“SANADIN ƘADDARATA”

Page-27

by @zahratulqalam51

*FASAHA WRITER'S ASSOCIATION*
     (*F.W.A)*©✍️
     ⭐⭐⭐

Ƙungiya masu aiki cikin salon hikima da fasaha gurin juya tunanin al-umma, kaifin alƙalumansu ya zarta takobi ©✍
___________________________________________________



بسم الله الرحمن الرحيم.
اللهم صلي وسلم على نبينا محمد. 




❁ 𝐒𝐀𝐍𝐀𝐃𝐈𝐍 Ƙ𝐀𝐃𝐃𝐀𝐑𝐀𝐓𝐀 ❁ 




Free book📓



By


*Aisha G Umar*
_*🌹𝑍𝑎ℎ𝑟𝑎-𝑡𝑢𝑙-𝑄𝑎𝑙𝑎𝑚🖋️*_




Page2️⃣7️⃣





Ni kam sa sarƙar na yi agaba ina kallonsa gaskiya yana da kyau sosai, a zuciyata na ce, "hmm yanzu idan Mama ta tarar da sarƙan nan a hannuna me zan...?" Ban ƙarasa maganar zucin ba, kawai na ji sallamar Mama da ya sanya zuciyata bugawa!!!.

Da mugun sauri na miƙe tare da ɓoye sarƙar da ke hannuna zuwa baya, na zare ido da ka ganni ka ga mara gaskiya, Mama kuwa bayan ta shigo ta ke cewa, "ina Wasila?" Baki na ɗan rawa duk da ina ƙoƙarin danne tsorona na ce, "eh? Oh ba ta nan, yanzu...yanzu ta fita".

Ko da jin maganar Mama ta tsaya tana bina da kallon son gano wani abu a gareni, sai kuma ta jefa min kallon rashin so sannan ta juya za ta wuce. Sauke kaina na yi ƙasa ina sauke ajiyar zuciya ganin na tsira, "me a hannunki?" Mama da bayan ta isa ƙofar ta dakata, sannan ta juyo ta furta wannan tambayar, saboda ganin yadda na ɓoye hannuna a baya kula alama ya nuna mata wani abu na ɓoye.

Fidda ido na yi sosai haɗi da ɗagowa à hankali na sake damƙe abun da na riƙe, Mama kuwa ta tako zuwa inda na ke, ta tsaya tana kuma bina da ido kamar ɗazu, ni dai wani nyawun na shiga uku! na haɗiye ina sake yin zuru-zuru da maganaina......

SADIYA.

Bayan fitan Faruq tana zaune a kan kujera a falonta, yayin da zuciyarta ya tafi can wani wurin daban. 'Ya Allah ina roƙonka ka kawo min sauƙi' ta faɗi a zuciyarta tana fitar da hawaye, abun ya sake yi mata yawa, wai ɗan wattanin nan da ta yi kuma ba bu labari, shikenan su Baaba su ka sake tsawwala mata, suna laƙabta mata wai ita juya ce, oh wata sabuwa!......

Faruq bayan fitansa sashinsu Baaba ya nufa don ya je ya gaishesu kamar yadda ya saba kafin ya wuce aiki, bayan Baaba da ke zaune bisa kafet ta amsa masa sallamar da ya yi, ya shiga haɗi da zama a ƙasa shima, "Baaba ina kwana, kun tashi lafiya?".

Ba ta amsa ba sai da ya kuma maimaita gaisuwar nan ma kamar ba za ta ce komai ba, sai kuma ta amsa da, "lafiya!" Ba tare da ta kalli ko inda ya ke ba, "am Baaba lafiya kuwa? Akwai wata matsala ne?" Ya yi tambayar saboda ya ga yau ɗin ta fi haɗe masa fiska, "me ka gani?" Nan ma ta faɗi a taƙaice, a sanyaye ya ce, "a a kawai dai na ga kamar yanayinki ya sauya sosai, shine na yi tunanin ko akwai matsala".

Da jin abun da ya ce nan da nan Baaba ta hau masifa, "oh tambayata ma Kake Faruq? Dole ka ga yanayina ya canza mana! Tun da kai dai ba za ki iya farantawa mahaifiyarka rai ba, babu ruwanka da abun da na ke so, ban isa in sanya ka abu ka yi min ba, bani da wani mahimmanci à gareka!" Cikin damuwa da maganganunta ya ce, "Baaba wani abun kuma na yi?".

