7
KOMAI YAYI FARKO...
Na
©®Rahma Kabir MrsMG.
Page 7.
Sarac Stars R Pen...✍️
Na cigaba da zuwa makarantar da nake koyarwa da kuma sanawiyyar da nake zuwa, sai ya zamana kwata-kwata bana zama a gida sosai shiyasa damuwar Umar bai fiye damuna ba domin babu abunda ya sauya a zamanmu na tun kafin na haihu zuwa yanzu, kamar yadda ya saba babu cefane sai dai manejin da ya sabar mini na cin abinci mai da yaji, sannan bana girki sai da wutar nefa dan yaƙi siyo kalanzir balle azo maganar gas, sauƙina a wannan lokacin babu ciki sai goyo, to na riga na sabarwa kaina juriyar yunwa, in kuma ina da kuɗi sai na tsumulmula na samawa kaina abunda zan ci. A haka har tafiyarmu ta miƙa muka kai wata shida cif da haihuwar Amir wanda har zuwa lokacin babu abunda ya shiga tsakani a da Umar bai kusance ni ba, nima kuma ban nime shi ba dan a zatona haka ake yi duk in mace ta haihu miji baya kusantarta saboda ba ni da ilimi akan haka, kuma babu wanda ya zaunar da ni ya faɗa mini ga yadda abun yake, sannan ni ina da zurfin ciki babu wata shaƙiƙiyata da zan iya faɗawa haka balle nasan cewar ba haka abun yake ba, saboda a hankali Umar sai da ya raba ni da ƙawayena saboda baya bari ina zuwa gurinsu, daga makaranta sai gidansu da gidanmu, ko sha'anin 'yan uwa ya taso sai ya gadama yake bari naje.
Da yamma na dawo daga makaranta dan yanzu na daina jiransa a gidansu ana tashi nake dawowa gida na ɗaura abunda nake da shi, na duba naga shinkafa kawai muke da shi sai sauran manja gwangwani ɗaya da ya siyo rannan, na duba jakata na samu Naira ɗari biyu da hamsin sai na fita na siyo tattasai na ɗari da Maggi na ɗari na dawo na ɗaura sanwar dafadukan shinkafa, sai na dawo falo na zauna ina duba wani takarda dan mun kusa fara jarabawa, a haka har aka kira sallar magrib na miƙe na duba abincina ya yi, sai na sauke na fito naje nayi alwala na gabatar da Sallah, dana idar na dawo falo na zuba abinci naci na ƙoshi kafin na kora da ruwa, na cirewa Amir pampers na saka masa na dare na lallaɓashi yayi bacci sai na miƙe na gabatar da sallar isha'i da ake ta kira, ina idarwa na zauna ina lazumi sai ga Umar ya dawo ya shigo cikin sauri kamar an jefoshi.
Lafiya ka shigo da sauri kamar an biyo ka.?
Na faɗa cikin tare masa hanzari, guntun tsaki yaja yana shiga kitchen ya fara buɗe buɗen tukunya, da ya gama ya fito yana tsayawa jikin ƙofar kitchen ya dafa bango.
Abunda kike dafa kenan.?
Eh ban daɗe da gamawa ba.
Gaskiya na gaji da cin shinkafar nan gashi da yunwa na shigo gidan.
To ita kenan gare mu, Kaga kuwa hakanan za muyi haƙuri tunda baka ƙaro kayan abinci ba.
Na ƙare maganar ina ninke dadduma, bai tanka mini ba ya ƙara ficewa daga gidan yana jan tsaki, sai na taɓe maki ina cewa.
Kai dai ka sani.
