8
*KOMAI YAYI FARKO...*
Na
©®Rahma Kabir MrsMG.
Page 8.
Sarac Stars R Pen...✍️
Umar ba dan yaso ba na cigaba da zuwa makarantar, sai dai kuma ya hudo mini da sabon doka na duk in zan fita dole sai na saka wando lagis a ciki da safa, musamman ma in zamu fita tare zai kaini gidanmu ko gidansu ko wani guri haka in zai ɗauke ni a mashin, ban damu ba saboda dole nayi masa duk abunda yake so matsayinsa na mijina, kuma kula da kaya ai yafi ban cigiya sai ana son mace ake kishinta, sai hakan ya fara bin jikina da wannan shigar koda siket na saka ko doguwa riga dole sai na saka wando lagis a ciki da safa a ƙafa ta, amma kuma duk ran da na manta ban saka ba sai ya fara faɗa cewar saboda naga Jikina yana da kyau ne shiyasa ina yiwa maza talla, kuma fa ba shi ne ya siya mini lagis ɗin ba ya dai ganni da shi ne kuma bai tambaya a ina na samu kuɗi na siya ba ko a ina aka bani ba duk bai sani ba, kuma dalilin da ya saka na siya lagis ɗin saboda wani lokacin ina takura da saka pant dan haka nake sakawa musamman in nasan zan daɗe a guri sai na saka na samu walwala. Sai ya zama duk lokacin da na kuskure masa sai ya riƙa jifana da ina tallar jikina ga maza. Rannan dana gaji da ƙorafinsa sai nace masa mai zai hana ya siyo mini wani lagis ɗin da safa, dan safata ta lalace ta ɓule bana iya sakata dan kwana biyu haka nake tafiya makaranta, wani lokacin ma a hana ni shiga saboda rashin safar, sai dai na je ta bayan ajinmu na amsa a gurin wata wacce muke zama benci ɗaya ta bani nata kafin na saka na zagaya na shiga makaranta. Sai naji yaja tsaki bai sake kula maganar ba, daga haka sai ya rabu dani na cigaba da harkokina ba tare da wani ƙorafi ba, sannan bai siya safan ba sai dai ni ce dana je gidanmu na samo wani safa cikin na Ƙannena na ɗauka na cigaba da amfani da shi.
Bayan mun shiga shekarar 2016, sai Babanmu ya sake biya mini jarrabawar WAEC ni da ƙanwata dan a lokacin zata fita Secondary, ni kuma ina da matsala a Maths kuma ance lallai sai ina da shi zan samu Admission a KASU, dalilin daya saka kenan naje na samu babanmu da maganar sai yace faɗuwa ta zo dai dai da zama itama ƙanwata zata zana, dan haka muka je aka yi mana registration a wata makarantar maza na secondary dake Kabala, duk da makarantar ta maza ne amma in lokacin WAEC yayi mata suna zuwa suyi, sannan centern makarantar yana da kyau shiyasa ake tururuwar zuwa can.
Lokacin jarabawa da yazo sai muka fara zuwa amma Amir ina barinsa a gidanmu, idan mun je mun zana mun dawo sai na biya gida na ɗauke shi na wuce gidana. To ranar da muka yi paper na uku na ɗauko Amir na koma gida ina kiciniyar haɗa mana abinci sai ga Umar ya shiga da yamma, nayi masa sannu da zuwa ya amsa yana cewa.
Ba dai sai yanzu kika dawo ba.?
Wlh kuwa shigowa ta kenan ko uniform ban cire ba, kasan sai da na biya gida na ɗauko Amir.
Gaskiya ina ganin dole zaki riƙa tafiya da shi.
Ya ƙare maganar yana zama, sai na dakatar da abunda nake yi na tsaya ina kallonsa.
Haba Umar me yasa zaka ce haka.? bafa jami'a bace, makaranta ce da nake zana exam, taya zan samu damar rubuta jarabawar da Amir.? Sannan kasan watarana tun safe nake fita sai yamma zamu dawo saboda yawan papern da zamu zana.
Ni dai na gama magana.
To wlh ba zai yiwu ba, tunda ba shirme nake zuwa yi ba, sannan Amir gidanmu nake kai shi ba titi nake barinsa ba.
Haka kika ce ko.
