Chapter: 3
by @zmchubado
*RA'AYIN ZUCI....*
#the accidental marriage#
Tun daga wannan maganar ban ƙara firta komai ba. haka tafiyar ta kasance a tsakaninmu tamkar masu ciwon baki. wanda hakan ba ƙaramin daɗi yaymin a raina ba don ban shirya yin magana mai tsaho dashi ba, har lokacin zuciyata a hasale take dashi. na kasa manta abinda kunnuwana sukai katarin ji yana furtawa ga abokinsa Doctor Umar, har yanzu ban huce da jin zafin kaifafan kalaman da suka ratso ta tsakanin laɓɓansa ba wayanda naji yana furtawa ga likitan dake karanta masa halinda rayuwata ke ciki ba ɗazu. wannan yasa na maida hankalina ga window ɗin motar ina kallon yanda mutane keta hada-hadarsu.
komawa nayi na jigina bayana a jikin kujerar da nake zaune akai tareda lumshe idanuna, a haka ya juya kan motar ya shiga cikin layin mu har lokacin ban motsa ba.
Horn yayi a bakin get kimanin wucewar mintuna uku, sannan ya tsayar da motar banyi motsin kirki ba balle in samu ƙarfin gwiwar fita daga motar. Inaji ya buɗe motar ya fita ba tareda yace dani ƙala ba, nima banyi gigin dakatar dashi ba don banga dalilina nayin hakan ba.
Murɗe kujerar motar nayi ta yanda zanji daɗin jingina kamar yanda nake buƙata, na jima ina tufka da warwara a ƙalla sai da na shafe mintuna shabiyar sannan na buɗe motar na fita. Cikin rashin guzari nake tafiya tamkar wadda na shekara ina jinya, komai na rayuwata yanzu baya min daɗi kamar yanda na baiyana a baya. A haka na isa jikin ƙofar falon zuciyata cike taf da tarin fargabar abinda zan tarar, tura ƙofar nayi daga can ƙasan maƙoshina nayi sallama. Abin takaici yanda nabar falon na tafi Asibiti ba haka na dawo na sameshi ba, kamar zan kurma ihu haka na dinga bin pillows ɗin da aka baza a tsakar falon da kallo.
ajiyar zuciya na sauke mai zurfin sosai ina jin yanda takaicin abin ke ƙara mamayata. Daga can ƙasan ruhina na ce,"ya ubangiji ka ƙaramin haƙuri akan duk abinda zan gani na ɓacin rai a cikin gidanan, sannan ka nuna min ranar da zanji daɗin zama a ɗakin mijina kamar yanda sauran mata sukeji a ɗakunansu." nayi adɗu'ar cikin gajeran sautin da babu me iya jina.
Takun takalman da naji sautinsu na fitowa daga hanyar kicin ɗina ce, tasa na juya da hanzari ina kallon Direction ɗin gurin. bisa ga mamakina Faridah Attahiru ce hannunta ɗauke da soyayyen ƙwai cikin faranti, kamar yanda nai kasaƙe ina kallonta itama ido ta zuba min tana kallona. Kimanin gushewar mintuna uku sannan na sauke idanuna ƙasa don bansan abinda ya kamata ince da ita ba.
Ɗan gajeran murmushi ta saki wanda sautinsa ya kutsa cikin kunnena sannan ta ce,"kin daɗe sosai a inda kikaje Bilkisu. Nayi zaton a can inda kika kai ziyarar zaki kwana."ta firta hakan tana ƙara tsareni da manyan idanunta, waƴanda babu komai a cikinsu face tsantsar fitsara da rashin kunya.
Kasa amsa mata nayi don bansan abinda ya kamata ince mata ba, a nitse na lumshe idanuna sannan na ƙara buɗesu tar akanta na ce,"idan zaki soya ƙwai don Allah ki dena soyawa a nan. Ƙamshinsa yana ɗaga min hankali sosai." nayi maganar a sanyaye tamkar ba daga tsakanin laɓɓana ta ratso ta fito ba.