Na koma Cushing na cigaba da duba takarduna, ina zaune haka har bacci ya fara kamani daga bisani na miƙe na koma ɗaki na saka Kayan bacci na kwanta kusa da Amir da baccinsa yayi nauyi. Ban san lokacin da Umar ya dawo ba sai sadda naji yana ƙoƙarin raba ni da rigar jikina, na yi saurin riƙe masa hannu ina bude ido da kyar tare da ƙare masa kallo dan na tantance shine ko shigo mini aka yi, ganin Umar ne yasa na cigaba da bin inuwarsa da kallon mamaki, dan ɗakin da duhu sai hanken wutan waje ne ke ratso wa da ya sa na gane shi ne, sai yau wata shida da kwana biyu ya tuna da ni matarsa ce zai iya samun abu a jikina, dan ni azatona sai na yaye kafin zai waiwaye ni, wata shida fa rabonmu da juna ai ba kwana shida bane, duk da a tunanina haka ake auren, dan haka ban yi masa musu ba na bashi haɗin kai ya samu natsuwa ni kuma ya barni da ciwon jiki, a daren sai da Umar ya kusace ni sau uku kafin hankalinsa ya kwanta. Haka na wayi gari da ciwon kai saboda rashin wadataccen bacci da kuma ciwon jiki da Umar ya haifar mini, amma duk da haka bai hanani yin aikina ba na wanke kayan Amir da kullun sai na wanke saboda bana so su tarasu, sannan na damawa Umar kamu da ya siyo yasha koko, ni kuma na sha lipton da sauran guntun biredin jiya, ina tsaka da shirin tafiya makaranta da yake yau Asabar makarantar safe muke da shi, sai naji Umar yana cewa.
Ina so zamu tashi a gidan nan saboda ba ni da kuɗin da zan cigaba da biyan haya.
To idan mun tashi mu koma ina.?
Zamu koma in da bai kai nan kuɗi ba, saboda dama lokacin aurenmu bani ne na biya kuɗin haya ba babanmu ne ya biya dubu ɗari da hamsin, to ni kuma yanzu bani da halin biya shiyasa na saka aka fara cigita mini gida, to an samu a can Badikko two bedroom filat ne amma da gyara sosai.
To ban da abun ka nan ai ciki da falo ne, taya zaka nima mai ɗaki biyu kuma kana maganar ba kada kuɗi.
Saboda nan cikin gari ne, can kuma baya ne sannan tsohon gida ne ko tiles babu kuma da gyara sosai, sun ce na bada dubu Tamanin, kin ga yafi nan sauƙi sannan ba muyi nisa da gida sosai ba.
Cewar Umar da ya cigaba da kurɓan koko yana jiran me zan ce, sai na nisa nace.
Allah yasa hakan shi ne mafi alkhairi a gare mu.
Ya amsa da amin kafin ya miƙe yace na fara haɗa kaya dan yana so mu bar nan gidan a cikin satin, nace masa to kafin ya wuce ni kuma na ƙarasa shirin makaranta na tafi. Tun daga wannan ranar sai na fara shirin tashinmu na haɗa kaya har ƙanwata na kira ta zo ta taya ni, na kuma faɗawa Iyayena suka yi mini addu'a akan Allah yasa hakan shi ne mafi alkhairi, Mamanmu ta bani kuɗi na je na siya ledar tsakar ɗaki dan na faɗa musu gidan ba tiles bane.
Ranar tashi ya zo ya kawo mota muka tattara kayanmu aka kwashe su tas zuwa sabon gida, nayi sallama da Zainab cike da kewar rabuwa da juna dan gaskiya munyi zaman amana da ita, na shiga maƙota suma nayi musu sallama muka wuce sabon gida Zainab ta yi mini rakiya. Ko da muka isa aiki muka fara tare da saka komai a muhallinsa, muka shimfiɗa sabon ledar tsakar ɗaki a falo da ɗakin da muka saka gado, ɗayan ɗakin kuma sai dai na zuba sauran tarkace kayana, dan kitchen babu kitchen cabinet dan haka wasu kayan sai muka zuba a ɗakin, muka gyara ko ina gida ya fito fes duk da tsohon gini ne kuma babu sabon fenti, ga toilet ɗin dake ɗakina ma na ploshing ne amma bana zama ba kamar na wancen gidan, a gaskiya dawowa na wannan gidan ba ci gaba bane sai ci baya duk da ɗaki biyu ne da falo, saɓanin wancen gidan ciki da falo ne, amma yafi tsaruwa na zamani kuma cikin mutane ne nan kuma kamar bayan gari duba da layinmu yana kusa da titin bypass, sannan mu huɗu ne ke haya nice ke da ɗaki biyu da falo, sauran matan gidan su biyu suke da ciki da falo, sai guda ɗaya da take da ɗaki ciki ɗaya. haka nayi girki muka ci kafin Zainab ta tafi ina yi mata godiya tace zata dawo in an kwana biyu, sai kuma Sakina itama ta koma gida aka bar ni da Amir.
