6
KOMAI YAYI FARKO...
Na
©®Rahma Kabir MrsMG.
Page 6.
Sarac Stars R Pen...
Na san ƙannen Mamanmu suna kushe kwalliyata ne dan basu da abunda zasu kushe a taron sunan duba dangin mijina sun fito dani, sunyi mini ƙoƙarin da na fita kunya ga 'yan uwanmu, dan ko ragon suna ƙato suka kawo aka yanka, komai sunyi babu ƙaranta, dan kayan Barka ma sun kawo mini atamfofi guda huɗu ga kuma kayan yaro set biyar da bargo da kayan sanyi, kaya dai masu kyau wanda har Amir sai ya taka yana morarsu, shiyasa idan na tuna da wannan sai naji farin ciki a raina ko ba komai auren ya jawo mini ƙima da raguwar ƙasƙanci ga 'yan uwana, duk da shi uban gayya ba jin daɗin zama da shi nake ba amma 'yan uwansa mutanen kirki ne da za a yaba musu. Haka aka watse taro kowa ya kama gabansa dan washe gari da wuri suka yi suyan naman rago aka raba aka kaiwa duk wanda yake da alhakin a kai masa, sai zaman ya zama daga ni sai 'yan gidanmu.
Washegari ina zaune a gefen gado ina shafa mai sai Mamanmu ta ɗaga labule tana cewa.
Idan kin gama ki fito ki gyara gidan nan, kiyi shara da wanke-wanke tunda su Sakina sun tafi makaranta.
Shara kuma Mamanmu.?
Na faɗa cike da mamaki, sai ta galla mini harara tana cewa.
Eh ko ba zaki yi bane.? Ai gwara ki nuna mini ban isa dake ba tunda kin zama cikakkiyar mace.
Kiyi haƙuri yanzu zan fito nayi.
Na faɗa ina miƙewa tare da ƙarasa goga mai a jikina, sai ta saki labule tana jan tsaki ta wuce na bi ƙofar da kallo ina mamakin wannan hukunci na mama, ni da nake jego me zai haɗani da aikin gida bayan nazo gida wanka ne dan na huta na warke sosai a kuma koya mini raino kafin na koma gidana, sai kawai na kawar da tunanin na gyarawa Amir kwanciya, na tare shi da filo yadda zai ji ɗumi yaji kamar ina tare da shi, na fito tsakar gida na fara shara, sai dai tsugunawar da nayi naji ƙasana yana yi mini ciwo dan har lokacin ɗinkin da aka yi mini bai gama warwarewa ba, haka dai na yi sharar a daddafe na koma kitchen na fitar da wanke wanke na fara yi anan tsakar gida ga iska da sanyin safe yana kaɗawa, bayan na gama na adana komai a inda yake sai na wuce ɗakin mama inda nake jin hirar ta da babanmu saboda bai riga ya fita ba, na rusuna na ce.
Sannu baba da hutawa.
Yauwa ina abokina.
Yana bacci a ɗaki, Mamamu na gama aikin.
To sai kije ki kwanta, ba gashi yanzu kin gama ba, wa zai ce kinyi aiki, kuma ma ai motsa jikinki shi ne zai sa ki ƙara samun lafiya.
Cewar Mamanmu sai na miƙe da nufin na tafi amma sai na ji babanmu yace.
Ke Farida, a gaskiya bana son ganinki a gidan nan maza ki shirya ki tafi makaranta, in ba haka ba sai dai ki koma gidanki. Ai yau ma kuna da shi ko.?
Eh amma lokaci ya tafi dan ƙarfe tara ake rufe gate kuma yanzu tara ta wuce.
Haka nan zaki tafi kiyi maza ki shirya ki wuce. Dan bana son ina shigowa ina ganinki koda yaushe a gidan nan.
To nace masa idona yana kawo kwalla na fito daga ɗakin na koma ɗakina na soma duba uniform ɗina dan dama lokacin na muka je asibiti sune a jikina sai da na haihu ne na sauya kaya, to an wanke su na adana, haka na cirosu ko guga babu na saka tare da goya Amir a bayana na ɗauki duk abunda zan buƙata, duk da jaka ta tana gidana, na gama shiri na fito na leƙa ɗakin Mamanmu na ce na tafi sai tace a dawo lafiya kar dai na zauna da an tashi na dawo gida, nace mata to sai na fito raina ba daɗi.
