5
KOMAI YAYI FARKO...
Na
©®Rahma Kabir MrsMG.
Page 5.
Sarac Stars R Pen...✍️
Bayan wani lokaci har na kai lokacin haihuwa, kuma duk da haka nauyin ciki bisa na daina zuwa Sanawiyya ba dan zuwa lokacin nayi lafiya sosai komai ina ci ba batun amai, sannan ni baƙuwa ce a haihuwa ga ƙuruciya ba sanin yadda yake nayi ba, saboda duk yadda aka yiwa mace bayani ba zata fahimta ba sai ta riski kanta a ɗakin haihuwa ne tukuna zata gane karatun cewar wata 'yar ajinmu. Kamar kullun yadda na saba daga makaranta ina wucewa gidansu Umar na zauna zaman jiransa, haka ma yau Alhamis na wuce gidansu da yamma dan yau karatun rana muka yi, na samu matar babansu a tsakar gida, muka gaisa sai ta miƙo mini kujerar tsuguno.
Gashi ki zauna mana ai tsayuwar ba daɗi.
Na ce mata to, sai dai kuma nayi-nayi na zauna na kasa zama, sai na ce.
Hajiya na kasa zama fa.
Kamar ya kin kasa zama.
Wlh yau ma a makaranta inna je fitsari sai dai na cire pant gabaɗaya nayi a tsaye bana iya tsugunawa.
Aiko Farida naƙuda kike yi.
Anya kuwa.? ba naƙuda bane.
Nace cikin gaskiyata, sai ta saki murmushi.
Haba ya zaki ce ba naƙuda kike yi ba, bari kuje asibiti a duba in ba ita bace sai ki wuce gida.
Nace mata to sai na koma gefe na tsaya tasa aka kira mata Umar, ba jimawa ya zo dan ba nisa yayi ba, ya ɗauke ni a mashin muka wuce asibitin Yusuf Ɗan Tsoho, muna zuwa nurse suka yi mini jagora zuwa cikin ɗakin haihuwa, na ga wasu mata suma sun zo haihuwa suna ta gumurzu, muka wuce ciki ta saka na kwanta a gado ta soma duba ni, nan take nurse ɗin ta saki murmushi.
Kin yi nisa fa kina 6cm, ina kayan da kuka zo da shi.?
Bamu ɗauko komai ba, mun zo a duba ne.
OK, ki fita ki faɗawa mijinki yaje ya ɗauko kayan haihuwa sai ki cigaba da tattakawa kafin abun yazo sosai.
Nace mata to sai na sauko daga gadon ina cije leɓe, dan gaskiya saka mini hannu da tayi sai naji tamkar ya taso da naƙudan ne, ƙasan marata ya soma karta mini da ciwo kaɗan-kaɗan. Na fito ina jan ƙafa na isa wajen Umar na sanar da shi abunda ake ciki yace.
Bari naje na ɗauko, kayan sune wanda kika haɗa cikin kit ko?
Eh.
Na bashi amsa a taƙaice ina cije baki, sai ya amsa jakata na makaranta ya wuce yana ce mini sannu da addu'ar sauka lafiya, na amsa ina bin bayansa da kallo har ya isa inda mashin ɗinsa yake ya hau ya wuce. Haka na koma ciki ina zagawa a ɗakin daga bango zuwa bango, da yake babban ɗaki ne da gado da yawa a jere hagu da dama, haka na cigaba da tafiya ina yi ina tsayawa saboda a lokacin abun ya taso sosai da kyar nake ɗaga ƙafa, tabbas na ƙara fahimtar Haihuwa tafi gaban kwatance, sai mace ta kai wannan matakin ne zata gane cewar uwa uwa ce ko min lalacewarta. Haka na cigaba da naƙuda har faya ta fashe Umar ma ya dawo ya kawo kayan, suka tsaya a waje suna zaman jira dan a lokacin da ya leƙo ɗakin da nake ciki ya sanar da ni Haj. Dada maƙociyarsu tana waje kafin matar babansu ta ƙaraso, saboda ita ta tsaya tayi mana abinci.
Sai wajen ƙarfe sha ɗaya na dare na haihu bayan doguwar mugurzu da na sha, aka fito dani ɗakin hutu na kwanta ina mai lumshe ido tare da tuno duniyar azabar dana shiga wanda faɗarsa ba zai misaltuba dan na ci baƙar wahala, gashi yanka shida na samu saboda girman baby a wajen fitarsa, bayan an cire mahaifa aka sake ɗaura mini fige kazar wahalar ɗinki, dan sai da suka ɗinke ni ciki da waje kamar wayar, a wannan lokacin har ihu nayi dan gaskiya zafin ɗinki daban yake. Ina tsaka da tariyo halin dana samu kaina a ɗakin haihuwa naji muryar Hajiya a kaina tana jera mini sannu, na gyaɗa mata kai ba tare da na ce komai ba dan bakina nauyi yayi mini, ta cigaba da cewa.
