RA'AYIN ZUCI..!

Chapter : 2 (the Criticism)

by @zmchubado

*RA'AYIN ZUCI.....*
(the opinion of the heart❤)

Zm-Chubaɗo✍️

Chapter 2

#the Criticism#

_Kiran da na yiwa Yusuf a wannan lokacin.shine ya zama silar buɗewar sabon babi a cikin littafin kaddarar rayuwarmu, Ƙaddarar da ta zama silar abubuwa da dama, waƴanda tunani bai taɓa hakaitowa ba. Da bugun waya ɗaya takk muka samar da shaƙuwa mai girma a tsakanin zukatan mu. hakiƙa soyayya ta na da girman sha'ani mai wahalar ƙaiyadewa, wanda Ubangijine kaɗai ya san sirrin da ke tattare a cikinta. A lokutan baya zuciyata a rufe take ruf, kafin sanadi ya haifar da haɗuwata da Ɗan Attahiru. mutumin da ya sauya rayuwata cikin ƙanƙanin lokaci da kaifin harshen da ubangiji ya yi masa baiwa da shi. wanda zan iya fassarawa da makami mafi girma da haɗari ga zuciyar ko wacce ɗiya mace a duniya. Duk yanda zan siffanta muku yusuf da kalaman bakina ba zaku taɓa fahimta girman sha'aninsa ba, har sai kunyi nutso cikin labarin Hikayata sannan zaku iya fahimtar komai tareda maƙasudin faruwarsa. Juyawa nayi a hankali na gyara kwanciyata bisa ƙatuwar katifar da na shimfiɗe da tattausan zanin gado, sannan na ƙara ƙanƙame wayar da ke riƙe a hannuna ina tunanin ta inda ya kamata na fara. Lumshe idanu nayi ina jin yanda ƙaunarsa ke ƙara farmakar zuciyata, kafin nayi ƙundumbala na danna hatimin kiran dake jikin wayar, ina jin yadda zuciyata ke bugawa da ƙarfin gaske.Wayar na manne a fatar kunnena ta fara ringing ban san sanda wani ƙayataccen murmushi ya ratso ta tsakanin laɓɓana ba. Sai dai ina ji kiran ya katse ba tareda ya ɗauka ba, murmushin da ke kwance a fuskata ne ya yi ɓatan dabo tamkar bai taɓa wanzuwa ba, ajiyar zuciya na sauke tareda ɗora wayar a ƙirjina na ƙanƙameta ina sauke numfashi da ƙyar. Na jima a haka ba tareda nayi gigin ƙara kiransa ba, haka na afka cikin duniyar tunanin dalilinsa na rashin amsa kirana, ina tsaka da wannan tunanin ƙarar kiransa ya karaɗe kunnuwana.Misalta irin farin cikin da zuciyata ta shiga a wannan lokacin abune da ba zai kwatantu ba a gareni, hannu na sa na shafe ruwan hawayen dake kwaranya bisa kumatuna, sannan na fizgo maganar dake maƙale a maƙoshina na ce,"Abin so!" na kirashi da sunan da zuciyata ta raɗa masa tun farkon fara soyayyata da shi._

_Lumshe kamilallun idanunsa ya yi tareda da sauke wani wahalallen Numfashi tamkar ya na gaba na. Kasa cewa komai ya yi illa sauke ajiyar zuciya da ya ke yi, wadda sautinta ke kutsawa cikin kunnuwana ba tareda shamaki ba, cikin sautin muryarsa wadda na jima ina kewa cikin ko wani dare idan na kwanta bacci ya ce,"An ɗauki lokaci mai tsayi ina fama da kewarki. ta yadda ba zan iya siffanta girman yanayin ba. bansan ta yanda zan kwatanta miki ki fahimta ba, amma nayi alƙwarin ba zan ƙara bari kiyi nisa dani makamancin wannan ba, no matter what happens to me sai nazo inda kike Ƙaunata!" ya firta haka cikin wani wahalallen yanayi mai kai farmaki ga zuciyar wanda ke sauraronsa. Rintse idanu nayi da ƙarfi ina jin yanda kalamansa ke yanka zuciyata suna samawa kansu mazauni, ban san me ya kamata in faɗa masa ba, amma har cikin zuciyata ina so na ba shi labarin yanda nayi kewarsa. Sai dai bansan ta ya zanyi Expressing how I feel about him ba!_