Yace cikin fusata sai nayi banza dashi ya cigaba na sababi, dana kasa haƙuri na biye masa muka cigaba da yin faɗan, kuma ba ƙaramin rikici muka yi ba a ranar, haka muka kwana a wannan daren ko wanne rai ba daɗi. Tun daga wannan ranar sai muka fara takun saƙa, daga wannan rikicin sai Umar ya hudo da cewar ai bai yarda da kuɗin motar da babanmu yake bani ba, kuma bai yarda na riƙa jerawa da Sakina ba saboda ita budurwa ce ni kuma matar aure, saboda wai inna jera da ita in saurayi ya tsayar da ita zasu ɗauka ni budurwa ce , shiyasa nake ɗaukar kaina ba zan riƙa tafiya na matan aure ba cikin kamala, sai nace.
Yanzu Fisabillahi Umar ya kake so nayi.?
Ai ni ne kawai zan riƙa ɗaukarki a mashin na kai ki.
Ya faɗa cikin haɗe fuska, na saki guntun murmushi nace.
To in ka kai ni waye zai ɗauko ni ya dawo dani.?
Zan riƙa jiranki ki gama mu dawo.
Ikon Allah! Tun daga safe har yamma kenan.?
Yace Eh, sai ban ƙara cewa komai ba dan ance sa kai ai yafi bauta ciwo, kuma dama nasan ba wata sana'a yake yi ba sai buga-buga dan har lokacin ban san takamaimai sana'arsa ba, tun aurenmu har kawo yanzu dana haihu Umar bai da aiki. Dan haka sai na kira gidanmu na faɗa musu amma babu wanda yace komai, sai na cigaba da zuwa exam, Umar zai ɗauke ni da safe ko ko wani time da muke da exam haka zai kai ni har bakin hol na sauka na shiga, shi kuma sai ya juya yaje ya samu guri ya zauna zaman jirana yadda inna shiga aji yana kallona haka lokacin fitowata yana kallon yadda zai hango ni, kuma sai ya nuna bai yarda in na fito nabi ayarinsu ƙanwata ba, sai dai na zo gurinsa na zauna, dariya kawai nayi masa na ce to. Ni kuma tunda muka yi haka bayan kwana biyu sai na watsar da maganarsa in mun fito papern farko bana zuwa gurinsa sai nabi su ƙanwata muje siyan abunda zamu ci, ina hango shi tare da wasu Mazan suna magana wanda suka shigowa cikin matarantar, takaici yake ƙunsa mini na zaman banza da yake yi, sai ya share awanni yana jirana shi bai je yayi kwadago ya samo kuɗin da zai ciyar damu ba, kuma kwana biyu haka muke fitowa bamu karya ba sai dai ya ɗaukeni ya kai ni gidanmu na aje yaro na fito mu wuce, haka zan yini a gurin nan ba abinci shima kuma banga alamar ya ci komai ba sai zaman banza da surutu mara amfani, a yadda yake tunanin ni daddawa sarkin son miji ce da mun fito na isa gurinsa na zauna tare da shi har sai zuwa lokacin shiga paper na biyu, ga baƙar yunwa yana cinmu muna warin rana, ulcer kuma ta gama yi mana lahani ni da shi, shiyasa na nuna masa bazan yi yadda yake so ba gwara nabi 'yan uwana mata ko zan ji sanyi, daga nan na samawa kaina abunda zan ci, saboda Babanmu in zai bawa ƙanwata kuɗi yana bata da nawa, shiyasa bana zama da yunwa. To in na same shi zamu koma gida mun ƙare jarrabawar ranar, surutu da mita yake yi mini akan bai ganni nazo gunsa ba sai a lokacin, bana tanka masa har ya gama yayi shuru.
Bayan kwana biyu, ranar ta zo ba ni da jarabawa, da yamma ina kitchen ina aiki sai ga shi ya dawo gidan nace masa sannu da zuwa ya amsa fuska a gimtse, ban damu ba, dan na saba da ganinsa a irin haka, saboda ba yi da fara'a, amma ban sani ba ko ni ce yake yiwa haka, tun abun ma yana damuna har ya bi jikina, dan ko ciwo nake yi ba nuna damuwarsa yake yi ba, shiyasa nima na dai na damun kaina a kansa. Sai ya samu guri ya zauna ya ce.
Farida ki aje aikin da kike yi ki shirya zamu je gidanku.
