafin mu wuce, sai da na ƙara hutawa kafin na shiga toilet ɗin ɗakin na ɗauro alwala na fito na gabatar da Sallah.
.....
A hankali lokaci ke turawa har gashi ina wata takwas, zuwa wannan lokacin mun fara shirye-shiryen zuwan baby, dan inata zuwa awo kuma likita ya tabbatar abunda ke cikin lafiya yake, duk da sun ce namiji ne amma ban sakawa raina lallai hakan zan haifa ba, tunda babu wanda yasan gaibu sai Allah suma likitocin lalube suke a duhu. Umar yayi ƙoƙari da nuna bajinta wajen bani kuɗi na tafi kasuwar bacci na siyo kayan haihuwa, duk wani abu da ake buƙata na baby dan amfaninsa na siya dai-dai na talaka tare da set ɗin bahon wanka, Sakina ce tazo muka tafi kasuwar, da muka gama ta wuce gida dan babanmu yace karta zauna, sai nima na dawo gida na dafa taliyar Hausa na ci na ƙoshi kafin na adana kayan cikin waldrobe ɗina. Sai dare da Umar ya dawo na ɗauko na nuna masa, bai wani duba ba yace na mayar sunyi kyau, na kwashe su na mayar na dawo ina dubansa.
Wai idan na haifi namiji wani suna zaka saka.?
Ki bari ki haihun tukuna kafin azo kan wannan maganar.
To nace masa sai na gyara zama dan in jashi da hira, amma sai ya gwasale ni da kar na dameshi akwai abunda yake yi, hmmm nace sai na miƙe jiki ba kwari na koma ɗaki na kwanta. Ina matuƙar sha'awar naga ina hira da shi cikin sakin fuska da raha amma baya bani wannan damar, kullun waya tana hannunsa idan kuma na zauna kusa da ci yace na takura masa, na dai fahimci baya so na ga me yake yi a wayar, sai na fara zargin ko hira yake yi da 'yan mata amma kuma yanayin kamewarsa dana sani sai ya shafe mini wannan tunanin.
Rahma Kabir ce.