_Shirune ya biyo bayan maganarsa. sai dai ta tsakanin shirun da ke kai komo ta mahaɗar kunne da ƙwaƙwalwa, ya ke jin sautin kukana a hankali yana fita, wanda ke ratsa ko wace kafa ta jikinsa, in a very calm voice ya langaɓar da kai ya ce,"kuka bai taɓa zama magani ga abinda zuciya ke so ba Ƙaunata. amma ina da yaƙinin cewa ganin juna zai iya ɗebe mana kaso tamanin a cikin ɗari na zugin da ke addabar zukatan mu. Gobe da safe zanzo gidanku taɗi, idan da Hali ina so naga BILKISU IBRAHIM SAMINAKA cikin ado mafi kyau da ƙawatuwa. wannan kaɗai ya isa ya samawa zuciyar YUSUF ATTAHIRU farin cikin da ya Jima beyi irinsa ba." ya firta haka cikin murmushi mai sauti. Hannu nasa na rufe fuskata da tafin hannuna ina dariya wadda na jima banyi irinta ba, a wannan dare munyi waya da juna mai tsaho gamida tsayawa a rai. irin wadda muka jima ba muyi kamarta ba, sannan mukai sallama da juna cikin maɗaukakin farin ciki gamida kewa me raunata zuciya da ruhi. A haka wani daddaɗan bacci ya yi awon gaba dani cikin yanayin da na jima ban tsinci kaina a ciki ba, washe gari da safe tunda na idar da sallar Asuba ban koma bacci ba, saboda zumuɗi tun takwas na safe na kallama duk wasu aiyukan da na sabayi a ko wacce safiyar Allah.Tareda Mama muka shiga ɗakin girki muka samar da abinda zamuyi karin kumallo da shi, Babana wanda muke kira da Baffah ma'aikacin bankine amma tun shekaru biyu da suka gabata yayi ritaya saboda nisawar shekarunsa. mu ƴan Asalin ƙaramar Hukumar Saminaka ne, aikine yayi sanadin dawowar mu cikin garin kaduna tun Mama ba ta haifeni ba. Yaya Na'imah Ita ce babba a ɗakinmu tana da shekara talatin da ɗaya (31years), sai yaya Zainab wadda keda shekaru Ashirin da biyar(25years). Shekaru uku ne tsakanin mu da ya Zainab sannan Mama ta haifeni. Rayuwar gidan mu rayuwace mai matiƙar tsayawa a rai. Irin rayuwar da ko wace ɗiya mace take fatan samun irinta._
_Gidanmu babban gidane me yalwar farfajiya wadda aka ƙawata dai-dai da zamani, a harabar gidan akwai rumfunan adana motoci manya guda biyu. Sannan ƴan shuƙe-shuken zamani da aka samar a jikin ko wace kusurwa wadda aka wadata da tukwanen shuka firanni, yanayin zubin gidan yanayi ne irin na ƴan bokon da suka amsa sunansu. Kai tsaye ba za a kira Mahaifin mu da attajirin da ya tara dukiya mai yawa ba, amma dai ya na da rufin asirin da baza'akirashi da suna talakan tilis ba. Auren zumunci ne tsakanin Baffa da Maman mu, wannan yasa muke sharing family guda. gidan mu yana da tsari sosai fiyeda zaton mai tunani, musamman akan ilimin boko da na addini. Gabaɗaya yayyena mata sai da sukai karatu sannan Baffa ya aurar da su, yaya Na'imah tanada shekara ishirin da bakwai tayi aure. A lokacin ta jima da kammala karatunta a jami'ar Amadu bello dake Zaria, inda ta karaci International relations, a yanzu haka tana aiki da indian Embassy dake birnin taraiya ƙarƙashin lamuncewar Mijinta Mahmoud Salahudden._
_Ita ma yaya Zainab ta zurfafa nata karatun sai dai ba ta kai ga kammalawa ba, akai mata Aure, da igiyar Aure akanta sannan ta kammala nata karatun, inda ta karanta Education English a Jami'ar bayero university kano. sai dai ita ba ta aiki tana ƙarƙashin kulawar mijinta Ibrahim Khabir Saminaka, saboda kasancewarsa mutum mai tsaurin kishi ga iyalinsa. Duk da cewa Auren zumunci ne a tsakaninsu hakan bai sa ya sauka da ga kan ra'ayinsa ba. yanzu haka ta na da yaro guda ɗaya mai Suna Ahmad saɓanin yaya Na'imah da ke da yara biyu maza, farouq da Imran. akwai shaƙuwa mai yawa a tsakanina da ya Naimah, sai dai duk irin shaƙuwar da ke tsakanina da ita ba na iya buɗe mata cikina. ya zainab ce kaɗai ke iya fahimtar damuwata ko da ace ban buɗe baki na firta mata ba, a taƙaice dai ta fi yaya Naimah sanin halayena dukda babu shaƙuwa a tsakanin mu da ita sosai saboda zafinta. duk da kasancewarta me zafin rai idan aka shiga gonarta, but Yaya zainab has a different kind of attitude, which's not everyone can understand. She is upside down but she also has a heart of compassion that yaya Naimah does not have. Ƙa'idar gidanmu ce duk wanda ya taso sai yayi Boarding school. ko da kuwa ba ka da ra'ayi wajibine sai kayita, wannan dalilin ya sa Baffa ya zauna dani ya tambayeni makarantar da nake so. Banyi ƙasa a gwiwa ba na sanar dashi cewar ina son a kaini Fggc Bauchi., nan da nan iyayena sukai na'am da zaɓina, aka fara shirin kaini makaranta tareda tanadar min duk wasu