Tsareni tayi da ido cikin tsananin mamakin jin abinda na firta, amma da yake ƴar duniyace sai ta gaggauta shanye mamakinta ta ce,"masu baiwar ɗuwawun haihuwa su ya kamata su firta haka a martaba maganarsu, ba juya irinki ba wadda baki iya komai ba sai dai kici kiyi kashi, ina ganin zaifi miki alkhairi ki tanadi hujjar da zaki gamsar da Hajiya akan fitar da kikayi." ta firta hakan tana jifana da kallon ƙasƙanci, wanda yasa naji a zuciyata na muzanta ainun.
Zuciyata ce tai wata irin motsawa wadda tasa allon ƙirjina ya fara barazanar darewa gida biyu, cikin wani irin yanayi mai narka zuciya na sauke mata rinannun idanuna cikin nata, cikin yanayi irin na zallar kaɗuwa. duk yanda naso na daure a wannan taƙin juriyata sai da ta raunata ainun, sai kawai na samu kaina da yin murmushi wanda ya taimaka wajen baiyana halinda zuciyata ke ciki. Kasa cewa komai nayi na daure na danne zuciyata gudun kar in rusa ribar haƙurina ta hanyar biyewa Shirman Faridah Attahiru!
Haka na raba ta jikin kujerar data raba tsakanina da ita na wuce kicin, don in kaucewa ganin fuskarta wadda a yau ta rikiɗe ta zame min baƙa sanadin gorin haihuwar da tayi min. tsintsiya na ɗakko da abin kwashe shara na ajiye mayafina da jakata na fara ƙoƙarin gyara falon. Duk don in hana zuciyata damar da zata tsinduma a cikin halwar tunanin da ka iya zama ajalina, mintuna goma ne suka ɗaukeni na kammala gyaran falon, sannan na fita da sharar na zuba a inda aka tanada don hakan.
turaren wuta na kunna a electric burner. cikin gajeran lokaci falon ya biɗe da ni'imtaccen ƙamshi tamkar bashi ba, sai da na tabbatar falon ya dawo hankalinsa sannan na kwashi jakata da mayafina na wuce ɗaki. Har lokacin ƙirjina bai dena harbawa ba, wani irin ƙunci da zafine ke huda zuciyata tamkar ana rura min wuta haka nakeji. zama nayi a bakin gado ina tunanin yanda zanci gaba da rayuwa a tsakanin mutanen dake ƙuntata rayuwata ta hanyar yimin gori, haƙiƙa akwai ciwo idan akai maka gori akan abinda ba kaine zaka baiwa kanka ba, "mai yasa Faridah Attahiru ke ƙuntata min ta hanyar gasa min duk maganar data fito daga bakinta?" na firta hakan a cikin raina, amma dana tuna cewa Hajiyama yimin take sena ƙara jin cewa na karaya.
Mayafin Abayar jikina na zame ya koma kan kafaɗuna, sannan na mike na fara takawa a hankali cikin rashin guzari ina kai komo. Ban sameshi a ɗakin ba sai ƙarar ruwan da nakeji alamar yana toilet, zama nayi a ƙasan kafet ɗin daya mamaye ɗakin nayi shiru ina tunanin makomar rayuwata. Sai kawai na saka fuskata a tsakanin ƙafafuna na fashe da wani irin kuka mai tsuma zuciya da ruhi, kuka nakeyi sosai har jikina yana rawa.
