KOMAI YAYI FARKO...

9

by @rahmakabir13

KOMAI YAYI FARKO...

Na

©®Rahma Kabir MrsMG.

Page 9.

Sarac Stars R Pen...✍️

Bayan Umar ya gama yi mini bayanin sauya gida sai ya ɗauke ni ya kai ni can unguwar Kurmin mashi wani uncomplete building Kuma Arean babu mutane sosai, ko katanga babu ba a ƙarasa ginin ba dan ko filasta babu sai ƙofofin da aka saka ba silin, gidan two bedroom filat ne, sai yace nan yake so ya kama mana kuma an ce ya biya dubu ɗari da ishirin, na ga gidan yayi sauƙi duk da ba a gama ba. sai na ce

Amma aiki ne a gabanka tunda kai ne zaka ƙarasa saka abubuwan da babu a gidan, zaka saka silin, kayi filasta, kasa tiles ko siminti, sannan babu katanga, ya zanyi ni da ba zama nake yi ba, kaga bubu security tunda ba mutane sosai a unguwar, kana ganin wani ba zai samu damar shigowa yayi mana ɓarna ba.?

Wannan maganar da na yi sai ya saka shi ya haɗe fuska ya fara faɗa, nima sai na dage masa akan zamanmu a gurin ba zai yiwu ba dan na ƙara nisa da makaranta tunda KASU ba nan kusa bane kuma wani lokaci tun safe sai yamma zan dawo, ya cigaba da mita akan bai ga aibun gurin ba, sai ban sake kula shi ba ya ɗauke ni a mashin muka dawo gida baram baram, ya sake fita ni kuma sai na kira Mamanmu, sai na ce mata.

Mamanmu na samu Admission anan KASU har zan fara screening, Amma tashi za muyi a gidan nan.

Ina kuma zaku koma.?

Kurmin mashi ne, har mun je mun ga wani gida.

Sai na kwashe labarin yadda gidan yake na faɗa mata ban ɓoye komai ba, na ɗaura da cewa.

Kuma na fahimci baban Amir baya aikin komai fa, idan ma yana aiki gyaran gidan nan yana da yawa, koda gidan kansa ne wlh za a ɗauki lokaci bai gama ba.

Ikon Allah, to Allah ya kyauta ya zaɓa mafi alkhairi.

Nace mata amin sai ta kashe wayar. Ashe bayan mun gama waya ta samu babanmu ta faɗa masa na samu Admission sannan ta sanar da shi halin da muke ciki na maganar tashinmu, to akwai wani gidan Babanmu da yake da shi anan sabon garin tudun wada kafin a kai gidanmu yake amma akwai tazara a tsakani, babban gida ne da aka gida self contain guda biyu ga kuma sauran fili a gefe, dan asali ya so yin makaranta ne a filin amma sai ya fasa aka yi wannan ginin sai ya zuba haya, gidan yana da kyau dan har rijiya a kwai kuma da ruwa a ciki sosai, sannan akwai mutane a ciki da suke haya, to dama akwai ɗaya daga cikin 'yan hayan zata tashi zata bi mijinta da yake aikin custom, har mutane sun fara zuwa duba ɗakin zasu kama, shi ne babanmu ya cewa Mamanmu ta faɗa mini Umar yaje ya same shi su yi magana. A ranar Mama ta sanar da shi ta bani labarin yadda ake ciki nayi mata godiya muka yi sallama, Naji farin ciki sosai dan nasan mahaifina gata zai yi mini, sai dai ban faɗawa Umar komai ba na dai sanar da shi yaje gidanmu Baba yana nimansa.

Umar da  ya samu lokaci a ranar yaje gidanmu yayi magana da Babanmu, wanda baba ya ce masa wannan ɗakin na gidansa zai ba shi haya kuma yadda ake biyansa dubu tamanin da biyar ne, amma zai yi masa lamuni ya bada dubu Hamsin, sannan kuma registration na makaranta na dubu ashirin da biyar sai sauran 'yan ƙananan abubuwa da zan siya wanda in an haɗa bai wuce dubu talatin da biyar ba, to duk shekara Umar zai riƙa biya mini har na gama, amma kuma abunda ya shafi ƙananun ɗawainiya na handouts da transport to babanmu ya ɗauke masa zai riƙa yi mini, Umar ya ce ya ji ya amince, daga haka suka yi sallama yayi masa godiya ya tafi. Sai Babanmu ya kirani ya sanar da ni duk yadda suka yi, na yi masa godiya da addu'ar ganawa lafiya da ƙaruwar arziki, ya amsa da amin kafin muka yi sallama na aje wayar cikin farin ciki ganin komai ya warware mana cikin sauƙi.