abubuwa da zan buƙata. sai dai abinda ban sani ba shine tareda Hajar ƴar yayar mahaifina aka shirya za'a kaimu. Duk wani Abu da baffah ya siyamin ita ma irinsa ya Siya mata se dai banbancin kala, sosai nai farin ciki da hakan tunda dama kawatace sosai don tare muka taso, Yaya khadir da Inno sune su kai mana rakiya har cikin makaranta. Duk wani abu da ya kamata shi yayi mana komai, sannan sukai mana sallama suka kama hanyar Kaduna bayan Inno ta yi mana nasiha mai ratsa jiki, sannan ta gargademu sosai akan mu kula da rayuwarmu tareda duk mutanan da zamuyi mu'amila da su. Sai a lokacin kuka ya taso mana mukaji ba zamu iya jurar kaɗaicin da ya tunkaro mu ba, da kyar Inno ta iya banbareni daga jikinta sannan tayi murmushi ta ce,"Ka da kuyi kuka yan-matan gobe. duk wanda kuka ga ya zama wani a wannan rayuwar da gwagwarmaya da kadaici ya fara, babu wata nasarar rayuwa da take riskar mutum yana zaune dole sai ya tashi." Ta kare maganar tana shafa gefan fuskokinmu ni da Hajar. Duk abinda mukeyi yaya Khadir yana tsaye yana kallonmu, Kai tsaye ba zan iya fassara yanayin da na gani kwance a kan kamilalliyar fuskarsa ba, Amma na tsinci wani al'amari mai kama da kewa ta musamman a tsakiyar idanunsa, wanda baki yayi kadan ya iya siffanta girman al'amarin._
_duk da inada ƙarancin shekaru a lokacin amma hakan bai hanani fahimtar inada matsayi na musamman a gurinsa ba, komai ya samo a kaina yake ƙarewa, duk inda zai ɗora ƙafarsa sai ya zo gidan mu ya sa mama ta shiryani ya tafi dani, haka yake min har na fara mallakar hankalina, a lokutan hutu nakan je gidan su nayi kwanaki har sai hutuna ya ƙare sannan zai dawo dani, a ƙarshe Baffa ya ce mama ta tattara min kayana ya bawa Inno ni. Wannan shine ya ƙara samar da gurbin shaƙuwa mai girma a tsakanina da yaya Khadir da Hajar, muka dunƙule muka zama abu guda. Zuwan mu bording shcool shine ya zama silar faruwar abubuwa masu wahalar mantawa, ciki kuwa harda haɗuwata da Yusuf Attahiru, mutumin da yay kutse a rayuwata ya kafamin tarihi Mai wahalar mantawa na tsahon har abada.!_
Ƙarar wayata dake cikin jaka ce tayi nasarar fizgoni daga cikin duniyar tunanin da na afka, a hankali na sauke gajiyayyun idanuna na a kan jakar ba tareda na motsa ba. Inno ce ta shigo ɗakin ta tsaya da ga can nesa dani tana kallona, ta tsakanin siririn hasken ranar da ya haska ɗakin kaɗan, sannan ta kai hannunta ta kunna ƙwan lantarkin da haskensa ya game ko ina still ba ta dena kallona ba. ta jima ta. na kallon fuskata wanda kai tsaye ba zan iya fassara ma'anar irin kallon da take min ba. Sai dai duk wani motsi da ƙwayar idanunta keyi a kaina ina jin tasirinsu a ilahirin jikina, numfasawa tayi sannan ta tako jikin gadon cikin nutsuwa ta kai hannunta saman goshina, wanda ya ɗau zafi sosai sakamakon zazzaɓin da ya saukar min. Cikin damuwa da nuna kulawa ta ce,"Zazzaɓi ne a jikinki Bilkisu."
Murmushi na saki mai sauti na ce,"karki ɗauki hakan da mahimmanci inno. Ni da ba tsahon rai zanyi a duniya ba ai bai dace ku sanya rai haka akaina ba." nayi maganar ina ƙoƙarin tashi.Ita ta taimakamin na tashi na zauna sannan ta tallafi fuskata cikin tafukan hannunta ta ce,"da rai da rayuwa duk a hannun Allah Suke Bilkisu. Sannan bawa bai isa ya ƙaiyadewa Kansa lokacin mutuwa ba, ubangiji shi kaɗai keda hurimi akan haka." tayi maganar tana kallon fuskata cikin yanayi irin na son ta bani karfin gwiwa.
Murmushi nayi sai dai wannan karon iyakarsa laɓɓana, bance komai ba se kallo da nake bin Inno dashi ina jin yanda zuciyata ke takurewa a tsakanin ƙirjina. Gabaɗaya na tsani duniyar da abinda ke cikinta, ji nake dama in mutu ko zan huta da rikicin mutum irin Yusuf, gabaɗaya na rasa dalilin da yasa ƙaddara ta sarƙafa rayuwata da tasa, "me yasa na kasa son wani mahaluki a duniya sai shi kaɗai kamar rai da ajali?" nayiwa kaina wannnan tambayar a can cikin zuciyata.
"Fuskarki ta faɗa sosai Bilkisu da alama kina matsawa kanki da tunani akan matsalarki da familyn Yusuf, ni banga dalilin da zesa ki ɗorawa kanki damuwa akan abinda bake zaki bawa kanki ba." cewar Inno. tayi maganar cikin nuna kulawa.
"zazzaɓine kawai a jikina amma ba abinda kike tunani bane. Ina shan magani zai sauka" nayi maganar a sanyaye.Ƙura mini idanu tayi tana karantar yanayi na sannan ta ce," baki taɓa zuwa gidannan kin kai irin wannan lokacin ba tun da kikai aure. wannan yasa naji a raina kamar kina da damuwa a Ranki Bilkisu!"