A haka Ya fito daga toilet ɗin cikin nutsuwa yana gyara zaman agogon fatar dake ɗaure a tsintsiyar hannunsa, tsayawa yayi cak a lokacin da kunnuwansa suka tsinkayo masa sautin kukana, wanda ke fitowa kai tsaye daga ƙasan zuciyata ba tareda wani shamaki ba. Hakanan sai yaji jikinsa yay bala'in sanyi don sarai ya san ba'a kyauta min, "to amma ya zeyi ya canza wannan murɗaɗɗiyar tifkar da aka jima ana tifkawa?" ya aiyana hakan a ƙarƙashin zuciyarsa wadda yake jin tana harbawa. Cikin ragowar guzarin da yay masa saura. A hankali yake takowa har ya iso inda nake zaune, risinawa yayi tareda zama a gefena ya jani jikinsa ya rungume. Yana jin yanda nake rera kukan tamkar wadda ke shirin shidewa. Al'amarin daya ƙara raunanata zuciyarsa kenan ya ƙara ƙanƙameni cikin ruƙonsa, tamkar zai maidani ɗaya daga cikin ƙasusuwan da ubangiji ya shirya a tsakanin ƙirjinsa!
kana kallon irin riƙon da Yusuf yay min zaka fahimci so yake ya rarrasheni amma gabaɗaya he don't know where to start. bayana kawai ya ke shafawa tamkar wanda aka saka gam aka manne masa baki, da ƙyar ya iya tattaro kalmar dake maƙale a tsakanin maƙogaronsa ya ce,"kiyi haƙuri Bilkisu!"
Wannan Kalmar hakurin da bakinsa ya firta yasa naji tamkar ya watsamin ruwan tafasashiyar dalma a fatar jikina, "hmmm lallai wasu mazan Sam basu da kunya ko miskala zarratan."
Ƙara saurin kukan nayi cikinta wata marainiyar murya wadda ke baiyana raunin zuciyata muraran,nan take zuciyata ta dunƙule a guri guda tamkar saqaqon da aka sarrafa da danyen qarfe, so nake nayi magana Amma na kasa sabida nauyin da bakina yayi. kafin nayi wani yunƙuri naji an turo ƙofar ɗakin ba tareda yin sallama ba, dukda cewa ban ɗaga kai na kalli bakin ƙofarba, jikina ya riga ya gama sanar dani wadda ke tsaye a gurin.
Da ga bakin ƙofar take aika masa da wani irin kallon Wanda tasirinsa ya nemi hautsina ƴaƴan hanjinsa, ba tareda ta janye idanunta daga kansa ba ta ce,"sannu Ayu uban bibiko. idan ka gama nacin rungumar sai ku fito ku sameni Kaida ƙadandoniyar taka, wadda ta kanainayeka a ɗaki da jaraba kamar akanta aka fara mu'amilar Aure." Hajiya ta firta hakan tana aika masa da wata danƙareriyar harara, sannan ta juya ta bar gurin fuskarta a ɗaure babu alamun wasa ko kaɗan.
Zame jikina nayi daga ruƙon da yay min ina ƙara jin zafin ƙiyayyar da nai katari da ita kwance a tsakiyar idanun Hajiya, ruwan ƙwallar dake ɓoye cikin ƙwayar idanuna ne ya keto ta tsakanin fatar ya zubo bisa kuncina. Cikin guzarin da yay min saura na kai hannu na sharcesu da bayan hannuna, sannan na miƙe ina ƙoƙarin saita nutsuwata wadda ke neman ƙwacewa daga gareni.
Hmmm mutane da yawa kanyi raddi da dogon sharhi akan Auren soyayyah, har kaji wasu matan suna kauɗi da iyayin cewar,"jin daɗin aure shine mutum ya auri wanda zuciyarsa keso. Yes da gaske auren soyayya ni'imane idan kayi Dace. amma a gareni bashi da maraba da auren ƙaddara, wanda gwagwarmayar rayuwa da zanan ƙaddara suka rataya min shi, a ƙarshe gashi ya zame min kara da kiyashi ɗaukar mara sani!