Da yake ina da kuɗi sai na hau napep na wuce gidana, koda na shiga ban tadda kowa ba dan nasan Zainab ba mai zama bace, dan haka na wuce na buɗe ɗakina dana ganshi kaca-kaca na ɗauki jakar makaranta na fito na rufe ɗaki, sai na sake hawa napep ya kaini kamaranta. Da muka ƙarasa na sallami mai napep na shiga cikin makaranta sai dai ban ƙarasa shiga ajinnmu ba naji Malama Fatima ta kwala mini kira, sai na juya na tsaya ta ƙaraso cikin sauri.
Farida baki da hankali ne zaki fito da ɗanya jego, ina ce shekaran jiya aka yi suna.?
Murmushi nayi mata ina sunne kai ƙasa, sai ta cigaba da ƙare mini kallo fuska a dame.
Wani irin son karatu ne da zai sa ki fito yanzu, Farida ba a fita fa, hala ba a yi miki ɗinki ba.? na tabbatar in anyi to bai kai ga warkewa ba, kuma wannan tafiyar da kike yi shi ne kesa gaban mace ya buɗe ta riƙa tusan gaba.
Murmushi nayi mata na kasa cewa komai sai kawai tace na wuce aji amma na kula da kaina dan haihuwar fari ba wasa bane, to nace mata ina yi mata godiya na wuce aji, nan ma haka 'yan ajinmu suka dinga yi mini surutun meyasa na fito, malama Hadiza itama ta shiga yi mini faɗa, ban iya basu amsa ba sai murmushi dan inna buɗe baki ban san me zan ce musu ba, haka na samu guri na zauna ina ɗauko littafin da ake karanta mana. Wajen ƙarfe sha biyu da kwata aka tashe mu dan haka koda na fito sauran malamanmu mata suka kirani suka yi mini ca da faɗa, ni dai sunne kai nayi ina wasa da hannun jakata, da suka gama Malama Hadiza tace.
Nasan kina da son karatu Farida tunda tsohon ciki bai sa kin daina zuwa ba, amma ya dace ace kin tsaya kinyi koda wata guda ne sai ki fara fita, ko da yake da baki samu lafiya ba ba zaki fito ba tunda gashi jikinki ya nuna, sauko da yaron mu ganshi.
Sai a lokacin na saki ɓoyayyen a jiyar zuciya na sauko da Amir na bata, nan suka shiga ɗaukarsa suna yi masa addu'a, da suka gama ta bani shi na goya sai suka haɗa mini dubu biyu na amsa ina godiya nayi musu sallama na tafi, ban ɓata lokaci ba na samu abin hawa na wuce gida, wajen ƙarfe ɗaya saura na isa na samu Mamanmu tana haɗa gawayi zata ɗaura girki.
Sannu da gida Mamanmu.
Yauwa kin dawo, to sai ki aje goyon ki cire uniform kizo ki ɗaura girkin nan, bari Usman ya je yanzu ya ƙaro kayan miyan, sai ki yi miya akan gawayi a ɗaura shinkafa a gas.
To nace mata na koma ɗaki ina sauke ajiyar zuciya dan na gajiya, na sauya kaya na bawa Amir nono ya sha kafin na kwantar da shi na fito na fara aikin abinci. Wanda sai wajen ƙarfe biyu da mintuna muka gama dan ma gas da gawayi nayi amfani da shi, dana gama na zuba naci na ƙoshi na sha ruwa sai na bi lafiya gado dan bacci ke damuna saboda bana samun bacci mai kyau da dare saboda rigimar Amir.
Tun daga wannan rana na koma makaranta sannan aikin gida ya dawo nawa, shara da wanke-wanke da girki saboda duk Ƙannena suna suna zuwa makaranta ita kuma Mamanmu ta samu damar hutu, wani lokacin kuma haka take fita anguwa a bar ni da tsaron gida. Tun ina yin aikin nan cikin jin daɗi da ƙarfina wlh har sai da na fara gajiya dan sosai na soma yin rama na kuma ƙara duhu, shiyasa na ƙosa mu ƙare wankan na koma gidana dan yanzu ma wanka ni nake yiwa kaina haka Amir nice nake yi masa, da yake nashi ya zama wanka ɗaya ne da safe idan nayi masa to shi kenan ba za a sake wani ba.