Ɗazun bayan sallar Isha'i iyayenki sun zo amma sun koma, dan mamanku cewa tayi da tasan muna nan da ba su zo ba, wai Umar ce musu yayi ya kawo ki asibiti haihuwa. Sun ce a gaisheki da addu'ar sauka lafiya.
Murmushi nayi a iya fatar baki ban ce komai ba, nasan dama da wuya mamanmu ta zauna, banma yi zaton zata zo ba.
Idan kin huta ki tashi kisha tea sannan ki bawa yaron nan nono.
Umm nace tare da yunƙura wa na tashi na zauna ina cije baki, a hankali na zauna ta gefe dan ina tsoron na zauna dai-dai na warware ɗinkin da aka yi mini, ƙanwarsa Abida da shigowarta kenan ta yi mini sannu sannan Hajiya ta bata yaron ta haɗa mini tea da kanta ta bani na fara kurɓa dan dama yunwa nake ji sosai, rabona da abinci tun wajen sha biyu na rana kafin na tafi makaranta, haka na shanye tea ɗin sai ta saka mini pillow a bayana na jingina, sai ta ɗaura mini yaro a cinyata ina ƙare masa kallo, sak mahaifinsa sai dai kuma fari ne tas kamar yadda nake, ya ɗauko haskena dan har ya ɗara ni kamar bature, gashi ƙato Tubarakallah gwanin sha'awa kamar ba nice na haife shi ba duba da ƙanƙantar jikina, ga hanci har baka dan zance wannan ma hancina ne ya ɗauko, yadda nake ƙarewa yaron kallo ya shagaltar da ni a inda nake, sai da naji Anty tana cewa.
Kama yake yi da Umar sannan kuma ya ɗauko hasken fatarki Tubarakallah. Saka masa mama yasha naga ya fara motsawa.
Hmmm nace sai ta taya ni ɗaga rigar, ta taimaka mini na saka masa nonon a baki tare da nuna mini yadda zan riƙe masa maman dan kar ya riƙa toshe masa hanci, bance komai ba sai runtse ido dana yi lokacin da ya soma tsotsa dan wani zugi na soma ji a saman maman. Ana cewa aure yaƙin mata to gaskiya haihuwa ce yaƙin mata dan wannan yaƙi ne tsakanin rayuwa da mutuwa, saboda gani nayi tamkar an sauya ni daga duniyar dana ke ciki an kai ni wata, shiyasa a yanzu ba zanga laifin ko wace uwa ba data fifita son 'ya'yanta akan komai, dan ita kaɗai tasan azaba da gumurzun da ta sha kafin zuwansu duniya, tun daga samuwar juna-biyun da laulayi tare da kuma ɗawainiyar cikin har na tsawan wata tara da kwanaki, sannan azo kan babban, wato haihuwa.
'Amma duk wannan wahalar da ake sha itama Mamanmu ta ji shi kafin ta haifeni ko?'
Na yi maganar a zucci ina jin hawaye yana cika mini zuciya tare da jin tsantsar ƙaunarta a zuciyata, sai dai duk irin wannan ɗawainiyar da Mamanmu tayi da ni bai sa ta nuna mini so ko kulawar da ya dace uwa ta bawa 'yarta, naga kuma auren soyayya suka yi da babanmu balle ace ƙiyayyarsa ce ta shafe ni. Amma ace duk irin wannan wahalar da Mamanmu tasha ta kasa nuna kulawarta a gareni a matsayina na babbar 'yarta wanda da yawa 'ya'yan fari sune mafi soyuwa a zuƙatan iyayensu, wannan tunanin shi ke saka mini shakku da tambayar anya Mamanmu ita ce asalin wacce ta haife ni kuwa.? Tambaya ce da nake da amsarta a zahiri domin nasan ba a taɓa sauyawa tuwo suna ba, dan kakarmu mahaifiyar Mamanmu tasha bani labarin rayuwar Mama kafin aurenta da kuma bayan auren har zuwa irin wahalar da ta sha a ɗaukar cikina da kuma haihuwata. Shigowar Umar ya dakatar da tunanina na cire yaro daga nono na bashi ya amsa fuskarsa a sake yana ƙare masa kallo, a wannan lokacin naga tsantsar soyayyar uba ga ɗansa a fuskar Umar, dan ko bai faɗa ba naga ƙaunar yaron a tare da shi, kuma wannan ne ya cire mini shakku akan yana son haihuwar ko baya so. Haka suka cigaba da zama suna hira shida Abida daga bisani su Hajiya suka tafi a motar gidansu Umar ya mayar dasu, sai aka bar ni da Abida ta zauna mini, ba jimawa bacci ya ɗauke ni.