Abin takaici har yau zuciyata ta kasa goge son da take masa daga cikinta, dukda cewa bana samun farin cikin ɗari bisa ɗari daga gareshi, babbar tawa jarrabawar da ubangiji yay min ita ce soyayyar Yusuf Attahiru. Mutumin da ya samu nasarar mamaye duk wani lungu da saƙo da hanyoyin jinin jikina, a cikin kwanaki bakwai kacal ya sauya alƙibilar rayuwata sannan ya kafa gwamnatinsa cikin ƙanƙanin lokaci a zuciyata.
A nawa tunanin Idan har zan iyay masa wannan soyayyar, kamata yayi ya zama mai tsaya min cikin duk wasu lamuran rayuwata no matter what.
Shirune ya biyo bayan fitarta kimanin mintuna uku ƙwarara, sannan ya yunƙura ya mike still idanunsa na kaina ya ce,"kiyi haƙuri bilkisu in sha Allah komai zeyi dai-dai." ya firta hakan yana me janye idanunsa daga kaina.
Cikin rashin guzari yake ɗaga sawun ƙafarsa tamkar wanda ke counting steps ɗinshi, a haka ya ɓace min da gani ya barni ina sharar ƙwallar data gaza tsayawa daga idanuna. Da ƙyar na iya tattaro guzarin da ya jima da yin ƙaura daga gareni na yunƙura na miƙe, tareda wawurar mayafin abayar dake jikina nabi bayansa cikin rashin sanin dalilin kiran.
A hankali nake tafiya harna isa falon, a zaune na sameshi a ƙasan kafet kansa a ƙasa yana sauraren Hajiya tamkar mai neman gafara daga gareta. Haka na ƙarasa na zauna daga can gefe ba tareda na bari mun haɗa idanu da ita ba, kallo ɗaya tayi min ta janye idanunta tareda gyara zama akan kujerar da take kai ta ce,"Yusuf!"
Ta kira sunansa da wani irin amo a cikin sautinta wanda ya haifar masa da faɗuwar gaba, a nitse ya ɗaga kansa ya kalleta sannan ya sake yin ƙasa da kansa ya ce,"na'am Hajiya."
"so nake ka ƙara Aure tunda ita wannan ta kasa haihuwa." cewar Hajiya cikin maɗaukakin sauti wanda ke cike da umarni.
Gabana ne yay wata irin faɗuwa wadda tasa nayi saurin dafe ƙirjina, Amma sai na daure na karfafa kaina ina me tsumayin Jin amsar da zata fito daga bakinsa, Jin amsar sa ita kadai ce zata sharemin tantama daga zargin da zuciyata ke masa tun bayan fitowata daga Asibitin su Doctor Umar.
Sosai na tsaida idanuna akansa numfashina yana fita da kyar, zuciyata na tsananta bugu tamkar zata dako tsalle ta fito waje. shi kansa a wannan gaɓar ya razana da ganin yanayina, amma da yake sawun giwa ya take na raƙumi dole tasa yay ƙasa da kansa, don ba zai iya jurar kallon tsakiyar idanuna a wannan lokaci ba. Fitina ce fal a tsakiyar idona irin wadda bai taba cin Karo da ita a tareda ni ba. Wannan yasa ya sha jinin jikinsa tamkar me Shirin nitsewa kasa saboda kunya....
"na riga na yanke hukuncin zaka auri Aisha yar ƙanin mahaifinka, mun riga mun gama zartar da hukunci tareda Babanta. Umarni nake baka ba shawara ba, ruwanka kayi min biyayya ko kuma ka bijirewa umarnina." Hajiya ta ƙare maganar tana miƙewa cikin nutsuwa tabar mana falon ya rage daga ni sai shi.
Har lokacin ƙirjina bai dena dokawa ba, yunƙurawa nayi na miƙe ba tareda nace dashi ƙala ba na koma ɗaki. Ina shiga na fashe da wani sabon kukan da ya ninka wanda nayi da farko, a haka ya shigo ya sameni ina wannan aikin tamkar wadda akai min bushara da mutuwar Baffana.