"Yo kai menene ma ba ka aikata min ba? Ai ka min komai kuma ka nuna min ban isa akanka ba, ni na ce maka bana son yarinyar nan ga Nusaiba 'yar Mairo, na ce ka aureta, amma kai ka ƙeƙeshe ƙasa ka ce sai wannan yarinyar Sadiya za ka aura, gashi yau wata kusan biyar ban ji wani labarin abun kirki a gareta ba, abokanka da ku ka yi aure kusan lokaci ɗaya, duk ga sunan matansu da ciki, amma kai ta ka matar shiru kamar shirwa ya ci ƙwai, wannan lamari har yaushe? To akan me ba za ka zo ka sameni cikin damuwa ba?".

Shiru Faruq ya yi domin bai san me zai cewa Baabar ba, ko da yaushe ba ta da wani magana sai ya auri Nusaiba, sannan ta rinƙa cewa wai Sadiya juya ce, to ina batun juya akan wacche kwata-kwata ko rabin shekara ba ta yi ba?. Baaba na shirin sake ɗauko wata masifar sallamar Malam ya tsaidata, wanda tun da Baaba ta fara zubawa Faruq masifar yana ji. 

Gaishe da Malam Faruq ya yi cikin girmamawa ya amsa da farin ciki haɗi da tambayarsa ya Sadiyar ta ke? Faruq ya amsa masa da tana lafiya, "to madalla, shirin aiki ka yi ko?" Faruq ya ce eh Malam ya ce, "to jeka abunka, sai ka dawo Allah ya dafa mana" "ameen Malam a wuni lafiya" faɗin Faruq sannan ya tashi ya ya bar ɗakin.

Malam kallonsa ya maida gun Baaba ya ce, "haba Talatu! Haba Talatu! Wai don Allah me yasa ki ke takurawa yaron nan ne? Me yasa ko da yaushe burinki ki faɗa masa munanan kalamai akan matarsa?" Baaba da ta yi shiru dama tana jiran jin abun da zai ce ne, domin ta san idan har ya ji abun da ta faɗawa Faruq to sai ya yi mata faɗa, sai da ta sauke numfashi ta dubi Malam.

Shi kuma ya ɗaura da cewa, "ina yawan faɗa miki abun da ki ke yi ba daidai ba ne, kuma da ki ke maganar haihuwa, ba sai an tsaya ana miki nasihar komai sai Allah ya yi ba, kin riga da kin sani ya kamataki gane gaskiya!" "Haba malam wace gaskiyar zan gane sai ka ce wacche ke aikata zunubi? Tun kan abun nan ya yi nisa na bika akan a fasa batun auren nan, amma kai me ka yi? Ka goyawa yaron nan baya, ka nuna masa bani da mahimmanci à gareshi, Malam ni ce fa na haifi Faruq, kuma shikanan ba ni da damar yi masa umarni ya bi? Ba ni da damar hanashi ya hanu?".

Samun guri malam ya yi ya zauna yana bin Baaba da kallon mamaki da takaici, ya ce, "don ke ki ka haifi Faruq ba yana nufin ki takurawa rayuwarsa ba ne, da ace yarinyar nan da ya aura ba ta da tarbiyya tana da mummunar hali, ke da kanki kin san da ko kusa ba zan taɓa amince masa ba, hasalima shine ya ke cemin halin Nusaiba da ki ke son aura masa ba mai kyau ba ne, me yasa ba za ki ɗau abun da ya faru ya wuce a wurinki ba? Akan me ba za ki fahimci auren Faruq da Sadiya shine mafi alkhairi ba?".

Tashi Baaba ta yi daga zaunen da ta ke, tana ƙoƙarin fita falon cikin ɓacin rai, 'yarinya ce dai ba na ƙaunarta kula ba zan taɓa ba!' Ta faɗi cikin ranta ta fice......