Bayan kwana biyu Umar ya ɗauke ni ya kaini makaranta a rana ta farko, a cewarsa ba zai bar ni na tafi Makarantar KASU ni kaɗai ba inyi screening sai tare da shi, ko da muka isa, tare da shi muka shiga hol ɗin da ake komai hatta bin layi da shi nayi, duk da layin maza daban na mata daban amma yaƙi barina a tunaninsa kar wani namiji ya ganni yace yana sona, haka muka yini a gurin nan tun safe har yamma kafin muka gama, kuma wlh babu abunda muka saka a cikinmu har wani hajijiya nake ji a saman kaina saboda yunwa, sai na je na siya nutric milk na sha saboda Babanmu ya aiko mini da kuɗi akan in ana buƙatar wani abu kamar yadda ya ɗauki niyyar zai yi haka, wannan nutric milk dana sha shi ne ya dawo dani cikin hayyacina, sai na koma can hol ɗin, wanda na karɓi wata paper na kai wani office ɗin wani lecturer ya saka mini hannu kafin ya sakani na kira 'yan department ɗinmu 'yan 100level, ba ɓata lokaci na riƙa bin mutane ina faɗa musu saboda a gurin screening duk na wayi wasu sannan mun taɓa hira da wasu matan, dan haka waɗanda na sani na faɗawa, suma suka shiga faɗawa waɗanda suka sani, sai nan da nan muka haɗu a ƙofar office ɗin Malam Hashim, nan ya sanar da mu cewar zamu fara lecture a ranar saboda da yawan wasu department sun fara karatu mune bamu fara da wuri ba, haka muka tarkata muka shiga aji muka fara karatu Umar yana waje yana jirana. Da yake Karatun sharar bage ne bamu daɗe ba aka gama muka fito, an dai yi introducing juna da kuma makarantar da mutum ya gama, dan haka ba zance mun samu damar yin magana da juna ba in ba wannan ba.

To bayan mun koma gida, zuwa dare sai naga Umar ya kwashe kayansa ya kai ɗayan ɗakin da babu gado a ciki ya shimfiɗa wani rigarsa akan wai a nan zai kwana, ban bi ta kansa ba saboda gajiyar dana yi sai na kwanta nayi bacci, sai can cikin dare ya zo ya tashe ni, na zauna ina murza ido dan da kyar na iya seta kaina dan bacci mai nauyi ya ɗauke ni, nayi zaton abu yake so nayi masa ko kuma buƙata ta ce ya kawo shi. Sai yace.

Magana nake so zamu yi.

Humm nace masa saboda bana son buɗe baki nayi magana saboda baccin da ke idona, sai ya ɗaura da cewa.

Farida wannan makarantar da kika samu kina nuna mini kamar kinfi ƙarfina.

Bangane ba Umar, naga babu wata hira da muke yi a gidanan balle kashe na soma yi maka rashin kunya, sannan tare muka je makarantar nan muka dawo banyi wani abu da zai ɓata maka rai ba, kuma cikin daren nan ni ina nan kai ka koma can ɗakin, bai kamata ka riƙa magana irin wannan ba a matsayinka na magidanci babba mai hankali.

Eh ni kawai na yanke shawarar mu haƙura da juna mu rabu.

To shi kenan Allah yasa hakan shi ne mafi alkhairi a gare mu. Ni dai inna je gida ban san me zan cewa Iyayena nayi maka ba, dan haka sai ka tanadi abunda zaka faɗa musu. Sannan ya kake ganin za muyi da Amir.?

Hmmm na yanke shawarar zan koma gurin kakata Dada mahaifiyar mamana a can Yola da zama, shi kuma Amir zan bar miki shi har ya kai primary 6 zuwa lokacin nayi aure, in ma banyi ba nasan na sami wani babban aiki da zan kula da shi sai na zo na ɗauke shi.

To shi kenan babu damuwa.

Na ce masa kuma daga haka sai na juya masa baya na gyara kwanciya, zuciyata babu daɗi duk da irin yanayin zamanmu amma rabuwa babu daɗi, shima sai ya tashi ya koma ɗakin daya kai kayansa ya kwanta, ni dai da tunani bacci ya ɗauke ni.

Washegari na same shi a ɗakin yana kwance sai na ce masa.