Wata guda kenan da haihuwata amma satin farko shi ne nayi shi cikin jin daɗi da kulawa a gidan mu, sauran kuma tamkar 'yar aiki na zama, ban mance shekaran jiya ba da naje makaranta, wata 'yar ajinmu tana yi mini magana sai ta dafa wuyana nan take taji ƙashi, sai ta zaro ido waje tace cikin faɗa.
Anya Farida kina cin abinci kuwa.? kin ji ƙashin wuyanki gasu nan sun fito, ɗanyan jego kike ciki fa dole ki riƙa cin abinci saboda yaronki ya samu ruwan nono.
Wlh ina cin abinci sosai.
Na bata amsa sai ta shiga bani shawara tana gaya mini yadda zan riƙa kula da kaina, na yi mata godiya dan gaskiya na ɗauketa kamar uwa dan babbar mace ce da yaranta manya, shiyasa zama da ita yake ƙara mini sanin yadda zamantakewar aure yake. Na sauke numfashi ina miƙewa da sauri dan naji mama tana kwala mini kira, na amsa na ƙarasa inda take tsaye.
Ga wuta nan na haɗa ki fara suyar wainar, idan Sakina ta kawo cefane ki ɗaura miyar a gas zan je nan maƙota na dawo, kiyi mini aiki mai kyau bana son shiririta.
To sai kin dawo nace, sai ta gyara mayafinta ni kuma na zauna a kujerar tsuguna na fara suyar waina zuciya ta a takure, ji nake kamar nayi tsuntsu na koma gidana ko zan huta, amma kuma inna tuna da irin riƙon da Umar yake yi mini sai naji gidan nasa ba wajen da za a yiwa ɗokin komawa bane, yadda banyi cikowar jegon nan ba nasan inna koma ƙara lalacewa zanyi tunda babu abinci mai kyau, nan kuma ina cin mai daɗi na ƙoshi, kawai hutu ne babu, haka dai na cigaba da aiki ina tunani har Sakina ta dawo daga kasuwa ta aje mini cefanen ta shige ɗaki, ganin ban gama suyar wainar ba na kwala mata kira ta amsa ta fito tana yatsine fuska.
Sakina ki taya ni wanke kayan miya ki jajjaga na ɗaura miya, kinga ban gama suyar wainar ba.
Wlh babu abunda zanyi nima na gaji.
Ni kike faɗawa kin gaji, kwata-kwata aikin me kika yi in banda wannan aiken.
Ni dai ba zanyi komai ba wlh.
Tana gama faɗar haka ta juya ɗaki ta kwanta, raina ya ɓaci amma babu halin nayi mata faɗa, nasan sai ta nima haɗani da mama shiyasa na ja baki nayi shiru na fara aikin miya kamar Agogo. Mamanmu ta jima bata dawo ba amma ko da ta shigo ta tadda na gama suya, miya ne yake kan wuta, sai ta rufeni da faɗa wai na bar gida kaca-kaca ban gyara ba, hala ƙazantar da nake yi kenan a gidana in ina girki, watarana abincina ba zai ciwu ba, ban ce komai ba sai na ɗauki tsintsiya na fara shara, dana gama na koma ɗaki na zauna ina mayar da numfashin gajiya, Sakina kuma ta miƙe tana jan tsaki ta fice a ɗakin, girgiza kai kawai nayi ina jin kamar na fasa kuka ko na samu sassauci.