Cikin rashin guzari ya shigo ɗakin, ganina da yay a wannan yanayi yasa yaji jikinsa yay bala'in sanyi. Ya jima a tsaye yana kallon yanda nake kuka kamar zan haɗiye raina, cikin sauran guzarin da ya rage masa ya ɗaga ƙafafunsa waƴanda suka jima da sagewa ya nufeni. Cikin nutsuwa yasa hannu ya jani jikinsa ya rungumeni ƙam, yana jin yanda zuciyata ke bugawa daƙarfi da ƙarfi.
Cikin wata tattausar murya wadda ban taɓa jin sautinta a tareda shi ba ya ce,"kiyi haƙuri Bilkisu in sha Allah komai zaiyi dai-dai"
Janye jikina daga ruƙon da yay min nayi ina kallonsa da idanuna waƴanda suka jima da jiƙewa da ruwan hawaye na ce," when? Yaushe koman zai yi dai-dai din?" na firta muryata na karyewa
"ki yarda dani na miki alƙawari komai zai yi dai-dai."
Raina ne yaƴ masifar ɓaci for the first time tunda mukai Aure dashi, miƙewa nayi tsaye don na fahimci Raina min hankali kawai yake kokarin yi na ce "kada ka aikata kuskuren da zai haifar da saɓani mai girma a tsakaninmu Yusuf. Idan ka aikata hakan tamkar kana nufin rabuwarmu da juna na har abada ne wllh." na firta hakan cikin mawuyacin hali. zuciyata na tsananta bugu tamkar zata tsaga ƙirjina ta fito waje
Tsareni yay da idanu yana karantar yanayina, sannan yay murmushi mai sauti ya ce,"wata saɗaukarwar ba sai da alaƙar jini kawai akeyinta ba Bilkisu. idan ta kama dole sai na Auri Aisha Sulaiman ki sani bani da wani zaɓi wanda ya wuce cika Umarnin mahaifiyata." ya firta hakan yana wadata fuskarsa da ƙayataccen murmushi, wanda ya taimaka wajen binne ainihin halinda zuciyarsa take ciki.
Daskarewa nayi a tsaye tamkar mutum-mutumin da aka sassaƙa da ɗanyen itace, tsoro ne ya baiyana ƙarara akan fuskata wanda ya rikiɗe ya haifar min da rawar jiki. Daƙyar na iya haɗo kalmomin da suka sarƙafe harshena na ce,"wannan maganar taka tasa naji a raina ina zarginka Yusuf. Ga dukkan alamu Aurenka da Aisha Sulaiman shiryayen al'amarine, Wanda aka Jima anai masa tanadi." nayi maganar ina murmushi tamkar zararriya.
sannan naci gaba da cewa"kana da ikon aurenta kamar yanda mahaifiyarka ta umarceka, amma fa inaso ka sani na rantse da zatin Allah sai dai ka zauna da ita bayan ka yanke igiyar auren dake tsakanina da Kai!." nayi maganar ina kai hannu ga jakata wadda na ajiye a saman gado tun shigowata ɗakin na farko.
Cikin ɓacin rai da wutar kishi na nufi ƙofar fita daga ɗakin cikin fushin da ban taɓa sanin ina da irinsa ba. Da wani irin sauri yasa hannu ya fuzgoni na faɗa jikinsa, sai dai har lokacin ya kasa sarrafani, ƙanƙameni yay ƙam tamkar zai tsaga ƙirjinsa ya turani ciki. Dukda fuskarsa bata nuna halin da yake ciki ba, zuciyarsa ta jima da baiyana asiri dake boye a tsakanin kirjinsa, ta hanyar bugawar da yake da ƙarfin gaske.