Lumshe idanu nayi wanda ya zame min tamkar dabi'a sannan na buɗesu tar akanta. har lokacin na kasa motsa bakina balle in bata amsar tambayarta. Lura da hakan ya sa tayi murmushi ta ce,"karki damu ba sai kin buɗe min sirrin dake ɓoye a bayan zuciyarki ba. Wata ƙila lokacin daya kamata ki gaya min ne beyi ba, ina roƙon Allah ya ba ki mafita akan dukkan matsalolin rayuwarki Bilkisu." ta faɗi haka ta na wadata fuskarta da murmushi sannan ta miƙe ta nufi drower ta fito da farin hijjabin da take salla da shi, sai da ta shimfiɗa sallaya sannan ta dubeni ta ce,"lokacin sallar la'asar ya yi. Ki daure ki shiga toilet kiyi alwala, idan kinyi sallar akwai Alalan gwangwani a kicin kije ki zuba kici."

Jinjina mata kai nayi sannan na sauke fararen ƙafafuna a ƙasan tattausan kafet ɗin da aka shimfiɗe ɗakin da shi, a nitse nake takawa har na isa jikin ƙofar toilet ɗin na tura. Wani lafiyayyen ƙamshin turaren wutane ya baƙunci hancina, da ga can ƙasan ruhina nake yabawa girman tsaftar da Inno keda ita, wadda har yau banci karo da wanda ya kai kamarta ba.Alwala nayi bayan na inganta tsarkina sannan na fito, bisa ga mamakina har ta shimfiɗa mini wata sallayar a kusa da ita tareda hijjabin da zanyi sallar dashi. Dedaita tsaiwata nayi sannan na kabbara sallah, mintuna bakwai na ɗauka ina sallah sannan na idar. Azkar nayi ina gabda shafa addu'a ƙarar wayata ta sake karaɗe ɗakin, ban miƙe ba seda na kammala komai tareda ninke hijjabin da sallayar na mayar inda take ajiyewa, sannan na isa inda jakata ke ajiye na buɗe na fito da wayar a lokacin kiran ya jima da yankewa.Miss call goma nagani kwance cikin Screen ɗin ban kai ga buɗewa ba wani sabon kiran ya sake shigowa, se dai a wannan karon kiran daga ya Na'imah ne. Ɗagawa nayi tareda karawa a kunnena na ce,"Hello!"