A haka dai na cigaba da jurewa har Allah yasa muka cika kwana arba'in cif da wanka. A washegari ƙaramar ƙanwar su Mamanmu tazo akan itace zata raka ni gidana, na gama haɗa kayanmu tsaf, sai dai kuma gyaran da ake yiwa mai jego ba'a yi mini ba dan ko garin magani mamanmu bata bani nasha ba, saɓanin lokacin bikina da aka haɗa mini kayan gyara sai kace wata bazawara dan har sai na ya hau kaina ya ishe ni, amma yanzu ko dabino ba a bani ba ban samu wannan arzikin ba, nima kuma bani da wayon da zan yiwa kaina wannan abubuwan dan bansan inda zan same su na siya ba. Haka nayi sallama da Mamanmu muka fito muka shiga mota da aka samo mana, ƙanwar Mamanmu tana zaune a baya da kaya ni kuma ina zaune a tsakiya da sauran kayanmu sai Sakina tana gaba kusa da direba, su biyu kawai suka yi mini rakiya zuwa gidana. Sai dai bayan mun isa gidan muka tadda shi kaca-kaca kamar na yi shekara bana nan, kitchen ɗina kuwa nan ne dabdalar ƙazantar yake, dan har bi tsami yake tashi akan kwanukan da aka yi amfani da su ba a wanke ba, ga kuma rice cooker ɗina an dafa makaroni a ciki ya ruɓe ya lalace yayi hunhuna har da tsutsa, risho ɗina kuwa anyi amfani dashi duk abinci ya zube akai yayi baƙi, haka tukwanena anyi amfani dasu bayan duk sunyi baƙi sosai, ƙanwar Mamanmu ta shiga yin faɗa tana sababi saboda takacin abunda muka gani, dole muka fara yin kwalima ba shiri da kaɗe ƙura, muka gyara ɗakin har da mopping, wanke-wanke ne suka yi mini kaɗan akan sauran na riƙa yi a hankali saboda an kira sallar magariba zasu tafi, da yake bayan sallar la'asar muka zo gidan, nayi musu godiya tare da rakiya zuwa ƙofar gida suka tafi, na dawo ciki na zauna ina mayar da numfashi, Amir ya fara kuka na ɗaukeshi na goya na koma kitchen ina duba kayan da zan yi kwalimarsu dan gaskiya da yawa, wasu kuma suna cikin kwali ban taɓa amfani dasu ba iyaka sai dai na goge su na mayar dasu mazauninsu, shiyasa na bari zan riƙa ɗiban aiki kaɗan-kaɗan ina yi dan ba zai wuyu na yi shi lokaci guda ba kuma ni kaɗai ga kuma rainon Amir, sai na koma uwar ɗaka na ɗauro alwala na zo na gabatar da Sallah, ina idarwa naji ƙarar waya daga jakata, sai na tuna babanmu ya bani ƙaramar waya na saka sim ɗina, na ɗauko na duba naga Mamanmu ce sai na ɗaga da sauri ina miƙa mata gaisuwa, bata amsa ba naji ta fara surfo mini zagi tana faɗa.
Yanzu saboda rowa Farida ba zaki iya yi musu girki ba, duk wannan uwar aikin da suka sha haka suka dawo da yunwa.
Wlh Mamanmu aikin ne da yawa saboda nima dole na saka musu hannu muka yi tare, shiyasa ban samu damar yin girki ba.
Wannan ba dalili bane rowa ce kawai.
Kiyi haƙuri.
Nace mata, haka ta cigaba da faɗan data gama sai ta kashe wayar na sauke ajiyar zuciya, banda abun Mamanmu na dawo yau da yamma ina naga cefanen da zanyi wani girki, kuma kafin mu tawo sai da muka ci abincin rana a gida, ko ni banda aikin da muka yi ba wani yunwa nake ji ba, Allah kaɗai yasan me Sakina taje ta faɗa mata dan na san halinta zata iya ƙulla mini sharri, sai na miƙe na cire hijab na ɗauki Amir na koma falo na soma bashi nono.
Bayan sallar Isha'i Umar ya dawo ya zauna yana kallona banga wani ɗokin ganinmu da yayi ba akan fuskarsa, nan muka gaisa ya amsa Amir ba jimawa ya miƙo min shi yana tambayata me na dafa, nace banyi komai ba tare da bashi labarin aikin da muka sha, sai ya mele baki yana cewa.
Ni kuma gashi ba ni nauyi sosai.
Aiko kayan tea zaka siyo da bread musha, Dan bani da ƙarfin yin girki yanzu.
Nace ina dubansa sai dai ban gane a wani yanayi yake ciki ba, daga ƙarshe ya miƙe ya fita ba jimawa ya dawo da kayan tea muka haɗa muka sha muka kwanta. Na ɗauka Umar zai neme ni a wannan lokacin duba da irin kwanakin da muka kwashe bama tare sannan ma na san halinsa na matsa mini da yake yi da, ban zata zai kalle ni ya kawar da kai ba tunda yasan nayi tsarki ina Sallah, sai dai abun mamaki haka muka shafe mako guda ba labari, dan haka nima sai hankalina ya kwanta saboda gaskiya ba son abun nake yi ba, sannan naji ance mace tana saurin ɗaukar ciki kuma bana son nayi gwanne.
Rahma Kabir ce.