Haka muka cigaba da rayuwa, sai dai abubuwa sun fara sha mini kai duba da nayi nisa da makarantar da nake koyarwa, ga kuma Sanawiyya da itama ta yi mini nisa, amma haka na cigaba da zuwa ina jurewa duk da na fara samun matsala da makarantar da nake koyarwa saboda lattin da nake yawan yi, na faɗawa mai makarantar mun tashi daga inda muke ne sai kawai yace hakan zai riƙa bamu matsala yana ganin mu haƙura, na shiga damuwa sosai na bashi haƙuri akan zanyi ƙoƙarin zuwa da wuri amma yace a'a, haka ya sallame ni zuciyata babu daɗi ya bani kuɗin watan duk da wata bai ƙare ba yayi mini fatan alkhairin samu wani koyarwar a inda nake, nayi masa godiya na dawo gida. Dama nayi wannan tunanin zan samu matsala da aikina duba da irin lattin da nake yi sai dai nayi zaton zasu karɓi uzuri na, saboda ina shiryawa da wuri to samun abun hawa ne ke yi mini wuya duba da safe 'yan makaranta da ma'aikata kowa yana son abun hawa, shiyasa nake latti kafin na samu na je. Sai na kira Mamanmu na faɗa mata sai tace da sauƙi tunda mun gama adashe amma nayi ƙoƙari na duba wata makarantar, dan zama haka ba zai yiwu ba saboda ta fara shirin shiga wani sabon adashen, nace mata to kafin muka yi sallama na aje kiran ina mamakin mama, wato damuwar ta shi ne nata ba nawa ba, madadin ta rarrashe ni amma damuwar ta na samu wata makarantar saboda wani adashen, sanin halin mama yasa na aje tunaninta a gefe dan zan ɓata lokaci ne akan abunda ban isa na sauya shi ba. Da Umar ya dawo na faɗa masa sai ya ce.
Ai barin aikin shi ne yafi miki sauƙi, kuma ya dace ki haƙura da zuwa islamiya tunda kin riga kin yi aure to me kike nima tunda kin yi saukar Al-Qur’ani.
Ya ƙare maganar yana kallona sai na yi shuru na kasa amsar da zan bashi da mamaki maganarsa, dama ba tun yau ba na soma fahimtar ya gaji da zuwa makarantar da nake yi, bai faɗa ba sai yau ne Allah ya matsi bakinsa, sai ya ce.
Kin yi shuru baki ce komai ba. Naga sanawiyya ce bai zame miki dole sai kin yi ba kuma JS 2 kike, ba nisa kika yi ba.
Hakane, sai dai ni bana son zaman gida tunda na saba da fitan, amma me zai hana na yi jamb na koma makarantar boko, kaga na samu damar cigaba da Karatuna sai na aje Islamiyan.
Eh hakan kuma ya yi, kin ga zaki samu ki zurfafa karatunki.
Na yi masa godiya cikin jin daɗi dan ban taɓa zaton zan samu wannan damar cikin sauƙi ba, cikin farin ciki na kwanta, a wannan daren kuma sam ban damu da yadda Umar ya dirjeni ba, duk na ƙosa Safiya tayi naje gidan mu na samu baba da maganar. Dan haka da safe ko da zai fita nace masa zan je gida nayi maganar da babanmu, yace ba matsala sai ya wuce, ni kuma na ƙarasa shirina na wuce gida.
Da sallama na shiga gidanmu na samu Mamanmu tana shara, da sauri na ƙarasa na amsa ina yi mata sannu, sai na ƙarashe sharan kafin na bi bayanta zuwa ɗakin babanmu dan can ta shiga, na kwance Amir na miƙawa baba daya kawo hannu, na zauna ina gaishesu, suka amsa cikin sakin fuska, sai mama ta shiga tambaya ta lafiya nazo da sassafe haka.? sai na ce cikin murna.
Umar ne ya amince da na cigaba da Karatun boko na, shi ne nazo na faɗawa baba.
Kai Masha Allah na ji daɗin wannan magana, dama kuma ina burin ki zurfafa Karatunki, kawai dai bana so na matsa da maganar ne mijin ki yazo baya so. To yanzu bari na baki kuɗin jarrabawar Jamb ki je ki biya, In Sha Allah ni zan cigaba da ɗaukar ɗawainiyar karatunki kamar yadda na fara.