Ya ƙare maganar yana miƙewa ya shiga bedroom, da ido na rakashi saboda gabana sai da ya faɗi dan irin haka bai taɓa faruwa ba, na shiga tunanin ko mutuwa aka yi ko wani ba lafiya daga cikin 'yan gidanmu, ya fito cikin sauya kaya nace cikin damuwa.
Lafiya.? Meyasa zamu je gidan mu.?
Lafiya lakau, saboda wannan makarantar da kike zuwa yin jarabawa akwai wanda yayi mini videonki kin yi saurayi a ajinku da kuke jarabawa.
Ikon Allah, wani ne ya faɗa maka haka.?
Eh.
Ya bani amsa a taƙaice, sai nace.
To shi kenan, bari na ƙarasa girki sai mu tafi.
Sai na ƙare maganar cikin damuwa na shiga kitchen, Naji kamar na ɗaura hannu akai na kurma ihu dan takaici saboda na nima hawaye na rasa, nasan Umar sharri kawai yake so ya yi mini amma babu abinda na aikata na cin amanar aurensa, nasan ƙarya yake yi dan babu wannan video da yace a ɗaukar masa, mamakina ma da wani ido zai kalli Iyayena yayi musu wannan bayanin mara tushe, idan kuma ya faɗa Iyayena zasu yarda da maganarsa ko kuwa.? Naji kwakwalwata ta bani wannan tambayar da bani da amsarsa, sai zuciyata ta ƙara tsinkewa jikina ya fara rawa, sai kawai na shiga ambaton Innalillahi wa Ina ilaihi raji'un, a hankali sai na samu natsuwa na cigaba da aikina. bayan wasu mintuna sai gashi ya ƙara leƙowa kitchen yace.
Kefa nake jira.
Wlh ba zan fita ba sai na gama aikina.
Na bashi amsa a ɗan fusace, sai naga ya girgiza kai ya yi kwafa ya koma, a zatonshi ƙila dan yace zai kai ƙarata zan rikice ne na soma kuka ina bashi haƙuri amma sai ya ga saɓanin haka, shiyasa yazo dan ya ƙara tuna mini ya ga yadda zan yi, amma sai yaga na nuna masa nima jan wuya ce. Can da ya ga bai samu yadda yake so ba sai ya kuma ce mini na zo falo na zauna muyi magana, nace masa to sai na fito na zauna ya soma ce mini.
Farida ki faɗa mini wani saurayi kika yi a makaranta.?
Ni banyi saurayi ba ban ma san maganar da kake yi ba. Saboda abunda banyi shi ina budurwa ba to banga dalilin da zai sa nayi shi ina da aure ba har da ɗa.
Sai ya soma yi mini faɗa, yana faɗa mini baƙaƙen maganganu ta inda yake shiga bata nan yake fita ba har ya gama, na ɗaga ido ina kallonsa nace.
Allah sai ya saka mini, in dai ƙazafi kayi mini ko wani malami ne yake faɗa maka ina tare da saurayi to da izinin Allah sai Allah ya saka mini.
Ina gama faɗar haka sai na tashi na shiga bedroom ɗina na share kwallar data cika mini ido, na zauna a gefen gado har aka kira sallar magariba, na miƙe na shiga bayi nayi alwala na fito na samu ya fita sai na sauke abincin da ya ƙarasa, na fito na gabatar da Sallah, dana idar na ɗaga hannu sama na kaiwa Allah ƙarar Umar tare da addu'ar Allah ya bi mini haƙƙina, dana gama na fito na zuba abinci na na ƙoshi. A ranar ban ɓata lokaci wajen tunanin Umar ba, dan bai dawo da wuri ba har bacci ya ɗauke ni, ban san lokacin da ya shigo ba.
.....
Haka zaman namu ya cigaba da tafiya kadaran kadahan, Amma kuma bai sake tayar da maganar ba har na gama zana exam. Sannan muka zo muka yi hutun islamiya sai ya zamana kullun ina gida sai sha'ani ke fitar da ni.
Kwatsam sai gashi na samu shigar juna-biyu kuma lokacin Amir yana da shekara ɗaya da wata biyu, na fara wani irin laulayi mai matukar wahala dan ya yafi na Amir, wanda ko ruwa nasha sai na amayar da shi ga kuma goyo, sannan ga ba abinci dan mun sha kwana ban dafa komai ba. Ina cikin wannan halin Mamanmu zata je gidan ƙanwarta sai ta biyo ta gidana ta same ni a cikin wannan halin, nayi amai har na gode Allah ina kwance jikina babu ƙarfi na fita hayyacina ga babu abinci, sai muka gaisa tace mini.