Cikin rikitaccen yanayi ya kai fuskarsa dab dani yana huci ya ce,"Aurena dake na har abadane banga wanda ya isa kawo ƙarshensa ba!" yayi maganar cikin fisata da bacin Rai
Fizge jikina nayi da karfin tsiya sannan na dubeshi cikin yanayin da bai taba ganina a cikinsa ba na ce," ta ya akai aurena da kai ya zama na har abada bayan ba daga sama aka daurashi ba? Kai wllh ko daga sama aka daura aurena da kai yau seka sakeni don bazan hada inuwa daya da Aisha Sulaiman ba!" nayi maganar cikin fisatar da ta zarce tunaninsa
"what do you mean by this statement Bilkisu?"
"Abinda nake nufi a fili yake ban boye maka ba Yusuf Attahiru."
Kuramin idanu yayi cikin tsananin kaduwar Jin na kirashi da full name dinsa, wanda ban taba yin hakan a gabansa yaji ba. takowa yayi har gaba na, sannan ya rankwafo sosai Yana kallon tsakiyar idona tareda Kai hannunsa Saman kaina ya dafa ya ce,"I'm sure something is botherng you in your head, shiyasa kike magana irin haka."
ture hannunsa daga kaina nayi, cikin zafin nama ya fuzgoni na fada jikinsa, kafin inyi wani yunkuri naji saukar laɓɓansa a saman nawa. daskarewa nayi don koda wasa ban taba kawoma Raina irin wannan abin zai samu muhali a tsakanin mu nan kusa ba, wata irin sumbata yake min mai wahalar siffantawa, cikin gajeran lokaci ya saukar min da gagarumar kasala wadda tayi nasarar sauyawa tunanina alƙibila. Seda na bari ya shagala a duniyar da yake kokarin jefa mu nasa karfi na tureshi daga jikina.
Kafin nayi wani yunkuri ya sake dankoni da da karfin gaske har sai da qashin haqarqarina yayi qara.
Da wannan damar yayi amfani ya samu abinda yake so ba tareda munkai ruwa rana da juna ba, sai dai har cikin zuciyata na ƙudurta cewar bazan haɗa inuwa ɗaya da Aisha Sulaiman ba. Dole a cikin biyu za'ai ɗaya don bazan taba yin saken da wankin hula zai kaini ga dare ba!
Bai sarara min ba sai da ya samu biyan buƙatar kansa sannan ya dai-daita nutsuwarsa har lokacin yana manne dani ya ce,"kada ki ƙara firta kalmar rabuwa a gaban idanuna bilkisu. muddin kika ƙara ambata kalmar saki zan ƙullaceki na iya tsahon rayuwata!"
Banza nayi masa don banda amsar da Zan iya bashi sabida haushinsa da ya gama cika min zuciya. Gyara rukon da yay min yayi sannan yaci gaba da cewa," taya kike zaton yusuf zai iya rayuwa ba tareda Bilkisu Ibrahim Saminaka a cikin duniyarsa ba?" yayi maganar yana ƙokarin jefa ƙwayar idanunsa cikin tawa.
Ɗaure fuska nayi don har lokacin ban sauka daga dokin ɓacin ran dana hau ba, babban burina shine ya sakeni in nisanta kaina dashi. Don wllh gabaɗayansa haushinsa nakeji kamar in rufeshi da duka haka zuciyata ke aiyana min, janye jikina nayi daga ruƙon da yay min, cikin wata daƙilalliyar murya na ce,"banajin kasancewata a duniyarka yana da wani mahimmanci, kai da za'a danƙarowa sabuwar amarya wadda keda ɗuwawun haihuwa ai bai kamata kayi marmarin zama da juya kamar Bilkisu ba!" nayi maganar ina miƙewa daga saman gadon na faɗa toilet har lokacin zuciyata bata dena tafasa ba.
Idanunsa na kaina harna bace masa da gani ya kasa kyakkyawan motsi, sabida yanda kalamaina suka shigeshi, nan take ya Kara Shan jinin jikinsa akan abinda ya ke Shirin aikatawa da sunan umarnin uwa.