Daga can ɓangarenta ina jin yanda ta sauke wata ɓoyayyiyar ajiyar zuciya sannan ta ce,"Bilkisu kina ina?"
"uhm Ya Na'imah!" na faɗa a kamar zan fashe da kuka.
"i said whare are you Bilqis" ta faɗa with seriousness.
"Hayin ɗan-mani" na firta a gajarce.
"kin gayama Yusuf za kije can?"
"no ban gaya mishi ba" nayi maganar ina sauke idanuna ƙasa tamkar ina gabanta."Amma kin san ubangiji ya na fishi da matar dake satar hanya idan ta fita unguwa ko?" cewar Yaya na'imah.
Shiru nayi bance komai ba saboda hawayen da ke kwaranya akan fuskata, jan hancin da nayi ne ya sa ta fahimci kuka nakeyi. gyara zama tayi akan kujerar da take zaune ta ce,"kuka kikeyi ko Bilqis?"

"a'a"

"hmmm ka da ki fara ɓoye gaskiyarki a bayan hawayenki Bilkisu. na san wannan matsalar ba za ta rasa nasaba da familyn Yusuf ba, na san akwai ciwo sosai idan dangin miji suka sako rayuwarka a gaba, amma idan kayi haƙuri da sannu komai zai wuce kamar ba'ayi ba. i know who you are Bilqis, and am very sure kina da haƙurin da za ki iya cinye wannan jarrabawan daya sameki!"

"matsalar familyn Yusuf ba shine matsalata ba a yanzu yaya Na'imah, Sai dai akwai ciwo sosai a zuciya idan wanda kake ƙauna ya cutar da yaddarka akansa!" nayi maganar hawayen fuskata suna ƙara tsananta zuba. Ka sa cemin komai tayi saboda yanda maganata ta ƙarshe ta huda mata zuciya. Cikin rashin fahimta ta ce,"what do u mean by this word?. How do you expect me to understand what is truly in your heart if you don't speak, Bilqis?" tayi maganar da wani irin emotion. Shiru nayi naƙi cewa komai don ba zan iya baiyana Mata abinda take san sani ba, na gwammace nayita dakon abin a Raina har kabarina. Jin naƙi cewa komai ya sa ta yi ƙasa da muryanta cikin sigan rarrashi ta ce,"na san akwai ciwo sosai amma idan kikayi haƙuri komai zai wuce ya zama labari. wasu lokutan sai munyi gwagwarmaya mai matiƙar wahala sannan muke cimma nasara, trust me Bilnqis in sha Allah komai zai wuce kaman bai taɓa faruwa ba kinji?"
Ɗaga mata kai nayi jin naƙi magana ya sa ta shiga rarrashina da kalamanta masu daɗi. Ina matiƙar son Ya Naimah sam ba ta da mahaɗi acikin zuciyata, ba ta kashe wayar ba har sai da ta tabbatar da nayi dariya sannan mukai sallama. Ina kokarin mayar da wayar cikin jaka Inno ta kirani na fita tsakar gida, na tarar ta zuba min Alala da manja da kuma yaji sosai. Zama nayi ina murmushi na ce,"Inno ba dan baki san da zuwana ba wllh sai ince gaya miki akayi ina hanya."
"saboda nayi Alalan gwangwani da manja?" ta faɗi haka ta na murmushi.