Gaskiya yaron nan zan tafi da shi gida a yaye shi.
To amma bai da kayan sawa banyi masa wanki ba.
Shi kenan idan zaki iya yi masa wankin to sai ki wanke, in kuma ba zaki iya ba zan aiko Sakina tazo ta ɗauki yaran da kayan sawansa.
Nace mata to tare da yi mata godiya sai ta miƙe ta tafi. To zuwa yamma sai ga Sakina tazo ɗaukar Amir, na haɗa masa kayansa duk da ban samu yin wankin ba ta tafi dashi. Sai ya zama ni kaɗai ce a gida sai wahalar laulayi, haka zan yini ina amai na kwana ina amai, sai yawan kwanciya ga wani irin jiri da yake damuna saboda yawan aman da nake yi, ga kuma yunwa ba abinci, wanda da zan samu abunda nake so na ci nasan ba zanyi amai ba amma Umar ya rungume hannu ya saka mini ido, da naga babu sauƙi sai na Allah na samu Umar nace masa.
Umar narantse da Allah ba zan iya riƙe cikin nan ba zubar da shi zanyi, saboda babu wanda zai taimaka mini kuma babu abinci, sannan in ka fita tun safe baka dawowa sai dare ka barni acikin huƙuba da bala'i.
Hmmm to ki bari zamu je Asibiti.
Abunda ya faɗa kenan, nace masa to amma jikina ya bani babu abunda zai yi akai, dan haka washegeri na matsa masa ya bani kuɗi na kama hanya na tafi wani chemist na samu wata mata a ciki, sai nataki sa'a na wayeta itama haka, na zauna muka gaisa nayi mata bayani, sai tace ya kamata nayi scanning naga ya watannin cikin, sai naga wannan duk dogon bayani ne na shiga roƙonta akan ta taimaka mini da magani na fitar da cikin dan nasan bai yi girman da zai gagara fita ba, sai ta ce to ta bani magani ta faɗa mini yadda zanyi amfani da shi, na bata kuɗin magani na dawo gida na yi amfani da maganin kamar yadda ta faɗa mini. A hankali sai cikina ya fara murɗa mini marata tana ciwo kaɗan-kaɗan, can kuma sai naji ciwo ya tado gadan-gadan kamar abu zai fito ta gabana sai kuma naji ya koma. Umar da ya dawo ya ganni kamar zan mutu sai ya saka na shirya muka je gidan Haj. Fati maƙociyarsu, muka yi mata bayani sai tace na koma gida muga ni zuwa Safiya, kuma itama ta bani goyon baya a cire cikin saboda zan fara karatu tunda bana laulayi mai sauƙi, kar nazo na samu matsala daga fara zuwa makarantar da zan shiga.
Washegari ciki bai fita ba muka koma can asibiti muka haɗu da Haj. Fati tayi wa wani likita bayani, sai ya tura mu wani ɓangare muka je aka yi ploshin cikin ya fita. Sai na samu kaina hankalina ya dawo jikina, ga Amir yana can gidanmu an yaye shi yana samun kula sosai sai kuma hankalina ya koma kan karatuna, a lokaci munyi shekara biyu da aure da kwanaki dan munyi shekara ɗaya a wancen gidan ga wannan da muke ciki shima mun shekara, cikin Ikon Allah sai ga exam ɗinmu ya fito na samu duka subject ɗin da ake buƙata, sai na ƙara zana jamb kuma shima na samu makin da ake so, kuma a shekarar muka taki babbar sa'a akan Gomna mai ci a lokacin ya soke jarrabawar post UME, sai na samu Admission anan KASU har zan fara screening, a wannan halin da nake ciki na cuku-cukun shi ga makaranta sai Umar ya hudo da maganar zamu ƙara tashi daga gidan da muke ciki.
*Wai shin wannan abu da Umar yake yiwa Farida So ne ko Ƙiyayya.? Banda na sakawa littafi nan suna komai yayi farko to da zan ƙara zaɓen wani suna na biyu to zan bashi So ko Ƙiyayya, daga ɓangaren Umar har iyayen Farida ɗan na rasa ina lamarinsu ya dosa.*
Rahma Kabir ce.