Ina shiga toilet ɗin na maida ƙofar na rufe tareda jingina bayana jikin ƙofar na fashe da kuka mara sauti. A wannan yanayin da nake ciki ubangiji ne kaɗai yasan yaƙin da ake gwabzawa a tsakiyar zuciyata, banyi zaton haka kishi yake da raɗaɗi a rai ba sai yau da abin ya faɗo kaina. Tambaya ɗaya zuciyata ke aika min "taya zan iya sharing Yusuf da wata ɗiya mace a duniya?"
Zubewa nayi akan ƙafafuna na fashe da wani marayan kuka wanda ke barazanar dagargaza zuciyata in to pieces. wannan shi ake kira gobara daga kogi maganinta sai ikon Allah, to in banda abin hajiya mai yasa bazata nema masa wata macen a gari ya aura ba sai Aisha Sulaiman? Yarinyar da kaf duniya babu wanda ta raina sama dani.
Duhu ne ya mamaye ganina ba tareda na ankara ba, in banda a zaune nake na tabbata idan jiri ya ɗebeni seya watsar dani a ƙasa. Ina nan durƙushe naji alamar fitarsa daga ɗakin cikin zafin nama na buɗe ƙofar toilet ɗin na fito, sabida ɓacin rai ko gabana bana iya gani sosai naje na dannawa ƙofar ɗakin key. still idanuna basu dena ɓarin ruwan hawaye ba, toilet ɗin na koma na sakarwa kaina ruwa har lokacin kuka nake, a haka na tsarkake jikina na ɗauro alwala na fito. A haka nayi sallar magariba ba tareda na san abinda nake fada a cikin sallar ba, ina nan zaune aka fara kiraye-kirayen sallar isha'i, haka na miƙe jiki baɓu ƙwari na kabbara.
Bayan na idar miƙewa nayi tareda ninke sallayar na nufi gado ko hijjabin ban cire ba, ina jinsa ya dawo yana buga min ƙofa nayi banza dashi. Haka ya ƙaraci bugun ƙofar ya haƙura ya koma falo ya kwanta, bacci akace ɓarawo a wannan daren duk iya satarsa kasa hilata ta yayi. Yanda naga rana haka naga dare.
Washe gari da safe sai wajen ƙarfe takwas sannan bacci ya samu nasarar ɗaukata still ban buɗe ƙofarba, a yanda zuciyata ke tafasa akan maganar ƙarin auren da hajiya ta umarci yusuf ji nake kamar in cinnawa gidan wuta kowama ya huta. "Ashe dama haka mata keji a zukatansu idan akai musu busharar gaiyato musu kishiya a gidan aurensu?" Na aiyana hakan a cikin raina.
Wasu kuraman hawayene suka fara kwaranya a kumatuna, ina tsaka da zancen zuci aka fara kwankwasa min kofa.
Biris nayi kamar banji bugun kofar ba naci gaba da sharar hawayena, a tunanina Yusuf ya jima da fita office wannan yasa naji haushinsa da kishinsa sun kara kamani, wato don renin hankali ya gama biyan bukatarsa dani shine yanzu zai kara aure su maidani bora.
Dafe kaina nayi wanda ke kokarin sarawa sabida tashin hankalin da yay min babakere a zuciya, Lumshe zagayayyun idanuna nayi ina tunanin majinginar da Zan jingina da ita naji dadi, ya Naimah ce ta fado min a rai Amma cikin sauri na kauda tunanin sanar da ita halin da nake ciki. hakanan sai naji bazan iya gaya mata halinda nake ciki ba, a tsarin rayuwata kai qara baya daya daga cikin dabi'una.
Ajiyar zuciya na suke mai nauyi ina jin yanda zuciyata ke takurewa a guri guda tamkar dunkulen da aka sarrafa da garin rogo.