"Ae mana" na faɗa ina kai lomar farko bakina har wani lumshe idanu nakeyi saboda daɗi. Wayarta wadda ke gefena ce ta ɗauki ƙara, don haka na miƙa hannu na janyo wayar na miƙa mata. Ina ji ta ɗaga wayar tareda yin sallama. daga can ɓangaren ya amsa sallamar tareda cewa,"inno ki fara shiri in sha Allah nan da two weeks za ki koma sabon gidanki." ya yi maganar yana murmushi mai sauti.
Gyara zama Inno ta yi da wani kalan farin ciki ta ce,"naji daɗin wannan labarin sosai Abdulƙadir.amma zuciyata tafi buƙatar waccan maganar da na daɗe ina fama da kai akanta."

Shiru ya yi na ɗan lokaci still yana murmushi bai dena ba ya ce,"ki ƙara dagewa da addu'a in sha Allah komai ya kusa zuwa ƙarshe."

"Abdulƙadir har zuwa wani lokaci za ka ɗauka a haka saboda Allah? Ya kamata fa a manta baya a fuskanci gaba, idan aka miƙa dukkan lamura ga Allah Ubangiji zai ba da mafitar da zuciya ba ta taɓa tsammani ba." inno ta furta haka da damuwa sosai akan fuskarta.
"don Allah ki kwantar da hankalinki ki daina damun kanki akan matsalar da na jima da warwareta, ina kyauta zaton shagali biyu za ki haɗa a lokaci ɗaya." ya yi maganar yana gyara kwanciyarsa akan lallausar kujerar da ta ƙawata falon da haskenta.
"Alhamdulillahi naji daɗin wannan magnar sosai Abdulkadir. Ubangiji ya daɗa sutura ya ƙara buɗa maka. Allah yasa kuma abokiyar Arzuƙinka ce yarinyar"

"Amin ya Haiyyu ya Qaiyyum! Amma ba zaki tambayi ƴar wani gida bace yarinyar?"

"Ba buƙatar sai na tambayi nasabarta, saboda na san Abdulƙadir ba zai taɓa zaɓo ɗiyar da ba ta mutunci ba!" ta faɗi haka tana dariya me sauti.

"lallai sanya ranki a kaina me girmane. Ni Kuma In sha Allah ba zan ba ki kunya ba."
"ina fatan haka." cewar inno, sun jima suna hira wadda duk rabin hirar akan rayuwarsa da ta mutanan kasar Australia sukeyinta, sannan sukai sallama da juna. Har ze kashe ta ce,"ga Bilkisu ku gaisa." ta faɗa tana miƙamin wayar.

Karɓar wayar nayi ina jin wata irin kunyarsa na mamayar zuciyata, cikin sanyi murya na ce,"ya khadir ina yini?"

Ina jin yanda sautin murmushinsa ke ratsa kunuwana sannan ya ce,"ina gajiya pafah. ya kwana biyu." Yayi maganar cikin sautinsa mai zurfi da kauri wanda na Jima banji irinsa a tareda wani halitta bayansa ba. Nan take sai na samu kaina da rudewa na rasa abinda zance, kasala da rashin karsashi ne suka saukar mini na kasa firta abinda nake son firtawa. A fakaice na saci kallon gurin da Inno ke zaune, ganin sabgar gabanta kawai take yasa nayi kundumbala na hadiye lomar alalan dake bakina da kyar na ce."yaushe za ka dawo?" na samu kaina da jefa masa tambayar da ko a mafarki ban taba zaton zanyi masa ita ba.
Numfasawa ya yi kafin ya ce,"soon in sha Allah."

"Allah ya dawo da kai lafiya."
"Amin ya Allah." sannan mukai sallama da juna. Miƙa mata wayar nayi ta karɓa har lokacin ba ta daina murmushi ba, hakanan sai naji na tsargu.

hirar sabon gidan da za su koma muka fara da ita. tun ina ɗari-ɗari har na saki jikina, Sai biyar na yamma sannan na fara shirin tafiya gida, ɗaki na koma don ɗakko jakata da na bari a kan gado. A dedai lokacin wayata ta fara ƙara. Zaro wayar nayi ina maida kallona kan screen ɗin wayar don ganin wanda ke kirana. Yusuf ne, da kamar ba zan ɗauka ba amma dana tuna nasihar ya Naimah sai kawai na ɗaga amma banyi magana ba, ina ji ya sauke wata nannauyar ajiyar zuciya sannan ya ce," gani a ƙofar gidan ki fito mu tafi gida" bai jira jin amsar da zan bashi ba ya katse kiran.Takaicine ya kamani amma ba yanda na iya haka na fita daga ɗakin na samu inno na ce,"zan tafi gida Yusuf yana waje yana jirana."