.....
Washe gari da safe Alhajinsu Umar ya zo ya ga yaro bai daɗe ba ya tafi, sai muka karya da kayan breakfast ɗin da aka aiko daga gidasu. Jikina duk ba daɗi saboda rashin yin wanka, duk na ƙosa a sallamemu mu wuce. Sai wajen Tara Likita ya bamu sallama muka tafi gidana, muka haɗa kaya nawa dana baby kafin Umar ya wuce da ni can gidan Iyayena kamar yadda ake zuwa wankan gida a haihuwar fari.
A ɗakinmu da nayi 'yanmatanci aka sauke ni wanda ada muke kwana tare da Sakina, nan da nan Mamanmu ta shiga hidima damu ta aika aka haɗo salulun salo na wankan yaro dan na manta ban siya ba, sannan tasa aka siyo bagaruwa da zan riƙa zama a ciki, nayi mamakin irin tarban data yi mini, ita ce tayi wa yaro wanka ta shirya shi, bayan ta gama ta sa na shiga bayi tayi miki wankan ganyen dalbejiya, sai dai ban zauna a ruwa mai zafi ba kamar yadda likita yayi gargaɗi, a ruwan bagaruwa na zauna bayan an dafa ya huce sosai, naji daɗin jikina sosai dan ina gama saka kaya na hau gado na kwanta sai bacci, haka 'yan barka suka dinga zuwa suna samuna ina bacci kuma an hana a tashe ni saboda na samu hutu sosai.
Zuwa yamma aka bani tuwo miyar kuka lafiyayye har da man shanu naci na ƙoshi tare da kunun kanwa, wanda nan da nan ruwan nono ya ƙara samuwa yaro yasha ya ƙoshi. Da daddare Umar ya zo tare da siyayyan madara da bombita na gwangwani medium ɗin, sai sinƙin pampers da yace mai shagon da yayi siyayya ya bashi a yiwa baby amfani da shi, nace mun gode kafin ya fita tsakar gida yayi hira da babanmu daga bisani kuma ya tafi. Ni kuma na adana kayan daya siyo a waldrobe ɗin ɗinkin cikin kayana akan in zan yi amfani da shi na riƙa ɗaukowa.
Sai dai kuma tun bayan kawo wannan kayan tea ɗin da Umar yayi bai sake kawo mini wani abu ba, kuma kullun zai zo da daddare amma baya riƙo komai, gashi kayan tea ɗaya kawo a kwana uku ya ƙare saboda Ƙannena da suka dinga ɗiba a ɓoye suna sha ban sani ba, sai da ya kusa ƙarewa kafin na ankara, gashi babu halin nayi magana dan ban san waye a cikinsu yake yi mini ɓarna ba, kuma ina gudun abunda zai haɗani da Mamanmu shiyasa dole na ja bakina nayi shuru. A hankali babanmu ya ɗauki nauyin hidima dani, kullun in zai dawo daga gurin aiki yana riƙo mini tsire ko balangu naci, sannan ya siyo mini kayan tea da special bread mai yanka-yanka, ko kuma akan hanya in ya ga inda ake sayar da chips da kwai ya tsaya ya siya mini, sannan suma 'yan gida ya siya musu sai dai nawa daban kuma da yawa. A gaskiya babanmu yana kulawa dani sosai irin kulawar da ban samu a gurin mijina ba, dan ko ɗan tsokar nama bai taɓa haɗani da shi ba a matsayina na mai jego.
Ranar ƙauri wanda ya kama kwana uku da haihuwa, babu wani bayani a gurin Umar dan ko jiya daya zo nayi masa maganar kunu bai ce komai ba har ya tafi, shiyasa da safe Mamanmu da ta tambaye ni ko munyi magana nace mata ba muyi ba, kuma ga ba waya a hannuna balle na kira na faɗa masa, tace na rabu da shi sun gama magana da babanmu har ya siyo kayan yin kunun gyaɗa dan shi take so suyi, nace mata to kafin ta fita. Wajen ƙarfe tara 'yan uwan mamanmu suka fara cika gida sai hada-hada suke yi na haɗa kunun gyaɗa, ni dai ina ɗaki ina jin hirarsu bayan duk sun shigo mun gaisa. Haka suka yi aikin kunu suka gama aka zubo mini nawa kafin su saka tsami sai na zuba madara nasha. Sai can rana Ƙannen Umar maza suka zo da gasasshiyar kaza irin gashin hanya ɗin nan suka kawo mini, dan sai a ranar suka zo ganin baby, nan suka zauna aka kawo musu kunu suka sha kafin da zasu tafi Ƙaninsa Abbas yake cewa ƙanwata.
Kuyi mana list ɗin abunda kuke so na suna.