"Wa Zan baiyanawa damuwata ya fahimci halinda nake ciki ba tareda ya tauye min hakki ba?" nayiwa kaina wannan tambayar daga can kasan zuciyata
"Ya ilahi" na firta cikin wani kassararren sauti Mai tsuma zuciya da bargon jiki. A dai-dai lokacin aka Kara buga kofar dakin tamkar Mai bugawar zai karya kofar, a fusace na mike na nufi kofar zuciyata na tafasa, a zatona Faridah ce Amma ina bude kofar idanuna sukaiwa kansu ma sauki cikin idon Hajiya.
Nan take nayi kasa da kaina na kasa cewa komai tamkar wadda aka sanya gam aka likewa Baki. har lokacin bata janye idanunta daga kaina ba , don ina jin tasirinsu a gabadaya ilahirin jikina, gyara tsaiwa tayi sannan tayi murmushi mai zurfi ta ce,"wllhi baki daukeni matsayin mahaifiyarki ba Bilkisu, na tabbata inda uwarki ce ba zaki taba yin gangancin barinta da yunwa kamar yanda ki kai min yau ba!" Hajiya ta fadi maganar cikin son ta cusa min haushi.
Yes, she succeeded in annoying me as she wanted, Amma kuma Se nayi shiru bance komai ba, cikin ikon Allah da hikimarsa nayi nasarar boye fishina in front of her, cikin sanyin murya wadda bata fita sosai na ce"don Allah kiyi hakuri bacci ne ya kwasheni shiyasa ban fito na dora ba. Amma yanzu Zan hada miki" nayi maganar ina kokarin fita daga dakin jikina a mace.
Bayan rigata ta riko da karfi kamar zata jefar Dani ta ce,"nafi karfin rashin kunyarki da duk wani tashen balagarki. Idan ma akan maganar auren Yusuf ne yasa kika tsiro da wannan tsiyar da kika sha a nonon uwarki. to wllh sai dai ki mutu, Amma aure kam babu fashi sai anyi shi saboda yusuf ba zai kare da auren juya ba"
Tunda ta fara magana zuciyata ya karye hawaye masu zafi suka Fara kwaranya a saman kumatuna, sosai naji ciwon kalamanta Amma ko giyar wake nasha nasan ba Zan iyay mata martani ko raddi akansu ba. duk da cewa banida daraja a idanunta I have to respect her because I am marrying her son, ko zata zagi iyayena so dubu a gaban idanuna ba zan iya daga Kai na kalleta ba.
Tsaki taja mai Kara sannan ta juya ta barni a tsaye ina kukan bakin cikin data kinsan min, duk da haka banda wani zabi haka na shiga kicin na hada musu breakfast sannan na dauka na Kai musu bangarensu. babu kowa a falon sai Faridah Attahiru wadda ke zaune a kan kujera ta Dora kafa daya kan daya, sallama nayi ba tareda na kalli inda take ba na wuce inda na saba ajiye musu abinci na dire na fice ba tareda na bata damar kallon fuskata ba.
A wannan rana haka nai wunin baqin ciki da bacin Rai Wanda ban san ranar gushewarsa ba, a haka Yusuf ya dawo daga office ya sameni a rikice kamar bani ba, sam bana iya jurar tashin hankali yanzu zakuga na fita daga haiyacina. Ina kallonsa ya shigo dakin ya ajiye briefcase dinsa a inda ya Saba ajiyewa, sannan ya fara kokarin sassauta necktie din dake daure a wuyansa.
Kokarin fita ya farayi still ban motsa daga inda nake zaune ba, don na kudirtawa kaina cewar sena nuna mai ni jinin Ibrahim Saminaka ce. Tunda ya nuna min halin ko in kula wllh sai na raunata tasa zuciyar kamar yanda yayi min, tunda haka ya zaba from today we will start the game, and we will see who will fall
Chubado 🥰