Hannuna ta kama cikin taushin murya ta ce,"kiyi haƙuri ki ƙarfafi zuciyarki da imaninki Bilkisu. Ko da wasa kada kice za ki biye tijara da gorin da maman mijinki ke miki, da sannu komai ze wuce kamar bai taɓa faruwa ba. Indai kina da rabon Haihuwa a duniya zaki haihu don haka ki manta da batunsu ki dage da addu'a kinji ɗiyar albarka."

Ɗaga mata kai nayi alamar naji duk abinda ta ce, sannan mukai sallama da juna jiki a sanyaye na nufi ƙofar fita, dukda ban juyo na kalleta ba nasan kallona takeyi don ina jin tasirin idanunta a ilahirin jikina. Daga can nesa da gidan yayi parking don haka tunda na fito ya ƙura min ido yana kallona, ina ƙarasawa na buɗe murfin motar na shiga na zauna ba tareda nace dashi ƙala ba.Shiru ne ya ratsa na mintuna biyar sai kawai naji ya ranƙwafo ya rungumoni jikinsa., ina jin yanda yake sauke numfashi daki bayan daki tamkar jaririn dake neman agajin uwa. Har lokacin ban motsa ba ina jin yanda yake yawo da hannunsa a bayana yana ƙara ƙanƙameni cikin jikinsa.Tsikar jikina ce ta fara tashi a hankali na fara ƙoƙarin ƙwatar kaina daga kasalar da yake ƙoƙarin saukar min, cikin wata wahalalliyar murya wadda bata fita sosai na ce,"pls Yusuf don Allah ka bari Bana so!."
Tsayawa yayi cak ya kasa motsi saboda tsananin mamakin maganar dana firta. a hankali ya janye jikinsa daga jikina yana kallon fuskata cikin maɗaukakin mamaki ya ce," Yau ni kike turewa daga jikinki Ƙaunata?"

Kauda fuskata gefe nayi don ba zan iya jurar kallon tsakiyar idanunsa ba. Saboda tasirin da ƙwayar idonsa take dashi a gareni ya wuce gaban na iya kwatantawa, al'amarine da ubangijine kaɗai yasan girma da tasirin sa!
Ako wace irin alaƙa tsakanim mutum biyu soyayya kaɗai ba zata wadatar ba, dole akwai wata buƙata wadda ke ƙoƙarin samawa kanta gurbi a tsakanin muradan juna. Sedai a yau ban shirya karɓar tayin da yake aika min ta bayan fage ba, ko da hakan ze haifar da saɓani mai girma a tsakanin mu.
"A halin yanzu zuciyata ta na buƙatar hutu sosai, ba na jin zan iya ɗaukar nauyin lalurar da kake ƙoƙarin sauke min!" na firta hakan ba tareda na juya na kalleshi ba.Tsayawa ya yi ƙam tamkar gunki saboda yanda maganar dana firta ta girgiza shi. Mamaki ne ya baiyana ƙarara akan fuskarsa, Inaji ya ida janye jikinsa daga jikina tamkar wanda akai masa bushara da tashin hankali mai girma. Ni kaina sai da na girgiza a lokacin da nai realizing abinda bakina ya firta, sai dai dukda haka bana jin cewar na aikata ba dai-dai ba.

Jikinsa a sanyaye ya kunna motar muka fita daga cikin unguwar zuwa kan babban titi, sannan ya ɗauki hanyar da yake ganin zata fi masa sauƙin zuwa gidanmu dake Malali, yana jin yanda zuciyarsa ke harbawa sanadin dakatarwa da nayiwa tayinsa cikin halin ko in kula, wanda hakan bata taɓa faruwa a tsakanin mu ba tsahon shekara biyar da Auren mu.......