Bayan Faruq ya bar sashinsu Baaba sashinsa ya nufa, don ya ɗauki jakarsa ya wuce aiki, a hanyarsa ya haɗu da Badiyya da Aisha. Gaishesa Aisha ta yi tana murmushi ya amsa yana cewa, "Antynki ta ce min kwana biyu ba ki zuwa gurinta Aisha, me ya faru?" "Baaba ce ta hanani zuwa, amma yau na tambayi Malam ya ce inje, zuwa anjima ina kammalawa Baaba aikinta zani", cewar Aisha.

Badiyya kuwa kamar ba ta so ta gaisheshi, da ya ke Faruq ya san halinta amsawa kawai ya yi ba tare da ya sake mata magana ba, ya maida kallonsa kan ƙanwarsa da ya ke ji da ita ya ce, "toh ba komai Aisha ni bari na je zan wuce aiki" Aisha da murmushi ta ce, "to yaya sai ka dawo".

Bayan Faruq ya wuce Badiyya ta juya tana harararta, da ya ke ita ce Babba akan Aishar, "ba inda zaki je munafuka, kuma sai na faɗawa Baaba, sai ka ce wani abun ta ke baki sai wani manne mata ki ke yi!" Ko sannu Aisha ba ta ce mata ba ta juya ta wuce abunta.......

Sallama sau huɗu Faruq ya yi bayan ya shiga falon, sai dai har yanzu gani ya yi kamar Sadiya ba ta ji sallamar ta sa ba, cikin damuwa da halin da matar ta sa ta ke shiga ya iso kusa da ita, har ya zauna ba ta sani ba saida ya sa hannunsa cikin na ta hannun, sannan firgigit ta baro duniyar tunanin da ta lula, kallonsa ta ke yi sai kuma ta sake mishi murmushi mai ciwo ta ce, "ka dawo? Ya su Malam ɗin suna lafiya?" Binta ya ke yi fa kallon rashin jin daɗi ya amsa, "suna lafiya ƙalau".

Murmushi ta sake yi masa ta ce, "to dearna ta shi da sauri ka wuce aiki lokaci na tafiya fa", "ta ya zan tafi bayan masoyiyata tana cikin damuwa?" Ya faɗi ba tare da ya kawar da idonsa akanta ba, miƙewa ta yi ta ɗauki jakarsa da ke gefenta tana miƙa masa ta ce, "ni lafiya ƙalau na ke my dear, tun da kana tare da ni bani da wata damuwa, don haka please ya kamata ka wuce office da wuri ka ji?".

Sai da ya sauke ajiyar zuci sannan ya miƙe ya amshi jakar ya yi mata sallama da cewa ta kula masa da kanta, kuma Aisha ta ce yau za ta zo su yi hira, da murmushi ta bisa sannan ta koma ta zauna.

YAMMACI. 

Su Lantana ne su ke zaune kusa da Baaba, Lantanar ce ta dubi Baaba ta ce, "yauwa Baaba kamar yadda na ce miki ina ganin idan har mu ka bi ta wannan hanyar to zamu ci nasara, saboda Sadiya tana da sauƙin kai, kuma tana matuƙar son Faruq, na san ba za ta so ace mahaifiyarsa ta tsine masa ba", Fatima da ke bin Faruq wacche ita ce sa'ar Sadiyar ma ta ce, "kin ga kuwa ita da kanta zata rabu da Faruq ɗin tun da dai shi ya ƙi rabuwa da ita" 

Badiyya ta ce, "kuma Baaba ina ganin yanzu ya kamata mu je, saboda malam ba ya nan kuma Faruq ɗin ma baya nan", girgiza kai Baaba ta yi domin ta gamsu da kalaman 'ya'yan na ta, ta dubesu ta ce, "toh shikenan ku tashi ku je yanzu, Lantana ina son ku tabbatar kun yi abun da ya dace, inga canji yau ba sai gobe ba!". Da toh su ka amsa sannan su ka tashi su ka nufi sashin Sadiya.....

Sadiya na ɗaki tana hira da Aisha, domin Aisha ce kaɗai wacche ke ƙaunarta a cikin 'yan uwan Faruq, tana jin daɗin hira da ita, wani lokaci ma Aishar ce ta ke ba ta haƙurin abubuwan da mahaifiyarta da 'yan uwanta ke yiwa Sadiya. Suna cikin haka su ka ji sallamar su Lantana, sai da zuciyar Sadiya ya tsinke domin kuwa ta san ba alkhairi ne ya kawosu ba, Lantana ta daɗe ba ta shigo sashin ba sai su Fatima, to ko yau kuma da mece su ka zo?.