Ina kwana, zan tafi makaranta ina da lectures ƙarfe tara.

Ba zaki je ba.

Ya faɗa yana tashi zaune, na tsaya ina kallonsa fuskata a haɗe nace.

Kai da kace zamu rabu meyasa zaka hanani tafiya makaranta.?

Idan har kika fita to bada yawuna ba.

Hmmm to shi kenan.

Na faɗa ina juyawa na fita na koma ɗayan ɗakinmu na tsaya na ciro waya a jaka na kira Mamanmu, data ɗauka na gaishe kafin ta tambaye ni lafiya na kira ta.? Sai nace.

Dama zani makaranta ne amma baban Amir yace inna fita bada yawunsa ba, kuma mun fara karatu sosai sannan har yanzu ban gama screening ba, amma yace ba zani ba.

To sabo da me.?

Wlh nima ban sani ba.

To ki shirya ki zo gida ki amsa kuɗin mota ki wuce makarantar kar Allah yasa ya barki ɗin.

Sai nace mata to daga haka muka tsinke waya, ashe Umar yana jin duk maganganun da muka yi saboda yazo ya tsaya a ƙofar ɗakin ban sani ba sannan wayar tana da speaker sosai, sai yasha jinin jikinsa ya tashi ya shirya ya ce na fito ya kaini makaranta, ba musu na fito muka wuce wanda ko karyawa banyi ba. Haka muka ƙarasa ya sauke ni ya ja ya samu guri ya zauna ni kuma na wuce ciki na cigaba da screening daga bisani na wuce aji muka yi karatu, to bayan malami na biyu ya fita sai kiran Mamanmu ya shigo wayata na ɗaga, sai take tambayata ya taji shuru ban zo ba, nan nake sanar da ita ai ya kawo ni, Mamanmu taja tsaki tana cewa.

Ɗan rainin wayo.

Daga haka muka bar maganar na aje wayar. Ɓangaren Umar kuwa tun safe har wannan lokacin ƙarfe uku na rana yana jirana tare da kallon duk wani shige da ficena, to bayan mun tashi a wannan lokaci sai ya ɗauke ni ya kai ni can gidanmu, saboda yasan gidana ba mu da abincin da zan dafa naci, shima nasan gidansu zai wuce ya samu abunda zai ci dan na tabbatar shima tun safe bai ci komai ba. Na shiga gida na samu Mamanmu a ɗaki, muka gaisa sai ta saka Sakina ta kawo mini Abinci dan ta san daga makaranta nake, na soma ci sai na ji na kasa ci, nan na yi shuru ina duba ƙaramar wayata wanda game ɗin maciji nake yi, ita kuma ta cigaba da aikin ɗinkin da take yi tunda har lokacin babu wata shaƙuwa a tsakaninmu da zamu yi dogon hira, sai na miƙe na fito na koma ɗakin da nayi zaman jegon wankan Amir, na zauna a bakin gado nayi ta kuka saboda baƙin cikin irin zaman da nake yi da Umar, dan lokacin da ya aje ni a ƙofar gidanmu na tambaye shi ƙarfe nawa zai zo ya ɗauke ni.? Sai cewa yayi sai sadda yaga dama ko kuma ni inna ga dama na gama abunda nake yi sai na kira shi, shiyasa na kasa cin komai saboda baƙin cikin da Umar yake ƙunsa mini abun ya taru mini goma da Ashirin, shiyasa dana samu damar keɓe kaina nake wannan kukan dan na jima ina buƙatar haka, kukan Amir ne naji daga tsakar gida wanda a zatonsa na gudu ne ban tafi da shi ba, sai naji muryar Mamanmu tana tambayar ƙanwata ina nake, sai ta shiga kwala mini kira, sai nayi sauri na share hawayen daya zubo mini na fito ina amsa kiranta nace gani nan, sai na ɗauki Amir na ƙara komawa ɗakin dana fito, sai Mamanmu ta biyo bayana saboda nasan ta gane nayi kuka tunda fara ce ni fuskata tayi ja ga idona sun koɗe. Ta tsaya ta ƙare mini kallo tace.

Menene yake damunki.?

Sai nace mata.

Babu komai.

Sai ta cigaba da matsa mini akan lallai sai na faɗa mata abunda yake damuna, sai na ce.

Baban Amir ne ya furta mini zai sake ni, kuma zai tafi ya bar ni da Amir sai ya je primary 6 kafin zai dawo ya karɓe shi.