Fulawa muke so da za muyi donot sai kuma drinks wanda zamu naɗa souvenirs.
Ƙanwata ta ba shi amsa, sai yace to kafin suka yi mana sallama suka tafi. Sai bayan sun wuce ne Sakina take ce mini.
Anty mun manta bamu yi musu maganar ɗinkin fitar suna da na baby ba.
To sai dai in Umar yazo sai na faɗawa masa, ga kuma lokaci ya tafi ni na manta ma.
Na faɗa fuskata a dame, tace to sai na faɗa masa asan abun yi dan ba ƙaramin taro mama ta shirya ba kuma ya dace a ranar a ganni na fito fes da baby, murmushi nayi ina kallon Sakina da take magana sai kace wata babba, haka ta cigaba da yi mini hira akan yadda suke so sunan ya gudana. Zuwa dare ko da Umar yazo nayi masa maganar ɗinkin fitar suna cewa yayi bai da kuɗi, dan haka bayan ya tafi na samu Mamanmu a ɗaki na faɗa mata abunda yace, sai tace zuwa safe na aika Sakina taje ta ɗauko mini wasu kaya wanda ba a ɗinka ba a cikin akwatina sai a kai ɗinki express, nace mata to sai da koma ɗaki na kwanta ina mamakin Umar daya rungume hannu komai sai dai a yi masa baya kataɓus ya sakarwa Iyayena hidimar daya dace shi zai yi, su kuma sun dage suna yi mini komai saboda babanmu bai yarda da ƙaranta ba kuma yana da rufin asirinsa dan haka komai ya yi mini bai faɗi ba, sannan ma duk abunda ke faruwa ban ji wani daga cikinsu yayi ƙorafi akan Umar ba.
Washe gari Sakina taje ta ɗauko mini atamfa super was da swizz les, Mamanmu ta bayar ɗinkin sauri a waje sannan ta aika ƙanwata kasuwar bacci ta siyo wa Baby rigar fitan suna mai kyau sai aka adana.
....
Ana gobe suna gidansu Umar suka aiko da shinkafa rabin buhu, fulawa da mangyaɗa da sauran kayan da duk muke buƙata, gaskiya sunyi mana ƙoƙari dan babu wanda yayi ƙorafi akan abinda suka kawo, wanda na san babansu ne yayi komai ba sisin Umar a ciki. Haka 'yan uwa suka fara aikin donot da sauran ayyuka kafin gobe, ni kuma na wanke kai Mamanmu ta kira mai kitso aka yi mini kitso da lalle anan ɗakin da nake jego, data gama aka biyata ta tafi ni kuma na fito shar dani kamar wata sabuwar amarya, saboda a ɗan kwanakin dana yi a gidanmu na yi kyau da kumari, ga jikina ya murje saboda zaman guri ɗaya ga kuma abinci dana ke samu mai kyau.
Ranar suna yaro yaci suna Sunusi sunan mahaifinsu Umar sai muka saka masa Amir, anyi taro lafiya an watse lafiya, sai dai ni kuma an watse an bar ni da ƙunar zuciya saboda irin yadda ƙannan Mamanmu suka dinga gwasaleni da kushe kwalliyata, dama na san ba zan taɓa fari ba a gurinsu duba da irin yadda Mamanmu take nunawa a kaina kamar ni ba 'ya bace, shiyasa Sakina ce tasu, ita ce in tayi abu suke yaba mata da fatan alkhairi saboda Mamanmu ta nuna tafi sonta, amma ni dama daga kushe ne sai fatan tsiya suke yi mini da mugun alkaba'ir, shiyasa Inna Maryam ta ciri tuta a cikinsu duba da irin kyautatawar data nuna mini lokacin da nake fama da laulayi, haka na tsare hawayena tare da kawar da damuwar a raina duba da ba yanzu ne mafarin abunda suke yi mini ba, saboda da iyayena basu nuna kyara a kaina ba to bana zaton akwai wanda zai yi mini mugun kallo, dan irin furucin da Mamanmu take yawan faɗa mini wanda har shima babanmu in ransa ya ɓaci yana faɗa mini mummunar kalami, to da ace ina da wani mugun halin da nake ƙuntata musu to tabbas da haƙƙinsu ya bini, da la'anta da lalacewa ta same ni, sai-dai kuma bani da haƙƙinsu duba da ina gudun ɓacin ransu da son kyautata musu, duk da wani lokacin in na yi abu dan faranta musu sai dai a gwasale ni da nuna ban yi ƙoƙari ba. Hmmm na share hawaye na ina murmushin takaici tare da godewa Allah da yayo ni cikin musulunci tare da samun wadataccen ilimin addini wanda yake kore mini damuwar da nake samun kaina a ciki.
Rahma Kabir ce.