Kallon Aisha ta yi cikin fargaba sosai, sai kuma ta tashi a sanyaye ta fita tana amsa musu Sallama Aisha biye da ita. "Ikon Allah yau sallamar ma ba za a amsa mana da wuri ba?" Cewar Fatima tana yatsine fiska da yiwa Sadiya irin kallon da dukkansu su ka saba yi mata.

Cikin dauriya Sadiya ta dubi Lantana da ke bin gidan da kallo kamar mai neman wani abu ta ce, "Anty Lantana sannunku da zuwa, ku iso ɗaki bismillah" wani irin juyowa Lantana ta yi wanda yasa Sadiya razana amma ta dake, Lantana ta ce, "yau kuma da wani sabon salon ki ka tashi? Ai kin san ko ban da wurin zama ba zan iya shiga ɗakinki ba" ta faɗi tana taɓe baki.

"To in kawo muku ruwa ko jus ku ke so? Ko in shimfiɗa muku tabarma a wajen?" Cewar Sadiya cikin share maganarsu, Badiyya ta ce, "ku ji wani munafurci, wato so ki ke muma ki mallakemu kamar yadda ki ka mallake mana ɗan uwa ko?", "haba Badiyya taya za ki ce mata haka? Anty Lantana don Allah ku daina faɗa mata magan-ganu haka, cikin kulawa ta tarbe ku amm..." cewar Aisha saboda abun da su ke yiwa Sadiya ɗin ba ya mata daɗi.

Sai dai kafin ta kammala maganar Lantana ta katseta cikin ɗagun murya, "rufamin baki sha sha-sha! Ke me ki ka sani dangane da duniya? To ki kiyayeni wallahi, tun tuni ina da cikinki daman, sai wani lilliƙe mata ki ke yi", shiru Aisha ta yi ba ta ce komai ba, Badiyya kuma ta amshe da faɗin, "Anty Lantana faɗa mata kam, ni gani na ke itama sihirceta Sadiyar ta yi, shiyasa ta ke mammane mata" "to mu dai ba ki isa ki sihircemu ba Sadiya!" Cewar Badiyya tana hararar Sadiya.

Ita kuwa da ta yi shiru tana kallonsu, ba ta ce komai ba sai zafin da ke ziyartar zuciyarta, idonta ya fara aikin taro ƙwallah. Lantana ta gyara tsayuwa ta dubi Sadiya ta ce, "duk ba surutan nan ya kawomu ba, saƙo ne daga Baaba!" Sadiya gaba ɗaya hankalinta ta maida kan Lantana jin Baaba ta aiko saƙo, tabbas ta san ba zai taɓa zama alkhairi a gurinta ba, Lantana ta ɗora da cewa, "Baaba ta ce! Tana son ki san hanyar da za Ko bi don ki rabu da ɗanta Faruq, idan ba haka ba kuma za ta tsine masa!!". 

Kamar saukar ƙarfe cikin ranta wannan maganar ya zame mata, sai da ta yi baya tana dafe ƙirji, yayin da zuciyarta ya fara yi mata wani irin harbawa daam dam kamar zai fito.....

INNA JUMMAI.

Tsaye ta ke tana sauraron magan-ganun da Halima ke sharara mata, sai da ta bari ta ƙare tass sannan ta dubeta ta ce, "kin gama?" Da murmushin da ta ke yiwa Innar ta ce, "eh na gama Inna ɗauko min in wuce" "to bari ki ji yau dai babu abun da zan baki Halima! Na gaji da yin adashen da ba kwasa, kullu yaumin abu ɗaya?". Haɗe fiska Halima ta yi tana faɗin, "Inna kin san me ki ke cewa kuwa?".....


Last page
___________________________________________________

Cab ɗi!🤔 Mama da Nuriyyah. Shirinsu Baaba da Sadiya, me ku ke tunani akai? Inna Jummai kuma ta ce ta gaji da bada dukiyarta wa Halima.

Mu dai kasance a kashe na gaba don jin me zai faru?.




_*🌹𝑍𝑎ℎ𝑟𝑎-𝑡𝑢𝑙-𝑄𝑎𝑙𝑎𝑚🖋️*_