To sai me in ya sake ki, miji goma ai ba Uba goma bane, idan ya ƙara faɗa mini haka ki ce ya sakekin.

Ta ƙare maganar cikin ɓacin rai, wanda ni kuma na shiga mamakin Mamanmu akan furucinta, dan wannan ne karo na farko a rayuwata da ta goyi bayana akan wani abu daya shafe ni, sai dai kuma tunanina ya bani saboda a yanzu na taka wani mataki da zan fara karatun jami'a, ƙila nan gaba zan taka wani matsayi a rayuwa shiyasa ta kwallafa rai akan Karatun da na fara. Haka mama ta cigaba da faɗa akan karna sake zubar da hawaye na akan wannan maganar, ai na godewa Allah ina da sauran ƙuruciyata bai tsofar da ni ba, nace mata to amma zuciyata bai natsu da maganarta ba.

Zuwa yamma Umar yazo, sai ya aiko yaro ya sanar da ni, sai na shirya na yiwa Mamanmu sallama nace in babanmu ya dawo ta gaishe shi tace mini zai ji, sai na fito muka wuce ba tare da ya shiga cikin gidanmu ba.

To washe gari ya kama Alhamis ban je makaranta ba saboda abun duniya ya dame ni, na rasa wa jan na faɗawa damuwata naji sanyi a raina, ina buƙatar wanda zai yi rarrashena yayi mini nasiha dan gabaɗaya maganganun Mamanmu bai bai kwanta mini a rai ba akan in auren ya mutu ba matsala bace, ina son shawarar wanda ba zai ce na kashe aurena ba na zauna a ɗakina na cigaba da haƙuri, da kalamai masu kwantar da hankali akan Allah yace Annabi ma ya ce, sannan a tuna mini akwai 'yan uwana mata waɗanda suka fini matsalar aure, irin wannan kalaman nake so amma na rasa wanda zai faɗa mini haka, sai damuwar ta hanani sukuni na yini sukuku ban da lafiya, a saboda yawan damuwar da nake ciki sai ya sakar mini zubar jini, kuma ba lokacin al'adata bane, sai dai  nasan har da iskan jikina ne suka motsa, dan haka naji zuciyata ta ƙara bushewa na je ɗakin daya zama nashi yanzu, na tsaya tare da rungume hannu a ƙirjina na ce.

Umar nima na gaji da zama da kai tunda ka zaɓa mu rabu, in kuma ba haka bane ka fara yi mini barazana da haka, to gwanda ko bamu rabu ba mu bawa juna hutu, mu ɗanyi nesa da juna.

To shi kenan zan je na samu iyayenki nayi musu magana.

Ya ƙare maganar cikin ƙananun surutu, ban sake bi takanci ba tunda na amayar da abunda ke zuciyata sai na juya na koma ɗaki na kwanta.

****

Washe gari Juma'a muna da biki a dangin Mamanmu a can Kabala, dan haka sai na yanke in naje makaranta daga can zan wuce tunda babu nisa da makarantarmu, sai na samu Umar nake faɗa masa, buɗar bakinsa sai cewa yayi.

Ai yanzu ba a ƙarƙashin mulkina kike ba, dan haka ki je ki yi duk abunda kika ga dama.

Sai na tsura masa ido na kasa ce masa komai saboda maganarsa ya bani mamaki, wanda a fahimtar dana yi yana nufin kamar baya aurena ko ya jingine shi a gefe, sai kawai nace masa to na fito na koma ɗakina na shirya cikin Swizz Les maroon color da hijab ɗina milk, Sai na ɗauki jakata na same shi har ya fita da mashin ɗinsa ya ɗauke ni muka wuce makaranta ya sauke ni ya wuce, dan yau bai tsaya jirana ba. Bayan mun fito lectures wajen sha biyun rana sai ga kiranshi a wayata, na daga sai yake cewa wai in tawo kawai shima gashi a hanya zai je gidanmu ayi maganar da za a yi a gama, yana gama faɗar haka ya kashe wayar, sai naji jikina yayi sanyi zuciyata ta tsinke da tunanin yadda Iyayena zasu ɗauki maganar, na tabbatar Umar zai kafa hujja da maganar dana yi masa jiya ne wanda hakan kuma damuwa zai haifar mini tsakanina da Iyayena, sai na kama hanya na fito gate na samu napep na hau, ya wuce dani gidanmu ina yi ina share hawaye dan na damu sosai.

Rahma Kabir ce.