Nagode baba Allah ya saka da alkhairi.
Ya amsa da Amin sai ya miƙo mini Amir ya miƙe ya isa inda ya aje kuɗi, ya ƙirga mini dubu biyar ya bani yace inda ƙari sai na kira shi na faɗa, na amsa ina godiya sai mama tace.
Sai ki tashi kije ki biya kuɗin tunda naji ana ta biya, Allah yasa basu rufe ba.
To Ameen nagode.
Na faɗa tare da goya Amir a bayana na ƙara yi musu sallama na tafi. Daga nan gidanmu can wata makaranta Nanu Acadamy dake tudun wada na wuce, dana ƙarasa ba ɓata lokaci na biya kuɗin dubu huɗu da ɗari biyar, sai kuɗin scratch card ɗari biyar, suka ce nayi sa'a dan an kusa rufe wa, nan nayi godiya na fito na koma gida cike da farin ciki bisa wannan sa'a dana yi tare da tunanin fara karatuna a Jami'a.
Tunda na biya jamb sai na shiga duba littafaina na secondary da addu'ar Allah ya bani nasara na ci, Kuma na cigaba da zuwa islamiya da niyar inna samu jamb da Admission sai na aje Karatun islamiyar, duk da ba haka Umar yaso ba amma dana yi masa bayani sai yace mini to. Ranar da zamu zana jamb ta zo naje nayi anan center da aka kai ni Kadpoly. Bayan wasu kwanaki sakamako ya fito na samu maki 180 kuma dama KASU suna buƙatar daga 170 ne zuwa sama. Sai dai kuma bayan na zana jarabawar post UME ban samu ba saboda suna niman maki Hamsin ne ni kuma na samu maki talatin da biyar, dan haka maganar cigaba da karatuna ya tsaya, sai na cigaba da zuwa islamiya.
Tafiya ta miƙa aka kai wani lokaci wanda anan ne kuma zuwa makarantar islamiyar ya fara zama mini matsala, dan Umar ya soma saka zargi a zuwan da nake yi, wanda ni kuma nasan duk lalacewata bazan je nayi rashin hankali a islamiya ba, sannan ma shugaban makarantar yana matsayin Uba ne a gurin Babanmu na family, shiyasa ko fashi nayi yana sani kuma sai ya kira Babanmu ya faɗa masa ban je ba, saboda duk in naje makaranta ina zuwa na gaishe shi ko kuma mu haɗu a bakin gate in zan shiga, dan haka ko dan Baba Ahmad ba zan yi wani shashanci ba dan duk abunda na aikata babanmu zai ji. Na kalli Umar fuskata a cikin damuwa dan ya dage akan dole na daina zuwa Islamiya, nace masa.
Dan Allah me nake aikatawa da zaka yanke mini wannan hukuncin.?
Hmmm, me kika mayar dani ne Farida, ko bani da hankalin da bazan san me kike aikatawa ba, to an gaya mini kina da tsofaffin samarinki a Islamiyan shiyasa kike son zuwa.
To idan har ka ɗauki haka sai ka bar ni da hali na amma ka bari na cigaba da zuwa Islamiyan, saboda babanmu yayi mini barazanar lallai in na daina zuwa Islamiyan ba shi ba ni, dan yaga so nake na daina zuwa, shi ne yace ya zama dole na riƙa zuwa in dai ina numfashi da lafiya, saboda babansu yana matuƙar son karatunmu.
Hmmm shi kenan ai.
Umar ya faɗa ya miƙe ya shige cikin ɗaki, ban bi bayansa ba na cigaba da zama a inda ya bar ni zuciya ta babu daɗi, Meyasa Umar yake zargina da kula samari.? Na fahimci tun farkon aurenmu ya taɓa faɗa mini magana makamancin wannan har ya cire mini Sim ɗina, a wannan lokacin gaskiya maganar ta ɓata mini rai sosai, duk yadda nake kafa-kafa da kar na ɓata masa rai amma sam baya gani, yanzu yadda ya sanni yasan halina har za a gaya masa magana ya ɗauka, bayan yafi kowa sanin wacece ni Farida, sai na girgiza kai tare da yin kwafa na cigaba da duba takarduna.
Rahma Kabir ce.